Sashe 32
Mabaraciya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"mtswwww ko bakace ba dama ai zan tafi ,se kije kibiya bokan ki Zainabu burinki ya cika Alh ya wulaƙanta ni a gabanki " ita dai Ammi batace komai ba se ma binta da tayi da ido har ta fice ,kafin ta dawo da hankalin ta kan Alh ,dogon nunfashi taja tace " Alh se nake ganin kamar Sauda ta fimu gaskiya ,itace da ƴa ya kamata ace anji ta bakinta tunda auren na gida ne me ze hana katafi kuyi shawarar abunda takeso da kaga maybe akwai abinda bataso ta faɗa a gabana ,se ka bata kudinta ta siya " da kata Ammi yanzu nan kika faranta min rai da irin amsar da kika bata hakan ya tabbatar mata ai da ba tsoron ta kikeyi ba kawai neman zaman lafiya ne ,saboda haka yanzu ma abinda nayi niyya shi zanyi ,ke ce uwar ango kuma uwar amarya inda mutun ci ,saboda haka babu ruwanki da duk wani kurari da zatayi ,ina so zan fita zuwa karfe ɗaya idan anyi Sallah ki shirya se na ajeki gidan Bilkisu na kwana biyu banje na dubata ba ,idan kuma ɗanki ze kaiki to ni se na tafiya ta " haba wane ɗana ga mijina ,kaine dai zaka kaini ,dan nasan tafiyar zatayi armashi ,amma da kanka zakayi driven gaskiya ,inaso ne na tuna ma na baya" dariya yayi yace " kardai maganar Saudah ta tabbata fa ,Ammi abar tsohon nan ya huta mana " hararan wasa tayi masa tace " ni dai a Idona mijina baya tsufa haka nake ganinsa kamar ranar farkon mu " dariya yayi kawai bece komai ba.
a falo Hajia saudah ta isko Meerah har ta fara kakkaɓe²n ta ,tana ganin ta se ta ɗan sake fuskanta " a'a Aminatu har kinxo kenan? Ehhh Hajia kintashi lafiya? tafaɗi haka ne saboda nauyin da bakinta yayi batajin zata iya duƙawa ta gaishe ta kamar yadda takeyiwa sauran mutane ,dan idan akwai macen da ta tsana a duniyar nan to befi Saudah ba ,ba ƙaramin yaƙi takeyi da zuciyar ta tana ɓoye wannan ƙiyayyar ba da har take yi mata dariya ,ganin kamar ta tafi duniyar tunani se Hajia saudah tace " ko akwai abinda kike buƙata ne? Da sauri ta girgiza kanta " a'a Hajia babu komai kaina ne dai yake ɗan ciwo " ayya sannu to idan mun fita anjima se mubiya clinic ko " a'a ba sosai bane nasha magani kafin nafito " shikennan zaki iya ci gaba da aikin ki ta faɗa tana hawa upstairs.
tunawa tayi da gargaɗin Mu'aisam na kar ta yarda tabisu Hajia Sauda inda zasu je " to kodai wani wurin zasu kaini ne? to idan haka ne taya akayi shi ya sani mtsssw shegen iyayinsa ne da neman suna dan haka babu abinda ze hanani binsu kilama wata ƙungiyar suke da ita anan kd kodai menene zanbisu na gane wa idona''
Da wannan tunanin taci gaba da aikin ta.
Misalin 12:30 aka ɗauko su Nawwara daga school lokacin Ammi har ta shirya tana jirane kawai Ayi sallah su tafi ganin zasu bata mata lokaci kafin tagama shirya su ga Rumaisa tana school dan haka ta tura Nawwara tace ta kira mata Meerah ,lokacin ta gama komai suna kitchen tana kamawa Larai aiki ,kiran Ammi ya risketa ,duk tayi mamakin kiran amma bata bata lokaci ba tabi bayan Nawwara suna tafe tanayi mata surutu har suka shigo ,gaishe da Ammi tayi bayan sun gaisa Ammi tace " ko kina wani abune a can? A'a Ammi na gama tun ɗazu wani abunne? Ehhh dan Allah su Auta zaki shiryamin fita xamuyi banaso su ɓatamin lokaci Alh bayason jira gashi nasata ko Rumaisa zata dawo da wuri ne da se nabarsu gida dan ban shirya fita dasu ba " ayya babu komai Ammi bara na shirya miki su" ɗaki Ammi ta nuna mata ,dan haka su Nawwara suka bi bayanta ,tsaf ta samu ɗakin ko ba'a faɗa mata ba tasan ɗakin Rumaisa ne duba da komai na ɗakin irin na Rufee ne ,da kanta tayiwa Nawwara wanka kafin tace Nurain ya shiga yayi da kansa ,ko da ya fito har ta shirya ta shima shafa tayi masa , kafin ta gama sega Ammi ta shigo musu da kayan da zasu saka " kai Masha'Allah gaskiya kin gyaramin Auta da ke kece shiyasa ta bari kika shafa mata kwalli mu da ta raina ai bata bari mu shafa mata "dariya kawai Meerah tayi " anfara kiran Salla kiyi sallah se ki rakamu ko? da sauri Meerah ta kalleta ,ya zatayi da fitar su Hajia saudah ga ta Ammi kuma batajin zata iya yimata musu "ko akwai abinda zakiyi ne Kinga karki damu idan bakida dama ,nima naso mutafi ne dan zan biya gidan ƙawata da nabawa ordern lefen yayanku tace sarƙoƙi sun iso shine zaki tayani dubawa kune yan zamani zakifini sanin me kyau " to Ammi bara nayi Sallahr se na rakaki " murmushi tayi mata tace " to nagode"
A mota ma duk surutun da Nawwara keyi Meerah bata kulata ba saboda Abba da yake yi mata kwarjini har bataso ma tayi magana kasancewar sune a abaya Abba da Ammi a gaba
Batayi mamakin bakin gidan da Abba yayi parking ba dan bazata manta gidan da suka taɓa zuwa ita da su Rumaisa ba , tare da shi suka shiga cikin gidan Umma da murnar ta , ta taresu.
