Sashe 31
Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kutumar uba ni za'ayi wa muna funcin ake neman a shiga tsakani na da Alh wlh baxe yiyu ba ,wato yanzu shima ya zama muna fuki ko?
Hajiya Laura da ke kan dadduma tana lazumi ta ɗago ta dubeta ,kafin da sauri ta shafa addu'ar dan ganin Saudah zata fita cikin fushi ,har ta kai baƙin ƙofa ta janyo ta ,rai a ɓace Sauda take kallonta " fushi ba naki bane Saudah ai duk wanda xe nunawa namiji irin wannan soyayyar da kike nunawa ta fo ƙarshen sakayyar da ze yi masa kenan ,kibar mutumin nan da kidahumar matarsa mana ,me kike nema gunsa wanda bakya samu ni banga dalilin ɓata lokaci akan namiji ba ,Kinga idan ma wani abun kike so ,ba gani ba zan yi miki abinda na tabbatar baze iya ba saboda duk da ban ganshi ba nasan dai i zuwa yanzu manyanta ya kamashi yaushe ne ze moru, Kinga zo nan dan Allah" ta ƙara sa faɗa tana turawa Saudah ƙir.
Bawai dan bata da bukatar hakan ba sedai bataji zata barwa Ammi mijinta ,duk da yanayin ta ya ɗan sauya ,cikin kasala ta raba jikin su tace " ina zuwa bari naje naji da wacce yazo kuma " bata tsaya jin ta bakin Hajia Laura ba ta fice daga ɗakin ,da harara ta takata tanayin kwafa ,a fili ta furta " se na tabbatar da na lalata komai da kike taƙama dashi Saudah".
Lokacin da ta shiga ɗakin Abba ,a gishin giɗe ta same shi kamar me bacci daga ƙasa kuma Ammi tayi kneeling tanayi masa tausa a ƙafafun sa ,bata san lokacin da taja dogon tsaki ba " an tsufa ba'a san an tsufa ba ,abun kunya wai mutum harda jikan shi amma yayi kwance mace nayi masa tausa wannan ai son a ɓatawa yara tarbiyyar su ne ,idan mace tasan jarabar tsufa na damunta ai da fita tayi tasamu yaro ta aura dan shine ze iya ,kar aje watarana a jajibo mana abun kunya"
Wannan karon kam Ammi taji bazata iya daurewa ba dan ta kula kauda idon da takeyiwa Saudah ne kesa tana tunanin ko tsoron ta takeyi ,saboda haka ta juyo da kyau ta kare mata kallo se kuma ta fashe da dariya ,wanda hakan ya saka Saudah tsarguwa " haba Saudah waya faɗa miki ana tsufa da soyayya ne ,sedai idan mutum be samu ba kidena damuwa da tsafan mijina danni a Idona shar yake kamar saurayi ɗan 25 danni se nake ganin ma kamar karfin sa daɗa ƙaruwa yake ko yaushe ,amma nayi mamakin da ke baki fahimci haka ba ko dai baya miki abinda yake min ne,kuma kidena damuwa da yara ,bazasu taɓa shigowa nan ba matuƙar sun san uwarsu na ciki ,dan tarbiyyar da na basu kenan ,saboda haka zaki iya zama idan kin gadama dan naga kamar yau dai da kishin tsoho kika tashi "
Ƙasa kai Saudah tayi tana kallon Ammi tunani takeyi" yaushe bakin matar nan ya buɗe da har zata fara maidamin magana irin wannan ,nice zata faɗa wa Karfin Alh karuwa yakeyi ,to ya akayi ma tasan cewar baya kwanciya da ita? Sedai idan shine ya faɗa mata "wata zuciyarta ta bata amsa ,cikin hargagi tace " Alh kanajin abinda wannan macijiyar matar taka ke faɗa min amma baka hanata ba ko wlh idan bata dena shiga sabgana ba zan shuka mata rashin mutunci ,yaushe kan mage ya waye da har ta san daɗin miji mtswwww ai idan ma kana da wani karfi nice nan Yakamata na faɗa ba ita ba " kafin Abba yayi magana ,Ammi ta tareta da faɗin " Saudah kina lissafi daidai kuwa ? Zainabu ce fa a gabanki kike zancen kece kikafita sanin mijinta haba dai nida na wanki abuna na fashe shi da kaina ,ai ina tunanin duk wacce zata faɗi wani abu akan sa to a bayana take dan nice na mori ƙuruciyarsa da kyau duk wata soyayya da kikaga ya nuna miki to nice na ɗorasa akan ta ,dan miji sirrin uwar gidan sa ne"
Rasa abun cewa Sauda tayi dan haka ta cewa Alh " wani muna furcin aka ƙulla da har zaka dawo garin nan batare da ka sanar dani ba kuma saboda rashin a dalci ka sauka anan ,ai a wurina yakamata ka sauka ko ?".
