← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 26

CHAPTER 13:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Ai kuwa ranar nan na ƙara ganinsa a kaina ina zaune a cool down, sai dai sa'ar da ya samu Ni ɗaya ce a wurin, a gefena ya zauna, na ɗago da niyyar yi mishi rashin mutuncin sai na kasa, ya dube Ni ya ce "Da alama ba ki san Ni ba ko?"
Na ce "e"
Ya ce "I'm Abbas Hashim Toro, popularly known as Abbas Toro, Ina HNd class, kina wani avoiding dina after all Ni senior É—inki me, I deserve some respect, Abi?"
Ban ce komai ba, yace "Fine, ba wani abu ya sa nake son Miki magana ba, I'm here just to earn the certificate, already Ina aikina a Companyn Daddyna, and na ji an ce you're SS (Kamar yadda muke faÉ—a, serious student) shi ya sa na ce zan taimaka Miki with tutorials a duk wani course da ke miki wahala" jikina ne ya yi sanyi na ce "Thank you, I'm very sorry for the other day, ban kyauta ba" ya yi Murmushi ya ce "Don't worry, I'm Abbas, and u?"
Ya miƙo min hannu alamun mu gaisa, na girgiza masa kai ina Murmushi na ce "I'm Jannat, jannatul Firdaus"
Ya ce "wow! What a nice name"
Na ce "thank you"

Tun daga wannan rana muke mutunci da Abbas Toro, mutane har mamaki suke idan suka ga yadda yake mu'amalanta ta, wasu kuma da suka jima suna son samun irin damar sai kushe Ni suke suna faÉ—in albarkacin bakinsu, sosai muka dinke abun mu, yana min tutorials akan FON (Foundation of nursing) da kuma Anatomy and physiology, and alhamdulillah, hakan yana taimaka min sosai, a haka muka cinye watanni uku a academic block, aka yi posting É—inmu hospital for clinical experience.

Sunana ya faÉ—o cikin waÉ—anda za su yi posting É—insu ne a orthopedic ward, na yi farin ciki sosai kasancewar shi a orthopedic ward a old site yake.

Ina dawowa gida ranar da list É—in nan ya fito na tarar BB ya zo gida, amma an ce ya tafi gidan Hajiya Dada, hakan ya sa ban samu ganinsa ba sai washe gari asabat da yamma da ya dawo, na gaishe shi ya amsa fuskarsa babu yabo ba fallasa, ya tambaye Ni ya karatu na ce masa "Alhamdulillah" ya ce "Best wishes of luck" na ce "Thank you". Har na tashi zan tafi ya ce "An ce course É—inku ba maza" na gyaÉ—a kai ya ce "Fine, ban da kula samari dai, har yanzu You guys are too young ki fara kula samari, idan lokaci ya yi zan ba ki damar hakan da kaina"
Na ce "To BB"
Ya ce "You can go"
Na tafi ina mamakin maganarsa, wai mun yi ƙanƙanta da kula samari, na yi dariya na ce "Don ba ka san tarin samarin da na yi ba ina ss 2 zuwa 3, kwanan nan kuma zan samo mijin aurena ma na huta, Rafi'at already ta kama na ta GT ɗin (guarantee"

Ranar Sunday, da yamma BB ya É—auke mu muka je Annor cosmetics, muka yi shopping É—in turaruka da mayuka da kuma sauran kayan gyaran jiki, Ni kam Duk abun da na ga ana tallarsa a facebook sai na É—auke shi, Ni ce facemask, Ni ce showergel, scrub, face cream, body lotion, face wash, body oil,cbody soap, sunscreen da sauransu, bayan mun gama wannan shopping É—in muka nufi check 'N' buy, nan ma muka yi siyayya, daga nan muka tafi Ayzan Fun pack.

Ƴan gayu sosai muka gani a wurin, iceream ya mana order muka sha, muna shirin fita wani saurayi ya tsayar da mu, Rafi'at ta wuce Ni kuma na tsaya, tunawa da waccar ranar da BB ya ganmu da wani na yi ba shiri na bi bayansu zuwa wurin da muka yi packing.

