CHAPTER 2:
Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Sunana Jannatul-Firdaus Sulaiman Shirama, mazauniyar unguwar Gandun wambai kuma haifaffiyar garin AZARE da ke jahar Bauchin Najeriya.
Tun ina ƙarama na kasance yarinya maras ji mai shegen rawar kai, hakan ya sa ko kaɗan ba ma shiri da mahaifiyata wacce muke kiranta da Ummi, haka zalika mahaifina Abuya, sai dai ta nashi ɓangaren akwai sassauci saboda ba ya bugu na, kawai dai shi ko yaushe yana cikin yi min faɗa ne.
Mahaifina Abuya, su huɗu ne a wurin mahaifinsu, Wansa babba, shahararren attajiri ne, Alhaji Abubakar Shirama, wanda muke kira da Daddy, Abuya shi ke biye wa Daddy, sai ƙannensu biyu, Hajiya Bara'atu wacce ke aure a garin Misau, muna kiranta da Mommyn Misau, autarsu ita ce Hafsatu, tana aure ne a ƙaramar hukumar jama'are, ita kuma muna kiranta da Mommyn Jama'are, Abuya da kuma Daddy gida ɗaya suke, ban da Kakarmu mahaifiyar su Abuya, wacce sam ta ƙi zaman Azare, a cewarta, ta fi so itama ta mutu a inda mijinta ya mutu, tana zaune ne a gidanta da Abuya ya gina mata a Misau.
Gaba ɗaya gidan su Abuya kansu haɗe yake, don kuwa duk wani hali da ɗayansu zai shiga, imma na rashi ko samu, suna kasancewa a tare da shi, Abuya da Daddy da suka kasance maza, tare suke yanke hukunci akan ƴaƴansu, though kusan ragamar yanke hukuncin a hannun Daddy take, kasancewar shi ne babba, hakan yana matuƙar burge Ni idan naga Abuya na bai wa Daddy girmansa, su dai tsakaninsu sai son Barka. Wani ƙarin abun burgewar bai wuce yadda matansu suka haɗe kansu ba. Don kuwa tsakanin Hajiya Turai (Mommy) da Hajiya Amina (Ummu) sai son Barka, kai, bare kam ma in ya gansu sai ya yi tunanin ƴan'uwan juna ne kamar dai mazajensu, Ni kaina ban da dai muna zuwa wurin danginsu da ba zan san da hakan ba. Mommy ƴar asalin ƙaramar hukumar Shira ne, yayin da Ummi kuma ta kasance haifaffiyar garin Giade.
Daddy na da ƴaƴa biyu ne, shi kuma Abuya uku. Ibrahim Khalil shi ne babban ɗan Daddy, muna kiran shi da BB, wato Big Bro, sai kuma mai bi masa, Abubakar Sadiq, ɗa na farko wurin Abuya, muna kiran shi Yaya Sadiq, tsakanin Yaya Sadiq da kuma BB akwai ratar shekaru huɗu, hakan ya sa da wuya ka gan su tare wuri guda, kasancewar BB mutum Mai Kamun kai. In ka gan su tare, to wata muhimmiyar magana za su yi, ko kuma dai shi Ya yana buƙatar wani abun wurin BB. Unlike Habib farouq mutum ne mai son barkwanci da raha, baka rasa shi da abun dariya kuma ko yaushe fuskar shi dauke da murmushi take, yanzu haka yana aiki ne asibitin koyarwa da ke garin Azare (Fuhstha).
Rafi'at ƙanwar BB ce, ta girme Ni da shekara guda. Amma dai tare muke komai namu tun muna yara, hatta Bacci wuri guda muke yi Ni da ita, ita ɗin matsayin da take da shi gare Ni suna da yawa, ƴar'uwata ce, aminiyata kuma Abokiyar shawarata kafin BB ya faɗo cikin duniyata da maganar soyayya.
Ni ce mai biyewa Rafi'at, sai kuma ƙanina Ayman, ɗan kimanin shekaru takwas a yanzu.
