← Book details Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 43

Sashe 34

Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kinyi shiru Ameerah ,baki so ko? Kiyi hakuri Bara ya dawo zan sanar dashi ya maida musu kayansu dama seda na faɗa masa mutuƙar baki amince ba to baza'ayi miki tilas ba " still dai Meerah bata ce komai ba ,haka Aunty ta ƙarashi surutun ta tagaji ta shige ɗaki tabar Meerah nan zaune

Ameerah kuwa banda zagaye babu abinda Kanta keyi tunani takeyi shin mafalki ne ko da gaske wai aure ta nan da 2 weeks to waye mijin? Shine tambayar da zuciyarta keyi sedai bakinta yaki bata haɗin kan da zata tambaya lokacin da Aunty ke sanar da ita ,haka ta ci gaba da zama wurin har aka fara kiran sallar isha' har aka gama bata motsa ba se kusan 9pm ta samu daƙyar ta ja ƙafarta tayi alwala tayi sallar isha'i da batayi ba ,tana sallamewa ko addu'a batayi ta zame a wurin ta kwanta ,tama rasa wane irin tunani zatayi ,a wannan yanayin Aunty tazo kiranta wai yayanta yana neman ta ,ko ba'a faɗa mata ba tasan dai zancen ɗaya ne ,dan haka bata ce komai ba tabi bayanta .

Cikin dasashiyar murya ta gaishe shi kamar tayi kuka ,wanda har se da yanayin Muryar ta yasa ya ɗago ya kalleta " bakida lafiya ne? " . Ya tambaye ta ,kai kawai ta girgiza masa alamar a'a dan haka ya soma kora mata bayani duk da dai maganar da tayi zato ita dince " Ameerah na bada auren kine a bisa wani dalili nawa ,kuma ina tunanin hakan xe temaki rayuwar ki ,kuma Auntyn ki ta shedamin cewar kina son sa ,kuma zakiyi daraja a gare su ,ina gaya miki girma da darajar iyayensa ne yayimin kwarjini na kasa Musa musu ,xe fita wajene wani aiki ya samu a can kuma matar shi tace ita bazata bishi ba saboda ita ma tana aikine a nan sukuma iyayensa sukace basu amince ya fita babu mata ba ,dan haka yazo neman auren ki ,da farko ban amince ba seda iyayen sa sukaxo da magiya,nace se nayi shawara da Auntyn ki ,itace tace na amince a ganinta wani dama ne zaki samu da zaki inganta rayuwar ki kema kuma zakiyi karatun da kike so a can ,amma karki cuci kanki idan baki amince ba" Yaya wai waye ? Kafin yabata amsa Aunty tace " Manager ne Muhsin Abban su Hanifa " shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhari a garemu "jin furucinta ya matuƙar faranta ransu dan haka sukayi ta saka mata albarka tare da fatan wannan auren yazama silar farincin ta na har abada

Ammi.........

Comments and share pls

#Real@Bazamfaria❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
   ( *On* *word* *together* )

*MABARACIYA*

*Story* *and* *writing*

    *By*

*FIDDAUSI* *SANI*
      (damsel feedorh)

🅿️:3️⃣2️⃣

Ammi
Har suka koma gida babu walwala a tare da ita ,har se da Rumaisa ta fahimci hakan " Ammi ko wani abu ya faru ne a fitar da kukayi? Kallon Rumaisa tayi tace " me kika gani? Kawai dai naga kamar kin shiga damuwa ne " babu komai ,Rumaisa ai har gidansu Ameerah muka tafi kinga alewa ma anbamu wai na auren ta nan da sati biyu masu zuwa " washe baki Rumaisa tayi tana duba alawan " kai Masha'Allah,amma wlh nayi mata murna zata huta da bautar wasu tayi auren ta duda kam tana da ƙarancin shekaru Allah ya sanya Alkhairi kusan tare da na su Yaya ma kenan aikam zamuje mata biki"

Ammi dai bata ce komai ba se bin ta da ido ganin yadda take ta washe baki.

