← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 26

CHAPTER 15:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Idanuwana na zaro Sannan na ce "Rufa min asiri don Allah kar ki min mummunan fata, wallahi duk Kyan nan nasa Ni bai burge Ni, beside mijin da nake fata ma ba irin qualities É—in BB gare shi ba"

Khairat ta ce "Kar ki ce Ban faÉ—a miki ba, muna nan da ke zai ce miki yana son ki ".na ce "Wai Ni?? Zan mutu kuwa ashe, ku duk bayanin da zan muku ba za ku gane ba, BB ya wuce tunaninku, wallahi shi fa har yanzu yara yake ganinmu"
Suka jinjina kai, Sady-Madaki ta ce "Lallai kuwa, to Allah ya kyauta, ko account dai kwa buÉ—e a handles É—in ko don ganin updates ko ba za ku yi amfani da shi ba, amma zandama zandaman Æ´an mata kamar ki a ce ba ki da media handles? Sannu Saratu"
Na ce "ko garajen buÉ—ewa ba zan ba Sady-Madaki, zan jira in ya gama isar tasa ya ba mu dama sai mu buÉ—e"
Ta ce "Tab, ai sai kin ga dama zai ganki, ki buÉ—e da wani suna mana"
Na ce "kuna ganin ba zai gane Ni ba?" Suka ce ,"Ta yaya zai gane in dai ba wayarki za ki ba shi ya gani ba"
Na ce *shi ke nan, ku buɗe min yanzu" na miƙa musu wayata suka buɗe min account a IG da tiktok, tare da ƙara wayar min da kai kan yadda zan yi amfani da su.
Sady-Madaki ta ce "Ko ke fa?" Na murmusa na ce Hmm.

A hankali na gama koyan yadda zan yi amfani da waÉ—annan handles É—in wasu lokutan har nakan yi amfani da tiktok ma na yi hotuna a school sai na sauya privacy zuwa only you, hakan ta sa BB Bai fahimci komai ba game da Ni to ta yaya ma zai fahimta bayan da Noor Saddam na buÉ—e?

Ranar wata juma'a da ba zan manta ba ne muka yi wanka muka ci gayu Ni da Rafi'at sannan muka fito tsakar gida muna hoto da tiktok filters masu mai da mu larabawan gaske, na ba wa Rafi'at ta min ita ma na karɓa na mata, wani abu da ban sani ba shi ne, lokacin da Rafi'at ta karɓa za ta min nan san cewa ta cire only you ba, hoto kam ya tafi public.

Bayan mun gama hotunanmu mun koma cikin gida kowa ya kama harƙar gabanshi.
Da daddare ina kwance wayata ta fara ringing, Ina dubawa na ga sunan BB É—aro-É—aro akan screen É—in wayar, É—an zaro eyes É—ina na yi sannan na tura bakina kaÉ—an na ce "Ko me ya sa yake kira na rai?"
Rafi'at da ke gefena ta ce "Waye?"
Ban kula ta ba coz lokacin na yi picking call ɗin, sallama na yi na gaida shi, bai amsa gaisuwar tawa ba na ji ya ce "Ke wato Jannat kina so ki nuna min cewa kin fi ƙarfina ne ko me?"
Na ce "BB me ya faru?" Ni dai iya sanina babu abun da nayi.
"Tambayata ma kike ko? Didn't I warned you people not to engage yourself in any social media platforms bayan Whatsapp?"
A É—an tsorace na ce "BB Ni kuma? Ba na komai fa, wallahi..."
Cikin ɓacin rai na ji ya ce "Will you shut that your big mouth ko sai na ɓata miki rai? Ki yi laifin tsabagen kin raina Ni za ki ce min ba ki yi ba? Am I your mate?"
Na girgiza kai kamar ina gabanshi na ce "No"
Ya ce "Ki tabbatar in na dawo sai na sauya miki kamanni perhaps hakan ya ladabtar da ke ki daina yin hotuna kina É—aurawa a media"
Yana faÉ—in haka ya katse kiran.

