← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 26

CHAPTER 9

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Part É—in Mommy ya nufa, ita kaÉ—ai ya tarar a parlour, gaishe ta ya yi sannan ya É—an dudduba, kamar zai wuce ya janyo su da duka sai kuma ya girgiza kai ya ce "Mommy ina yaran nan?"
"WaÉ—anne yara kuma?"
Ya ce "WaÉ—annan yaran nake nufi, su Rafi'atu "
"Suna ciki, Rafi'at! jannat!"
Mommy ta ƙwala musu kira daga yadda take kwance.
"Na'am" muka amsa a tare, cikin daƙiƙa biyu suka fito, Rafi'at gaba ina bayanta, a lokcin da idanuwana suka sauƙa kan halittar da ke tsaye take na ja Baya da wani irin sauri ina dafe ƙirjina, "Allah dai ya sa ba shi ke kiranmu ba" na faɗa cikin raina.

"Ya kika tsaya baya?" Mommy ta faɗa tana kallona, wanda maganar Mommyn ita ta sanar da shi kasantuwa ta a wurin kallona ya yi ya jinjina kai wanda hakan sosai ya sa kayan cikina juyawa, na riga na tabbatar in dai har ya ci abincin to ya zo hukunta mu ne "ni kam na gama yawo" na faɗa cikin raina ina aro wata ƴar jarumta na ƙarasa wurin Mommy ina faɗin "Mommy ga mu, ina yini BB"
Mommy ya ce "Yayanku ke nemanku" ai wani irin ƙwalalo idanuwana waje na yi ina mai dafe ƙirjina.
"Lafiya?" Mommy ta tambaya tana mai tsare Ni da ido, saurin girgiza kai na yi, Mommy ta ce "Anya?" Cike da shakku "Ko dai laifi kuka masa?"
"A'a e a'a Mommy ba mu yi komai komai ba" na ba ta amsa ina Æ´an kame-kame.
Mommy ta ce "Shi ke nan, sai ku bi shi ai, kafin ku ƙara wani laifin don waɗannan idanuwan naku sun nuna tsantsar rashin gaskiya.

Sai lokacin na samu damar mayar da dubana ga bigiren da yake, ganin ba ya nan ya sa na ja jiki a saɓule na bi bayan Rafi'at wacce ta riga ta yi gaba, Ni kaɗai na san halin da nake ciki a yanzu, tsoro da firgici sun lulluɓe Ni, Ni dai kawai na san yau na gama yawo wurin BB, Allah dai ya sauƙaƙa haɗuwarmu da shi.

Har sai da muka isa bakin part É—in Ummi Rafi'at ta juyo ta kalle Ni sannan ta ce "Ana ganinki an ga marar gaskiya, wace masifar kika kuma jaza mana wurin BB?"
Na ce "oho, in kin je kya ji" tsaki ya ja sannan ta ce "Wallahi kika sa aka bani punishment akan ki zan rama" tana faɗin haka ta shige part ɗin Ummin a ɗan fusace, Ganin haka ya sa na taɓe baki nima na shiga ciki.

A parlour muka tarar da shi ya hakimce akan kujera, Rafi'at ta yunƙura za ta tsugunna ya ce "Tashi" a matuƙar fusace.
"Cikinku waye ya yi girki É—azu?"
"Mu mu mu ne BB"
Ta ba shi amsa muryarta na rarrabewa.
Ya ce "Ku wa?"
Na ce "Ni da ita ne"
ÆŠagowa Ya yi ya kalle Ni sannan ya ce "wacce ta kai min bedroom É—ina ta je ta É—auko ta kawo shi nan"
A saɓule na wuce kamar wata Munafuka na ɗauko abincin na kawo gabansa na ajiye.

Wani irin mugun kallon da ya aiko mana sai da hanjayen cikinmu suka yi colliding da juna hakan ya sa muka sunkyar da kanmu ƙasa.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce "Ku ɗago ku kalle Ni"
Jiki na rawa muka É—aga kanmu sai dai kwarjininsa ya hana mu sanya idanuwanmu cikin nasa.

