Sashe 13
Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da sauri ta samu ta kammala lokacin har yabar sashen ,zama tayi kan ɗaya daga cikin kujerun falon tana tunani " tabbas idan dai har haka wasu ke rayuwa to zata iya cewa suna cikin halaka ,yanzu kamar Rufaidah ,saboda wani dalili da be kai ya kawo ba za'a ba'a tashin ta sallah shiyasa se ta gadama take tashi ashe tun tana yarinya ne akayi mata wannan sabon kuma abun takaicin wai uba mahaifi da aka sani da sa ido da kula akan addinin iyalinsa ,shine ke faɗar wai ba'a tashin ta ,mutum nawa ne keda cutar da tafi nata amma hakan be zama uzuri gurinsu sun wo fantar da ibada ba, and migraine ai ba ko yaushe yake tashi ba ,yanzu yarinyar da ko yau akayi mata aure zata haihune suke treating lyk a baby ,waye ze kula mata da tarbiyyar yaranta idan tayi aure ta haihu bayan ita kanta tana da ƙarancin tarbiyyar. Tayi nisa sosai cikin duniyar tunanin ta har batasan lokaci ya tafi ba se saukar zagi ,me haɗe da tsawa da taji akanta " Uban wa yabaki damar zauna mana a inda muke zama ,kina matsiyaciya ƴar matsiyata ne zaki zauna min anan ,ok ki kina tunanin shirun da nayi miki yana nufin nabaki dama ne kiji daɗi to bara kiji ,alƙawari na ɗaukar wa kaina maganin kin wulakanta yanzu ma ina tunanin abinda zanyi miki ne wanda harki koma ga Allah baxaki manta ba wanda zesa kigane banbancin da ke tsakanin talaka da me kuɗi ,ko da yake na daɗe ina tunanin cewar gata nayi miki ɗaukoki daga yawon titi kina bara na kawo ki gidanmu ,amma wlh se kin kwanmace yawon bara akan zaman gidan nan ,shegiya me fuskar jajayen Aljanu.
Ita dai Meerah da ido kawai take binta dan kallon taɓaɓɓiya yanzu takeyi wa Rufee ,to miye banbancin ta da Mahaukaciya ,ace mace sam ita a rayuwarta bata san menene mutunci ba " kina bacci Alh yashigo ,harma ya daɗe anan sedai be samu ganinki ba inaga Yakamata kitafi kigaisheshi dan yasan cewar kin tashi lafiya ko" Meerah ta faɗa cikeda rashin damuwa kai kace ba ita Rufee tagama zurfawa zagi ba, aiko iya baƙin ciki Rufee ta shaka dan idan akwai abinda ke ƙara sakata baƙin ciki befi idan tayiwa Meerah masifa itakuma taƙi kulata ba ,har xatayi magana kuma se ta fasa kawai ta fita daga falon " kyaji dashi masifaffiyar banza banazo nan saboda ke bane da uwarki zanyi dan zaman jiran ta nike ,badan haka ba ko ance kibuɗe baki ki zagi Ameerah ai zaki musa ,mtsswww se kace garesu farau arxiƙi kome dai ida masu arxiƙi wannan ranar da ta fahimci arxiƙin da take taƙama dashi ko na miye to bansan ya xatayi ba " ita kadai tayita da batun ta daga ƙarshe dai ta wuce sama dan gyarawa kafin ta janyo wata masifar.
Rufaidah na fita ta nufin ɗakin Abba ,saboda ma bata so ta haɗu da ɗaya daga cikin su Ammi se kawai tabi ta baya inda kai tsaye xe sadata sa falon Abba dan tanada tabbacin yana ciki shikaɗai saboda a irin wannan lokacin yakan buƙaci keɓewa a cewsrsa ze huta ne to baya buƙatar ganin kowa
Knocking tayi ,daga ciki Abba yabata izinin shiga,da Sallama ta shiga , sedai haɗe fuska tayi sakamakon ganin Rumaisa a ɗakin ,dukansu suka amsa mata sallama wuri tayiwa kanta ta zauna " Abba ina kwana an ce ka shigo ina bacci ,ai bansan zakazo da na tashi da wuri " Murmushi Abba yayi mata yace " karki damu ,kintashi lafiya ko " Ehhh Alhmdulilah Abba ya gajiya "ba gajiya ya amsa mata " bakiga ƴar' uwarki ba ? Yafaɗa yana kafe ta da ido dan ganin tunda ta shigo bata kalli Rumaisa ba ,narke fuska tayi kamar xatayi kuka tace " na ganta mana " amma shine kika kasa yimata magana wai Rufaidah meyasa ke bakijin magana ina jiyan nan nagama yi muku faɗa akan ku haɗa kanku" haba Abba nide bansan me akafaɗa maka akaina ba wannan karon duk kabi ka tsaneni ,ina nice babba idan gaskiya za'ayi waya kamata ya gaisheda wani a tsakanin mu ?. "Ungo nan Rufaidah"Abba yayi mata daƙƙuwa " ni kike faɗawa idan gaskiya za'ayi ok wato yanzu banyi gaskiya ba ko " yi haƙuri Abba ,ai tana da gaskiya nice yakamata na gaisheta ,but banyi hakan ba nikuma a tunanina na amsa mata sallama ,shiyasa naga babu bukatar se na gaishe ta ,amma tunda gaisuwar takeso zanrika gaisheta ,shikennan ko?Rumaisa tafada tana kallon Rufaidah ,harara ta zabga mata tare da jan tsaki " muna funcin banza nide duk yadda za'a so shiga tsakanina da Abba ,Allah yafi mutum" girgiza kai kawai Abba yayi tare da furta "Allah ya shirya "da Ameen Rumaisa ta amsa tana ci gaba da bashi labarin da sukeyi tun ɗazu ,itadai Rufee shiru kawai tayi tana sauraren su , lallai ta yarda Mama ce gatan ta duk ranar da aka ce babuta a gidan kila ko ganin Abba se yayi mata wuya
