← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu
Rufaidah ta sake samun Hajia Sauda da zancen Mu'aisam,wanannan karon sosai taci mata mutumci ,saboda haka ta yanke shawarar samun Abba da zancen ,a lokacin yana sa shen su Ammi dan haka ta saci jiki ta same shi ,yana gishin giɗe tayi sallama ,amsawa yayi yana tashi zaune " a'a Rufaidah kece cikin daren nan? " Ehhh Abba barka da dare "wuri ta samu ta zauna tace "Abba, dama.." se kuma tayi shiru ta kasa faɗa ,tattara hankalin sa yayi kanta dan yasan tunda yaganta haka to maganar me muhimmanci ce " come on Rufaidah menene? ina fatan dai ba wani matsalar bane "
Abba dan Allah ka temaka min wlh ina matuƙar son Yaya Mu'aisam nide bazan iya auren wani ba sedai na zauna bazanyi aure ba" ta ƙara sa kamar xatayi kuka " shiru Abba yayi ,dan gaskiya ba ita ya so aurawa Mu'aisam ba ,sedai babu komai tunda Allah yasa beriga ya furta wa kowa ba and dukan su ƴaƴan sane "ashsha saboda kina son yayanki shine duk kika zama wata iri haka? Ko shine yace baya sonki?".
A'a.Abba Mama ce tace bazata bari na aure sa ba wai ita tana da wanda take so na aura ,dan Allah Abba katemakeni ,kasan halin Mama, bansan me yasa bata so na' auri Yaya ba " karki damu Rufaidah,ni nasan ta inda zan ɓullo mata kisaki ranki ,aure kamar kin auri Mu'aisam ne kinji ,banason kisa damuwa a ranki ,jeki kwanta " to Abba nagode Allah ya ƙara girma ,seda safe " har takai ƙofar fita se ta dawo ,kallon ta yayi yace " wani abunne? dama Abba banaso kafaɗawa Mama nice naxo" murmushi yayi mata " karki damu kedai ki saki ranki ita ai bata isa ta hana abinda nayi niyya ba ,shiɗin ɗan uwanki ne dan haka ita bata isa ta rabaku ba"

"cikin jin daɗi tace " to Abba Nagode sosai Allah yaƙara girma".

Bayan kwana biyu Abba ya tara duka iyalan sa ,duda seda aka kai ruwa rana kafin Hajia Sauda ta yarda ta sameshi a sashen Ammi ,se wani harare² take Mu'aisam ne ya buɗe musu taro da addu'a ,kafin Abba ya fara magana " maƙasudin taraku anan ,ba wani abu bane face saboda ke Rufaidah da kuma Rumaisa ,duk abinda yakamata nayi muku nayi to gaskiya yanzu so nike na aurar daku na huta naji da su Mimi" wannan abun da yafaɗa yaƙara ƙona zuciyar Saudah " dan haka idan kuna da wanda kukeso ku sanar dani, dan banaso nayanke hukunci kuga kamar banyi muku adalci ba ,ke Rufaidah dake zan fara shin kinada wanda kikeso ne? Ɗago kai tayi ta kalli Hajia Sauda,aiko tayi mata wani kallo me haɗe da gargaɗi ,wanda duk a idon Abba ne ,da sauri ta duƙar da kanta kasa cikin rawar murya tace " a'a Abba ni babu wanda nikso " girgiza kai kawai yayi yana maida akalar tambayar sa akan Rumaisa " Abba kasan ni ban rigada na kammala karatuna ba " Rumaisa aure ai baze hanaki karatu ba , sedai idan kince bakida wanda kike so a yanzu to wannan kam ,zanyi miki uxuri saboda karatun amma kitabbatar kafin ki kammala kun shirya kanku da wani ,idan ba haka ba ni zan zaɓa miki kamar yadda zanyiwa ƴan'uwanki a yanzu .

