← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 43

Sashe 27

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zafin rai Rufee ta fincikota " ke dan ubanki har kin isa ki gayamin magana ,ina kyau yake anan ,me kike taƙama dashi? Maimakon Meerah tasakeyin magana se ta harɗe hannu tana kallon ta , Mu'aisam kuwa shiga yayi mota yayi mazan sa kamar ma besan abinda sukeyi ba , Rumaisa ce tayi saurin shiga tsakanin su tana jan Rufee " haba sis Rufee wannan ai girmanki kike zubarwa ,taya za'ayi ki tsaya sa insa da ƴar aikin ki ,kuma ina lefin wanda abun alkhairi ya sameka yataya ka murna?wanann ai kin zubar da girmanki ne a gaban ƴar aikin taki"a fusace Rufee ta fixge hannu ta tare da jan dogon tsaki ta shige mota ,haƙuri Rumaisa ta bawa Meerah tare da miƙa mata ledar da Mu'aisam ya bata ,ƙin amsa tayi dukda batasan wanda yabata ledar ba a tunanin ta ma ko Ruimasar ce ta kawo mata wani abun ,da taga ma ta matsa mata se ta amsa se kawai tayi tafiyar ta da sauri tana ɗaga musu hannu ,shiga Mota itama Rumaisa tayi tace" yaya tafaƙi amsa" batare da ya kalleta ba yace fita kisamu yaro ya kaimata ,tunda idan tabarshi me za'ayi dashi ko kina so ne? Ƙunshe dariyar ta tayi tace" a'a yaya ko ina so ai bazemin ba tunda nafita tsayi kuma nasan length nata ka ɗauko " jin maganar da suke yasaka Rufee fincikar ledar tana buɗe wa ,ganin tsala-tsalan rigunan da ke ciki yasakata kafeshi da ido tana masa kallon tuhuma ,yi yayi kamar be ganta ba ,ya kunnan mota ze tayar ,fixge key din motar tayi cikin fushi tace " Mu'aisam me kake nufi da siyowa wannan matsiyaciyar tsadaddun kaya ,nifa ban gane ba wani muna funcin kuke ƙullawa ,taya ma kasan gidansu ,dama nasan ƴan uba miyagun bayi ne ,to wlh koma me kuke ƙullawa baku isa ba ,dan nafi ƙarfin wulaƙancin ku kuma kubari mukoma gidan zan sanar da Abba shine yahaɗa auren nan idan baze yiyu ba tun wuri a warware.

"haba sis Rufee me kike faɗa haka ,ina kome yaya yiyuwa Ameera to saboda ke ne tunda zaman ki takeyi besides ma yaga tana buƙatar kayan ne kina ganin yadda take zuwa aiki a duƙunƙune "ɗaga mata hannu tayi tace "dakata bana son muna funcin kinayi kamar bakisan komai ba ,dama shiyasa kikace zakizo gidan wlh da nasan nan ze kawoni da gara na hau Napep na tafi gida dan yagama tozarta ni ,ita kuma zata zo ta sameni ne idan ma wani asiri ne tazo dashi to wlh a banza ,dan batada muhalli a gidan mu " ke Rufaidah bana son rashin hankali ,haba ke baki gajiya ne kinbi kin dameni da surutun ki marasa amfani ,me kike tunani , me zuciyar ki ke baki ko bansan ciwon kaina bane wlh kar ki kaini bango ,yanzu na ɓaɓɓalaki anan sakaryar yarinya ,duk haukar da kikayiwa ƴar mutane kinji na ce wani abu sauƙin ta ma itama ta iya tsiwar irin naki ,kinja yarinya ƙarama ta faɗa miki magana kuma hakan be isheki ba ,kinzo nan kinayi mana hauka ,duk ranar da kika ƙureni wlh zan baki mamaki"

Aiko Rufee se ta fashe da kuka ,abunka da ƴar uwa se tausayin ta ya kama Rumaisa kuma se taga rashin kyautawar Mu'aisam ,sedai shiru tayi batace komai ba ,haka suka ci gaba da tafiya sheshekar kukan ta kawai ke tashi a motar ,har suka kai gida.........

