← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 26

CHAPTER 23:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Wuraren ƙarfe Sha ɗaya na ji shigowar BB ɗakin, hamdala na yi da ya kasance ba na parlour, Ina ji suka gaisa da Mommy Rafi'at ma ta gaishe shi.
Sallamar da na ji ya yi wa Mommy ya sa Ni jin wani sanyi a raina duk da cewa zaman da muka fara yanzu da shi ya min daɗi ƙwarai amma tun daga daren juya nake jin cewa nasanta kaina da shi shi ne kaɗai maslaha gare Ni.

Addu'o'i Mommy ta ringa yi masa, bayan ta gama nata Rafi'at ma ta ɗaura da nata. Har ya juya zai fita sai kuma ya dawo sakamakon rashin sukuni da zuciyarsa ke ciki na rashin ganin Abar ƙaunar tasa hakan ya sa shi dawowa ya dubi Rafi'at ya ce "Ina jannat?"
Ta ce "Tana ciki, ina tunanin Bacci take"
Ba don ya so ba ya ce "Fine, Mommy na wuce"
Mommy ta amsa mai da "Allah ya tsare hanya" daga haka ya fice cike da takaicin rashin ganin Jannat É—in.

A ɓangarena ajiyar zuciya na sauƙe jin amsar da Rafi'at ta ba shi akaina.

Ina kwance idanuwana lumshe na miƙe zaune, sauƙa na yi daga kan bed na nufi bakin drawern da na jefa wayar da ya kawo min, tsintar kaina na yi da ɗauko lettern da ya bar min ina ƙara karanta ta. Jin motsin shigowar mutum ya sa Ni ba shiri mayarwa na rufe.

"Wai dama idanuwanki biyu?"
Rafi'at ta tambaya hannunta na riƙe da labule
Fuska na yamutsa tare da juyawa ina fuskantarta "E"
Kina ji "BB na nemanki kuma kika yi shiru?"
Na ce "To sai me, bayan kin ce ina Bacci so kike na fito kuma?"
"Kya ji da shi kuma"
A É—an hasale na ce "To ai da kin zo kin ja Ni kin kai Ni na masa sallamar tunda Ibrahim Shirama ne"
Kafe Ni ta yi da ido jin ta yadda ba ɓullo, cikin sanyinta ta ce "Abun bai kai ga haka ba Jannat, Allah ya ba ki haƙuri"
Na ce "In ya ba Ni Ki ƙwace" ba ta amsa min ba ta fice a ɗakin.
Ganin ta fita ya sa na ja dogon tsaki kana na ce "Daga mutuncin Æ´an kwanaki da ya mata har ta manta irin muguntar da ya shata mana"

Kan gado na koma na kwanta tare da yanke shawarar kada na sanar da ita komai batun BB, sannan kuma na ranƙwashi zuciyata tare da shawarar watsar da komai da ya danganci kalaman BB, mafitar da na samu shi ne duk lokacin da ya tayar da maganar kawai na ce da shi ban gama shawara ba ya ƙara min lokaci. Da wannan shawara na ji kamar an yaye min wani tulin nauyi da ke kaina.
Tare da Ya Sadiq suka tafi, har Bauchi ya kai shi sai da jirginsu ya tashi ya dawo gida. Tun da BB ya shiga jirgin gaba É—aya ya kasa sukuni wanda hakan na da nasaba da rashin ganin Jannat kafin ya tafi, ga shi ya tafi ya bar ta, bai san wa da waye za su kula ta ba, uwa uba kuma rashin sanin nashi stand É—in, wanda hakan ya sa shi lumshe idanuwansa.

Jawabin da ya ji ana yi gare su game da saka belt ya sa shi aiwatar da hakan, babu jimawa jirginsu ya tashi. Ya Khalid ne ya zo ɗaukarsa tare da Nimrah. Jakarshi Ya Khalid ɗin ya saka a Boot, shi kam bai ma san da Nimrah aka zo ba sai da ya gyara zamansa a cikin motar zazzaƙar muryarta ta sauƙa akan kunnuwansa tana gaida shi.
Amsawa ya yi daidai lokacin da Ya khalid ya ja motar.
"Sannu da Hanya Yaya Khalil"
Ba tare da ya juyo ba ya ce "Yauwa Nimrah, yaya islamiyya?"
Ta amsa mishi da "Alhamdulillah" cikin muryarta wacce ke fita kamar balarabiya sakamakon sabo da harshenta da ya yi da karanta Alqur'ani tare da bashi duk wasu haƙƙoƙinsa.