Mu'aisam ,nasani kai yaro ne me biyayya,dan haka nayi shishigi a cikin rayuwar ka ban sani ba ko zakayi farin ciki da hakan ,na yarda da tarbiyyar ka Mu'aisam ,a kwai kuma dalilan da yasa nayi maka wannan zaɓin ,iya sani na dakai ,na sha tambayar Ammin ku ko kana da wacce kake so amma dai amsar ɗaya ce babu shekarun ka se ƙara ja sukeyi amma sam kai babu tunanin auren a ranka ,Amminku itama ta saka ma ido ,saboda haka ga kanwar ka Rufaidah nan ,nabaka ita kuma banason auren ya wuce sati 3 masu zuwa ,ina fatan zakuyi min biyayya ku rike junanku amana.

duka mutanen Uku a firgice suka kalli Abba ,Ammi ,Hajia Sauda,da kuma uban gayya Mu'aisam,da yaji zuwan maganar a bazata ,meyasa Abba xe zaɓa masa Rufaidah bayan duka halayyar ta babu me burge shi? innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,kawai yake maimaita wa cikin zuciyar sa ,dan har wata zufar wahala yaji tana titsatso masa

"Wlh Alh baka isa kayi kyautar ƴata a wurin da ba'a son ta ba kuma na barka , taya ma ka rasa wanda zaka zaɓa mata se waƴanda kasan cewar ba ƙaunar mu suke ba ,idan har yazama dole ne se kayi haɗin naga akwai mace a ɗakinsu meyasa baka bashi ba ,ok se tawa " yar ko to idan ma wani muna funcine akayi ,tun wuri a warware maka dan narigada nayiwa ƴata miji " cikin tsawa Abba yace " ya ishe ki haka Saudah ,waike se yaushe ne zakiyi hankali ,ace a gaban yaranki ma bakisan ki kama kanki ba yanzu wannan abun da kikayi shine me? Haka kike so itama ƴar taki taje tanayiwa mijinta kome ,wlh kar ki kaini bango shirun da kika ga inayi miki bawai tsoron ki Nike ba kuma wlh idan kika sake furta kalma ɗaya a wurin nan to a yau ɗinnan zan ɗaura musu auren ba se gobe ba kuma kinji na rantse idan kuma kina wasa to ki tanka " duda Abba mutum ne wanda bayada damuwa amma fa idan ransa yabaci to yakanyi abinda yafi abinda ya faɗa ,kuma tasan idan ya ɗaura auren shikennan anshiga gabanta dan haka ta ja hannun Rufaidah da karfi suka bar falon. Mu'aisam ma jiki a mace yatashi ya fita ganin haka Rumaisa da Mimi harda su Nawwara ma suka fita duda itama zuciyarta babu daɗi.

Yayi saura daga Ammi se Abba ,kallon yadda ranta yake a ɓace yayi ,se yanzu ne ya fahimci cewar be kyauta mata ba ,dan ya hango tsan tsar rashin jin dadi a idon ta ,cikin sanyi murya yace "Hajia" ɗaga masa hannu tayi alamar dakatar wa ,cikin sanyi murya batare da hargitsi ba tace " me zakace Alh hukunce ka zartar akan ɗanka ko to miye na wa se fatan alkhairi Allah yabasu zaman lafiya ,bazan damu ba kuma bazanji haushi ba ,tunda ba Mu'aisam bane yanunamin wariya ba ,na yau kawai an nunamin cewar banice na haifeshi ba ,bayan tsawon shekarun da wanann ya shafe a lissafina sedai inaso na tuna maka ,bakaine ka bani Mu'aisam ba bare kayimun katsalandan a rayuwar sa, sam ban amince da wannan haɗin ba sedai idan har shine yacemin yana sonta da bakin sa ,kamar yadda tayiwa ƴarta miji haka nima ɗana yanada wacce yake so" tana gama faɗar hakan ita ma ta bar falon
Lallai kam be kyauta ba ya sani tunda har Ammi ta nuna fushin ta ,macen da xeyiwa rashin adalci kai tsaye amma bazata taɓa nuna fushi ba,dafe kai yayi yana jan tsaki.