Manage

Comments and share pls

Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:2️⃣7️⃣

*_Wannan page ɗin* *wa_* *dukkan* *_Mabaraciya fans ne Nagode sosai da soyyayar ku Haƙika comments naku nasakani nishaɗi* *one* *luv guys* ❤️_

tunda suka dawo Mu'aisam yake tunanin hanyar da xebi dan dakatar da Meerah daga bin Hajia saudah,sedai yasan beda wani mahita matuƙar iyayenta suka amince da ta tafi ,amma ai akwai mafita guda wacce yake tunanin itace zata iya hana Meerah fita daga Kaduna ,Aure ne kawai xe hanata barin garin dan yasan cewar duk mijin da zata aura baze barta sake fita ba "to waya faɗa maka ma tanada saurayi? Zuciyarsa ta tambayeshi ,tunawa da Muhsin da suka gani ɗazu yazo wurinta ,yasakashi jan dogon tsaki "daga ganin wannan irin ƴan Yahoo ne ba auren yarinyar xeyi ba ,sekuma ya tuna da kalaman Rufee da tace sedai idan lalata xeyi da ita "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un"ya furta dan jin irin faɗuwar gaban da ya riskeshi.

Rumaisa kam lokacin da tafaɗawa Ammi abinda ya faru lokacin da suka fita ,dariya kawai tayi tace " bansan me yasa Hajia Sauda ta tusa wa yaranta rashin ƙaunar talaka ba ,bayan ita dinma ,bawani arziƙine dasu ba hasalima koda Alh ya aurota , basuda komai business ɗin da take yi ne take riƙe iyayenta dashi dan kuwa duk sun tsufa ,da ta samu Alh ne abubuwan suka fara walwale mata ,kuma a haka take ƙyamar talauci ,kai Allah dai ya kyauta " nifa Ammi ko kamar akwai abinda nake hange a game da yaya ,se nake ganin kamar son yarinyar nan yake ,idan ko hakane ai Meerah ta zama abun tausayi ,ina ita ina kishi da sis Rufee?".

Murmushi Ammi tayi irin nasu na manya tace " Rumaisa kenan to inbanda ke da abunki ,ina ruwanta da Rufaida ina mijine dai kuma duk matsayin su guda a wurin shi ,kuma da ya samu ma mace me biyayya gaskiya ,dan nide tunda na fara ganin yarinyar naji ina son ta a zuciyata ,musamman ma da takeyimin kama da matar Birrester ,itama nasan Allah xe bata mijin da ze kula da ita ba dole se Mu'aisam ba

"hmmm amma Ammi nifa nayi mamakin ganin Mama tayi sanyi a maganar auren nan ban taɓa tunanin zata amince cikin sauƙi haka ba ,anya ba wani abun take shirya wa ba? Ke Rumaisa banas ofon shiga abinda be ganoki ba ,kiyi mata kyakkawan zato mana ,ai mutum baze riƙa girma yana cin kasa ba ,kuma dama ƙiyayyar saboda ni ne ,nikuma sam bata gabana ina nan dai inayi masa addu'ar zaɓi mafi alkhairi a rayuwar sa ,dan nikam bazanyi shishigi a lamarin Ubangiji ba" har Rumaisa zata sake magana Ammi ta katse ta da faɗin " dare yayi kije ki kwanta ,ina morning lectures kike da shi? tashi tayi tace to Ammi seda safe da wuri kam zan fita ga Amrah ma tace zata zo goben "to shikenan Allah yabamu alkhairi.

Rumaisa#
Wannan daren kam kwanan baƙin ciki tayi musamman da ya kasance bata da wanda zatayi sharing problems nata dashi ,dama ace abun da Mama ke so ne ,tasan da ita ce zatayi mata yaƙi akan wannan wulaƙancin ,to ita ɗin ma ba so takeyi ba ,dan haka ta yanke shawarar kiran Aunty Khadija gobe dan tasan ita bazata ƙi ta auri Mu'aisam ba ,da wannan tunanin ta samu kwana (bacci) ɓarawo ya ɗauke ta.

