← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 26

CHAPTER 8:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Hannu muka haɗe muka fara masa magiya, can dai ya ce "Na haramta muku karatun Littattafan Hausa at your early stage, idan kuma kuka ci gaba wallahi na lahira sai ya fi ku jin daɗi, kar ku ga kamar kun girma, har yanzu ƙananan yara nake kallonku, wallahi in na kama yarinya ko? Hmm" ya wani cije leɓensa.
Rige-rigen gyaɗa kai muke, BB ya ƙara da faɗin "Kuma wallahi ko da wasa na ji labarin kuna kula samari ko? Wallahi ku da karatu sai dai ku ga ana yi, ko kuma in ce sai a gidajen mazajenku "

Cikin rawar murya muka ce "in sha Allah za mu kiyaye ma"
"Ku ba Ni waje"
Tsaye muka miƙe muna faɗin Mun gode daga nan kuma muka juya za mu tafi, sunana ya kira cikin wani irin sauti da ban taɓa jin an furta sunan da shi ba har sai da zuciyata ta yanke, juyowa na yi, Rafi'at ta wuce abun ta, na koma gabansa na tsugunna.
"Yaushe za ku kammala exams É—in?"
Na ce "Neco ce ta rage, next week za mu fara itama"
Shiru ya yi can ya ce "How about your jamb results?"
A kunyace na ce "I scored 134, Rafi'at Kuma 230"
Sai da ya gama isar tasa ya ce "ma sha Allah, Dama me kuka yi applying?"
Na ba shi amsa da faÉ—in "Ni MBBS, ita kuma Law"
Kansa ya jinjina can ya ce "Karatun littattafan nan ne ya sa kika ci low score a jamb É—inki ko?"
Na girgiza kai
Ya ce "To mene? Ga shi yanzu Rafi'at ma ta fi ki ci, garin yaya?"
Cikin sanyin jiki na ce "Haka Allah ya ƙadarto"
Ya ce "shi ke nan, amma kin san cut off mark na MBBS ko?" Na gyada kai ya ce "Good, zan bincika na ji me ya kamata a nema miki, itama Rafi'at ta haƙura da law ɗin ta zaɓi wani abun, don ba za ku yi karatu a wajen gari ba beside ma rawar kanku ta yi yawa"
Ni dai ban ce mishi komai ba, haka na sunkyar da kaina ƙasa kamar wata mai ɗaukar karatu.
"Karɓi nan, Jannat" sai da na karba ya ce "Kada na ƙara gani ko jin labarin kuna karance-karancen hausan nan kin ji ko?" Na ce "e"
Ya ce "fine, you can depart"
Kamar abun da nake jira na ji ya faɗa da sauri na miƙe zan tafi ya ce "Come back"
Na dawo na tsugunna gabanshi "Wato yanzu kin yi girman da ba za ki iya godiya ba ko?"
Na ce "Ka yi hakuri na gode"
Ya sauƙe numfashi tare da nuna min hanya da hannunsa jiki ba ƙwari na wuce nima.

Tun daga wannan rana na fara wasan ɓuya da BB don kk kaɗan ba na son abin da zai haɗa Ni da shi, ba don komai ba sai don abun da na fara ji dangane da shi mai kama da so, wanda barin wannan yanayi ya ci gaba da girmama cikin zuciyata zai iya zama babban KUSKUREN da zan aikata a rayuwata, beside BB is not a kinda guy I want, ba na son mutum mai ji da kansa ko kuma dai miskilanci, i want someone very simple Wanda komai na yi masa zai min uzuri ya za Ni a turbar yarinta.

Lura da hakan da ya yi ya sa shi zama a part din Mommy ranar, sai dai abun da bai sani ba muna makaranta lokacin, bayan mun dawo kuwa ya tsare mu, muka gaishe shi, Ni dai kunya gaba É—aya ta ishe Ni, bai ce mana komai ba muka shige ciki, shi ma tun daga ranar ya sauya mana ya koma ainihin BB É—insa, Wanda ba ya wasa da mu, wanda burinsa mu yi laifi ya jibge mu.

Yau ma kamar ko yaushe mun dawo daga makaranta ke nan muka shiga part ɗin Ummi, bayan mun gaishe ta ne take shaida mana cewa ba ta jin daɗi, ko za mu yi wa BB girki, Ni dai kamar na ce ba zan yi ba, amma babu dama. Haka muka cire uniform muka shiga kitchen, ba don na so ba haka muka yi girkin muka zuba a flask, sai da muka tafi haka kawai zuciyata ta raya min in dawo in ƙara yaji a abincin sanin cewa ko kaɗan BB ba ya ƙaunar yaji.

