← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 26

CHAPTER 12:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Two months BB ya yi sannan ya dawo kuma takanas saboda mu ya dawo, ai kuwa lokacin an fara sayar da fork É—in Midwifery ya siyo da kansa bayan ya kai Rafi'at ta yi online screening a ASCOE azare.
Bayan sun dawo gida aka cike min Form aka yi submitting, ranar da za a yi entrance exams BB ya koma, Driver ne ya kai Ni, bayan na gama ya dawo da Ni. Bayan kwana biyu aka kira Ni aka ce na ci wannan sashen, za mu je mu yi oral interview, zo ku ga farin ciki akan fuskata, a ranar da kaina na karɓi numbern BB na sanar da shi, ya taya Ni kurma ya kuma min fatan Allah ya ba Ni sa'ar cin oral interview ɗinma.

Yana sauƙe wayarsa Ya Khalid ya dube shi ya ce "Irin wannan farin ciki haka Babban Yaya?"
BB ya É—an harare shi kana ya ce "Jannat passed the first step, yanzu za su yi oral interview"
Ya Khalid ya ɗan kwaɓe fuska ya ce "Khalil"
BB ya dube shi
Ya ce "Har yanzu ba ka ganin abun da nake gane maka ko?"
BB ya ce "Me ke nan?"
"Yanzu ka yarda ta tafi Makaranta kafin ka furta mata muradinka?"
BB ya ɗage kafaɗa, Ya Khalid ya ce "Try to understand my friend, wallahi akwai illa sosai hakan, za ta yi interacting da mutane daban daban, You know how special she's, Ba abu mai wahala ba ne wasu mazan su yi ƙoƙarin samun kusanci da ita ba..."
"Na yarda da ita" BB ya faÉ—a a gajarce.
Ya Khalid ya ce "Fine, idan kai ba ka san ina ke maka ciwo ba Ni zan kira ta na faÉ—a mata komai"
Da wani irin sauri BB ya miƙe yana bin Ya Khalid da wani irin kallo, ya Khalid ya kashe masa ido sannan ya ce "Ya dai?"
BB ya wani kwaɓe fuska ya ce "A beg friend, don't spoil this fun, In Sha Allah wani juyin da za Ni sai na mata maganar ko?"
Ya Khalid ya ce "To, Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri"
BB ya amsa da "Amin".

Ranar oral interview Rafi'at ta raka Ni, muka shiga layin waÉ—anda za a yi wa interview É—in, har aka tantance mu na bar Rafi'at a reception, muka shiga, kasancewar ina cikin mutane na farko da aka fara yi wa da wuri na fito, na nemo Rafi'at muka wuce guda tun da dama Ba Driver na jiranmu. Washe gari ita ma na raka ta ta yi physical screening daga nan muka dawo gida.

Yau Laraba tun da na tashi jikina ke min ciwo hakan ya sa ban fita ko ina ba ina kwance, A yanzu dai ba na ce komai ba dangane da BB, ba na jin haushinsa kuma ba na jin sonsa amma dai abu ɗaya da na sani shi ne, yana da matsayi na musamman a cikin rayuwata kuma ina girmama hakan cikin raina, har yau ban cire tsammanin kira daga Ya Khalid ba, sai dai ganin shirun ya yi yawa ya sa na fara ba wa zuciyata haƙuri tare da tunanin hala Rafi'at yake so, kuma ya faɗa mata ta ce tana da wanda take so.

Tsaki na ja na ƙara jan bargo na lulluɓe, ƙarar shigowar saƙo na ji a wayata, hakan ya sa na laluɓo ta, baƙuwar number be, har zan ajiye wayar sai kuma na shiga saƙon, me zan gani "congratulations, Dear Jannatul-Firdaus, you've been offered an admission in to Adamu Adamu College of nursing sciences...."
Ko ƙarasa karantawa ban yi ba na cilla wani ihun murna, Rafi'at ta shigo a ɗan kiɗime."lafiya Jannat?"
Na mika mata wayar na ce "Ki ga, ki ga, na samu admission É—in"
Itama ihun ta É—an yi tare da rungume Ni tana faÉ—in "Congratulations, Allah ya sa albarka, mu je mu faÉ—awa su Mommy"
Nan muka É—unguma muka je muka nuna ma Mommy sannan Ummi, addu'a da fatan alkhairi suka yi min, na dawo na yi forwarding message É—in wa BB.