Ya Khalid ne ya dubi BB É—in ya ce "Ai ba É—auka Jannat ba za ta bari ka dawo ba"
Harararsa BB ya yi ganin yadda ya kawo topic É—in a gaban Nimrah wanda ya rasa dalilin da ya sa idan tana wuri yakan ji shi uncomfortable sai dai ya danganta hakan da Kasancewarta nutsattsiya kuma mai kamun kai, ba kamar sauran matan da ya yi ta cin karo da su ba.

Suna isa BB ya samu kyakkyawar Tarba daga Mami da kuma Big sis, Mufeed da kuma Sophie Wanda suka zo yinin gida, zo ka ga yadda suke nan da nan da shi kamar za su cinye shi, shi kansa kowanne lokaci yakan ƙara godewa Ubangijin da ya haɗa shi da Ya khalid da kuma familynshi da suke tsananin ƙaunarshi, jakar snacks ɗin ya ajiye musu yana faɗin "Bari na je na watsa, wanan Ummi ce ta ce a kawo"
"To madalla! Madalla"

Tare da ya Khalid suka nufi É—akinsu sai Uwar zuba Ya Khalid É—in ke yi.

A nan ɓangarenmu yau ne muka karɓi baƙuncin Mommy Misau da kuma Nasmah, wanda suka zo da kuma alamun za su yi kwana biyu, farin cikin zuwan nasu ne ma ya sa na ƙara yasar da batun BB.

Kwanana uku ina ajiye da wayar da ya kawo min sai a rana ta huɗu na fito da ita tare da nunawa Rafi'at da Nasmah a taƙaice na ce musu yanzu Ummi ta ba Ni, wai BB ne ya siya min a madadin wayar da ya fasa min.

Nasmah da Rafi'at ne suka kalli juna tare da kashewa juna ido, cikin haÉ—in baki suka ce "Iyyyeee"
Fuska na yamutsa Sannan na ce "Ai shi ya fasa min tawa akan abun da bai taka kara ya karya ba"
Nasmah ta ce "garin yaya"
Nan Rafi'at ta ba ta labari tas, Nasmah ta dube Ni ta ce "Sister anya kuwa ba sonki BB yake ba?"
Gabana ne ya bada wani irin sauti, a É—an tsorace na ce "ba dai sun gano wani abun ba!" Cikin raina na yi maganar hakan ya sa ba su ji Ni ba, Rafi'at ce ta kwashe da dariya sannan tace "Wallahi kuma Nas, kema sai kya faÉ—a, Ni wallahi gani nake ma kamar raina mana hankali take soyayyar suke yi, ki ga fa waya don Allah! Kuma kin san me?"
Saurin rufewa Rafi'at baki na yi tare da harararta "Wai ke lafiyarki kuwa?" Duban Nasmah na yi na ce "Ke kuma ki zauna tana ɗaura miki karatun ƙarya, ku kanku kun sani Ni ba na soyayya, beside ko zan yi ma kun sani tsarina, ba namiji irin BB zan so ba"

Nasmah ta taɓa baki sannan tace "Lallai yarinyar nan, to wallahi yau in aka ce kin samu ya BB wallahi kin gama morewa"
"Rabu da ita dai, Yayana ai sai mace mai Sa'a" Rafi'at ta faÉ—a tana É—agewa Nasmah gira"

"Ikon Allah" na faÉ—a cikin raina "Na gode Allah da ban faÉ—a musu cewa BB na so na ba, tabbas waÉ—annan biyun will do whatever to see su samar mishi da soyayyata which I'm not hoping for"
Ya zama min dole na yi taka tsantsan da takuna kafin su gano hakan.

Washe gari bayan na dawo daga school kasancewar washe garin tafiyar BB muka koma su Nasmah suka raka Ni Wani shago na yi sim swap Sannan na sayo charger, Bluetooth da sauransu, sauran kuÉ—in dubu takwas na saka su a opay É—ina.

Da daddare na gama saita da waya tsaf, na É—aura Whatsapp É—ina a Kai.

Ƙarfe takwas na shiga ɗaki na bar su Nasmah a parlour suna hira da Ummi da Mommy da Mommyn Misau da kuma Rafi'at.

