← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutuwar zaune Rufaidah tayi dan bata taɓa tunanin zuwan ranar da zatace tana son abu Mama tace a'a ba ,a iya saninta duk abinda takeso shi Mama keyi koda kuwa hakan be gamshe ta ba "kai wasa Mama take wata ƙila dai saboda bata cikin kwanciyar hankali ne shiyasa tayi mata hakan dan ta kula tun abinda ya faru ɗazu har yanzu bata dawo dai² ba ,kema Rufee meyasa zakiyi mata wannan maganar bayan kinsan bata cikin natsuwa"duk zuciyar ce ke faɗa mata wanann ,kuma ta yarda da hakan ,dan haka bata wani damu ba ,takoma ɗakinta tayi kwanciyar ta ,se kuma abinda ya faru tsakanin Hajia saudah da Meerah ya dawo mata ,abun ya matuƙar bata mamaki ganin irin firgicin da dukansu suka shiga anya basun san juna bane ? "Kai ina ma Mama zata san wannan matsiyatan tun da ta san babu wani alaka ma da ze iya shiga tsakanin su ,to ko de mayyar ce? Idan kuma hakane da gaskiyar Ya Mu'aisam da itace zata fara cinyewa ,amma dai bara tagani wlh idan har gobe Mama bata dawo hayyacin ta ba to se tasaka an kama Meerah kai ba itaba ma har shegun iyayen ta "da wannan saƙe-saƙen har bacci ya ɗauke ta .

Meerah#

da wuri tagama shirinta ,bayan tagama aikin gida kamar yadda ta saba ko wace safiya bata fita se ta ragewa Aunty aiki ,dawo wa tayi ta zauna tana jiran fitowar Aunty saboda tanaso taji ya sukayi da Yaya, ya amince ko kuwa ,ganin lokaci yana ƙure mata ,se duba agogon wayarta takeyi ,daga ƙarshe dai ta yanke shawarar zuwa ɗakin su ta duba su ,a bakin kofa sukaci karo da Aunty , murmushi sukayiwa juna suna shigowa ɗakin "nasan ko wani bacci bakiyi ba ko kina tunanin ko Yaya ya amince ko a'a"wlh kuwa Aunty ,inajin tsoron yaki amince wa ,kinsan wanann mijin naki se ke "dariya tayi tace aikuwa dai dan gashi na tsara sa ya amince harda baki kuɗin abun hawa "kai Aunty da gaske nikam ne kika faɗa masa haka? Banyi tunanin ze amince cikin sauƙi ba " Meerah kenan duk yadda kike tunanin Namiji ,to ba komai bane a gaban matar sa sedai idan ita ɗin batasan kimarta ba ,bayan ya dawo ne dai yaganni kamar ina cikin damuwa ,shinefa yaketa tambayar menene ,nace masa babu komai ,dana ga ya damu kansa shine nace " wlh Yaya wani ,karambani nayi ,se yanzu ne nake nadamar yinsa batare da na ji ta bakin ka ba ,inajin tsoro bansan tata zaka ɗauki al'amarin ba ,wato gani nayi Ameerah ko yaushe tana zaune a gida ita ba karatu ba kuma ba sana'a ba ,se zaman banza shi ne ,ranar da naje gidan ƙawata na sameta tana koyar da yara dinki ,se nayi sha'awar itama Meerah ta koya ,nasan gaba zeyi mata anfani a rayuwar ta ,to shine fa take zuwa kullum da safe zuwa karfe 2 ta dawo jiya ma da kadawo baka sameta ba tana can ne ,naji tsoron na sanar dakai ne ,saboda bansan ya zaka ɗauki zancen ba ,amma dai dan Allah kayi haƙuri ,karkace zata dakata da zuwa"

Shiru yayi ,yana saurare ,kafin ya ja dogon nunfashi yace " Haba Nafisa wanann ai abun karuwa ne menene na ɓiyemin kuma ,bawai zan hana ta bane ,amma baki ganin illa a cikin sammakon da takeyi tana fita sanin kanki ne se tayi tafiya kafin ko zata samu abun hawa ,banason wani abu ya sameta kamar yadda ya samu Maryam " Insha'Allah Yaya babu abinda ze faru se Alkhairi kaaide kayi mana fatan nasara " to shikennan Allah ya temaka yabada abinda ake nema" kinji fa yadda muka yi dashi ,har tabada kuɗin abun hawa".
Rungume ta Meerah tayi cike da farin ciki tace " Aunty Nagode miki sosai wlh naji daɗi , Insha'Allah babu abinda ze faru yanzu Bara naje nayi masa godiya ko ,dama tun ɗazu na shirya ke nake jira"
a dawo lafiya Aunty tayi mata ta fita.