Ameerah#
Tunda ta kammala gyaran ɗakin ta rufo ƙofa ,se ta dawo warta harabar gidan jikin flowers ɗin da take zama batasan meyasa zaman wurin keyi mata daɗi ba ,tana zaune tana kallon ma'aikatan gidan da suke ta kai da kawo kowa sha'anin gaban sa yake yi wasu yan kyawawan yara da bazasu wuce 7 years bane suka fito daga sashen su Mu'aiseen mace da na miji ,macen ta biyo namijin tanaso ta amshi abinda ke hannun sa ,shikuma ya hanata daganan suka fara kokuwa, cikin rashin Sa'a namijin ya tura macen da hannu biyu se tayi baya ta faɗi ,da sauri Meerah ta isa wurin dagata tayi tana lallahin ta saboda kukan da takeyi ,daƙyar yarinyar tayi shiru tana cewa " Aunty kice yabani abuna nawane Aunty Mimi ta bani" maida hankalin ta tayi wurin Nurain tace " zo kabata kayanta ,ganin zata kamoshi se kawai ya ruga da gudu cikin gida ,dariya Meerah tayi dan sosai yaran suka burgeta ,kama hannun Nawwara tayi tace " kinga ki kyalesa gobe zan kawo miki wanda yafi wannan kyau "cike da jin daɗi tace " da gaske? Ɗaga mata kai tayi tace to shiga daga ciki kema ,goben zan kawo miki ,amma baki faɗa min sunan ki ba " Abban mu yana cemana twince ,Ammin mu kuma tace auta Yaya Rumaisa ke cemin cutie , Aunty Mimi ita ke mun Nauwara ,amma kinsan yayanmu me yake cemin? Girgiza nata kai Meerah tayi, tace" last born"Kai kice sunan naki da yawa duk ke ɗaya lallai ke yar gata ce shikennan shiga ciki kinji kar Ammi ta nemeki " Aunty ni bantaɓa ganin ki ba a gidan su Ya Rufaidah kike? Ɗaga mata kai Meerah tayi dan ta fahimci Nawwara irin yara nan ne masu shegen surutu ,duk da gaskiya yarinyar ta burgeta kasancewar ta wacce ta saba da sabgogin yara duk da bawai tana da ƙanne bane a gidan su .
"Nawwara Nawwara tun daga cikin gidan ake kwala mata kira ,sakin hannun ta Meerah tayi tace " kinji ana nemanki ,kafin ta tafi sega Rumaisa ta fito cikin sauri ,da alama ta dade tana nemanta ,ganin ta tare da wacce bata sani ba yasaka ta karasowa da sauri ,takama hannun ta ,tace " me kike yi anan ? nuna mata Meerah tayi tace wannan Auntyn ce tace zata kawo min abuna da Nurain ya kwace ,kallon Meerah tayi ,suka sakarwa juna murmushi a tare tace " kinsha surutu ko " a'a babu wani surutu sun fito ne suna faɗa shine na fabasu " Allah sarki ,ke baƙuwar Rufaidah ce kenan ? Murmushi Meerah tayi tace " a'a me aikinsu ce dai ,tana faɗa ta kalli Nawwara tace " to ƙanwata natafi se goben idan Nazo ko zan kawo miki alkawarin ki " daga haka ta tafi ,da kallon mamaki,Rumaisa ta bita ,haka kawai se taji yarinyar tabata tausayi ,gata karama da ita ,kamata yayi ace tana school a halin yanzu ,amma rashi yasaka ta zuwa aikatau ,kuma tasan a yadda Rufaidah batada kirki ba lallai bane ta sarara mata ,gaskiya da Abba xe yarda da ta rokesa ya temaki rayuwar yarinyar a mayar da ita school ,amma zata gwada sa'ar ta tagani ko zata da ce.
Tun da suka shiga ciki Nawwara ke bawa Mimi labarin sabuwar Auntyn ta ,abu kaɗan idan Nurain yayi mata zatace se ta gayawa Aunty ,Ammi da tagaji da jin sunan Auntyn ne yasaka ta cewar wai nikam Auta wace Aunty kika samu ne haka "yawwa Ammi inaso ma muyi maganar dun dazu mantawa nayi ,wlh wata sabuwar me aiki ce su Rufaidah suka dauka sema kin ganta kyakkawa da ita kuma yarinya ce bazatafi 15 yrs to 16 ba ɗazu da kikace na nemo Auta ne naganta ashe itace ta raba musu gardama da sukeyi ,wlh tabani tausayi shi ne nace zanyiwa dady magana ,ko ze temakawa iyayen ta se ta koma school" tun kafin ta ƙara sa Ammi tace " kinsan na haneki da shiga abinda be ganoki ba ko ,so kikeyi ki yawo mana wata jarabar, kinsan dai zasuce wani muna funcine ,kuma daga ganin yarinya kinsan alakar da ke tsakanin su ,to babu ruwanki ban amince kiyi magana akan masu aikin su ba ,da ace ana bangaren take aiki to zaki iya amma a can bakida wannan hurumin " cikin sanyin jiki tace to shikennan Ammi dama nima seda nayi wannan tunanin shiyasa ma ban fada masa ba nace se naji ta bakin ki.
Zahra#