← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 26

CHAPTER 5:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

"Ba abun da kuka yi sai shegiyar rawar kan tsiya, saboda haka, ku sa a ranku ma day school za a nema muku, za kuma kuna zuwa islamiyya don ba zai yiwu mu zauna gida da masu duhun kai ba, ɓata min lokaci kuma da kuka yi, za mu haɗu ne, for now, ku je ku yi breakfast ku yi wanka, sannan in kuka ga masu aiki sun shiga kitchen ku bi su ku taya su, idan kuka saɓa abun da na faɗa," sai kuma yayi shiru yana cije gefen lips dinsa alamun mun san sauran.
Da sauri muka haÉ—a baki muna faÉ—in "Mun gode BB, Allah ya saka da Alkhairi."
Daga haka kuma muka wuce sai sauri muke kada mu je mu ƙara yin wani laifin ya ƙirawo mu.

Sai da yaga ficewarmu daga garden ɗin tukun ya miƙe ya nufi part ɗin Ummie, wanka ya samu yayi ya shirya cikin wasu ƙananan kaya da suka amshi jikinsa yayin da ya fito hannunsa riƙe da wayarsa sai zuba ƙamshi yake yi. Babu kowa a dining lokacin, hakan yasa ya zauna tare da ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya fara danna wayar tasa cike da isa da mulki, Mama Sala ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da wani bowl, ganinsa yasa tayi saurin ƙarasowa tana faɗin "A'a, har ka fito ke nan."
Fuskarsa ya É—an saki don kuwa sosai yake mutunta Mama Sala, "Na fito Mama, yaran nan kuwa sun shigo kitchen É—in nan?"
"Ƙwarai ai tare muka haɗa karin kumallo da su, ga abun karyawarka."
Ta idasa tana ajiye masa bowl É—in da ke É—auke da sliced fruits of different kind.
"Na gode Mama" ya faɗa tare da kai hannunsa ya jawo bowl kamar wanda dama shi yake jira, Bismillah yayi ya fara sha a hankali har ya gama, bayan ya sanye yayi hamdala, mintuna biyu yayi zaune ya miƙe ya nufi bedroom ɗin Ummie don yana da tabbacin cewa tana ciki.

Knocking ƙofar yayi kafin ya murɗa handle ɗin ƙofar, Da sallama a bakinsa ya shiga, jin babu response yasa ya tabbatar tana bayi, hakan yasa ya wuce part ɗin Ummi. A mutunce suka gaida da Ummi ta gabatar masa da fruits itama, babu yadda ya iya haka ya karɓa ya taɓa don ba zai iya ce mata a'a ba tun da can dama kullum in yana garin a nan ɗin yake sha. Kaɗan ya taɓa sannan yayi hamdala.

Cike da kulawa Ummi ta dube shi tace "Khalil"
Amsawa yayi da "Na'am Ummi"
"Kun gaisa da Daddynku ne?" Ya jijjiga kai
"Ok" kawai tace tayi shiru, dubanta yayi yace
"Ummi nace wai yaran nan kuwa ba za su dawo day school ba?"
An taɓo wa Ummie abun da ke mata ciwo hakan yasa tace "Ba dai su Jannat ba?"
Ya gyaÉ—a mata kai
"Wallahi Khalil Nima ba na son wannan boarding É—in irin tasu, yara duk sun tashi sakaka, dama Daddy ne ya nace amma Abuya ma bai so, nima gaskiya ina ga yanzu kam ya kamata a sauya hanya."
"Haka ne kam Ummi" ya faÉ—a yana gyara zama "Gaba É—aya rawar kai ta musu yawa, common sallah ba iyawa suka yi ba bare kuma suke yi, Alqur'ani kuwa babu, zan yi magana da Daddy in na dawo, gobe zan kai su islamiyya, idan result nasu na Common entrance É—in ya fito sai a nema musu wata school haka mai kyau."