Bai kira Ni ba sai dare, na masa uzurin aikinsu, É—agawa na yi na gaida shi a mutunce, ya ce "Ma sha Allah, I've seen your message"
Na ce "uhmm"
Ya ce "Congratulations, Allah ya sa albarka"
Na ce "Amiin"
Ya ce "Gobe sa ki karbi admission letter É—in, ki yi snapping ki tura min sai na tura wa Ummi kuÉ—in ta ba mu Atm card É—inta ki ciro ki yi registration É—in"
"Na gode na..."
"Ya isa, ina da abun yi." Yana faɗin haka ya katse kiran, wayar na bi da kallo na ce "oh, mutum sai shegen faɗin rai kamar wani ƙaramin mutum"
Washe gari Baba Driver ya kai Ni na karɓo admission letter na, muna dawowa na yi snapping na tura masa.

Washe gari Ummi ta kira Ni sashenta, da na je ta miƙa min atm card ɗinta ta ce "Yayanku ne ya ce a ba ki, ya tura 250k a ciki na registration da sauran abubuwan da za ki yi"
Na karɓa na ce "Allah ya saka da alkhairi " ta amsa da "Amin"

Har na tashi zan fita Ummi ta ce "Dawo ki zauna nan jannat" na dawo wurin data nuna min
Shiru ta yi can ta ce "Kina ji na Jannat?"
Na jinjina kai, ta ce "Ni na haife ki Jannat, ina kuma so yau na tunatar da ke wani abu game da rayuwa"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ci gaba "Kin ga Khalil ko?" Na gyada kai "Ba Ni na haife shi ba, amma dai ina jinsa a jikina fiye da ɗan da na haifa ba don komai ba sai don yadda yake mutunta Ni yake kuma ba Ni girma, yake so na yake son ƴaƴana, kin ga tun da nake da Khalil bai taɓa saɓa umarnina ba, bai taɓa yin musu da wani hukuncina ba, ko kuma a zo batun rashin ɗa'a, bai taɓa ƙin ba Ni matsayin mahaifiya ba, yadda yake yi wa ƙannensa hidima haka yake wa ƴaƴana, kin ga Mommy, Mommy ba ta taɓa nuna rashin jin daɗinta ga yadda muke da shi ba, saɓanin wasu matan da za su iya tunanin ko mallake shi na yi ta hanyar asiri, Mommy mutuniyar kirki ce, haka Daddy, Ina da tabbacin halin dattakon Khalil daga wurinsu ya koya."

Ni dai shiru ba yi ina sauraron Ummi tare da tunanin ina maganganun nata suka dosa.
"A duniyar nan ba ki da tamkar Khalil Jannat, Ko bayan ranmu Ni da Abuya, ina da tabbacin zai ci gaba da kulawa da ke kamar yadda yake yi a yanzu haka Mommy, na tabbatar ko bayan raina za ta ci gaba da ba ki kulawa a matsayin mahaifiya."
Ummi ta numfasa, Ni dai zuwa yanzu kalaman Ummi sun fara ba Ni tsoro, sai ka ce mai bayar da wasiyya? Na faÉ—i hakan cikin raina.

"Jannat, ina gargaɗinki kuma ina mai ba ki umarni, ko bayan raina kada ki kuskura ki ce za ki saɓawa mutane masu karamcin nan, saɓa musu kamar saɓa min ne biyayya gare su kamar yi min biyayya ne"

Kalaman Ummi sun taɓa rauna ainun sai da ƙwalla ta zubo daga idanuwa, Ummi ta ce "Kina ji na ko?"
Na ce "E Ummi"
Ta ce "To, Allah ya miki albarka ya sa wa karatun da za ki yi albarka, ki tabbatar kin kira shi kuma kin masa godiya" na ce "To Ummi "
"Za ki iya tafiya "
Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na miƙe na koma part ɗin Mommy Ina ta nanata kalaman Ummi cikin raina.