a ɓangaren Ammi ma tana barin ɗakin ,kai tsaye ɗakinta ta shiga ,zama tayi bakin gado ta fara tunanin rayuwar su ta baya

Asalin labarin

Alh Yusuf tsoho haifaffen garin Kebbi state ne a wani ƙauye da ake kira ɗakin gari ,mutanen garin dukansu fulani ne sedai irin baƙaƙen fulanin ne ,mafi yawanci mutanen garin ƴan boko ne kuma babu lefi sunada kudi sedai akasarin masu kuɗin basa zama a garin wasun su suna dawowa cikin Kebbi ne da zama wasu kuma Sokoto wasu Abuja ,kaduna da dai sauran su ,sedai sukan haɗu bikin sallah kowa yakanyi kokarin ɗaukar iyalinsa yaje sallah saboda basa son yaransu su tashi da rashin jin Yaren fulatancin ,duk da nasu Yaren yasha banban da na sauran Fulani ,kamar dai yadda kuka sani ko a fulanin akwai banbancin yare

Alh Yusuf su 3 ne a wurin iyayen duda matan Babansa biyu amma ita ɗayar Allah be bata haihuwa ba ,shine Babba se kaninsa Yahuza da yake zaune a nan cikin Kebbi se kanwar su Bilikisu ,wacce take aure a Kaduna
Anan cikin garin su yayi auren fari wacce ta kasance itace uwar gidan sa wato Zainab (Ammi) ita ta kasance farar macece kyakkawa ,sam bata kama da mutanen garin wanann ya samo asali ne kasancewar babanta ne ɗan ɗakin gari amma Mahaifiyarta fulanin Gombe ne ,kuma ita ɗin kamannin mahaifiyarta ta kwaso.

Kasancewar ta fara yasaka hankalin samarin ƙauyen dawowa kanta ,da yake mace bata auren mijin da ba nata ba ,se gashi ta tsayar da Yusuf a matsayin wanda take so ,bayan anyi bikin su ne ya ɗauki matar sa ya wuce da ita a buja lokacin a can yake zama

suna zaune cikin lfy da soyayya sedai matsalar da suka fara fuskanta shine ra shin haihuwa ,dan kuwa yanzu shekarar auren su 7 kenan amma ko batan wata bata taɓa yi ba ,kusan ma itace me damuwar dan shi Alh Yusuf sabgogin gabansa ma sun hanashi zama ya natsu bare har ya fahimci cewar yakamata ya samu yara ,gashi yaki yaje asibiti bare agane matsalar daga ina ne duda ita tasha zuwa ana faɗa mata lafiya lau take lokaci ne de beyi ba ,ana haka kwatsam ,yace zasu baro Abuja su dawo Kaduna da zama ,hakan yayi mata daɗi dan a Kaduna kanwar sa take zaune da nata mijin ,harda yaransu guda uku, ko ba komai ta samu ƴar uwa ,tunda dama ita kaɗai iyayen ta suka haifa kuma Dukansu sun rasu tun bayan auren ta da shekara 3 babanta ne yafara rasuwa kafin mamanta ,se ta zama kamar batada kowa a ɗakin gari tunda dama babanta ne anan kuma dangin uba ba kowanne suke damuwa da lamarin ƴaƴan yan uwan su ba idan basa raye.

yau da gobe bata bar komai ba segashi kwatsam Alh Yusuf yazo mata da zancen karin aure ,sosai ta ɗaga hankalin ta saboda tana tunanin xeyi aure ne saboda yaga ita bata haihuwa ,kanwar sa ce Bilkisu (Umma) take kwantar mata da hankali ,daga ƙarshe ta fawwala wa Allah komai ta saki ranta.
Chapter 19 · 0% Book details