Cikin sanɗa na baro Rafi'at a sashen Mommy na taho part ɗin Ummi, a hankali na lallaɓa kitchen, na Fara binciken containers ɗin da Ummi ke ajiye reserved pepper powder a ciki, cikin ikon Allah kuwa na hango ta a sama, ai da sauri na ɗauko stool na haye Sannan na fara ƙoƙarin ɗauko ta, alhamdulillah, har na ɗauko ban ji motsin kowa ba, na sauƙo na ciko spoon na pepper powder ɗin na zuba cikin pepper soup ɗin kayan cikin da muka yi ba ɗauko wani spoon na gauraya da kyau, na ƙara ɗebo spoon of pepper powder ɗin na buɗe jallop ɗin taliyar da muka masa mai ruwa ruwa na zuba nan ma na gauraya, ƙara ɗebo wani na yi na ƙarawa taliyar zuciyata fal farin cikin abun da nake aikatawa, komawa na yi na haye stool ɗin sannan na mayar da container na sauƙo, sai da na ɗan ɗebi pepper soup ɗin na zuba a hannuna na ɗanɗana, waro idanuwana na yi jin uban yajin da ya yi, da gudu na nudi dispenser na samu na sha ruwa tukun na dawo na rufe pepper soup ɗin na dawo kan taliyar itama na yi tasting, kan balai, ai saura kadan asirina ya tonu don yajin da ya ziyarci ƙwaƙwalwata sai da na kusa cilla ihu, da sauri na toshe bakin nawa Sannan na rufe na ƙarasa gaban dispenser na sha ruwa sosai tukun na zo na gyara jeren abincin, ina kammalawa na kaɗe jikina ina sakin wata irin dariyar mugunta don na san yau BB idan ba Sa'a ba sai mun ji ihunsa, to dai nima da na kasance Gwanar cin yaji wallahi ba zan iya cin wannan abincin ba, in na yi good three spoons ma wallahi da ƙyar.

Bedroom ɗin Ummi na nufa na sanar da ita cewa mun kammala, ta ce "Allah ya muku albarka, ki miƙa masa bedroom ɗinsa kafin ki tafi"
Na amsa da "To Ummi" fuskata sake samun abun da na riga na ƙulla masa.
Ina fitowa daga bedroom ɗin Ummi na dauƙo tray ɗin da na jera flasks ɗin kai na nufi ƙofar bedroom ɗinsa, a ƙasa na ajiye na yi knocking Sannan na murɗa na ɗan tura kaɗan sai na ɗauko tray ɗin na nufi ɗakin bakina ɗauke da sallama, kasancewar ba ya ciki ya sa na sauƙe wata irin ajiyar zuciya tare Da godewa Allah da ya ara min such a golden opportunity. Ina dire abincin na fito tare sauƙe numfashi ina wani rolling eyes ɗina cikin wani irin salo daga nan na koma part ɗin Mommy da ƙudirin ba zan fito ba ko sau ɗaya, ba kuma zan bari ko da wasa BB ya ganni ba.

Ina fita a ɗakinsa ya fito daga bathroom, yana gama goge jiki yayi routine ɗinsa sannan ya zura jallabiya abun sa. A bakin gado ya zauna nan ya hango abincin da na kawo, wani cute smile ne ya yi escaping akan lips ɗinsa, cikin ransa yana ƙara jin ƙaunar Ummi a ransa.

Wani medium sized carpet ya shimfiÉ—a sannan ya É—auko tray É—in ya dire. Fridge ya buÉ—e ya É—auko drink ya ajiye gefe da kuma bottle water sannan ya samu wuri ya zauna yana ambaton sunan Allah.

Ɗaya bayan ɗaya ya buɗe girkin, daddaɗan ƙamshin girkin ne ya buge shi take ya wani ja dogon numfashi yana mai lumshe idanuwansa, the scent, the aroma, ya Allah, was very good smelling.

Serving kansa ya yi da paper soup ɗin tare da yin bismillah ya fara ci, alive ɗin farko na naman da ya kai bakinsa ya waro idanuwansa jin yaji sosai, a haka dai ya daure ya tauna ta haɗiye sannan ya yi saurin buɗe lemon ya kai bakinsa, sai da ya sha kusan rabin lemon tukunna ya sauƙe yana sauƙe ajiyar zuciya, this food definately no be Ummi's, ko dai masu aiki suka yi ko kuma dai, masu aikin nema, ya faɗa cikin ransa, rufe flask ɗin pepper soup ɗin ya yi tare da janyo spaghetti ɗin without knowing that, yajin da aka ƙara mata ma ya fi na farkon da ya ci.

Kaɗan ya zuba a plate itama sannan ya yi bismillah ya kai one spoon bakinsa, wannan karon kan kasa haɗiyewa ya yi tsabagen abun da ya ji ya ziyarce shi ba nau'in yaji, tuni ya nufi toilet, kusan mintinsa biyar ashe dai da ya yi brush ya fito har lokacin amma zafin yajin yake ji. Gaba ɗaya abincin ya fice masa daga rai, hakan ya sa ya rufe flask ɗin ya ture shi gefe ransa na masa ba daɗi da abincin ga shi kuma yunwa yake ji don tun breakfast bai ƙara cin komai ba.

Sallar la'asar ya fita Masallaci ya yi da ya dawo ya tarar da Ummi a parlour, gaishe ta ya yi har zai wuce kuma ya dawo ya ce "Ummi me za ki ci a yi order?"
Ummi ta É—an dube shi fuskarta na É—auke da tambaya
Ta ce "Ban gane ba, order kuma? Ai akwai sauran abincin da su Jannat suka maka É—azu, bari ma na saka su su maka dinner"
Saurin ce mata "A'a" ya yi ta ce "Why? Ko dai girkin É—azun bai maka daÉ—i ba?"
Ya É—an sako fuska ya ce "A'a Ummi, bari zan kira su da kaina ma"
Ba tare da kawo komai a ranta ba Ummi ta ce To, BB ya ce bari na je.

Yana fitowa bakin apartment ɗin Ummi ya jinjina kai tare da jinjinawa mugunta irin ta yaran nan, duk yadda aka yi ya tabbatar da sani suka masa haka sun sani sarai ba ya son yaji ko kaɗan, lallai kuwa yau zai koya musu hankali ƙwarai.

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 9 · 0% Book details