Wanka muka yi muka fita tare da Rafi'at, ba Driver ya ajiye mu muka ciri cash sannan muka tafi AACNS, tas muka gama registration muka zauna jiran Baba Driver da ya fito siyo stationaries, yana dawowa muka yi submitting na yi signing, daga nan na tambayi wani mutumi da ban da waye shi ba when za mu fara zuwa, ya ce "in the next two weeks" na jinjina kai daga nan na karɓi tai sets na uniform muka taho, a hanya muka tsaya na sayi hard cover Notebook manta, da kuma school bag rinɗimemiya, Rafi'at sai dariya yake min wai wannan jakar ai za a iya jefa mutum a ciki. Da haka muka koma gida duk na ƙagu da mu fara zuwa jami'a, a wannan ranar ce wani abun farin cikin ya ƙara riskarmu, itama Rafi'at ta samu admission, itama dai cikin satin muka je ga yi registration bayan BB ya Turo kuɗin, ranar Monday muka je Branch na FCMB muka buɗe account aka mana atm kamar yadda BB ya ce Mu yi.

Alhamdulillah rabbil alamin!
Dukkan godiya da jinjina ga mahalicci suke, kuma duk wani mataki na rayuwa da bawa zai taka sai da sahalewarsa, ina cikin farin ciki a yanzu, walwala kuwa ba a magana, a yanzu dai ba Ni da wata damuwa da ta wuce na fara karatuna, batun wani ƙalubalen rayuwa har yanzu Ni Jannat ba na ce na sani ba, abun da ban sani ba shi ne, fara karatuna shi ne zai fara buɗe min wasu muhimman darussa na rayuwa da ban san su ba a baya.

Satin da muka fara zuwa makaranta aka mana orientation, bayan kwana uku muka fara lectures, alhamdulillah kawai zan ce, ina fahimta sosai, da na dawo gida kuma zan ƙara bitar abun da aka mana a makaranta, hakan ya sa har abokan karatu da lecturers ɗinmu sun fara fahimtar ƙwazo da basirata, hakan ya sa aka naɗa class Rep.

Sati ma biyu Rafi'at ma ta fara zuwa lectures, tare muke fitowa tun 6am saboda samun front seats, da abinci muke fitowa da kuma isassun kuɗi don BB ya saka mana 50k each a account ɗinmu, su Rafi'at 3pm suke gama lectures mu kuma 3:30pm, idan sun tashi sai Baba Driver ya ɗauko ta ya biyo ta school ɗinmu by that time muma min tashi. A yanzu ba mu da wani tunani da ya wuce n karatu, duk da Ya Sadiq yanzu damun Rafi'at yake kan ta bar shi ya sanar da su Abuya alaƙar da ke tsakaninsu amma a ta ƙi, a cewarta sai nima na samu wanda muka daidaita tukun.


Ranar wata juma'a mun gama first period lectures É—inmu na fito don siyan wani abu na ci saboda yunwar da nake ji, ina cikin tafiya don zuwa shagon Mukhtar, wanda ke kusa da area class É—inmu, karo muka ci da wani senior É—inmu da ke ND nursing, da sauri na ja Baya ina faÉ—in "I'm sorry please"
Ya wuce na wuce ba tare da ya ce komai ba, bayan na koma class wata colleague É—ina Hamra wacce kusan tare ma muke karatu da ita kuma muna yawan zama seat É—aya da ita ta zo gefena ta ce "Shirama guess something" na ce "wetin?"
Ta ce " Yanzu na ji ana gurmin wai kin ci karo da Abbas Hashim Toro" na ce "ban gane ba"
Ta ce "To ai yanzu ma an tura a Whatsapp group abun da ke trending yanzu ke nan"
Na ce "kamar ya, Ni fa ban fahimce ki ba"
Ta gyara zamanta Sannan ta ce "Abbas Toro shima student be, yana HND nursing ne, set 1, na ji maryam saddiqa na cewa tun kafin ta shigo school É—in nan take jin labarinsa wurin yayarta"
Na ce "ikon Allah"
"E, an ce guy ɗin is fine, shi yasa yake da rashin mutuncin, he's arrogant, ga masifar wulaƙanci"
Cike da ƙosawa da zancen nata na ce "Hamra Please, can You excuse me in ci gaba da kwafan note ɗina?"
Ta ce "To ai ban faÉ—a miki abun da na zo faÉ—a miki ba, ki ga" ta nuna min wayarta, idanuwa na saka don ganin mene ne, hotona ne da nasa lokacin da muka ci karo, da Caption É—in "Finally Mrs. Arrogant was taken"
Na ce "Waye wannan É—in ya dauki hoton har da turawa a group?"
"Wallahi ban san waye ba, kin san channel ne kuma ban san su waye ke da ita ba"