Saurayin ya biyo bayanmu da sauri, ina shirin shiga Mota na ji ya ce "Haba Baiwar Allah, ko minti biyu ne don Allah ki ba Ni" ban kula shi ba na shige cikin mota, kawai sai na ga BB ya buÉ—e sashensa ya fito, kai tsaye ya tunkari mutumin, Ni dai ido na waro ina duban Rafi'at wacce ta kawar da kanta tana faÉ—in "Ke ko kaÉ—an ba kya gudun magana"
Na ce "Haba Rafi'at, me kuma na yi? Ban fa kula shi ba, beside in na kula shi ma ba laifi ba ne tun da Ni ba Ni da wanda yake so na, ko don ke dillalinki ya shiga inuwa?"
Ta É—ago ta banka min wani irin kallo
"Amma kin san BB dai ba ya so ko?".
Na ce "To in ba ya so shi zai aure Ni ne?"
Saurin rufe bakina na yi da hannuna jin abun da na faÉ—a.

A ɓangaren BB fitarsa ba don ya gan Ni da wani ba ne, fita ya yi zai yi takeway wa su Mommy, ji ya yi an dafa ƙafarsa ana faɗin "Yauwa Yayanmu, ashe ka gan Ni?"
Sai a lokacin BB ya dubi saurayin ya ƙare masa kallo shi dai bai san shi ba gaskiya a iya tunaninsa.
Saurayin ya ce "Yayanmu ka taimaka ka ba Ni ƙanwarka don Allah, wallahi aurenta zan yi, ta ƙi kula Ni"

Wani irin haushinsa ne ya cika zuciyar BB ji ya yi kamar ya sa shi tsallen kwaɗo sai kuma ya sauƙe numfashi ya dubi guy ɗin yadda yake wani roƙonsa, a taƙaice ya ce "Matata ce ba ƙanwata ba"
"Habaaa Yayayana wallahi kamanninku sun yi yawa da za a ce matarka ce Don Allah to ka faÉ—a min unguwarku sai na turo iyayena, wallahi ta shiga raina"
Tsawa BB ya daka masa, ba shiri ya sake shi "Kar ka sake fadin wata magana akan matata! Miyasa ku mutane ba ku da hankali ne?"
Yana faɗin haka ya juyo bai ma ƙarasa ya yi abun da ya fitar da shi ba.

Allan da ya taimake Ni BB Bai ji abun da na faÉ—a ba, sosai Na ji sanyi a raina tare da marairace fuska ina kallon Rafi'at, ta cije gefen lips É—inta daga nan muka wuce Baby Ayman sai surutu yake yi.

Da daddare Ya Khalid ya kira BB, bayan sun gaisa ya tambayi lafiyar kowa sannan ya jaddada masa ya bayyana min soyayyarsa, nan fa BB ya sauƙe ɓacin ran da wancan mutumin ya ƙunsa masa, shi kam Ya Khalid dariya ya yi ya ce "To ai dama na faɗa maka, ka ma godewa Allah da a gabanka ne ka lalata komai, ina kuma ga in ba ka nan? Kana tunanin za ta yi rejecting duk wanda ya zo mata da kalmar soyayya ne saboda kai? To ai ba ta san ma kana yi ba K".
BB ya numfasa sannan ya ce "Hmm"
"Kar ka tsaya sanya Friend, kawai ka faÉ—a mata cewa kana son ta, I'm sure za ta amince, da zarar hakan ta faru ba ka da wata fargaba, komai zai tafi maka yadda ya kamata"
BB dai bai ce komai ba, daga nan suka yi sallama, BB ya sauƙe numfashi yana tunanin abun yi.

Ranar Monday muka fara zuwa asibiti, da yake Ni A FMC old site nake ya sa ana sauke Ni na kira ƙawayena da muke tare ina tambayarsu a ina za a taru, suka faɗa min da yake ban san wurinba na tambaya aka nuna min, da misalin ƙarfe takwas daidai clinical instructors ɗinmu suka iso wurin aka yi orientation sannan aka sada kowa da ward ɗinsa aka damƙa mu ga head of units tare da posting letter.