Mun kai minti uku a wurin shi bai ce komai muma haka, can dai ya numfasa ya ce "A cikin wace ce ta yi girkin nan?"
Muka haÉ—a baki wurin faÉ—in "Tare muka yi" ya ce "Ok, ku buÉ—e shi yanzun nan ku cinye shi"
Ba musu Rafi'at ta janyo tray É—in ya buÉ—e flask É—aya na buÉ—e É—aya, and luckily mai pepper soup ta buÉ—e Ni kuma mai taliya.

A É—an zafafe wannan karon Ya ce "Ku zauna ku cinye shi tas kafin na ba ku punishment É—in da ya dace da ku"
Tun da ya ambaci punishment na Fara ambaton Allah cikin raina ina addu'ar Allah ya shigo da Mommy don É—azu ta ce za ta shigo ta duba jikin Ummi.

Allah sarki Rafi'at da ba ta san komai ba ta ambaci sunan allah tare da sanya hannunta cikin flask É—in pepper soup É—in yayin da Ni kuma na zubawa taliyar gabana ido ina tunanin ta ina zan iya cinta tun da na riga na san masifar da ke cikinta.

Lomar farko da Rafi'at ta kai take ta juyo ta kalle Ni tana zaro eyes ɗinta, da ƙyar ta iya haɗiyewa Sannan ta kwaɓe fuska, da Yaren kurame ta ce min "ya haka?"
Na ɗage kafaɗata, duk abin da muke ashe BB na ganinmu, hakan ya sa shi gama tantance wacce ke da kaso mai tsoka wurin cika yaji a abincin amma bai nuna mana ba, sai ma tsawar da ya saka min ya ce "Ke kin fi ƙarfin ci ne?"
Yadda tsawar ta dake Ni ya sa Ni tsoma hannuna cikin taliyar ba tare da na aune ba nan na fara kai lomar farko bakina, sai lokacin na tabbatar ashe É—anÉ—anawar da na yi lami na ji, yanzu ne na ji asalin É—anÉ—anon abincin, cikin dakiya na kai loma ta biyu na yi ta uku, ai take nima na fara kuka, irin voluntary kukan nan da ke zuwa da kansa, juyawa na yi na fuskaci Rafi'at, itama kukan take, cikin raina na ce "Don ma naki bai kai nawa masifa ba."

Koma shida na yi tuni na gigice kamar ba Ni ba, yunƙurin miƙewa na yi na nemo mana abun sha na ji ya daka min tsawa, "Zauna ki ci gaba da ci" ba shiri na zauna, ya ce "Sai kun cinye shi tas kafin na ba ku exact punishment ɗin da ya dace da ku"
Rafi'at da azaba ta mata azaba ne ta ce "Na rantse da girman Allah BB bamu saka yaji haka ba, akwai sauran abincin a kitchen" ta ƙarashe numfashinta na cikewa yayin da hawaye ke bin kuncinta, tausayinta ne ya kama ni ganin yadda take karɓar hukuncin abun da ba ta aikata ba, hakan yasa Ni dole magantuwa cikin fitar hayyaci na ce "Wallahi Ni ce! Ban da ita.." ƙafarsa ya sa ya shure flask ɗin gaban Rafi'at ya nuna mata fridge da hannu sannan ya min alamar na matso kusa da nawa flask ɗin.

Tun daga lokacin na san cewa nikam tawa ta ƙare, Ko da Rafi'at ta dawo ce mata ta yi ta je abun ta ya kuma gargaɗe ta kan kada ta faɗawa Mommy, a guje ta fice ta bar Ni ina ta jefa abincin a cikina, ko rabi ban ci ba na fita hayyacina sosai, ganin hakan ya sa shi sakin murmushin mugunta Sannan ya ce "Ni aka so na shiga wannan halin ko? Ci gaba da ci maza, da sauri"
"Numfashina sama sama na ce "Don Allah! Zan mutuuuuuu"
Ya ce "ki mutun mana, sai kin cinye shi tas"
Kaina na girgiza don yanzu kalaman ma ba sa iya fita, ture nawa flask ɗin ya yi, amma bai ce na tashi ba, raɗaɗin da na ji bayan na daina cin ma Ni ya fi min cin wahala bai sani ba, idan kuma ya sani to ba shakka shi ɗin ya cika ƙaton mugu, sai da BB ya ga ina shirin shurawa haiƙan tukun ya miƙo min lemon peach da ke hannunsa, da wani irin sauri na karɓa sa of my life totally depend on it, murmushin mugunta ya saki ganin yadda nake shan lemon, sai da ya ƙare tas na ɗage gorar amma har lokacin zafin yajin na nan kamar wadda aka sabunta shi.