Murmusawa Ummi tayi tana ƙara yabawa BB, tunaninsa na manya ne, ra'ayoyi nasa da yawa sun zo daidai da nata shi yasa tun yana ƙarami ya fi zama da ita fiye da Mommynsa.
"Ma sha Allah, Allah yayi albarka Khalil, ya ƙara girma"
Da "Amin" ya amsa mata, nan suka taɓa ƴar hirarsu kafin yayi mata sallama. Addu'a ta masa sannan ya wuce, part ɗin Mommy ya wuce, lokacin kam tana bedroom ɗinta hannunta riƙe da wani littafin addini yayin da ta sanya farin glasses ɗinta wanda ke taimaka mata wurin gani.
Gaisawa suka yi yake tambayarta yashe Daddy zai dawo, tace masa yau, daga nan sallama ya mata ya fice, bai bi ta kan driver ba ya wuce abunsa.

A ɓangaren mu tun da muka samu muka bar garden muka saka a na kare sai part ɗin Mommy, ba mu tsaya ko ina na muka nufi ɗakinmu, muna shirin shigo muka jiyo Mommy na faɗin "lafiyar ku kuwa kuke wanann uban gudun??"
Dif muka ci birki kamar abun hawan da aka tsayar, kamar munafukai muka juya muka tsaya gaban Momyn.
Kallo Mai cike da tambayar da Mommy ke aika mana yasa Ni saurin faÉ—in "ga mu Mommy"
"Lafiyarku kuwa?" Ta tambaya tana mai ƙara nazartarmu.
Da sauri Rafi'at ta saita muryarta tace "Laa Mommy ƙalau muke fa, mun dai ɗana bayin flowers ne mun gaji, wanka muke son yi ba mu lura ma da ke ba ne ko Jannert?"
Ƴar dariyarsu tayi irin ta manya kana tace "To, ku je ku yi wankan" sai da suka wuce ta jinjina kai kana ta ce "Lallai dodonsu ya dawo kam, dubi yadda suke rarraba ido. yanzu duk za su bi su rame, Gara ya gama hutunsa ya wuce, ko kuma su wuce wurin Dada in ya wuce sa dawo in ba haka ba sai ɗan buzunsu, su da rashin ji, shi kuma da tsaurin rai."

Muna shiga ɗakinmu Rafi'at ta dube ni tace "Kai gaskiya yau da Sa'a muka tashi, ki ba BB bai haɗa mu da punishment ba, Allah mun gode maka" ta wani sauƙe ajiyar zuciya kamar wacce ta tsira daga hannun ƴan boko haram.
"Ke?" Ni da na fi ta shan wahala nace "Ni zan ce miki mun taki Sa'a, yanzu dai mu samu mu gasa jikinmu don wallahi na gama yawo nikam, ko breakfast ba zan yi ba baccin wahala zan yi, ki tashe Ni don Allah idan Mama Sala ta fara aikin lunch."
Da sauri Rafi'at tace "Kan bu! Idan kin isa na tsaya a nan, yadda kika gaji wallahi na fi ki, don haka ki tabbatar in kika kwanta Ni ba zan tashe ki ba, don wallahi barin ki zan yi in yazo ya ganki ke É—aya ya ba ki kashi."
Marairaice fuska na yi ina faÉ—in "Allah sarki, yanzu Rafi'at yaushe kika fara kware min baya? Don Allah ki taimaka min ki bar Ni na kwanta."
"Can ta matse miki, kin ga shiga ta toilet" Rafi'at ta ba ta amsa tana mai shigewa bayi abunta.

Bayan mun yi wanka dining muka nufa, Sauran abincin da ya rage muka ci, daga nan muka tafi part É—in Ummi don yin abun da ya dace da mu a yanzu. Tare muka yi lunch aka jera a dining ba mu tsaya ci ba muka dawo part É—in Mommy gaba É—aya jikinmu a gajiye. Sallar azahar muka samu muka yi don har ga Allah nasihar da Mommy ta mana jiya ta ratsa mu, kai ko ba don wannan nasiha ba, abun ka da yara. Wallahi gani muke kamar BB na ganin mu. Whatever the case may be, da alamun sauyi dai ya fara samuwa a tattare da mu.