suna cikin gaisawa sega Amrah ta shigo ware ido tayi lokacin da tayi arba dasu da tabbatar dai su ɗinne se kuma tazo da sauri ta faɗa jikin Ammi cike da murnar ganin ta tace " Ammi dama seda nayi mafalkin ki jiya ashe kina hanya " itama dariya tayi tace" aiko dai kinganni ,kina lafiya ko? " Lafiya lau Ammi. Mimi fa?
"Kinsan se 3 suke dawo wa daga school" tashi tayi daga jikin Ammi ta tafi kusa da Abba ta ɗan rankwafa tana gaishe shi fuska a sake ya amsa yana tambayar ta school ,daganan dai hira ta barke tsakanin Abba ,Ammi da kuma Umma ganin haka Amrah tace " sis Ameerah ko? Murmushi tayi mata tana daga mata kai " to mushiga daga ciki kinji dan idan su Umma na wurin nan mantawa da kowa sukeyi" babu musu kuwa tabi bayanta dan dama duk jinta take a takure cikin su
ɗakin ta suka shiga tace" ina zuwa" ruwa da lemu ta kawo mata tana faɗin " kisha ruwa ,yau bamu dora girki da wuri ba , ni gwamma da Allah ya kawo ki dama yau Umma tace se nayi mata tuwo Kinga se ki tayani ko? Nan ma dai murmushin tayi mata " hararan wasa Amrah tayi mata tace " wai nikam ke bakya magana ne se murmushi ,last time ma fa har kika bar gidan nan banji maganar ki ba ,ke wannan ai bazaku shirya da yaya Mu'aisam ba dan ya tsani yayi magana kayi masa shiru ko kayi nodding ,ke kuma na fahimci kamar halin ki kenan ,ranar da kuka fara zuwa Allah na zata ko ke budurwar sa ce kundace sosai" rufamin asiri dan Allah wace Ni" ta faɗa tana zare ido ,aiko Amrah se ta fashe da dariya tace " aikinga yanzu kinyi magana ko? To ma miye na zare ido kika san ikon Allah " Kinga bar zancen nan ,ina cewa kikayi zakiyi girki muje kawai mu fara dan maybe ba daɗewa xamuyi ba naji kamar Ammi tace zamuje wani gida..........
*Typing yafara bani* *wahala saboda issues na* *school*
_Ku daure kuyi comments_ yadda _ya kamata maybe hakan yasa nariƙa squeezing time inayi muku_
Kunsan dai akwai rikici idan Hajia Sauda ta gane cewar Ammi ta fitar mata da yar'aiki
Comments and share pls
Real Bazamfaria ce ❤️
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
( *On* *word* *together* )
*MABARACIYA*
*Story* *and* *writing*
*By*
*FIDDAUSI* *SANI*
(damsel feedorh)
🅿️:3️⃣1️⃣
*Bansan ta* *ina zan fara ba but what I know is I offended ,kuyi haƙuri , insha'Allah na dawo kenan se mun kammala ,kuma ku daure kuyi comments domin na ƙara samun ƙwarin gwiwa, Nagode sosai da nuna soyayyar ku akan wannan littafin feedorh na matuƙar kaunarku* ❤️
Tsaf su Hajia Sauda suka shirya ,kafin ta aika Larai ta kira mata Meerah ,cike da girmamawa tace " Hajia kamar ta tafi gida dan gaskiya tun ɗazu banganta ba "Gida? kai a'a tasan zamu fita bazata tafi gida ba jeki kidubota dai "
Babu musu Larai ta sake fita duk inda ta san Meerah na zama idan ta gama aiki seda ta duba amma bata ganta ba ,dan haka ta dawo ta shedawa Hajia Sauda ,kallon² aka fara tsakanin ta da Hajia Laura kafin suyi magana Larai tace " am Hajia bansani ba ko ta shiga bangaren su Nawwara"wani irin kallo tayi mata tare da faɗin " dama tana shiga can ne? Batare da Larai tasan matsalar da fadan xe kawo ba tace " ehhh sosai ma Hajia ai idan ta gama aikinta ta kan shiga can kafin lokacin ta shinta yayi "
Cikin tsawa tace " amma kinsan da wannan me yasa baki faɗa min ba bayan kinsan dokana duk wacce ke aiki sashen nan bana bari tayi hulɗa da su ,maza jeki can sashen ki dubomin ita" har ta kama hanya se kuma ta dakatar da ita " bara intafi da kaina dan inji dalilin Zainabu na ƙulla alaƙa da me aikina".
da sauri ta fita Hajia Laura na ta ke mata baya ,shigansu sashen yayi dai² da fitowar Mu'aisam ,shikuma yana sauri xeje masallaci ,daga sama har ƙasa yake binsu da kallo ganin suna shirin raɓashi su shiga ciki yace " akwai matsala ne"?.