← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 26

CHAPTER 18:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Kwanan BB uku ya ƙara komawa bakin aikinsa, tsakanina da Dr. Junaid ba a magana, alaƙa ta ƙullu tsakaninmu kai ka yi tsammanin ƴan'uwan jini ne mu idan har ba faɗa maka na yi ba, hatta ƴan class ɗinmu yanzu sun san shi, komai nawa Yaya Doctor, Yaya Doctor, cikin waɗanda suka yarda cewa shi ɗin Yayana ne har sun fara takura min akan na haɗa su suna son shi, this and that, a ɓangaren ƴar'uwata Rafi'at kuwa na rasa me ya sa ba ta son alaƙata da Dr. Junaid after all ta san ba soyayya muke yi ba, kullum tana cikin kushe shi da duk wani abu da ya danganci shi, hatta Abu idan ya kawo min ba ta ƙaunar ko da kallon abun ne, tun ina ɗaukan hakan a ba komai ba har dai na fara tunanin wani abun na daban, na gama lura da ita ko gaisawa za ta yi da Yaya Doctor kanta sama, wanda hakan ba ya min daɗi ko kaɗan don shi ma ya fahimci cewa Rafi'at ɗin ba ta son alaƙarmu da shi, da ya kawo min irin zancen nan sai na yi ƙoƙarin kawo wani zancen don kore wanda muke yi ɗin.

A ɓangaren BB bayan ya tafi ma yakan kira mu mu gaisa, zafin nan nashi sai nake ganin kamar ya fara raguwa though ban yi na'am da hakan ba saboda sanin halinsa, yanzu zai iya sauyawa zuwa wani iri daban.

Yau gaba É—aya gidansu Ya Khalid in ka cire Mami da Abba dukkan suna gidan big sis, ciki har da BB. Shi dai BB tun da Sophie da Mufeed suka zo jikinshi sai zuba mishi surutu suke.

Sophie ce ta sauƙa daga jikinsa ta nufi wurin Nimrah, yayin da Mufeed ya saki safiyar farin ciki hana faɗin "Ai gara da kika bar min Uncle ɗina"
Daga cinyar Nimrah Sophie ta ce "Ai sai ka cinye Uncle É—in, kuma nima a wurin Mommy Nimrahh zan zauna, idan Uncle ya tafi za ta yi min baking cakes, plenty ones, ko É—aya ba zan ba ka ba"

Yaron ne ya kwaɓe fuska sannan ya dubi BB ya ce "Uncle ina za ka Kaini Bakery nima a min?"
BB ya saki wani ƙayataccen Murmushi tare da faɗin "Rabu da Sophie my boy, za mu je Bakery in ba ka son na bakery ma in na je Azare Jannat za ta maka masu daɗi"
Kukan shagwaɓa Yarinyar ta saki tana faɗin "Ai dai na Mommy Nimrahh ya fi daɗi, kuma idan Mom ta fita Aiki babu kowa iya Ni za ta yi wa abinci, ko Mommy?"
Nimrah da ba ta ce uffan ba tun da yaran suka fara rikicin nasu ta murmusa tare da gyaÉ—a kanta.

Ganin yadda suke shirin ɓata daren da rikicinsu ya sa Ya Khalid faɗin "K, ya kamata mu tafi fa"
BB ya ɗan kane wuri guda ba tare da ya ce komai ba, satar kallonsa Nimrah ta yi tare da sakin wani ƙayataccen Murmushi wanda caraf ta yi shi akan idon Big Sis. Basarwa ta yi ta ce "Yanzu sai yaushe ke nan?"
BB ya É—an saki fuska ya ce "Ni kam ina tunanin next week zan wuce Azare, i don't think if we'll have another chance to be here kafin nan"
Big sis ta ce "Kai Haba Bro, ka ce dai kana so ka koma wurin Jannat"
Da biyu big sis ta yi maganar don ta lura da ƙanwar Tata yadda take satar kallon BB ɗin, ai kuwa Big sis na faɗin haka Nimrah ta ƙara satar kallon BB don ganin face reaction ɗinsa, ganin ya saki Murmushi ya sa ta haɗe fuska ta miƙe tsaye.