BB, kamar yadda sunan nashi ya nuna ya cancanci a kira shi da hakan, domin kuwa mutum ne mai matuƙar kamun kai da jan aji, la'alla ko don kasancewarsa kyakkyawa ne? Allah kaɗai ya bar wa kanshi sanin hakan. Kyakkyawa ne kam ajin farko, fatar shi nada haske amma ba irin dau ɗin nan ba, siririn hancinshi da ke a tsakiyar fuskar shi tamkar ajiye shi aka yi, lips nashi basu fiye girma ba sai dai suna da dan kauri, sama black na ƙasan kuma pinkish, ga uwar cikakkiyar girar shi da ta ƙara bayyana ainihin kyau na guy din. Sajenshi na da ɗauke da wadataccen kwancaccen gashi da ya yi luf ya manne jikin fatarsa, Sumar kansa kuwa ta kasance baƙa siɗik sannan kuma a yalwace take, shi ya sa kusan ko yaushe za ka ga kansa tsaf-tsaf yana ƙyalli, yau this hairstyle and tomorrow that hairstyle.
BB mutum ne mai izza, isa, da kuma taƙama, ko kaɗan ba ya ɗaukar raini a wurin ko ma waye ne, bai ma shiga sabgar mutum ba bare ya samu damar raina shi, yadda BB yake a waje na ya fi sauƙi akan a cikin gidan musamman ga mu ƙannensa, tun muna yara yake cin ƙwal ubanmu, yadda muke shakka da tsoronsa ko iyayenmu ba ma yi jin hakan kansu, slight mistake za mu yi ya ba mu punishment ɗin da sai mun kwana mun yini muna jin jiki, abun da ma na lura da shi shi ne, ya fi takura mana Ni da Rafi'at, lafiya lau za ku gani shi yana yi wa Ayman dariya kamar wani abokinsa, amma mu kam ina! BB kamar dodo yake a gare mu. Duk yadda zan kwatantawa masu karatu halayen BB, zai yi wahala su fahimci irinsa, don ko a cikin jerin jaruman litttattafa, ba a taɓa yin kwatankwacinsa ba.
Ta ko ina BB is perfect with life. Yana da matuƙar Sa'a da nasara a rayuwarsa, don kuwa duk wani abu da ya sa gaba in Sha Allah sai ya same shi cikin sauƙi, a lokacin da BB ya cika shekaru goma sha takwas a duniya, ƙofofin nasarorin rayuwa suka fara buɗe masa, kasancewar shi mutum mai so da kuma ƙaunar motsa jiki da ƙwallon ƙafa don har gym room yake da shi a gida a wannan lokacin. Wannan hub ɗin da yake da shi a wannan fanni ya sa shi samun wani irin experty a fannin. Nasararsa ta farko a fannin ƙwallon ƙafa ta fara ne a shekarun nan, ya samu damar bugawa ƙasarsa ƙwallo har ya yi nasarar lashe musu kofi, wannan ne ya ba wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban daban son samun shi a matsayin ɗan wasansu, wanda da ƙyar ya amince ya kuma ba su dama, a shekarar ba ƙananan kuɗaɗe ya samu ba, a hakan kuma bai daina samun tayi daga wasu clubs ɗin ba.
Su Daddy sun yi matuƙar farin ciki da ire-iren nasarorin da BB ke samu a wannan fage. Amma can ƙasa, Daddy, ya fi so BB ya zama jami'in tsaro ne, ko dai ɗan sanda, soja, ko dai wani aikin ɗamara, bayan tattaunawa da Kaka da suka yi ne Abuya ya tunkari BB da maganar, babu musu ko taurin kai kuwa ya amince, Daddy ya nema masa Form a makarantar aikin sojoji, cikin ikon Allah ya tafi domin samun horo da kuma gwaji a wannan fage, alhamdulillah, nasrun minallah, sunan BB ya fito na biyu ne a jadawalin waɗanda suka yi nasara a wannan gwaji da aka musu, take Gwamnatim ƙasa ta ɗebe su aiki a matsayin ƙananun sojoji.
Ƙwazo da yanayin kuzari da kuma kazar-kazar irin na BB ya taka muhimmiyar rawa wurin ƙara buɗe masa matakan nasara, wata rana bayan artabu da suka yi da wasu ƴan fashi da makami ya samu lambar girmamawa, da shi da wani abokin aikinsa da suka haɗu, Khalid Usman Usman sun kuɓuta da rabon ƙara karatu, wanda hakan ba ƙaramar dama ba ce suka samu, da yawa sun buƙaci hakan ba su samu ba, wani abun burgewa da ƙarin karatun da za su yi shi ne, za su ƙara samun matsayi ne da kwalin wannan karatu.