Ina cikin chat a Whatsapp sai ga Salam daga wata number, abunku da wacce ta yi welcome back numbern ba su na.
"Wslm" na yi typing na tura ba jimawa aka ce "Ykk"
Na ce "Kalau, and You?"
"Ƙalau nima, how studies?"
Na tura "Alhamdulillah"
"Ma sha Allah" ko da na buɗe na ga ma sha Allah sai na fice na bar Mai numbern a blue ticks, ba jimawa naga ana typing, sai kuma aka Turo Abu buɗewa na yi "Me ya sa ba ki kira Ni ba bayan na ce ki kira Ni, ko ba ki ga saƙo na ba?"
Gaba É—aya ban kawo cewa BB ba ne a raina, hakan yasa na tura "Ban gane ba"
Emojin Murmushi aka turo min da kuma "You'll never change, Captain Ibrahim Abubakar Shirama ne, your big bro"
Emojin surprise na tura sannan na ce "Yi haƙuri BB ban gane ka ba ne, ka san in mutum ya yi swapping SIM ɗinshi yana rasa contacts ɗinshi me"
"No problem " shi ne abun da ya Turo.

Murmusawa na yi tare da gyara kwanciya ta na tura masa "Thanks, ka isa lafiya? Ya mutanen gidan"
Ya Turo min "Lafiya lau, suna ma gaishe ku"
Na ce "Uhm, muna amsawa, amma sun sanmu ne? Ina Ya Khalid?"
Ya Turo min "Lafiya ƙalau yake, shima ya ce a gaida ki"
Surprise emoji na tura tare da faÉ—in "ina amsawa"
"Ok, kun koma school ko?"
Na tura mishi da "Yes"
Ya ce "Fine, Allah ya ba ku Sa'a, a yi karatu da kyau Banda kula samari da ƙawayen banza" tsintar kaina na yi da sakin Murmushi sannan na fara typing "in Sha Allah"
Ya turo min da "Kar Na takura Miki, bari na bar ki kiyi Bacci kar ki makara da safe"
Stockern Murmushi na tura masa, ina ƙoƙarin kashe data sai ga message ɗinshi ya shigo.
"As the stars shine above, my heart only beats for you 💞. The night feels empty without your words or your voice to soothe my soul 💌✨. You are the dream I want to hold onto forever, the reason my heart smiles even in the dark 🌹.
Mi corazon, before you close your eyes, Remember you’re always on my mind, and my heart belongs to you tonight and forever, Sleep peacefully, Good night."

Saurin kashe data na yi sakamakon rashin sanin amsar da zan tura mishi, ƙara shiga chat ɗin namu na yi na sake karantawa daga farko zuwa yadda muka tsaya, murmusawa na yi na ce "Hmm" daga haka na shige cikin blanket, ba jimawa Bacci ya kwashe Ni.

A ɓangaren BB ganin Jannat ta yi viewing last chat ɗin nasa amma ba ta yi reply ba ya sa shi jan siririn tsaki, Wani irin takaici ne ya kama shi sai ya ji dama bai dawo ba, kuma dai yanzu ne ya kamata ya jawo jannat jikinsa, su samu fahimtar juna ta yadda za ta kamu da son shi kamar yadda yake ɗawainiya da tata soyayyar. Kashe datarsa ya yi daga nan ya ɗauro Alwala ya kwanta ba tare da ya kira Ya Khalid da ke yin waya a parlour ya dawo ciki ba.

Satinmu guda da komawa school aka mana speciality posting na tsawon 2 months , sosai Na ji daÉ—i ko ba komai ma huta da uban note É—in da ake É—irka mana da kuma zaman lectures. Gynae emergency aka kai Ni, kuma wannan karon muma students Za mu yi shifting kamar yadda staffs suke yi, a ranar aka mana roster, zan yi morning na seven days, sai na yi 3 days off, daga nan na fara night na seven days, sai na yi seven days off, in na dawo kuma sai na yi evening na seven days four days off, haka kuma sai mu yi rotating mu koma post Natal ward.

Kwanana biyu ina zuwa morning sosai aikin ke min daɗi, a kwana na huɗun ina zaune Ni da Maryam Muhammad Mahmud, da kuma Joanna John, dama tare muke shift da su, muna cikin zaune lokacin aiki ya tsagaita sai ga Dr. Junaid ya zo, gaishe shi muka, ya amsa daga nan ya ƙarasa nurses station, ban san me ya cewa Nurse on duty BA na dai ji ta ta ce "To babu damuwa"
Daga nan ya dawo wurinmu ya dube Ni ya ce "Jannat"
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 24 · 0% Book details