Big sis ta ce "Ke kuma ina za ki je?"
Nimrah ta ce "Ruwa zan É—auko a fridge"
"Shi kuma wannan ruwan dake gabanku da?"
"Mai sanyi nake so big sis" tana faÉ—in haka ta yi saurin barin wurin kamar za ta faÉ—i, big sis ta jinjina kai tare da dawo da hankalinta wurin su BB.

Ya Khalid ya ce "ke dai Big Sis ki bari kawai, mutumina Ya yi ambaliya a tekun soyayya, kuma har yanzu kin san bai faÉ—a mata cewa yana son ta ba?"
Big sis ta dubi BB ta ce "To me kake jira Bro?"
BB ya ɗan sosa kai ba tare da ya ce komai ba, yayin da Ya Khalid ya ce "Kin san shi fa, kin san halin mutumin da shegen jin kansa, wallahi kusan shekara yanzu ake nufa ina nuna masa illar rashin faɗa mata ya ƙi ji"

Duk abun da ake Nimrah na tsaye tana jinsu, ita ta kasa ƙarasowa ciki ta kuma kasa komawa don gaba ɗaya ta shiga shock da wannan tattaunawar da ake yi.

Big sis ce ta dubi BB cikin ido sannan ta ce "Haba ɗan ƙanina, to meye na ƙin faɗa matan kuma? Ai Gara tun wuri ka yi magana kafin wani ya maka shige layi, ka san da zafi-zafi ake dukan ƙarfe ga"
"Rabu da shi Big Sis, wallahi duk yadda zan yi K ya faɗawa yarinyar nan yana son ta ya ƙi, ga shi yarinyar Allah ya mata farin jini kamar me" Ya Khalid ne ya faɗi hakan yana ɗagewa BB gira, wani irin banzan kallo ya jefi Ya Khalid da shi, a tare big sis day Ya Khalid suka sanya dariya.

"To be sincere bro, zan ba ka shawara ka yi maza ka bayyanawa Jannat soyayyarka, haka kawai nake jin ina son yarinyar tun da kaima kana son ta, ka san mu mata ba ma gane kurman yare, ko da a ce ta san kana son ta In har ba ka faÉ—a mata ba wallahi za ta iya take soyayyarka ta amshi ta wani, Allah ya kiyaye"
"Amiin" suka haÉ—a baki wurin faÉ—i.

BB ya ce "Thank you Big sis in sha Allah zan ƙoƙarta na ga komai ya tafi yadda ya kamata"
"I'll be glad if they happened"
"Now are we good to go?" BB ya faɗa yana sauƙe Mufeed daga jikinshi.
Tare suka miƙe shi da Ya Khalid wanda yake faɗin "Ina Nimrah kuma?"
Big sis ce ta ƙwala kiran Nimrah tana faɗin "Wai shan ruwan ne har yanzu? To ki zo za ku wuce?"
Kamar wacce aka jefo Nimrah ta shigo parlourn tana gyara rolling ɗin veil ɗinta "Ayya big sis, na tsaya na ƙara chips ɗin nan ne shi yasa "
Murmusawa kawai big sis ta yi tare da miƙewa don yi ma su BB rakiya, har parking space suka rako su BB ya ɗauko wrappers na 1k guda biyu ya damƙawa Mufeed da Sophie kowa a hannunshi Yana faɗin "Sai na dawo ko?"
Cikin farin ciki yaran suka nufi Big sis suna nuna mata kuÉ—in "Mommy kin ga Uncle ya ba mu kuÉ—i"
Big sis ta ce "kun ce wa Uncle Kun gode ne?"
Yaran suka ruga suka nufi wurin BB tare da faÉ—in "Thank you Uncle "
Sunkuyawa ya yi ya ja kuncinsu É—aya bayan É—aya, ita dai Nimrah kallonsu kawai take gwanin burgewa har take ji a ranta kamar Æ´aÆ´anta ne da babansu, Murmushi kawai ta saki tare da nufar tasu tana faÉ—in "To big sis, mu kwana lafiya, my baby, next time in zan zo I'll bake some cakes for you"
Sophie ta daga tsalle tana faÉ—in "Thank youuuuuuu" cikin farin ciki.
Mufeed ne ya kwaɓe fuska tare da faɗin "Uncle Nima"
BB da ya rufe mota bayan ya shiga ne ya bude tare da É—agawa Mufeed hannu alamun rarrashi."
Tayar da mota da Ya khalid ya yi ya sa yaran suka fara É—aga musu hannu, nan motarsu ta fice zuwa gida.