Abun da ya ban mamaki ko tausayina BB Bai ji ba haka ya ajiye Ni gabansa lokaci bayan lokaci yana sakin murmushin mugunta, sai da ya tabbatar na azabtu tukun ya dube Ni ya ce " Jannat" na ɗago na dube shi, ya ce "yanzu har ƙiyayyar da kike min ta kai wannan matsayin da za ki iya cutar da Ni?"
Ni haushinsa ne ma ya turnuƙe Ni, yana ganin halin da nake ciki ba zai ce na tafi ba zai tsaya min wani bayani?
"Har yanzu ku ɗin yara ne shi ya sa nake daga muku, amma tun da kun nuna min wuyanku ya isa yanka shi ke nan, mu zuba mu gani, ɓace min da gani." Cikin wani irin hanzarin da ban taɓa tunanin ina da shi ba na miƙe da shirin tafiya ya dakatar da Ni "Ki je ki faɗawa Mommy kin ji?"
Yana faÉ—in haka na wuce abuna sai part É—in Mommy.
Ina zuwa na nufi kitchen, Ina shiga da niyyar duba kunu NA ga madara, a haukace na buɗe gwamgwanin madarar na ɗauko cup na zuba a ciki, ruwa na tara a dispenser ko gaurayawa ban yi ba na kai baki, sai da na shanye tas tukunna na ajiye kofin, ajiyar zuciya na sauƙe tare da jinjina kaina.

Lallai yau na taka siraɗin mutuwa Allah ya cece Ni na kuɓuta, bedroom ɗinmu na nufa, Allah sarki Rafi'at har lokacin kuka take yi sosai Na ji jikina ya yi mugun sanyi, wurinta na ƙarasa da niyyar lallashinta, a fusace ta ture Ni gefe tana faɗin "Ki har Ni na mutu don Allah Jannat, miye abun da kika aikata haka?
Baya na ɗan ja ina ƙare mata kallo, after all the hard punishment da ɗan'uwanta ya ba Ni tanada da gut ɗin da za ta ce Wani abu.
Cikin ɓacin rai nima na ce "Tambayata ma kike Rafi'at? Bayan duk azabar da ɗan'uwanki ya gana min kina da bakin tambayata me na aikata?" Kaina na fara girgizawa ina faɗin "wato kin zaɓe shi fiye da Ni ke nan?"
Rafi'at ta ce "Haba Jannat, abun da kika yi kema bai dace ba, ramin mugunta kika gina masa sai kika janyo mu kika jefa mu ciki."
Wurin na bar mata don ita kanta wallahi haushinta nake ji a lokacin, shi kuwa BB ya gama fice min daga rai da wannan izayar tasa.

Washe gari da safe muna breakfast na ji Mommy na sanar da Daddy tafiyar BB É—in wai zai koma bakin aiki can Abuja, daÉ—i ne ya kama na ji kamar na tashi na taka, ko ba komai za mu samu salama da nutsuwa.

Tun da BB ya tafi wani irin walwala muke abun mu, a haka har muka kammala Neco ya zama babu inda muke zuwa. Wata Guda BB ya yi sannan ya shigo Azare, ko kaɗan ban ji daɗin hakan ba, duk da cewa yanzu ba na iya juran abubuwan da yake mana, wasu lokutan idan ya ɓata min rai har akan fuskata yake gani.