Cikin halin ko in kula na ce "Allah ya kyauta" sannan na ci gaba da kwafan note ɗina. Ina gani mutane na shigowa time to time su kalleni sai su fita, a haka har lokacin break ya ƙare, bayan gama second lectures muka yi closing, Baba Driver ya yi picking ɗina saboda yau Ni kaɗai ce Rafi'at ba ta da lectures.

Tun da na fito ake ta nuna Ni amma na kafse kamar ban san suna yi ba na nufi motar gidanmu na shige ciki, wani abu da ba su sani ba Ni ba Ni da lokacinsu, karatu ne ya kawo Ni kuma shi na zo yi, hatta Whatsapp group iya official group nake shiga wanda akwai lecturers a ciki kuma ta ciki ake tura mana note, don haka duk wani abu da suke ma Ni ban san ana yi ba.

Ranar Monday da na koma makaranta ma haka aka yi ta nuna Ni ana ƙus³ Ni kuwa ina ruwana, sai na ƙara yi kamar ban gansu ba, saboda yadda ake nuna Ni ya sa ko fita waje ma ban yi ba, Allah ta taimake Ni na taho da ruwa, ko dana ci abinci na sha ruwa da lokacin sallar azahar na fita, shima cikin zugar ƴan class ɗinmu na fita.

Bayan na yi salla class na dawo, Ni kaɗai ce sauran duk suna waje, ina zaune na yi shiru ina tunanin rayuwa tare da fatan Ubangiji ya yi wa rayuwata albarka. Tsayuwar mutum na ji a kaina, babu shiri na ɗago, ban gane shi ba, kasancewar ko ranar da muka yi karo ban ga fuskarsa ba haƙuri kawai na ba shi na wuce. Ban ce uffan ba sai ma kwantar da kaina da na yi akan desk na juya masa baya.

Hayaniyar dana fara ji ne ya sa na É—ago da sauri, colleagues É—ina sun shisshigo ajin, shi kuwa har lokacin yana tsaye a wurin. Dakewa na yi na dube shi na ce "Mallam lafiya ka min tsaye a ka? Ko na ci bashinka ne?"
Mutanen da ke ajin suka saka ihu, ya murmusa tare da zagayowar ta ɗaya barin ya zauna a wurin zaman Hamra fuskarsa ɗauke da Murmushi, ai babu shiri na miƙe don rabona da zama kusa da namiji haka tun ina dolphin Maria college.
Ihu aka ƙara sakawa a ajin Ni kuwa na fice har sai da na ga Nurse. Salim sai shigo na dawo, haka ta sa dole Abbas ficewa, kowa ya koma mazauninsa aka ci gaba da gulma.

Yanzu kam abun ya ɗan dame Ni, I'm not ready for any relationship now, karatu na zo, don haka ba zai yiwu a ɓata min shiri na ba, don haka na ƙudiri aniyar Duk ranar da guy ɗin nan ya kuma zuwa inda nake zan yi casting ɗinsa sai ya rasa wannan class ɗin da ya samu a AACNS.
In ban da ma iskanci babba da shi ya zo yana yin irin abubuwan nan?

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 13 · 0% Book details