← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin ƙarfe 7 na dare dangin Muhsin suka zo tafiya da amarya ,nan fa hankalin Rumaisa ya tashi se yanzu ta tabbatar da gaske ne barin gidansu zatayi ,Umma ta kaita falon Dady dan suyi bankwa na kusa da Dady ta zaunar da ita ,nasiha yayi mata sosai tare da saka mata albarka banda kuka babu abinda takeyi lokacin da ya sallamesu se ta sake fashewa da kuka ta rungume Dady Muryar ta ko fita bayayi tace ''Abba shikenan zan tafi kayafemin idan na taɓa saɓa maka kariƙa sakani a addu'a Allah yabani ikon cin jarabawar nan yabani ikon biyayya ga reshi ,zantafi gidan da bansan kowa ba Abba mijin ma be Sanni ba wataƙila ya soni wataƙila kuma ya tsangwameni , shikenan na rasa komai na rayuwa Abba " be san lokacin dahawayen tausayin ta suka zubo masa ba shi kansa ya yarda ba'ayiwa ƴarsa adalci ba ,ƙur'ani ya ɗauko da Hisnul-muslim ,ya damƙa mata a hannun ta cikin dauriya yace " wanan sune garkuwar ki Rumaisa ,Allah yana tare da ke kiriƙe ibada ki kuma zauna da mijinki da zuciya ɗaya ,Kinga dai yadda Ammin ku ke biyayya kiyi koyi ,Allah yabaku zaman lafiya"ganin idan ya ci gaba da magana ze sautin kukan sa ze iya fitowa ,shikuma baya so ya sare mata gwuiwa dan haka yaɗagawa Umma hannu alamun su tafi ,kamata Umma tayi se aka kaita wurin Ammi kuma , nan kam babu magana da Ammi kuka takeyi bilhaƙƙi ,ta kasa cewa komai ga Rumaisa tsugune a gabanta " ki samata albarka zamu mikata ga mijinta "cewar Umma " lalubo hannun Rumaisa tayi ta haɗa da na Ammi ,dukan su biyu jikinsu rawa yakeyi ,ganin Ammi batace komai ba se Rumaisa tace " Ammi kisakamin albarka dan nasamu ƙarfin zuciyar biyayyar aure dan Allah " rungumeta Ammi tayi tana kuka tana magana " ke me biyayya ce Rumaisa a koda yaushe albarka ta tana biye dake bazan gushe ina yi miki fatan dacewa ba , Allah ya sanya wannan auren ya zama silar farin ciki a gareku ,kiyi biyayya daidai iyawarki ,ki kuma sanya haƙuri a rayuwar ki "ganin kukan nasu na ƙara ƙarfi se Umma ta janye ta ta fita da ita ,ai ko suna fita Amrah ,Mimi da Nawwara suka ƙankame Rumaisa dukansu suka zube kasa ,itama ƙankame su tayi ,tsawa Umma ta daka musu" Wane irin iskanci ne wanan Amrah kinzo kin tara yara kun sakata a gaba da kuka keda zaki ƙarfafa mata gwiwa ,shine saboda iskanci zaki sake ɗaga mata hankali shiyasa nace baxaki je gidan ta ba se bayan kwana biyu " a'a Umma dan Allah kibarta mutafi tare nasan ba lallai bane ma ya shigo yau ba "fincike ta tayi su dai dangin Muhsin da ido kawai suke binsu ,sosai familyn ya burgesu lallai akwai soyayya shaƙuwa a tsakanin su ,wata babbar mace daga cikin su ce tace " Hajia dare yanayi dan Allah kubamu amaryar mu mu zamu tafi" daga Umma se Hajia Inno suka tafi raka Rumaisa ,nan kuma da ƴar'uwar Ammi da ƙawarta ne zasu tafi bikon Meerah.

Tun da akayi sallar Magrib Aunty ke fama da Meerah akan ta sake yin wanka kafin dangin mijinta su iso amma fir taƙi seda Yayar Mamanta tayi mata tsawa ,da su basu da labarin auren ba na soyayya bane ,dole ta shiga tayi wanka da ruwan turaren da Aunty ta haɗa mata ,da ta fito ma Aunty da kanta ta shirya ta cikin atamfarta Mid green se dirty white Vail sosai tayi kyau duk da kumburin da fuskanta tayi na kukan da tasha ,hijab Aunty ta bata tace tayi sallah tukuna ,babu musu tayi sallah ta dade tana kai kukan ta ga Ubangiji akan ya sanya mata son Muhsin ko kaɗan ne Gaishe²da ta fara jiyowa ne ya tabbatar mata da lokacin rabuwa da Auntyn ta ne ya zo ,sedai tayi ƙoƙari wurin ganin batayi kwallah ba sedai kukan zuci ,da Yaya kawai sukayi sallama Aunty cewa tayi bazata iya ganin tafiyar Meerah ba ,sedai letter da ta rubuta ta damƙa mata a hannun ta tun kafin masu bikon su iso ,jikin ta yayi sanyi sosai lokay da yaya ke faɗin " ƙanwata muna fatan sauyin ƙaddararki ya zamo Alkhairi a gareki , bansan ya zaki ɗauke mu ba yayin da kika ga wanda muka aura miki a matsayin miji sedai kisani komai munayi ne domin rayuwar ki ta inganta ,kiyi haƙuri ki kuma yi biyyaya ,Allah ya albarkaci rayuwar auren ki "envelope ya dauko yace " wannan sadaƙin auren ki ne mallakin ki ne "janye hannun ta tayi tace " duk abinda yake mallakina zan iya mallaka wa iyaye na ,kune iyayena waƴa da suka jiɓinci al'amurana ,saboda haka kuriƙe kudin Yaya zakuyi wani hidma dashi ni yanzu addu'ar ku kawai nake nema " sosai suka burge mutanen da ke wurin Kowa se saka mata albarka yake a haka aka fita da ita dan kaita gidan mijinta .