A wannan dawowar ganin babu yadda muke zuwa ya sa BB yi mana register da wani catering school Wanda da farko da cewa nai Ni ba na so, Ummi har bugu na sai da ta yi akan haka ta yi min faÉ—a sosai wai ana min gata ba na gani.

Yau juma'a, da wuri muka kammala karatun kasancewar practical ne, gani na yi a madadin tsayawa jiran BB gara kawai mu tsari mai keke ya kai mu, da kyar Rafi'at ta amince Don ita har yanzu tsoron BB da take yana nan, unlike me da nake jin yanzu duk abun da ya min nan ji daÉ—i ba sa na rama ta wata hanyar.

Muna cikin tafiya ne wata danƙareriyar mota ta faka gefenmu, mai motar ga sauƙe gilashin motar sai dai ko kaɗan ba mu yi gigin tsayawa ba don mun san hakan ba koyarwar gidanmu ba ne.

Gaba muka yi abun mu kamar ba mu ganshi ba, mun É—an yi tafiya kaÉ—an muka ji an ce "Hi" Rafi'at wacce take a tsorace ta ce "Malam mu matan aure ne, don Allah ka tafi abun ka"
Kyakkyawan saurayin ya yi ƴar dariya sannan ya ce "Lallai kam, na ga matan aure a nan, to ko za ku shekara kuna ce min ku matan aure ne Ni ba zan yadda ba idan ba mazajenku na gani ba, kai ko na gansu ma Ni da ƙyar na yadda"
Wani ƙayataccen Murmushi na yi sannan na ce "To shi ke nan, idan ma mu ƴanmata ne inaga bai kamata ka tsayar da mu akan hanya ba, beside ba shigar banza ka gani jikinmu ba bare ka ce ka ga alamun rashin kamewa a tattare da mu"

Kamar dai kalamaina sun yi tasiri akan shi, ya sosa sumar kansa sannan ya ce "Haka ne, ku yi haƙuri don Allah, na san cewa ban kyauta ba, amma ku sani babu yadda zan yi ne shi ya sa na tsayar da ku, don Allah ku yi haƙuri, ku ba Ni 11 digits ɗinku sai na tafi"
Na jefe shi da wani kallo, ya marairace fuska ya ce "Haba sister, duk da cewa na ga Æ´ar'uwar tamu na kunya ke kam ya kamata ki ba Ni ai, in kin ba Ni kin ga shi ke nan, ba zan kuma muku magana akan titi ba sai dai na kira na tambaye ku gidanku sai iyayena su zo"

Ƴar dariya na yi sannan na ce "Kawo wayarka na saka maka"
Ya ce "To" da sauri yana miƙo min wayarsa ƙirar iPhone 16, na karɓa ina bin wayar da kallo Sannan na zuba masa numbern wayata. Bayan na gama na miƙa mishi muka yi sallama, har ya juya zai wuce sannan ya juyo ya ce "Amma dai bai kyautu a ce kuma bin titi haka ba, ku shigo na sauƙe ku mana"
Na girgiza kai na ce "A'a, kar ka damu, za mu tari abun hawa ai"
Ya ce "Ai ba lallai ku samu ba in dai a wannan titin ne, tafiyar kuma da yawa hala"
Rafi'at ce ta ja veil É—ina ta ce "ki ci gaba da biye shi, Ni dama sai da na ce miki ba zan taho ba zan jira BB kika ce sai mun taho"
Na É—an harare ta sannan na dubi saurayin na ce "Shi ke nan, mu je"
Waro eyes Rafi'at ta yi kafin ta ce "Ba ki da hankali ne jannat?"
"Wow! Jannat, Nice name from sweet voice, na roƙe ki ba don Ni ba ki shigo kin ji?"
Rafi'at ta ce "I'm not going with you guys, ku je, Ni zan koma na jira BB"
Ba tayi tsammani ba na ja ta zan nufi da ita wurin da motar guy É—in take Na ji an daka min tsawa. Ai take na shiga taitayina don ko ina cikin magagin mutuwa ba zan mance sautin Muryar nan ba.
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 10 · 0% Book details