Meerah#

tun da ta koma gida yanayin ta ya sauya ,komai cikin sanyin jiki takeyin sa wanda har se da Aunty ta kula da hakan ta tambayeta " waike me ke damunki ko jikin ne "yaƙe tayiwa Aunty tare da faɗin " me kika gani? " Ai naga duk kinyi wani iri ne kamar kar ki fita rakiyar mutanen nan ,ko sunyi miki wani abu ne? ".
"Hmmm Aunty wai ina yarinyar Hajia saudah , kinsan na faɗa miki cewar itama bata da mutunci ko?to wai ansaka musu lokacin aure ,ita da babban yaron gida ,ai na taɓa baki labarin sa ko? "Mu'aisam? Ehhh shifa ashe baki manta ba nan da wasu kwanaki ma za'ayi bikin, ta ƙara sa yanayin da ke bayyanar da cewar abinda ta faɗa ya taɓa xuciyar ta " ƙureta da kallo Aunty tayi kamar tana nazarin ta tace " to ke miye Matsalar ki da hakan? ba ɗan uwanta bane " hakane Aunty kawai dai Ammi ce ta bani tausayi dan sam ɗanta beyi dace da mace ta gari ba and Kuma inajin tsoron sakamakon Hajia saudah ya sauka akan jikokin ta ,Kinga har yau dai Ammi ce zata kwana a ciki mace me kirki da ita " Meerah kalleni nan " ɗago kai tayi ta kalli Aunty " akwai wani abu ne tsakanin ki da Mu'aisam ko? zaro ido tayi tana nuna kanta cikin rawar baki tace " ni kuma Aunty ,miye tsakanina dashi ,mutumin da ko magana be taɓa shiga tsakanina dashi ba ,hasali ma haushin sa nikeji ya cika kallon tsiya ga kuma shegen izza"

Dariya Aunty tayi tace" kina son Mu'aisam Meerah sedai yarinta ya hana ki gane hakan "kai tafara girgizawa ,idon ta tana kawo ƙwallah " a'a Aunty meyasa zaki faɗi haka kinfi kowa sanin wace ce Meerah ,babu soyayya a gabanta ,idan ma akwai ,ai tasan wanda ya dace da ita ,ba wannan ba "hmmm Ameerah sanin halinki da nayi shi yasa na faɗi hakan ,duk da ban taɓa ganin Mu'aisam ba amma tabbas nayi Miki kwaɗayin samun sa a matsayin miji" hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa ne suka samu damar zubowa ,cikin Muryar kuka tace " wannan karon ,kam xuciyar ki bata baki dai² akaina ba Aunty ,dan ko ba Rufaidah bace zaɓin sa ,to baze taɓa zabana ba ,idan ma ya xaɓeni kinsani ni bazan taɓa amince masa ba dan babu aure a tsakanin mu kinsani fansace ta kaini gidan su , taya zan so ɗan gidan kuma na torzata matar mahaifin sa sam hakan baze faru ba ,kima Dena wannan zancen "ta tashi da gudu ta shige ɗakin ta.

Dariya kawai Aunty tayi dan ta fahimci soyayya ce kawai a zuciyar Meerah kuma ta Mu'aisam ,wanda ƙuruciya ya hanata ta fahimci hakan ,ga kuma kishin Rufee da ta fahimta a xuciyarta " Allah ya zaɓa miki nafi alkhairi Ameerah" Aunty tafaɗa ,tana naɗe tabarmarta dan koma ɗaki itama.

Washe gari ta tashi da ɗan ciwon kai saboda kukan da tayi a daren jiya marar dalili ,haka dai ta shirya dan zuwa aiki ,kamar yadda tayi alƙawari
Chapter 27 · 0% Book details