NIMRAH
Nimrah ita ce Autar Mami, yarinya ce kyakkyawa son kowa, fara ce, siririya, kana ganinta ka ga bafulatana Usul, bayan kyanta abu na gaba da yake jan hankalin mutane gare ta shi ne nutsuwa da kuma kamun kai, hatta tafiya idan Nimrah na yi abun kallo ne don kuwa ko irin sautin takalmin nan ba ka ji idan tana tafiya, komai nata tana yin shi ne cikin natsuwa, Nimrah na da ilimin addini sosai, ga haddar Alqur'ani kamar me, yanzu haka tana gab da tafiya musabaka ne ƙasar Egypt don wakilta ƙasarta najeriya, a fannin karatun boko ma Alhamdulillah, ta kammala secondary shekaru kusan biyu da suka wuce. Interest dinta akan ilimin addini ya sa ta ci gaba da zuwa makarantun hadda a madadin jami'a.

Wani abu da babu wanda ya lura da shi bayan big sis shi ne, Nimrah son BB take, ta lura da hakan ne tun BB Bai jima da fara zama gidansu ba, ranar ita ma ta je yinin gida ba ta mantawa, yadda Nimrah ke bin duk wani motsi na BB hakan ya sa ta dasa Ayar tambaya akan ƙanwar Tata, to yanzu ta gama tabbatarwa don kuwa ko makaho ya ga yadda ta miƙe babu shiri ɗazu daga ji an ambaci Abokiyar takararta zai fahimci inda ta dosa.

Sati guda da zuwan su BB gidan big sis BB ya dawo gida, wannan karon sosai ya ba wa kowa mamakin sauyawarsa. A ranar da ya dawo ya sa aka kira mu, kowa da tsarabarshi tun daga kan Abuya, Ummi, Mommy, Daddy, Ya Sadiq, Rafi'at, Ni da kuma auta Ayman. Bayan siyayyar Æ´an gida har da na su Mommyn Misau da Mommyn Jama'are, abu dai gwanin burgewa, abun da ya daure wa kowa kai bai wuce ganin tsaraba ta ta fi ta kowa yawa ba, sai dai babu mai bakin magana ciki kuwa har da Ni kaina da tsarabar tawa ta mugun ba Ni mamaki.

Washe gari da safe, da yake muna hutun semester ta biyu a aji É—aya ya sa ban tashi da wuri ba har Rafi'at ta wuce school.
Bayan na tashi na yi wanka na fito muka gaida da Mommy da Daddy, sannan na wuce na gaida Ummi, abuya ya tafi wani conference na malaman addini na ƙasa, hakan ya sa na fito da niyyar komawa part ɗin Mommy don gaba ɗaya na manta da cewa BB is home.

Har na kusa fitowa daga bedroom É—in Ummi na ji ta tsayar da Ni "Kun gaisa da Khalil ne?"
Na ce "Tab, wallahi har na manta da ya dawo"
Ummie ta ce "Dole ki manta ai duk rashin mutuncin da kike masa da ya tashi kawo tsaraba ai bai manta da ke ba, taki ma ta fi yawa"
Bakina na É—an tura gaba, cikin raina na ce "Ai ba Ni Na ce ya kawo min ba" daga haka na fara takawa zan fice, ina ji Ummie na faÉ—in "Ki tabbatar kin je kin gaishe shi kin kuma yi masa godiya kin ji?"
Ban samu damar amsa mata ba ina tura baki na fito, ai kuma sai muka kusa cin karo da shi.

