← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 43

Sashe 10

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido kawai Meerah take bin Larai ganin yadda take yabon kirkin Sauda , murmushi tayi tace " Allah sarki kice ita tana da kirki ni har najima da tana nan kila da zamu ɗan fi samun alkhairi ko" sosai kuwa gaskiya tana da Alkhairi base kuɗin aikin ka take baka ba kuma idan zata koma haka zata baka kuɗi da yawa tace kayi mata addu'a" cike da jin daɗin labarin Larai Meerah tace " to wai ita wane irin business takeyi haka?shiru Larai tayi kamar me tunani zuwa can tace "to gaskiya dai ban sani ba ,amma dai ko wane irin business ne nasan babbane kam shiyasa bata iya zama anan ,mijinta yayi har ya gaji mafi yawancin lokaci ma idan Kinga tazo to tana neman masu tayata raba kayanne dan tana ƙorafin ma'aikata sunyi mata kaɗan ,saboda hidimar raba kaya wai idan sun iso ,shiyasa ma kike ganin bata aje masu aiki anan da yawa da tazo taga me aiki se tace zata tafi da ita can wai acan tafi bukatar su ,saboda jigila"kiran da Rufaidah ta ƙwallowa Larai ne yasakata tashi da sauri dan amsa kiran.ajiyar zuciya Meerah ta sauke "kenan idan ina zama da Larai zan ƙara fahimtar wasu abubuwan ,lalai Hajia saudah ta cika shu'umar mace ,wato ta killace ta ta yar a gida tana kai ƴaƴan wasu.......

Akwana a tashi babu wuya ,yau ga shi Meerah ta kai tsawon sati biyu da fara aiki a ƙarƙashin Rufaidah,babu abinda yake bata mamaki kamar ganin yadda Rufee ta fita harkarta ,sam bata shiga sha'anin ta ,duk da hakan yayi mata daɗi ,amma kuma wani ɓangare na xuciyarta yanaso ko da rashin mutuncin ne yariƙa shiga tsakanin su ,domin tana kallon illa da yawa a rayuwar Rufaidah ,ace teenager like Rufaidah amma Sam bata damu da ibada ba ,koda harda rashin zuwa makaranta da kuma hulɗa da batayi da jama'a,dan ko a ɗan zuwan da takeyi ta fahimci cewar ,rayuwar kaɗai ci Rufaidah keyi dan bata taɓa shiga sashen su Mu'aiseen ba ,haka idan ba shine yazo nan sashen su to babu wanda yataɓa zuwa daga can sashen.

tana cikin wannan tunanin ne xuciyarta ta kwaɗaitar da ita son shiga bangaren su Haisam ,san ko tunda take zuwa gidan ,iya kacinta shiga sabgar aikinta babu ruwan ta da kowa ,ɗakin Larai ta leƙa se ta sameta kan dadduma da alama bata idar da addu'a ba ,saboda haka kawai ta nufi sashen su Mu'aiseen kanta tsaye batare da tunanin komai ba

Tun daga nesa take jiyo hayaniyar mutanen gidan ,lokacin da ta karasa bakin kofar da ze sadata da main falon su ,se taja ta tsaya tanabin takalman da ke zube a kofar ,se hayaniya suke da alama musu sukeyi akan wani abun ,ɗaya bayan ɗaya takebin takalmin da ido kamar me son gano wani abu ,ganin idan ma ta shiga batasan abinda zata ce dasu ba ,se kawo ta jiyo ta fito ɓangaren.

Sedai abinda Meerah bata sani ba shine tun shigowar ta Mu'aiseen ya ganta ,tsaye yayi yana tunanin yarinyar ,tabbas yana zarginta sam bai yarda da itaba, zuciyar sa na bashi cewar wasu suka turota gidansu ,dan su cutar dasu ,idan ko hakane yazama dole yasaka ido sosai a kanta kuma zejawa Rufaidah kunne ,duk da yasan ba kula masu aiki takeyi ba ,xeyi bincike sosai akanta.

Seda taje tayiwa Larai sallama ,kafin ta wuce gida.

Niger state

Hajiya Sauda ce zaune a tsakiyar aminan ta ,magana sukeyi amma sam baka jin me suke faɗa da alama suna tattaunawa ne akan abinda ya shafe rayuwar su wanda basa so kowa yaji ,sun daɗe a haka kafin kira ya shigo a wayar ɗaya daga cikin su ,kallon juna sukayi ,se ta saki muemushi tace "Alh Tanko ne kisan sa sarkin naci tunda yaga hoton wata baby a wayana shikennan ya ɗaga hankalinsa kuma na faɗa masa cewar tawa ce bazan bashi ba amma ya dage ,akan ze bani ko nawa ne wai yarinyar irin wacce yakeso ne"ta karashe faɗa tana yamutsa fuska " haba ke ko Hajia mene ne idan har ze bada abinda kikeso aikawai kibar masa ,ga matan nan da yawa kuma kwanan nan Hajia saudah zata yi tafiya na tabbata zata samo mana wasu hot babies kinsan dai Hajia bata tafiyar banza" dukan su kallon Hajia saudah sukayi,cikin son tabbatar da Abinda Hajia Laura ta faɗa ,gyaɗa musu kai tayi cikin tabbatar wa tace " kema kinsan hana wa Alh Tanko yarinyar ze iya janyo mana matsala ,sune masu ɗaure mana gindi da yanzu zaman Niger yafi karfin mu kuna sane da sa idon da mutanen gari sukayi mana ko? to ki kwantar da hankalinki ,ki ta tsesa sosai kuma ai zaku iya riƙa anfani da ita ku duka biyun Kinga kenan riba kan riba" Hakane fa Kinga farko duk banyi wannan tunanin ba ,amma Hajia Sauda yaushe ne tafiyar ina fatan dai bazaki ɗauki lokaci a can ba?".