Ai nima kamar jira nake ya katse kiran na fara lalumen buɗe IG da tiktok ɗina amma kash, IG ɗin ya ƙi loading alamun data na ya ƙare, Rafi'at na kalla wacce hankalinta kwance take kwance sai chat ɗinta take, ɗaka mata duka na yi ina faɗin "Wai ke ina cikin tashin hankali ke kuma hankalinki kwance ma chat kike?".
Tashi ta yi ta zauna tana hararana.
Na ce "Don Allah wayar taki da data ki ban aro?"
"Me zaki yi da shi?"
Cikin tashin hankali na ce "Ni in za ki ba Ni kawai ki ba Ni Malama"
Yatsina fuska ta yi ta ce "To na ga dai ba assignment za ki yi ba"
"To kar ki bayar dalla, ki cinye abunki?"
Miƙo min ta yi, da har na ce zan yi zuciya sai kuma na miƙa hannu na karɓa na yi connecting hotspot, nan da nan na shiga IG na Fara laluɓa account ɗina ban ga komai ba, na shiga tiktok account ɗina me zan gani? Hotona da Rafi'at ta yi min jiya ne wanda na yi kyau sosai.

Ɗaka mata duka na yi na ce "Shi ke nan kin kashe Ni Rafi'at." Na ƙarashe ina zuba mata idanu.
"Me na miki za ki maka min wannan dukan?"
Na miƙa mata wayata na ce "Duba ki gani, a rashin iya amfani da tiktok kin je kin posting min hotona har BB ya gani, Rafi'at kin kashe Ni!"
A razane itama ta tashi ta zauna tana zazzaro idanuwa "Na shiga uku, garin yaya hakan ya faru? Ke É—in yaushe kika buÉ—e account a tiktok?"
Maimakon ta taya Ni nemo maslaha sai ta jefo min tambayar yaushe na fara toktok, tsabar kaicinta da ya cika Ni sai na ce "ban sani ba"
Ta ce "shi ke nan, sai ki tanadi abun da za ki ce masa ai"
Tana faɗin haka ta fara ƙokarin komawa ta kwanta, cike da masifa na ce "To an gaya miki shi ɗin mala'ika ne da zan ji tsoronsa? Ke kuma in kin isa ki kwanta na yi kwantai, ki tashi mu samo maslaha tun da ke kika yi posting hoton"
Kallon ba ki da wayo ta aika min kafin ta ce "taki ake ji kuma, Ni sau nawa kina jefa Ni a uƙubar BB bayan kuma ba Ni da laifi?"
Ganin yadda ta ɗau zafi itama ya sa na sauƙar da murya na ce "Haba Rafi'at, yanzu haka za mu yi da ke?"
Dariya ta yi sannan ta ce "Ai na É—au kema BB É—in ce, ashe kin iya magana politely haka?"
Ban biye ta ba na ce "koma dai mene ne yanzu mu san abun yi kafin ya dawo"
Ta ce "to, kin goge hoton ina de?"
Na ce "A'a, ya riga ya gani, ba ki ga har comment ya yi ba akai?"
Ta ce "what? Mu gani"
Na mika mata wayar, kai ta jinjina na ce "Mun mutu"
Na ce "wallahi ba mu mutu ba, bari dai na goge yanzu"
Deleting post ɗin na yi sannan na ce "Haba! Wannan wace irin masifa ce wannan Rafi'at, wane irin hali haka BB yake da? Wannan ai abun ƙi ne a ce mutane na fargabar ko da ganinka ne, amma shi ina? Don Allah don Annabi at this stage of Life da muke miye Aibu don mun yi social media?"
Rafi'at ta jinjina kai ta ce "To ya za mu yi, kin san ko iyayenmu ba su da say akan hukuncin BB"
Na ce "Gara ma Daddy da Mommy, ammma Ummi da Abuya kam su suke ƙara ɗaure mishi gindi yana maida mu kamar ƴaƴansa, Ni wallahi na fara gajiya da rayuwar takura irin ta BB, duk ta silar shi ga shi ko dangi ba wani saninsu muka yi ba."