A hankali na ce "Ina kwana BB"
Kansa ya gyaɗa tare da nuna min kujeru alamun na jira shi, ɗakin Ummie ya shiga can sai ga shi ya fito, Ni kuwa ina tsaye akan carpet kamar wacce ta haɗiyi taɓarya, ina ganinsa har ya ƙaraso ya zauna akan kujera mai zaman mutum ɗaya, sai da ya zauna tukun ya ce "Ba ki iya zama ba ne?"
Na ce "Ni?"
Ya ce "a'a Ni"
Ƙoƙarin zama na fara yi kan carpet na ji ya ce "have a seat" kusan daskarewa na yi saboda mamaki coz tun da nake ji dai ban taɓa zama wuri guda da BB ba, kai ko lokacin da muke yara idan yana sama ba na hawa sama, sai dai ƙasa.

Saurin girgiza kaina nayi cikin son dawowa cikin hayyacina, nan na ranƙwashi kaina da yaƙinin cewa kunnena ba su ji min daidai ba, hakan ya sa na ci gaba da ƙoƙarin zama a ƙasa.

Muryarsa da ta doki kunnena a wannan karon ita ta sa Ni fahimtar cewa tabbas ɗazu abun da kunnena ya ji gaskiya ne, ɗagowa na yi da niyyar na kalle shi cikin rashin Sa'a idanuwanmu suka sarƙafe da na juna, duk ƙoƙarina na ganin na ɗauke nawa idon abun ya gagara don kuwa ji na yi kamar an manne nawa da nashi wuri guda.

Mun shafe kusan daƙiƙu uku kafin na iya janye nawa idanuwan a kunyace ina mai sauƙar da kaina ƙasa
Cikin sassanyar Muryarsa ya ce "Can You have a seat ko sai.."
Bai ƙarasa faɗin abun da zai ce ba na miƙe na ɗosana mazaunaina akan kujerar da ke fuskantar shi.

"Ki zauna da kyau mana, sai ka ce kina gaban wani aljani"

Mamaki kalaman nasa suka ba Ni ban iya ɓoye haka ba sai da na saci kallonsa sai dai ga mamakina hankalinsa kwance yake zaune babu wani alamu na ya fadi wani abu da bai kamata ba.

Kallona ya yi yayin da ya ciro wayarsa daga aljihu sannan ya ce "Ina Rafi'at?"
Na ce "ta tafi schol"
"Ke me ya hana Ni zuwa?"
Na ba shi amsa da "Muna hutu"
Shiru ya yi can ya ce "Fine, ya karatun?"
"Alhamdulillah"
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Shiru muka yi can dai na ce "BB mun ga kaya, mun gode Allah..."
Katse Ni ya yi ta hanyar faÉ—in "Allah shi ne abun godiya"

Kasa na yi da kaina ina jiran jin abun da zai ce, har na cire tsammanin zai yi magana sai kuma na ji ya ce "Yau za mu fita da yamma, idan Rafi'at ta dawo ki faÉ—a mata, ku shirya da wuri kun san ba na son African time ko?"
Kai Na gyaÉ—a tare da faÉ—in "In sha Allah"
Ya ce "You can go" kamar wacce ke zaune akan allura haka na miƙe na fice daga parlourn ina haɗawa da sassarfa, wani irin dogon numfashi na shaƙa bayan na fita tare da dafe ƙirjina.
Anya wannan BB ne? Yau shi ne har da gaisawa da Ni haka a mutunce? Lallai kayan mamakin BB ba ya ƙarewa. Da wannan tunanin na koma part ɗin Mommy, gaba ɗaya na kasa manta abun da ya faru.

Around 3:50pm Rafi'at ta dawo daga school sai da ta yi wanka ta ci abinci Tukun nake faɗa mata ce za mu fita tare da BB anjima, kasa ɓoye mamakinta ta yi tare da faɗin "ikon Allah, anya kuwa ba Ya Sadiq ne ya ce Miki za mu fita ba?". harararta na yi sannan na ce "Tun da dusa ne a idona ban san Ya Sadiq ɗin ba"
"To abun dai ya ba Ni mamaki"
Na ce "ki tsaya mamaki kina tunanin Ya Sadiq ne zai fita da mu ki yi African time ki karɓi baki punishment ɗin"
Dariya Rafi'at ta yi kana ta ce "Kan ki ake ji kuma, duk muguntarki ta ƙare akan ki"
Dariya mu biyun muka yi, daga nan kowa ya ci gaba da danna wayarshi.
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 19 · 0% Book details