Rafi'at na kalla bayan mun yi sallar azahar na ce "Allah sarki, mu kan mun gama yawo Rafi'at, yanzu haka za mu yi ta rayuwa har hutunmu ya ƙare?"
Rafi'at ta dube Ni ta ce "To ya za mu yi? Allah na jarrabar kowa, mu tamu jadrabawar BB ne wallahi"

Na marairaice fuska kamar zan yi kuka na ce "Hmm, Ni kaÉ—ai na san me nake ji a tattare da shi, Rafi'at Wani lokacin ko sunanshi aka faÉ—a wollah ina firgita sosai, Allah dai ya sanyaya ran BB ya yi rayuwa irin ta mutane"
"Amin fa." Rafi'at ta faÉ—a tana sanya idanuwanta cikin nawa "Wai kin ji islamiyya zai kai mu, kuma za a cire mu a Dolphin a mayar da mu wata daya school haka"
Kamar na cilla ihu haka na ji, mun saka rai sosai kan in min shiga secondary mu ma za mu yi enjoying kamar yadda muka ga Æ´an secondary ke yi, mun tsara abubuwa mabanbanta da rayuwarmu za ta tafi kai.

Kwanciya muka samu muka yi. Take wani wahalallen bacci yayi abin gaba da mu, Rafi'at ce ta fara farkawa jin ana kiran sallar la'asar, tashi na ta yi, muka yi salla, daga nan muka nufi part É—in Ummi. Sallar magrib da iska ranar suka min yi muna yin dinner kuwa da wuri wuri muka kwanta don har lokacin jikinmu tambayarmu yake kasancewar aikin da muka yi ya girmi shekarunmu ga kuma rashin sabo a ciki.

Washe gari ma BB ne ya tayar da mu daga Bacci sannan ya wuce masallaci, da ya dawo ya tarar mun koma ya ƙara tayar da mu daga Baccin ya ce Mu yi karatu zuwa wayewar gari sai mu je kitchen mu ga yadda su Mama sala ke girki, mu tabbatar mun taimaka musu da abubuwan da za mu iya. Hakan ce kuwa ta kasance, bayan mun kammala muka koma part ɗin Mommy. Kamar yadda na faɗa muku dama, Mommy mace ce mai sanyin hali, ai bayan mun je haka ta tsare mu ta ce Lallai sai mun faɗa mata dalilin da ya sa muke shigewa ɗaki ba kuma ma walwala, da ta matsa akan sai ta sani ne nan muka faɗa mata komai, kai kawai ta jinjina tace zai shigo ya same ta.

A ranar da Azahar BB ya kwashe mu ya nufi da mu wata makaranta Bilal academy, da take lokacin makarantar iya yadda ake yi, sai da ya gama mana cuku-cukun komai kafin ya koma, da yamma kuma bayan an tashi ya zo ya ɗauke mu. Duk wannan abu da ya faru cikin Ummi da Mommy babu wanda ya san da aukuwarsa, sai da muka koma ne muka shiga part ɗin Ummi take tambayarmu "ina kuka ɓuya? Ko dai kuna can muna baccin asarar ne?"
Ni da abun ya ci damuna na ce "Ummi BB ne ya kai mu islamiyya wai ba mu iya komai da ya danganci Musulunci ba, yanzu Ummi mu da muka zo hutu muke shirin komawa me ya sa za a kai mu islamiyya don Allah?"
Bakina Ummu ta buge tana bi na da kallon takaici "Ba za ki taɓa yin hankali ba Jannat! Don ubanki idan ya shigo ko tare shi ki faɗa masa abin da kika faɗa min kin ji?" Tana gama faɗin haka ta ƙara kawo min duka tana faɗin "Na rasa yaushe za ki yi hankali Jannat, ke shi ke nan sai dai ki yi rayuwa sakaka haka kike so? To bari ki ji, ungulu ma da ta rasa mafaɗi kashi take ci. Haka kika ga ƴar'uwarki tana yi? Ina ce dai duka tare aka saka ki a islamiyyar? Kin ji ita tana ƙofafi ne?"