Haka Meerah ta kwanta a wannan daren badan ta na tunanin bacci xe iya ɗaukan ta ba se juyi kawai takeyi tarasa dalilin Muhsin na yi mata wannan aika-aikar dan ita bata wani yarda cewa uzurin tafiya ne yasaka shi yin haka ba Idan ma haka ne kamata yayi ya tuntuɓeta kafin yazo wurin iyayenta ,taso ta kira shi amma setaga rashin dacewar hakan tunda har shi be ne Meta ba to ita ma bazata neme shi ba kuwa ko hakan yana nufin har zuwa ranar da za'a kaita gidan shi.

Biki se ƙara kankama yake shirye shirye akeyi a ɓangaren Ammi dan suna saka ran fara saukan baƙi a gobe da bikin yayi saura sati ɗaya ,dan haka duk wasu ɗakuna da ke rufe a sashen ta ta saka an buɗe an gyara su fess , ɓangaren Hajia Sauda kam sha'anin gaban ta kawai takeyi dan tabarwa Hajia Laura wuƙa da naman yi duk abinda take ganin mafita ne gareta.

tunda Muhsin ya kawo kayan auren besake zuwa gidan su Meerah ba kuma be nemeta a waya ba dan yana tsoron rikicin da zata iya yi masa ,ita kuma hakan da yayi se ya ƙara ƙona ranta ,tafara tunanin kawai auren rashin mafita ne zeyi mata tunda matarsa ita tanada abunyi tace bazata bishi ba ,shine yayi anfani da talaucin su yazo wurinta ,tana wannan tunanin hawaye yafara bin fuskanta ,tausayin kanta takeyi ,wannan wane irin aure ne to zatayi ace baze ma kira yaji me take bukata ba ,juyi kawai take kan katifar batasan shigowar Aunty ba sedai taji ta rungumota daga kwancen da take tana share mata hawayen fuskanta ,ai kamar jira take se ta sake fashewa da kuka me ƙarfi ,Aunty batace da ita komai ba se tapping bayanta da takeyi alamar rarrashi seda ta fara ajiyar zuciya alamar tayi kukan me isarta kenan ,kafin Aunty tafara yi mata magana " menene damuwar ki Meerah,idan auren nan ne bakiso wlh se a fasa ni bazan lamunci ganinki cikin wannan yanayin na damuwa ba kece da kanki fa kika ce kin amince ko Muhsin ɗin yayi miki wani abu ne?".

"Aunty yau kusan sati ɗaya kenan fa da ya kawo kudin auren sa gidan nan ,amma ko a waya be nemeni ba bare yazo gidan nan me hakan ke nufi? "Baya nufin komai Ameerah Yakamata kiyi masa uzuri ,jiyama ya kirani yake sanar dani be samu zama bane yana cuku-cukun tafiyar ne ,amma idan ya samu lokaci yau ze shigo ,shiyasa ma nazo na tambayeki ko akwai abunda zakiyi na tarbonsa se gashi na sameki kina kuka " haba Aunty beda number na ne ko me ni ban isa ya kira ya sanar min bane komai ,nifa dama nasan dalilin da yasa ya biyo ta wurinku kenan to ni yayi zaman sa bana buƙatar zuwan sa ya jira se ankaini gidan sa yanzu ma barin gidan nan zanyi "

Da ido Aunty ke binta ,dan ganin sabon halin da take ƙoƙarin takitawa kanta ,har tagama surutan ta ,tashi Aunty tayi tace " nide na faɗa miki ze zo kuma zaki fita.