Sati guda muna zuwa, ranar wata juma'a muna tsaye ana ward round sai consultant Dr. ÆŠin ya yi mana tambaya dukkanmu har da OTOC Dr, gaba É—aya aka yi tsuru kowa na tunanin amsar, caraf suka ji na bayar da amsar daidai, Consultant Dr É—in ya ba Ni kyautar 10k, shima Dr. Junaid ya ba Ni 5k. Tun daga ranar ya fara shige min, haka kawai zai ware Ni daga cikin colleagues É—ina Wai zai min lectures, tuni su Sa'adatu Muhammad suka fassara mu wai soyayya muke, Ni dai na san ba soyayyar da muke yi da shi kawai karatu yake min.

A hankali tun ba na damuwa da shi har na Fara jin shi cikin raina duba da irin gudunmawar da yake ba Ni wajen ganin na iya abubuwa, su Sa'ada kuwa tuni sun fara jin haushina, a haka muka ƙarar da four weeks ɗin da za mu yi a clinics muka koma academic block.

Karatun 1 month muka ƙara daga nan aka fara shirye-shiryen fara exams, kasancewar da kaya sosai gabanmu ya sa na mayar da hankalina kwacakom ga karatuna, ko a gidan ba sosai nake kallo ba, chat kuwa yanzu na yage shi, Abbas Toro ma na ja masa layi saboda karatun exams kuma ya fahimce Ni. Har zuwa Lokacin kuma BB Bai ƙara zuwa gida ba a haka muka yi weeding exams cikin amincewar Ubangiji, and luckily we were able to make it, mun samu clear pass, sosai Na yi farin ciki, na kira BB na sanar da shi, a wannan lokacin su Rafi'at suna second semester ɗinsu saboda su 3months suke per semester unlike mu da muke 6months.

Tsakanina da Dr. Junaid kuwa iya gaisuwa ne coz na riga na ba shi numberna kuma yakan kira lokaci bayan lokaci, Ni da shi kuwa ba mu ƙara haɗuwa ba tun da muka bar clinical environment muka koma area class, wata rana ina zaune ina jiran zuwan baba driver sai ga kiran DR. Junaid, na yi picking call ɗin muka gaisa cikin mutuntawa, ya tambaye Ni ya studies.
Na ce "Alhamdulillah"
Ya ce "Ma sha Allah" sai kuma ya yi shiru "Kina school ne?" Na amsa masa da "E, wani abu ne?"
Ya ce "A'a, dama na shigo school É—in naku ne na ce Ko zan zo mu gaisa"
A É—an tsorace na ce "Ai mun tashi ma, yanzu haka Driver nake jira zai zo mu wuce"
Caraf na ji ya ce "To ai ga Ni nan, sai na kai ki gidan ko?"
Na ce "A'a, so kake Abuya ya min shegen duka in ya gan Ni da kai?"
"Shi ke nan tun da ba kya so na zo"
Wani irin na ji, ko ba komai dai bai kamata na masa haka ba after all shima kamar tutor yake a wurina, wannan dalilin yasa na ce "Shi ke nan sai ka zo"
Yace "thank you"

Ko mintuna goma ba a ƙara ba Dr. Junaid ya zo, ina waigawa na hango shi jingine jikin wata lafiyayyar mota yana laluɓen numberna, ban bari ya gama kiran ba na ƙarasa wurinsa kasancewar ba mu da wani nisa da shi.

Na ƙarasa wurinsa ina yin sallama, ya amsa min fuskarsa ɗauke da Murmushi.
Ya ce "a'a kina kusa ma ashe"
Na yafa Murmushi kan fuskata na ce "E, a can nake " na É—an waiga na nuna masa cool down É—in da nake zaune.
Ya ce "fine, ya na ga kin ƙara kyau ne"
Na ɗan kwaɓe fuska jin ta yadda ya ɓullo, ban iya ce masa komai ba saboda na ji zancen wani banbaraƙwai, ya ce "Ya kika yi shiru RM. J?"
Na girgiza kaina na ce "Babu komai"
Ya ce "Shi ke nan, in kin amince zan na zuwa muna gaisawa a nan tun da ba ki so nake zuwa gidanku shi ya sa ma kika ƙi yarda na mayar da ke"
Na ce "a'a wallahi ba haka ba ne, kuma ka san tsarin school É—in nan, tsayawa da saurayi ma is an offence"
Da sauri ya É—ago eyes É—insa ya dube Ni yana faÉ—in "Am i your boyfriend?"
Zaro eyes É—ina ma yi na ce "Ban ce haka ba Dr. As far as Kai ba É—an gidanmu ba ne then saurayi za a kira ka"
Ya ce "ke dai ba za a ci ki a zance ba, an bar miki, how studies?"
Na ce "Alhamdulillah"
Ya ce "ma sha Allah"
Horn É—in motar da na ji gefena ya sa na waiwayo and to my surprise motar gidanmu ne, hakan ya sa Ni dole na yi mishi sallama na wuce abuna.