Bakina na turo gaba, ba tare da na aune ba na ji sauƙar hannun Ummi akai ta buge min shi. Kukan shagwaɓa na saka ina damfe, yadda na ga ya yunƙuro za ta cafko Ni ya sa na ruga a guje sai part din Mommy. Bayan tafiya ta Ummi ta dubi Rafi'at sannan ta ja ta jikinta ta ce "Rafi'at kina yi wa wannan ƴar'uwar taki nasiha, na ras game ko iskokai ne da ita ko me? Islamiyyar da Khalil kuma ya kai ku an jima in ya dawo da ke da Jannat ku ne ku masa godiya, ƙaunarku ce ta sa ya muku hakan, duk wanda ya ke nuna maka hanya yake faɗa maka gaskiya ko da yaushe son ka yake da rahama, wanda ba ya son ka kuwa ko zargin Allah za ka yi ba zai ce maka uffan ba, zai zuba maka ido ne ka yi abun da ka ga dama."

"Kina faÉ—a mata gaskiya kin ji Rafi'atu?"
Rafi'at ta gyaÉ—a kai sannan ya ce "Na ji Ummi"
Ummi ta dube ta ta ce "na san hankalinki ya yi tun ta ai tun da ta tafi, je abun ki, ki tabbatar kun ke kun masa godiya kin ji?"
"E" Rafi'at ta ba ta amsa tana bin bayana.

A part É—in Mommy muka haÉ—u, Mommy ta dubi Rafi'at da ta shigo ta ce "Yanzu Jannat ke faÉ—a min wai Khalil ya kai ku islamiyya ko?"
Rafi'at ta gyaÉ—a kai tana faÉ—in "e Mommy"
"Shi ne ku kuma kuka wuce kuka tafi ba ku faÉ—a min ba"
"Mommy dai kin san halin BB ba ya son a ɓata masa lokaci, yanzu kam ai ga shi mun faɗa miki "
Mommy ta ce "To ai ban yi tunanin yau zai kai ku ba ma, Allah dai ya saka masa da alkhairi"
Ni dai "Amin" kawai na ce cikin raina kuwa baƙin ciki nake da yadda kowa bai ganin laifin BB, Mommyn ma da nake tunanin za ta yi magana akan saka mu islamiyyar da ya yi jin ta masa albarka ya sa na yi saurin miƙewa zan tafi ɗakinmu. Muryarta ne ta doki kunnena ya sa na tsaya
"E Jannat, ku je kam ku ce masa kun gode, don ba ƙaramin jahadi ya yi ba"
Ba tare da na juyo ba na ce "To Mommy" daga nan na wuce ɗaƙinmu zuciyata na tuƙuƙin dalilin da ya sa aka fi son sa a kanmu da kuma dalilin da ya sa komai ya yi ake ganin daidai ne.
Zuciyata nake ji wani iri, haka kawai nake jin kamar ba na ƙaunar BB, ta iya yiyuwa yarinta ne take ɗawainiya da Ni, amma a babin gaskiya na san da gaske nake har cikin raina ina ƙinsa.
Washe gari su Abuya suka dawo daga tafiyarsu, shi ya gama nashi workshop ɗin, daga shi har Daddy Babu wanda bai mana tsaraba ba, mun ji daɗin hakan ƙwarai da gaske.

Dawowarmu daga islamiyya Daddy ya mana kyakkyawan albishir na zuwan Dada ta yi kwana biyu a gidanmu. Murna sosai nake saboda ko ba komai zan yi rashin ji na son raina ba tare da Dadan ta bari wani mahaluki ya taɓa Ni ba kasancewar ni ɗin takwararta ne. Murnata gaba ɗaya ciki ta koma lokacin da na tuna BB na nan, duk zai kwashe ƴar kulawar da zan samu daga wurin Dadan.