Misalin ƙarfe 5 na yamma kuwa ya iso gidan ,be kirata ba se ya kira Aunty ya sanar da ita zuwan shi ,haka ta tasa Meerah ta sauya kayan jikin ta ta fito ,kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa idonta sunyi ja sosai ga kumburin da sukayi daga sama alamun ta daɗe tana kuka ,a zaune ta sameshi cikin zauren gidan ,an shimfida masa dadduma ,tasan aikin Aunty ne dan haka ta samu wuri daga dan nesa kaɗan ta zauna ,bata ce masa komai ba se ma binsa da ido da takeyi " Subhanallah Ameerah badai zancen auren mu ne ya sanya ki shiga cikin wannan yanayin ba ,Kinganki kuwa? daga jin yadda Muhsin keyi mata tambayar kasan hankalinsa ya tashi ganinta cikin wannan yanayin ,share hawayen da suka zubo mata tayi cikin dasashiyar murya tace

"Abban Hanifa me ya kawo ka wurina da har kake tunanin zaka aureni ta hanyar da ka biyo ?" Soyayya" shine amsar da yabata a takaice ,wani irin Murmushi tayi me hade da hawaye wanda ke bayyanar da irin kuncin da zuciyarta ke ciki ,tace " Soyayyah tanada matuqar tasiri,tasirinta yana dawwamane a ckin zuciya yanada tsantsar karfi yana kuma sanya zuciya ta jigata qarfin tasirinsa yawuce misali d hasashe.idan soyayyah tasamu tanada matuqar tasiri haka kuma tana mallakar wani qarqarfan qarfi ne Wanda zaizamo tubalin dake manne d ruhin dan Adam, ina faɗa maka ma'anar soyayya ne ,to a tunanin ka taya za'a mallaki wannan karfe? dole hanya ɗaya ce idan kana so ana sonka , meyasa kai baka yi wannan tunanin ba kafin ka samu magabatana? ko da yake bazakayi ba saboda ku masu kudi a koda yaushe nasara kuka sani ba faɗuwa ba ,amma karkayi tunanin zan aure ka saboda soyayya ne ko ɗaya auren biyayya zanyi maka domin bazan iya cewa a'a ga magabata na ba ,saboda haka kayi tunanin yadda zaman biyayya yake saɓanin na soyayya ,idan zuciyar ka ta amince a haka zata zauna da ni shikenan ,tawa ƙaddarar kenan "tana gama faɗa ta sake fashewa da kuka .

Duk da bata fito kai tsaye tace bata son shi ba amma kalaman ta sun isar da sakon ta zuwa gareshi ,tabbas da ze iya haƙura da ita to da ya barta sedai Allah ya sani so ne yake mata na gaskiya kuma yana da tabbacin itama watarana dole zata so shi ,dan haka duk wannan kalaman nata baze dameshi ba , handkerchief ya Ciro daga aljihunsa ,batayi tsammani ba se ganin sa tayi tsugune a gabanta yana share mata hawayen fuskan ta ,wani irin baƙin ciki taji ya sake lulluɓeta,lallai se yanzu take nadamar sake masa da tayi tun farko ga abinda yayi mata yanzu

" zan shiga daga ciki dan naga kamar baka da abun faɗa '' Murmushin gefen baki yayi yace " dole zan rasa abun faɗa tunda kin ƙaramin ƙarfin gwiwa tare da tabbacin cewar zanji dadin rayuwa da ke a matsayin mata ta ,na gode ma Allah da har kika fahimci menene soyayya da abubuwan da ke samar da ita ,hakan yabani tabbacin cewar zaki soni watarana ko da a yanzu ma bazan iya cewa baki so na ba ,kiyi haƙuri Ameerah kisani Allah ne yayi keɗin rabo na ce kuma duk kiyayyar da zaki nuna baze saka a fasa abinda Allah ya rubuta ba mace bata auren mijin da ba rabon ta ba ina sonki ,kuma ina fatan kema ki so ni. Nazo ne domin naji abubuwan da kike da buƙata ,kiyi hakuri da jina shiru da kikayi".
Chapter 34 · 0% Book details