Rafi'at ta ce "Ni fa kin ga, Mommyn Misau ma ba wani saninta na yi ba, in ban dan albarkacin zuwa gidan Dada ai da ba za mu taɓa saninta ba tun da ita mijinta ba barinta yake tana yawo ba, ƴaƴanta kam ba na ce zan tuna wani cikinsu ba"

Na jinjina kai na ce "Allah dai ya kyauta, Ni yanzu har na Fara gajiya da zaman gidan nan, Gara ma na yi aurena na huta da fargabar wannan bawan Allahn"
Rafi'at dai ba ta ce komai ba, komawa ta yi ta kwanta abunta bayan ta karɓi wayarta, shigowar saƙo cikin wayata ya sa na duba, Data aka saka min amma ban san waye ba, damuwar halin da nake ciki yasa ban ma damu da na San koma waye ne ya tura ba.

Washe gari da na je school ma Dr. Junaid ya zo wurina a school and lucky to him, mun samu lokaci sosai. Haka kawai yau na ji in saki jiki da shi muka yi hira sosai, hirar da ta min dadi ba kaɗan ba though kusan dukkanta shi yake riƙe da akalarta. Tabbas yau na ƙara fahimtar Dr. Junaid fiye da tunani, da haka ta min sallama ya wuce abunsa.

Yana tafiya kuwa baba Driver ya iso, na shiga mota cikin walwala muka koma gida, ina fitowa daga mota ban bi ta kan Rafi'at ba na wuce part din Mommy a madadin sashen Ummu tun a bakin kofa na ji zuciyata ta yanke, school bag ɗina na yi dropping sannan na cire uniform ɗin jikina tare da watsa ruwa na saka wata riga maras nauyi, fitowa a toilet ya yi daidai da shigowar Rafi'at ɗakin, ta dube Ni ta ɗan taɓe baki sannan ta ce "Da ba ki jira Ni ba kin kyauta"
Ba tare da na kalle ba na ce "A'a, to zafi ne ya addabe Ni dole kin ga na cire wadannan uniform ɗin kafin na ji sanyi." Ina faɗin haka na fice tare da nufar dining,ajiyar zuciya na sauƙe bayan buɗe flask ɗin da ke jere ɗaya bayan ɗaya tare da yamutsa fuskata, gaba ɗaya girki da ke jere babu wanda ya min, kitchen na nufa don dafa ko da noodles ne idan na taɓa sai na je part ɗin Ummi na dubo me ta yi.

Ina tsaye ina tunanin guda nawa ne za su ishe Ni wata irin fargaba ta mamaye ruhina sakamakon ƙamshin turarensa da na ji ya kaure kitchen ɗin. Da wani mugun speed na juyo ai kuwa idanuwana suka sarƙafe cikin nasa, wani irin waro idanuwana na yi yayin da ƙafafuna suka saki har suna shirin kasa ɗaukata sai ma wani ɓari da suke yi.
Cikin raina na ce "Shi ke nan, na gama yawo"
Murmushin da BB ya saki ya sa Ni ƙara shiga wani tashin hankalin da ya ninka na baya, don na gama tabbatar da cewa wannan murmushin ba na Allah da Annabi ba ne.

Cikin takunsa na ƙasaita ya fara takowa kusa da Ni, yayin da na kasa ɗauke idanuwana daga gare shi na kuma kasa ko da motsa wata gaba a jikina.

Gyaran murya ya yi, hakan ya sa Ni dawowa cikin hayyacina, saurin girgiza kaina na yi trying hard to be normal yayin da na shaƙi wata iska tare da fesar da zazzafar iska.

A hankali na ce "Sannu da dawowa BB"
Ya dube Ni tun daga sama har ƙasa sannan ya wani yamutsa fuska.
"Me kike girka mana ne?"
Ban san lokacin da na É—ago idanuwana na sanya su cikin nasa ba jin maganar da ya yi amma ga mamakina babu wani reaction akan fuskar tasa da ya wuce ma kwanciyar hankalin da na gani shimfiÉ—e kanta.

Kansa da babu wata wadatacciyar suma ya shafa kana ya juya, ajiyar zuciya na yi saurin sauƙewa tare da jinjina kaina, sai da ya kusa barin kitchen ɗin sai kuma ya dawo, Ni dai har lokacin ina tsaye wurin da ya bar Ni, kitchen cabinets ɗin ya fara buɗewa ɗaya bayan ɗaya kamar mai neman wani abu, taɓe baki Ni dai na yi tare da sauƙe numfashi tare da juya masa baya ina jiran ficewarsa.

