← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 43

Sashe 29

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitar Rufee yayi dai² da shigowar motar drivern da ya ɗauko Hajia Laura daga gareji ,dan motar haya ta shigo ,duk da taji lokacin da Hajia saudah ta tura driver zuwa ɗauko ta ,hakan besata kallon ko inda take ba saboda ranta a ɓace yake ,dan haka tana shiga ko falo bata tsaya ba kawai ta haura ɗakinta lokacin Meerah tagama gyara shi tsaf tana janyo ƙofar se gata ta iso "biyoni" shine kawai abinda ta faɗa tana shiga ɗakin ,bin bayanta Meerah tayi kamar yadda ta buƙata ,a bakin faɗa wa tayi kan gado tana dafe kai ,seda ta ɗan sauki lokaci kafin ta buɗe idonta ta sauke akan Meerah" zaki iya gane yarinyar da tazo wurin sa? Meerah da tafita rainin wayo se tace " Wafa? sosai tambayar ta baiwa Rufee haushi ,se kawai taja tsaki tace " Yaya Mu'aisam " au wata ce dai ,xata kai sa'ar ki ,sedai kamar tafiki wayewa ,kyakkawa ce kam gaskiya gata doguwa ,dagani batada hayaniya dan kuwa duk irin bayanin da nayi mata batace komai ba sema murmushi da tayi min and abu ɗaya naji ya faɗa da yana bata haƙuri ko Mine ko me ,sunan nan ne dai irin na ƴaƴan masu kuɗi da kukeyiwa samarin ku,gaskiya dai kam tanada kyau"ke shasha shar ina ce abinda na tambayeki daban abinda kike bani amsa daban ,me ya shafeni da kyan ta dalla fice min daga ni sakaryar banza " sumui² Meerah ta wuce tana ƙunshi dariyar ta ,dama abinda takeso kenan ta samu hanyar gasa Rufee tunda ta fahimci tanada hassadar jin ance wani yafita kyau

Tun daga upstairs take karewa Hajia Laura kallo ,da tayi rashe-rashe kai ka ce a falon gidan ta take a gabanta ko kalolin abinci ne aka jera ,drinks har da su fruit "ikon Allah wai duk mutum ɗaya aka jibgewa to wannan kuma daga ina take? Idan baƙuwar Hajia saudah ce to tabbas tafiyar ɗaya ce ,amma bara na gani ,karasowa tayi cikin falon ,zuwa lokacin kuwa attention na Hajia Laura ya dawo kanta ,dan haka se tayi murmushi tana zuwa har gabanta tace " sannu da zuwa Hajia ina wuni? Instead ta amsa se ta kalli Hajia Saudah da ke gefenta zaune da ido ta yimata alama da wacece ,itama da idon ta bata amsa ,dan haka se ta yi murmushi tace " Aminatu ko? Kallon mamaki Meerah tayi mata ,se kuma ta ɗaga mata kai " ohhhh kinyi mamakin ya akayi nasan sunan ki ne ? Ai Hajia Sauda tunda ta dawo take bani labarin ki akan irin tausayin ki da taji tace yarinya ƙarama da ke amma kina fuskantar rayuwa ,babu karatu ,har take cemin tanaso idan iyayen ki sun amince ta ɗauke ki ta maida ki school ai kinaso kiyi karatu ko? Kamar wata sokuwa Meerah ta washe haƙora tace " inaso sosai ma Hajia ,dama wannan aikin da nikeyi inaso ne idan mun tara kuɗin se a sakani makaranta " ayya to ki kwantar da hankalin ki Hajia Sauda mace ce da tasha temakawa yara irinki wanda iyayen su basuda halin saka su school ,Kinga daga ganin ki kinada natsuwa da biyayya ,zakiyi daɗin sha'ani,se kuma ta maida kallon ta da Hajia saudah da keta faman doka murmushi da alama tanajin daɗin kalaman yaudarar nan da Laura keyi " Hajia ko zaki bani yarinyar nan se ki nemi wata ,Allah haka kawai nakejin tausayin ta ,dama na faɗa miki ai saura 2 months bikin me aikina ,itama seda na maisheta school ta kammala ,yanzu bakiga mijin da zata aura ba babban mutum ne dan yanada kudi

"tunda Meerah taji bayanin ta ta fara daria a xuciyarta take faɗin " duk tafiyar ɗaya ce kenan ,amma menene dalilin wannan zuwa gidan Saudah tunda Yaya Maryam ta ce ,bata bari abokan hulɗar ta su zo gidan ta ,lallai akwai wata a ƙasa ko ma menene zata saka ido sosai kan lamarin

Katse mata tunani Hajia Saudah tayi da faɗin " kingama aikinne " ehhh na gama ɗakin ki ne yayi saura bansan kin tashi ba shi yasa ba shiga na gyara ba amma yanzu zan gyara Insha'Allah "ta yunƙura da nufin tashi taje gyara ɗakin " a'a kinga kibar shi kawai ,ma zaki iya tafiya amma gobe kixo da wuri ,dan akwai inda zaki rakani kafin ki wuce " to Hajia Nagode " kuɗi Hajia Laura ta fitar zasu kai 10k ta bata ,cikeda rawar jiki Meerah ta karɓa tana washe haƙora se godiya take zabgawa kamar zata kife ,seda suka dakatar da ita kafin ta tafita

Wannan duk tayi ne saboda kar ta lalata plan nata ,tasan idan tanuna musu cewar ita ɗin mayyar kudi ce to zasu fi saurin sakin jiki da ita tare da tunanin zata aikata duk abinda suke so saboda kuɗi

Seda ta fita gidan tukuna ta tuna da alƙawarin da tayiwa Nawwara na cewar zata jira ta ,juyowa tayi da niyyar ta koma gidan se ta hango me agwaluma dan haka se tayi tunanin siya mata ,aiko kuɗin ,da Laura ta bata ta cire 500 tace abata na 200
Har ta tsaya jikin flowers ɗin da take zama se kuma ta tuna da Mu'aisam,da kuma irin haɗin da tayi masa wurin Rufee ,dan haka se ta tashi da sauri tace " nasan dai yanzu yana wurin aiki idan na tsaya jiran Nawwara xe iya riskata gara kawai nakaiwa Ammi nace ta aje mata.