"Masha'Allah" shine abinda masu kawo amarya Meerah suke ta furta wa yayin da suka saka ƙafarsu a luntsumemen falon da aka kira da mallakin ta wani lafiyayayyen sanyi da ƙamshine ya ratsa su ,duk tunda suka ga motocin da aka zo ɗaukar ta suka fara tunanin me kuɗine mijin ,basu tabbatar ba to seda suka shigo cikin gidan Alhannar duniya kenan ,babu abinda ba'a zuba mata ba na more rayuwa ,dan haka suka ƙara yi mata nasiha ,duk da sun san ita yarinya ce me biyayya amma shi zaman aure seda haƙuri ,suna cikin zagayen gidan Aiken Ammi ya riskesu manyan kuloli ne dauke da abinci farfesun kaji se drinks ,aikam zama sukayi suka cika tumbin su ,daga ƙarshe sukayiwa Meerah sallama suka kama gabansu

Ai suna fita se ta samu nasarar fashewa da kuka ,ta daɗe tana kuka ganin wannan baze zaman mata mafita ba ga ko sallar isha'i batayi ba dan haka ta shiga toilet ta ɗora alwala ta fara gabatar da Sallah

da ta idar ta koma kan gado tayi zaune tana jiran ganin ta inda ango ze ɓullo shiru² har ƙarfe 11 be shigo ba ,aiko se ta kara tabbatar wa kanta zaman wulaƙanci zatayi ,ace kusan 4 hours da kawo ta amma bezo ya duba ta ba hala ma matar sa ce ta hanashi zuwa gare ta ,s
Kifewa tayi taci gaba da risgar kukan ta ,dan zuciyarta tayi mata nauyi

Ɓangaren Muhsin kam ,yana ɗakinsa ya kulle yana baccin hankali kwance ,babu wanda yaga shigowar sa gidan ,tun bayan ɗaurin aure bashi ya tashi ba se after 5 a gaggauce yayi wanka yayi sallah sannan ya dauko wayarsa da ke silent kusa missed call 35 ya gani a wayar kira 5 na Ammi ne se 2 na Dady ,Umma ma dai kan wannan karon ta kira shi har kira biyu sauran kiran kuma na abokanan sa ne ,dafe kai yayi ,dan yasan tunda yaga kira Umma to abu me muhimmanci ne ,zama yayi da niyyar bin kiran nasu sega wai kiran abokin nasa ya shigo , yana ɗagawa,ya rufe shi da masifa akan wulakanci da yayi musu ,haƙuri yafara basu sukace ya fito gasu a harabar gidansu ,dole yamaida wayar aljihu ,ya samu ya fita ta kofar baya dan mutane sunyi yawa a gidan , ɗaukar sa sukayi suka wuce hotel a can suka bashi kayan da ze canja wai ashe sun haɗa masa walima ne na iya maza kawai ,aiko abun ba ƙaramin ƙayatar da shi yayi ba dan sun kashe kudi iya kudi ,ga har wanda be sa ran sun san da maganar auren ba ma sun halarci walimar ,wanann hidimar ita ta ɗauke hankalin sa har dare yayi ,se kusan ƙarfe 10:30 suka kamo hanyar gida ,a parking lot yayi musu sallama akan ya gode base sun shiga ba daya daga cikin su ne me suna Awwal yace " wlh baka isa ba se munga amarya ka sani ko a cikin ƙawayenta mu ma mu samu " aiko bazakayi aure ba kenan ,na faɗa maka babu wanda ze shiga yanzu kwa dawo daga baya ganin ta "ganin dai da gaske yakeyi ,dole suka juya bayan sun gama zaginsa ,shidai da dariya ya rakasu

Shiru ya samu falon se sheshekar kukan da yake jiyowa a cikin bedroom hakan ne yabashi tabbacin tana ciki mamaki ne ya kamashi me ze saka Rufaida kuka bayan burinta ya cika na ganin ta aure shi idan ma kuka ne ai shi Yakamata yayi ba ita ba ,haɗe fuska yayi yana nufar ɗakin ,a kife ya sameta kan gado batamaji motsin shigowar sa ba ,cikin faɗa²yace " wannan wane irin muna funcine ina ke kika ce kina sona kuma aka baki to kukan uban me kike yi bana son gulma" kamar a mafalki Meerah take jin Muryar Mu'aiseen ,hakan ya sakata yaye nayafinta da sauri ,karaf suka haɗa ido wani irin zabura sukayi dukan su ,ita bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba suka fara nuna juna da yatsa kowa yakasa magana ,shine ma yayi ƙoƙarin haɗa kalmomi cikin rawar baki yace ...........

Comments and share pls

#Real@Bazamfaria❤️
*MABARACIYA*

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'ى*  *ASSɷ* 📚✍*
  _{Onward Together}_

_STORY AND WRITTEN_
                  _BY_
////////////////////////////////////////////////////
*FIDDAUSI SANI* ( _Damsel Feedorh_ )
///////////////////////////////////////////////////

🅿3️⃣5️⃣

_Baki_ _baze iya furta irin jindadin da kuke sakani rabbi yabar ƙauna_ _one_ 💞
Chapter 39 · 0% Book details