Murmushi Abba yayi saboda ya fahimci yau Ammi ta kashe bakin Sauda ,kafin yace " amma dai kya bari mugaisa kafin kifara wannan ƙorafin ko? " Ai baka nemi mu gaisa ba Alh dan yanzu sam baka a hayyacin ka an juye tunanin ka se yadda akayi da kai " Saudah" ya kira sunan ta da ɗan karfi "banason fitinan nan naki ,tunda na tafi kin ɗaga waya kin ji ya na sauka bare da na dawo inzo wurinki ke sam baki damu da damuwar kowa ba se naki ,meyasa ni banyi miki ƙorafi akan duk wannan ba se ke da kika fini sanin ciwon kanki ko ,to ban kiraki saboda tashin hankali ba ,ki natsu magana xamuyi
" Kunsani natafi ɗakin garine saboda na sanar da dangi bikin da za'ayi nan da kwana 12 idan Allah ya kaimu ,saboda haka na dawo shine nakeso naji menene shirye shiryen ku , ma'ana me kuke bukata me kuka tsara a bikin?
tsaki Saudah ta ja tana faɗin " saboda wannan ne ka kirani ina bacci na dama ? Me kake tunanin zan tsara bayan bada yata da kayi ga mutumin da besan mutunci na ba ,ni dai ina guje maka ne dan nasan baka shawar haɗa su akayi dan ayi amfani da ƴarka a kwashe dukiyar ka " ɗaga mata hannu yayi " ya isa haka bawannan ne dalilin kiran ki ba me kike buƙata na bikin kayan ɗaki dai babu matsala dan nasa anyi order tun tuni ,da ita da Rumaisa Kinga da ta samu miji itama bikin kawai za'ayi se kayan kitchen ne wannan ke zaki fi sanin wanda ya dace saboda haka kiyi lissafin ko nawa za'a kashe ki faɗa min zan bada kuɗin "
Jiyowa yayi wurin Ammi yace " se ke uwar Ango kece zaki haɗa lefe kinsani saboda haka nayi muku biza keda Bilikisu zuwa jibi zaku tafi se ku haɗo lefen ko ? Haba Alh ai da se kayi shawara kafin kayi Biza dan nide har na gama haɗawa ɗana lefe ,wurin Hajia Binta kasan itama ta na zuwa kasashe to ita nabawa kwangilar haɗa lefen saboda haka inaga ba bukatar se mun tafi ,idan kayan sun iso zan kawo ka gani ai idan akwai abinda beyi ba se a canja ko?
cikeda farin cikin karamci irin na Ammi ,Abba yace " Allah yayi miki albarka Zainabu , nasan ma komai zeyi ai shikenan yanzu dai kema se kuyi list na abubuwan da zaku bukata keda Bilkisu da yaran duka ma da kuma abun da xakuyi hidimar bikin dashi ,Kinga se na bada kuɗin ko " ehhh sedai wannan kam Amma ai munyi waya da Umma ,kasan halinta wai bazata zo ba shine nace to ni zan je zuwa anjima se mu tattauna ,idan munyi shawara dai zaka jimu "
Alh shin ka ajiyeni anan ne saboda ka wulakanta ni ko kuwa ,wannan ai cin fuska ne ,nida ƴata sannan ace wata ce zatayi hidimar bikin ta haka gaskiya tace? wlh bazan yarda da wanann ba " kallon mamaki yayi mata kafin yace " Saudah wai me yasa ke a komai bakida lissafi ne ,a ina kika taɓa ganin uwar amarya ta haɗo lefe ina sedai uwar ango ko ,idan kuma ankawo lefen kika akwai abinda babu shi seki sanar dani na baki kuɗin ki siyo balle na ba tabbatar da duk abinda ake bukata Zainabu zata saka shi a akwati dan haka roƙo ɗaya zanyi muku kubari ayi bikin nan cikin kwanciyar hankali bana son ku zubar min da mutunci a cikin dangina dan nasan zuwa wani sati baƙi zasu fara sauka dan Allah ayi komai cikin mutunci ,kuma ke Saudah ban amince da wualaƙancin ki garesu ba , dan kisani daga iyayena se ƙanne na to ki kula "
Cike da harzuƙa ta mike tsaye " ya isa haka Alh ko kakanni ka ne su zo miye nawa a ciki kasan dai babu dole se na kulasu ko dan ban saba harka da kauyawa ba ka ga se kabarsu ga yar uwarsu ,dan bazan iya da rashin hankali na fulani ba " Saudah kin kuwa san me kike faɗa iyayen nawa ne basuda hankali, amma ai kinsan ni Fulani ne kuma kika aure ni ko ,ban taɓa wulaƙanta Miki iyaye ba meyasa ke bakya girmama nawa ,to wlh kinji na rantse ko kallon banza kikayiwa ɗaya daga cikin su har kika bari na samu labari ,zan ɗauki mummunan mataki akan ki mutuniyar banza kawai wuce kibani wuri"