Amamakin Meerah tana fita daga gidan ta samu motar Manager a kofar gida ,tabbas ta gane motar amma se tayi kamar bata gansa ba taci gaba da tafiyar ta , seda takai bakin titi tana shirin tsaida mashin se taga yayi parking a gabanta ,ɗauke kai tayi taci gaba da tafiya ,da sauri ya fito daga motar yasha gabanta " haba Ameerah wai ya kikeso nayi da kaina ne sam kin ƙi bani damar da zan samu kusanci dake ,ki yi haquri idan na takura miki amma wlh lefin xuciyata ne ina sonki ,dan Allah kixo kishiga na ajiye ki inda zakije se mu karasa maganar a mota" ganin idan bata shiga ba zeci gaba da binta se kawai ta bi bayanshi da kansa ya buɗe mata motar ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ,seda suka ɗauki hanya yace " ina muka nufa? dama bakasan inda zanje ba amma shine ka dage seka ɗaukoni " Murmushi yayi yace " to ayi hakuri ni ai banki mu zagaye garin nan a haka ba saboda haka idan ma baxaki faɗa ba zanci gaba da zagaye dake " aikin naka fa? Uhmmm zan kira nace yau Madam ta hanani fitowa" bata lakacin da murmushi ya suɓuce mata ba ,harseda haƙoranta suka bayyana " haba koke fa ,kina da kyau idan kika haɗe fuska to ya kike tunani a lokacin da kikayi dariya? Cike da son kauda zancen tace " unguwar da ka ganni ranar can zaka kaini" kallon ta yayi cike da son karin bayani ,se dai ta kauda fuskarta gefe saboda Allah yagani bata son yawan shige matan nan da yake yi ,dan ita fa babu tsarin auren me mata a rayuwarta ,sedai abinda Allah ya rubuta a gareta.
Har bakin get ɗin gidan yakaita,duk da ya dage akan se ya shiga da ita ,daƙyar ta samu yayi parking a wajen ,a xuciyar ta take ayyana dan besan matsayinta a gidan bane ,kafin tagama tunani taji ya sakomata tamabaya " me kike zuwa yi a gidan nan ? Da sauri ta kalleshi ,seda ta buɗe murfin motar kafin tace " Aikatau" daga haka ta rufo masa kofar ko waigowa batayi ba tayi knocking me gadi na buɗe mata ta shige da sauri kamar zata kife , A harabar gidan ta samu Mu'aisam yana karanta jarida ,sauri ta kara dan bata so ya ganta ,seda takusa shigewa taji saukar muryasa akanta " ke zo nan..........

Comments and share pls

Real Bazamfaria ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:1️⃣9️⃣

jiyowa tayi cike da addu'ar Allah yasa ba da ita yake ba ,kusan hakanne dan hankalin sa na kan jaridar da yake karatu ,bama zaka taɓa tunanin shine yayi magana ba "wata ƙil nice banji da kyau ba ,dagani ma beyi magana ba" abinda zuciyarsa ta gaya mata kenan aiko se taci gaba da tafiyarta ,har ta shige party ɗin da take aiki, hakan da tayi ba ƙaramin ɓacin rai ya saka shi ba ,idan akwai abun da ya tsana befi yayi wa mutum magana yajishi kuma ya share shi ba ,wanda ya kula ɗabi'ar yarinyar kenan duk lokacin da zakayi mata magana ko tambayarta kayi se tayi kamar ma bata ji ka ba "amma zan koya mata hankaki ai " daga haka yaci da abinda yake yi

da sallama ta shiga falon ,sedai kamar kullum bata isko kowa a ciki ba ,dan haka kawai ta fara aikin ta ,tana cikin aikin ne Hajia saudah ta fito daga ɗakin Abba turus tayi tana kallon ta ,maganar da Abba yayi ne yasaka ta saurin amsahi cikin rawar murya " Saudah kema Kinga abinda nagani ko? cikin rawar Murya tace " me kenan? Nuna mata Meerah yayi yace nasan kema Kinga kamar "a'a ni banga komai ba ,kamar wa kuma kagani gareta " wlh Hajia ina ganin ta na tuna da Birrester,badan nasan da ya mutu be bar kowa ba kuma ba dangine da shi ba to da se nace tabbas wannan ɗin jinin su ce "kai Alh idon ka ne kawai yagane maka haka ,to taya ma wannan zata zama jinin su bayan Rufaidah ta faɗa min a titi take yawon bara shiyasa ma ta temake ta ,kaima kasan wannan batayi kama da masu arxiƙi ba " hakane kuma ,amma dai ni kam gaskiya naga kamar su ,ke bani ba ma nasan ko Hajia Ammi ta ga wannan zatace suna kama"
Cikin fushi tace " to ko suna kama dai bance wata can ta rika shiga lamarin gidana ba ai koda basuyi kama ba zata iya cewa sunyi tunda har kai kace ,kasan ta da muna furci ,nikuma bazan faɗi karya kawai saboda na faranta ran wani ba ,kuma wlh wannan ƴar aikin dai tawa ce babu wanda ya isa yayi min shishigi a kanta"

Shiru yayi yana sauraren ta ,mace kamar me aljanu to menene abun faɗa anan ,tun da ba wani yace xe ɗauke yarinyar yakai wani gu ba ,sanin idan yayi Magana zasu iya seda hali a gaban Meerah se kawai yace " to nide asamu a shiryamin abun kari da wuri na faɗa miki zuwa 10 fita zanyi bara naje mugaisa da su Ammi ko ? Taɓe baki tayi tace" banda damuwa da wanan kuma salon nayi magana kace na cika kishi kaidai wlh Alh kaji tsoron Allah ,mutum ya girma amma besan ya girma ba ko yaushe se rawar ƙafa akan mace mtsswww" ta barshi tsaye a wurin ,ita dai Meerah al'ajabi ne ya kamata ,a zuciyar ta take ayyana wane irin mutum ne Abba ,shikennan shi beda kataɓus a lamarin iyalin sa ,a fuska dai kaga cikakken mutum amma a zuci ba haka bane" ganin Hajia Sauda ta shige cikine ya saka Meerah saurin duƙawa tana gaishe shi " yauma dai babu lefi ya amsa mata fuska a sake "duk da yanayin da yaɗan sauya ,da alama abun da Saudah tayi ne ya taba zuciyarsa sedai yakasa nuna hakan a gabanta.
Chapter 16 · 0% Book details