"Ehhh to kema kinsan badan Alh yace ze dawo daga Cyprus ba to babu abinda zesa na koma gida yanzu ,to bazan iya barma munafukar matarsa shi ba ,shegiya wai ita me kirki duk abinda zanyi mata bazata taɓa tankani ba ,shiyasa nagaji na ƙyaleta ,raina yana baci idan naga tana mammanewa Alh" tafaɗa cikeda takaici ,tsaki Hajia Laura tayi tace "wlh Hajia ni kina bani mamaki ,miye abun kishi ga namiji ,bayan macece keyi miki abinda ko rabinsa baze iya yimiki ba ,ni da zaki bi nawa ma da kinbar mata shi can su karata ,amma ina mamakin me wanan Alh yake da kike masa wannan son har kike ɓoyemana saninsa ,ko kina tunanin zamu iya kwace Miki shine,kinsani dai ni Namiji baya gabana ,idan ko kikaga nabashi kaina to inada bukatar wani abunne" Murmushi Hajia saudah tayi tace " komai zan faɗa baza ku gane ba mijina ba kamar sauran mazan bane shidin na dabanne ,ni ce nasan kan abuna ,saboda haka kudena ma tunanin wai zan barshi ,a'a ko ba komai auren ma wani kariya ne a tunanin ku idan da banda aure waye ze yarda da zaman nan da Nike ai dole za'a zargeni ,amma da yake Alh wayayyen mutun ne rayuwar sa irin na turawa baya tauyewa mutum hakkinsa tunda na faɗa masa dalilin zamana anan shikennan ya yarda so kudena wanna maganar ,jibi zan tafi amma bazanfi sati ɗaya ba dan a wannan karon inaso na shiga kauye saboda na samo mana yaran da suka dace"

da harara suka bita a kaikaice ,saboda sunajin haushin yadda take nuna mijinta yafi kowa, bayan wasu daga cikinsu a ta dalilinta suka rasa nasu auren........

Follow me on wattpad@damselfeedo

Real Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:1️⃣4️⃣

Ameerah#

A ƙofar gidansu ta tarad da wata haɗaɗdiyar motor tayi parking,da kallo takebin motar Kasan cewar baƙin galass ne bata iya ganin wanda yake ciki ,sedai a zuciyarta tana mamakin wanda yayi kasadar shigowa da mota lungun su dan ta tabbata se yasha wuya kafin yafita ,idan ma beyi Sa'a ba yaran unguwar zasu zane masa mota ,janye idon ta daga motar tayi tanufi shiga cikin gidan su " Ameerah" ta tsinkayi ankirata da wani calm voice ,faɗuwa taji gabanta yayi batasan dalili ba , addu'a tayi tana jiyowa dan ganin wanda ya kirata ,jiyowanta yayi dai² da isowarshi inda take ,dan zare ido tayi ganin kamar ta ganeshi ,shine mutumin nan da yataɓa neman ta shiga motan shi

" Kinyi mamakin ganina ko? ai nafi 2 hours a wurin nan ina jiran dawowar ki saboda na fahimci kamar bakison magana a titi ,any way sunana Muhsin ni managern banki ne ,inada mata da yara biyu kuma gaskiya a da banda ra'ayin karin aure saboda gwargwado matata tana kula dani amma tunda na ganki naji na kamu da sonki ,shiyasa ranar da kika ƙi yarda nakawo kiga se nabiyo bayanki har seda naga unguwar da kike ,fatan zan samu karɓuwa a gareki"ya ƙara sa yana kafeta da ido.

Kamar yadda yake kallon ta ita ma kallon sa takeyi ,dan sosai yabata mamaki,koda bata taɓa soyayya ba amma bata tunanin haka tsarin yake ,daga ganinta bema nemi izinin ta saurare shi ba kawai ya saki baki se zuba yake ,koda ace tanada ra'ayin soyaya ma yanayin tsarin sa beyi mata ba " ke nike saurare ranki ya daɗe " murmushi tayi wanda ya kasance kamar halayyarta ne yawan yinsa ,cikin sanyin murya ita ma tace " kayi haƙuri baza'a barni nayi soyayya a yanzu ba" tana faɗa masa bata jira jin me zece ba kawai tayi shigewarta gida kasancewar dama a bakin zauren gidan suke.

Murmushi Muhsin yayi dan ze iya cewa ya hango alamun nasara dan ya fahimci yarinyar xatayi sauƙin kai,bin gidansu yayi da ido a ranshi yace "tabbas masu kyau na irin wuraren nan wanda talauci ya boye a gansu bare har a ga kyansu yanzu wannan da ace gidan masu kuɗi take aikam da se irin yaran masu kuɗi nan zata aura" matarshi ya koma se gashi yafito da wata leda a hannunsa irin na shopping dinnan ,duk da dai kayan ciki kamar bamasu yawa bane saboda ledan ba wata babba bace ,waige² yafarayi dan neman yaron da ze aika,cikin Sa'a ko ya ga wani yaro ya fito daga wani gida kiran yaron yayi ya basa ledar yace " shiga ka kaiwa Ameerah kaji"
Chapter 10 · 0% Book details