Da daddare muna part ɗin Mommy bayan an yi Dinner Daddy ya kawo zancen islamiyyar da BB ya saka mu. Nan ya ja hankulanmu akan mu nutsu mu koyi abin da aka mana, ya faɗa mana cewa Alqur'ani na da falala sosai, har ya faɗa mana irin falala da darajar da mahaddaci sa ke da shi a wurin Allah a duniya da kuma ranar gobe ƙiyama, wannan bayani na Daddy shi ne ya sa na ɗan ji sanyi kaɗan a cikin zuciyata ina addu'ar Allah ya sa dai nima na shiga sahun mahaddatan, kuna mamakin dabi'u na ko? To babin gaskiya abun da ya sa nake wasu abubuwan Ni kaina na san rashin zama kusa da iyayenmu ne, tabbas da a gabansu muke karatu na tabbata za mu kasance nagartattu kamar dai yadda suke.

Bayan an gama cin abinci ne Daddy ya dube mu ya ce "Ibrahim ya ce Ku shirya da wuri gobe, akwai inda za mu je?"
"BB Kuma?" Na furta ina zaro idanuwana waje.
Daddy ya tabbatar min da shi É—in dai. Nan dai na tafi É—aki raina wani iri, daga nan Bacci ma ya kwashe Ni ba tare da na San yaushe Rafi'at ta dawo ba.

**********
Kamar yadda BB ya Fara sabar mana da tashin asuba, yau ma kafin ya wuce masallaci sai da ya biyo last É—in Mommy ya tayar da mu, bayan ya dawo ma ya biyo ya duba mu, gaishe shi muka yi ya amsa, ganin Alqur'ani a hannayenmu muna karatu ya sa shi ficewa ya koma part É—in Ummi.

Sanin cewa ya ce Mu shirya ya sa muka shirya da wuri, kasancewar muna tsoron yin laifi a wurinshi. Ko giftawarsa ba mu gani ba sai wuraren tara na safe, kamar ko yaushe sassanyan ƙarmshin sa ne ya ankarar da mu da shigowarsa parlourn, gaishe shi muka yi a ladabce, da "Lafiya" kawai ya amsa daga nan ya wuce bedroom ɗin Mommy, lokacin da ya fito mun riga mun fice muna tsaye jikin motar da zai fita da ita, ko da ya ƙaraso shigewa ciki ya yi ba tare da ya ce mana komai ba, dama ba mu yi expecting hakan daga gare shi ba.

Sai da muka yi sallama tukun muka shiga, abun mamaki ya amsa sallamar, Ni ce a front seat sai kuma Rafi'at a back seat. Mun share kusan mintuna biyar cikin motar bai tayar da ita ba bai kuma yi mana magana ba, wannan ɗabi'ar tasa na daga cikin abun da ke ƙara ba Ni mamaki akan shi, mutum ba zai iya buɗe baki ya yi magana ba sai ka ce Ubangiji ya haramta masa?

Ganin dai ba mu fahimci komai ba shi ma ya gaji da tsayuwa ya sa ya ja siririn tsaki Sannan ya ce "Gidan uban wa za ku je da mayafi?"
Ai kafin ya rufe bakinsa ma mun fara kiciniyar buÉ—e mota mu fita, sai da muka sanyo hijabi tukun ya ja motar.

Ban taɓa jin takaicin BB ba irin na ranar ba domin wata makaranta ya kai mu wai Ummul Qura science academy, makarantar Boko ne da islamiyya a haɗe, in aka tafi tun safe sai ƙarfe biyar ake dawowa. Haka ya baro mu a can, wuraren sha biyu Driver ya kawo mana abincin rana, ƙarfe biyar ɗin daidai BB ya zo ya ɗauke mu ya mayar da mu.

Kwana uku ya jera yana jigilar kai mu da ɗauko mu yayin da Driver ya ɗauki ragamar bayan tafiyar BB wurin Dada, kwana biyu ya yi a can ya dawo, daga nan ya wuce abun gabaɗaya, kar ku so ku ji irin farin cikin da na tsinci kaina da tafiyarsa, na so yin gardamar ƙin zuwa makarantar da ya saka mu amma gargaɗin da ya mana kafin ya tafi shi ya hana Ni.

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

_No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 6 · 0% Book details