Ina shiga motar Baba Driver ya ja muka wuce, Rafi'at ta dube Ni ta ce "Sannu ko?"
Na ce "Yauwa"daga haka na ja bakina na tsuke saboda ba na son maganar da za ta min, muna isa na ajiye jakana a bedroom ɗinmu na watsa ruwa, Rafi'at ma ta watsa Tukun muka nufi dining, muna cin abinci na dawo na yi sallar la'asar, ina ganin yadda Rafi'at ke bi na da wani kallo Mai kama da tuhuma Ni dai na ƙi ba ta damar yin magana saboda ina idar da azkar ɗina na jawo school bag ɗina tare da fitar da Anatomy and physiology textbook.

Kusa da ni ta dawo ta ce "Jannat"
Na dago na kalle ta ba tare da na ce mata komai ba, ta ce "Na san kina ji na"
A É—an fusace nima na ce "tun da kin san ina jinki ai sai ki faÉ—i abun da ke ranki"
Ta jinjina kai sannan ta ce "Duk masifar da za ki yi kuwa ba za ta hana Ni tambayar taki ba, da wa na ganki a school É—azu?'
Na É—ago na dube ta na yatsina fuska sannan na ce "Toooo Mommy ce Ko Ummi? "
Ta ce "idan ma ba su ba ne yayarki ce Rafi'atu"
Dariya na kwashe da ita sannan na ce "Afwan Yaya Rafi'atu, amma babu ruwanki da wanda kika ganni tare da shi, beside I'm not a kid, I'm an adult, ko ban kai na tsaya da namiji ba ne?"
Tace "Amma kin san dai BB ya gargaɗe mu da kula samari a waje, ba ma wannan ba mu muka zaɓi karatu akan aure"
"Sai na ce miki Ni kuma aure zan yi yanzu?"
"Kin san ba auren za ki yi ba kike kula saurayi?"
Na ce "Ba saurayi ba sai dai bazawari, ke Ni fa ki ƙyale Ni haka nan, karatu zan yi"
Tace "shi ke nan, Ni dai na riga na fita hakkinki da na faÉ—a miki gaskiya"
Kallonta na kuma yi kana na ce "To Hajiya, kema sai ki daina kula ya Sadiq "
"Hmm" kawai ta ce daga haka ba ta ƙara ce min komai ba.

Washe gari sai ga BB ya dawo. Ni dai ba na ce ban so ya dawo ba ba kuma zan ce na yi farin ciki da dawowarsa ba, lokacin da muka dawo daga school mun biya gaida ummi muka ganshi kwance akan sofa Yana bin azkar É—in da ake yi a Sunna TV na yammaci, sallama muka yi, muka gaida shi ya amsa a gadarance, Ni dai a raina na ce "Ka ji da shi dai, sai shegen son mulki kamar wani basarake "
Bayan mun gaida ummi muka wuce part É—in Mommy, da daddare muna kallon wani series a Bollywood Sai ga BB ya shigo part É—in Mommyn, Ni dai ban ji komai ba dangane da shakka ko tsoronsa, ina ji Rafi'at na raÉ—a min cewa "Ga BB nan, ke Ga BB "
Banza na mata na dake har ya shigo, haka kawai nake jin yanzu kam zan nuna mishi rashin tsoronsa la'alla mu samu zaman lafiya da shi.

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 14 · 0% Book details