Kamar a mafarki na tsinkayi Muryarsa na kiran sunana, I tried to hesitate Kar na je sai na juya kuma ba kiran nawa ya yi ba.
"Hey!" Muryarsa ta ƙara sauƙa a kunnuwana.
Saurin juyawa na yi ina faÉ—in "Na'am BB"
Cike da isa ya ce "Come here" Yana illustrating circle da yatsarshi, ba musu na ƙarasa kusa da shi tare da tsayawa a wurin da ya nuna min yayin da kaina ke ƙasa
"Take this"
Ɗagowa na yi don ganin mene ne, wani ɗan ƙararramin cup ne irin extra gift da ake samu a pack ɗin wani abu kamar maggi, da sauransu.

Hannu na da na karɓa tare da riƙe cup ɗin.
"Follow me" ya faɗa yana mai fara stepping cikin takunsa na ƙasaita, har sai da ya isa parlour ya zauna kan kujera tukun ya kai dubansa gare Ni.
Zaro wayarsa ya yi tare da faÉ—in "ÆŠauko min bucket"
Da sauri na juya na nufi kitchen tare da dauko bucket É—in na kawo gabansa na ajiye ina faÉ—in "Ga shi"
Ya dube Ni ya ce "Using this cup da ke hannun ki, lemme check the time" wayarsa ya duba yayin da ya bar Ni tsaye ina jiran jin cikakken bayanin nasa.
"It's five minutes past five, Ina duba lokaci ina kika wuce 30 minutes ko?" Ya jinjina kai sannan ya ce "Hmm" tare da cije lips É—insa.

Cikin rawar murya na ce "ehm, e, ehm BB me za a yi?"
"Kina zuwa kitchen sink kina ɗebo ruwa da cup ɗin har ki cika min bucket ɗin nan" ya ƙarashe yana nuna min bucket ɗin da yatsarsa.
"What?" Na fada cikin raina yayin da na zaro idanuwana da suke cike da tsoro waje.
Gira ya É—age min sannan ya ce "Your time already start Jannat"

Gagara tafiya na yi tsabagen yadda na firgita sai na cup ɗin hannuna da na duba Sannan na ƙara duban bucket ɗin, yanzu fisabilillah ta ya zan iya cika bucket ɗin nan da wannan ƙararramin cup ɗin beside ya san ruwan a hankali yake zubowa ai.

Ganin na ƙi motsawa ya sa BB daka min tsawa ta ce "Za ki wuce ki fara ne ko sai jikinki ya faɗa miki?"
Bai kai ga rufe baki ba na ɗiba a guje na nufi kitchen, duk ƙarantar cup ɗin sai da na kusa minti guda tsaye tukunna ya cika sakamakon yadda ruwan ke zuwa a hankali, haka na fito na zo na juye cikin bucket ɗin sannan na juya da gudu saboda na samu na yi akan lokaci kafin na ƙara yin wani laifin.

Haka na yi ta jido ruwan nan yayin da BB ke zaune yana daddana wayarsa ya wani harde ƙafarsa ɗaya kan ɗaya kamar wani basarake.

Na yi ya kai sai ashirin Amma yadda kuka san cup ɗaya na zuba a cikin bucket ɗin, Ni dai nake ganin ma ko kwana aka ce na yi ina zuba ruwan nan da cup ɗin da ya ba Ni ba lallai bucket ɗin ya cika ba gashi gaba ɗaya jikina ya yi tsami, ga yunwar da nake ji ta ƙara dawowa sabuwa kar, halin da nake ciki is a true definition of TSAKA MAI WUYA.

Yanke hukuncin ba shi haƙuri na yi idan na kawo wannan san, hakan ya sa bayan na juye na fashe da kuka ina faɗin "Don Allah BB ka min afuwa wal..."
Katse Ni ya yi ta hanyar faÉ—in "Will you wipe these your crocodile's tears and keep doing your tasks or?"
"Don girman Allah BB na tuba na bi Allah..."

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 16 · 0% Book details