Da sallama ta shiga Ammi dake kitchen ta amsa tare da faɗin " ina zuwa " jin haka se ta samu wuri ta zauna ,befi 5 minutes ba Ammi ta fito tana ganin Meerah ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace " kai wai Aunty Aunta ce da kanta " itama Meerah murmushi tayi tana zamowa daga kujerar da take zaune ta gaishe da Ammi cike da kulawa ta amsa tare da tambayar ta " ya jikin ki ashe bakiji daɗi ba ,se Rumaisa ce take faɗa min ,danma sunje ganin ki " Ehhh wlh Ammi amma Alhmdulilah naji sauƙi ma ma, dama zan wuce gidana shine nace bara nakawo saƙon Auta a ajiye mata" ta mikawa Ammi ledar agwaluma " a'a lallai kam duk auta kaɗai wannan amma fa Ameerah kina son kai ,Auta kaɗai kika ware Nurain fa ? Rufe baki tayi tana dariya tace " Au Ammi wlh mantawa nake da Nurain dinnann na ga alamun shi miskili ne ai ,be cika dariya ba ,ba kamar Auta ba " kai Ameerah kema haka zaki faɗa ,kune dai baku ganin dariyar sa ,kinsan nide nasan yana dariya " to Ammi ayi haƙuri idan yazo se ace su dukansu na kawo wa su raba " yawwa dai to yanzu naji zance to yayi angode Allah ya saka da Alkhairi, amma har kin gama aikin naki ne da wuri haka ,da zaki tafi " Ehhh dake yau Hajia tayi baƙuwa ne wai ƙawarta ce tazo ,shine ta sallameni tace gobe nazo da wuri zamu fita "

Zaku fita? Ammi ta maimaita maganar "Ehhh haka suka ce Ammi " ina suka ce miki zakuje ? Wlh ban sani ba " to shikenan Allah ya kaimu goben "da Ameen ta amsa tana tashi da niyyar fita ,Sega Mu'aisam ya fito ai tana ganinshi tace "Ammi na tafi se anjima " a'a dakata Ameerah "se da gabanta ya faɗi haka dai ta kalli Ammi ta tsaya " Mu'aisam ba kace fita zakayi ba? Ehhh Ammi wani abun ne ? dan Allah idan babu damuwa ka sauke Ameerah a gida kaga yau ana rana kafin ta samu abun hawa zata wahala "to Ammi " fita yayi itakuma tayi tsaye seda Ammi tace " kibishi mana ,kar yatafi nasan halinsa bayason jira"

jiki a sanyaye ta ta fita ,ganin har ya shige mota seta nufi get da saurin ta ,cikin rashin Sa'a Sega Ammi ta fito kiranta tayi da sauri ta jiyo ina zakije ,kinga motar sa can ta nuna mata ,dan dole ta doshi motar ,har ta buɗe baya zata shiga still Ammi tace ta zauna a gaba ,kamar zatayi kuka haka da buɗe motar ta shiga ,seda Ammi taga fitar su tukuna ta koma ciki ,banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi dan tsoron abun da ze yi mata ,sedai a mamakin ta ko kallon ta beyi ba bare ma yayi mata magana ,kaɗan² take sauke ajiyar zuciya wanda duk yana kula da ita ,haka suka ci gaba da tafiya ,har seda yakai unguwar su a bakin titi ya yi parking ganin beyi magana ba se ta yunƙura zata fita sedai ƙofar a rufe tayi² yaƙi buɗuwa ,cikeda tsoro ta kalleshi sedai ma shi danna wayarsa yakeyi kamar ma besan da ita ba ,cikin salon magiya tace " zanfita dan Allah" wani irin kallo yayi mata wanda seda hanjin cikinta suka motsa ,fuskar shi babu alamun wasa yace ...........

Comments and share pls

Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:2️⃣9️⃣

Fuskan shi babu alamun wasa yace" me kika faɗa wa Matata? shiru batace komai ba cikin tsawa yace " don't let me repeat my self " turo baki tayi tace " to ni ina nawani san Matarka bare in faɗa mata wani abun,kabuɗemin ƙofa na fita nide " kinsan Allah se kin faɗa min abinda kika faɗa mata " to ni kamun tambayar da nake da amsa ba wannan ba " ok bakisan amsar wannan ba kenan " to banma san Kanada mata a gidan ba se yanxu da kake magana ,kaga kuwa ina zansan abinda na faɗa mata ,idan kuma ita matar takace ta sanar dakai na faɗa mata wani abun ai se tafadi me na faɗa mata wataƙil ko tanada taɓin hankaline se ka kaita asibiti a duba ta gaskiya danni yau ,daga Hajia se Rufaidah na gani a gidan se yanzu da naje gaishe da Ammi,to ina zan ga wata matar ka ?
Chapter 29 · 0% Book details