Cikin farin ciki da addu'ar iyaye BB ya tafi ƙasar Cairo shi da mutumin da ya nace sai ya shiga rayuwarsa, wato Khalid,
Ba na mantawa lokacin muna primary school, boarding school aka saka mu ta ƴaƴan masu hannu da shuni, gari gari har Bauchi, abun ka da makarantar ƴaƴan masu hannu da shuni, babu mai takura mana a Dolphin Maria college, hatta salla sai mun ga dama muke yi, wanda hakan ya sha banban da tarbiyyar gidanmu. Daga Ummi har Mommy tsayayyu ne akan ibada, suna kuma tsananin saka mana ido wurin ganin salla ba ta kuɓuce mana.
Tsautsayi ne ya faɗa kanmu wata ranar hutu, Daddy da Abuya duka ba sa gari. Ga shi kuma ko da wasa ba a saka Driver ya ɗauko mu daga school, Daddy ne ko Abuya mafi aksari suke ɗauko mu. Wannan Ranar ta zo da wani irin arashi, ranar BB ya dawo daga ƙasar Canada bayan sun je buga wani wasa, yana dirowa ko hutawa bai yi ba Mommy ta tare shi da batun ɗauko mu daga makaranta.
Though ko kaɗan bai ƙaunar abun da zai haɗa shi da mu haka ya amsa da to, daga nan ya fito Mommyn na saka mishi albarka. Daga cikin motocin da ke packing space BB ya sa aka goge masa ɗaya, sannan ya shiga ya ja motar ƙiiiiiiiiii ya bar gidan.
Cikin nutsuwa motar ke tafiya kan titi yayin da BB ya ke sauraran karatun surah al'anbiyÄ' cikin muryar babban Æ™ari'i Muhammad ayyub yayin da yake bi a hankali da irin muryar, so Masha Allah, kamai nashi na musamman ne.
Yana isa Dolphin Maria college securities suka gama checking motar daga nan ya samu damar harba motar zuwa titin dan da zai sada shi da dormitory É—inmu.
Bayan ya magantu da securities na wajen ne aka fara fito da bags da trolleys É—inmu, yayi da muke biye da masu É—aukar kayayyakin namu shi kuma BB already ya wuce zuwa cikin motar yana jiran shigowarmu.
Ba mu tsaya ɓata lokaci ba ganin mutumin da ya zo ɗaukarmu, ya sa ba mu tsaya ɓata lokaci ba, cikin rawar jiki muka shiga ciki, Ni na faɗa buɗe seat ɗin baya na zauna, hakan ya sa Rafi'at buɗe front seat ita kanta zauna sanin halin BB tsaf zai CE mu fita mishi a mota ya ja ya tafi kayan shi.
Cikin rawar muryar da ban taɓa tunanin Ni kaina ina da ita ba na ce
“BB sannu da sauƙa fatan ka dawo lafi..†ban kai ga ƙarasa faɗin abun da zan ce ba na ga ya daga min hannu ba tare da ya juyo ya kalle Ni ba, hakan ya sa na ja linzamin bakina na tsuke shi..
“ina yini BB†Rafi'at ma ta gaida shi gudun yin wani laifin a wurinshi. Ko samun kallon arziƙi ba ta yi ba ita ma bare ta yi tsammanin zai amsa mata, dama kuma ba mu yi expecting amsawar daga gare shi ba.
Shiru ne ya wanzu cikin motar har muka isa garin Azare , gidanmu da ke unguwar gandun wambai muka nufa, cike da ɗaukin ganin iyayenmu da muka yi kewa muka fara murmushi, yana parking na sa hannuna na taɓo bayan Rafi'at, ƙin juyowa ta yi haka ya sa Ni dole tsayawa jiran umarnin BB ganin itama ba ta fita ɗin ba.
Wani mugun kallo BB ya juyo ya aika mana daga Ni har Rafi'at, take hantar cikinmu ta kaɗa don a lokacin har wani ƙugi cikina ya yi saboda tsananin tsoro.
"Jira kuke sai na ce ku fita um?" Ya faÉ—a cikin kaushin murya tare da jan tsaki. Ai bai gama rufe baki ba jiki na rawa muka fice daga motar.
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*
*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*
1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA
2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT
3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN
4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE
5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA
Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.
Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k
Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu
Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇
09023907030
09161720046
+20 150 885 6397
09065856251
07061707238
*Masoya ina Æ™ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub âœï¸ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*
*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~
https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS
*No 04*
*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_
07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim
.