CHAPTER 21:
Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read
Daga haka na nufi kitchen na dafa masa kamar yadda ya bukata sannan na yi preserving nakai mishi É—akinsa.
Godiya ya yi min daga nan na fito ina ƙara mamakin BB.
Duk wannan haushi da tsanar tasa da na yi ta ji a baya yake na ji sun yaye kamar ban taɓa ba, Ni kaina hakan ba ƙaramin mamaki ya ba Ni ba, amma dai na danganta hakan da ƴan'uwantaka ne a kuma gudanuwar jini ɗaya a gangar jikinmu.
Yinin ranar haka na yi shi cikin farin ciki na rasa dalilin hakan, haka Rafi'at ta saka Ni gaba ta tambayar Ko Lafiyata ƙalau don ta kama Ni several times Ina smiling Ni kaɗai wanda nima kaina ina mamakin hakan. Ko da ta ga na share ta sai ita ma ta watsar da zancen daga nan ta shafa min lafiya.
Yau ta kama juma'a, na je gaida Ummie da safe muka haɗu da BB, gaishe shi na yi ya amsa fuska sake, daga nan na shiga muka gaisa da Ummi wacce ke kitchen da alamun baking take yi don ƙamshin gashin nata gaba ɗaya ya addabi ƙofofin hancina har ina jin kamar na ci babu, ina fitowa daga kitchen ɗin na ga BB tsaye ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa cikin wata irin tsayuwa irin ta dakakkun mazan nan masu jini a jika.
Shirin wucewa na yi na ji ya ce "Jira Ni mu fita"
Ba musu na tsaya, taku ɗaya ya yi ya iso Ni, take wannan sassanyan ƙamshin nasa da ban taɓa jinsa a jikin wani mahaluki ba bayan shi ya doki ƙofofin hancina, idanuwana na lumshe yayin da bugun zuciyata ya fara fita da sauri sauri.
A jere muka fita daga parlourn, ba tare da ya kalle Ni ba ya ce "Ya kika yi shiru?"
Na ce "Ai ba ka son surutu"
A ba zata na ji ya ce "Ban da naki surutun"
Saurin tambayar sa na yi don tabbatar da abun da na ji, maimakon ya maimaita min sai na ji ya ce "Ba ko yaushe ba"
Wani Murmushi ne ya suɓuce min, a tare muka shiga parlour lokacin shima murmushin yake yi.
Mommy ce ta kalle mu fuskarta dauke da Murmushi ta ce "A'a, ku kuma daga ina?"
Cikin jin kunyar mommyn na ce "Na je gaida Ummie ne shi kuma ya ce zai zo nan"
Na yi saurin faÉ—in hakan ne gudun kada Mommyn ta kawo wani batun cikin ranta.
Satar kallonsa na yi, ganin wani ƙayataccen Murmushi akan kyakkyawar fuskarsa ya sa na ɗan sunkuyar da kaina ƙasa tare da wucewa ɗakinmu.
Gaisawa BB suka yi da Mommy, its dai Mommy sosai ta yi farin ciki da ganinmu tare har ma ta fara ƙisssima abun da na ƙi a cikin ranta. Abun ku da manya tuni Mommy ta hasaso wani abun tsakanina da BB Wanda ya samarwa kanta tabbacin cewa ɗan nata ya faɗa tarkon soyayyata ne, ko da BB ya fita murmusawa Mommyn ta yi ta ce "Allah ya tabbatar musu da alkhairi" ko ba komai tana sa ran cewa ina har wannan hasashen nata ya zama gaskiya to fa ba ƙaramin dacewa muka yi da juna ba, wani abu da ba ta sani ba shi ne, Ni dai kam ba na jin wani abu mai ko da kamanceceniya da soyayya ne dangane da BB ɗin cikin raina.
Ba dai kai tsaye zan ce ba na ƙaunarsa ba, idan na ce haka na san ƙarya ma nake, don ko a da da babu wani kusanci tsakaninmu ba wai na tsane shi ba ne, sai dai kuma ina jin haushinsa ba shakka.
Abu ɗaya da zuciyata ke haska min akan alaƙata da BB shi ne ƴan'uwantaka, ina jinsa yanzu kam a jikina sosai, domin wannan zumunci da yanzu muka fara ya taka rawar gani wajen samar masa da gurbi da musamman cikin zuciyata.
Wuraren ƙarfe huɗu da rabi na yamma bayan Rafi'at ta dawo daga school, muna zaune akan gado muna taɗin zuwa Misau. Kallona Rafi'at ta yi ta ce "Ke labari da ɗumi ɗuminsa"
Kusa da ita na matsa ina faÉ—in "Ba Ni Na sha"
Ta ce "Ke dazu da safe na je gaida Mommy BB ya yi zance Dani"
"Zancen me?"
Ta ce "Wallahi kamar ba shi ba, har da tambaya na ya school? Ina maida hankali kuwa? Ke har Murmushi ya min"
Ajiyar zuciya na sauke na ce "Um, lallai kin ciri tuta"
Ta ce "Wallahi kuwa, To shima ai da haka yake mana ai za mu fi jin dadi"
"Uhm" kawai na ce, ban kuma ba ta labarin tawa dramar da shi ba, haka kawai na ji ba sai na faÉ—a mata ba.
Washe gari dukkanmu muna gida daga Ni har Rafi'at.
Da daddare wuraren ƙarfe takwas na dare muna gama dinner muna zaune a parlour muna kallon wani Korean series Mai sunan perfect crown a wayar Rafi'at when suddenly her phone rang.
Tsaki na ja saboda an zo wurin rashin hankali kawai aka kira, murya ƙasa-ƙasa Rafi'at ta ce "Ke BB ne, bari na ɗaga"
Ban ji me ya ce mata ba sai na ji ta ce "To BB, e, yanzu ma" daga haka kuma ta sauƙe wayar. Kallona ta yi ta ce "BB na kiranki, wai ki same shi a parlourn Ummi"
Tura bakina gaba na yi, Rafi'at ta kalle Ni ta ce "Kya ji da shi ai"
Banza na mata daga nan na zari Hijab ɗina na fita hankalina kwance cikin raina ina mamakin irin wannan kira da BB ya min Wanda a tarihi zan iya cewa hakan ba ta taɓa faruwa ba.
Zaune na tarar da shi a parlour ya yi zaman naÉ—e a kan carpet yayin da ya yi resting kansa jikin kujerar idanuwansa na lumshe kamar mai bscci.
Sallama na yi, ya amsa ba tare da ya motsa ba, ɗan nesa da shi na zauna tare da gaishe shi, sai lokacin ya sauƙe kansa ƙasa tare da gyara zamansa, fuska sake ya amsa min yana faɗin "Na yi tunanin ai kin yi bacci"
Na ce "Tukunna dai, kallo ma muke"
"Me kuke kallo?"
Na ce "K drama ne"
Kansa ya jinjina sai dai ga mamakina bai ce komai ba, Nima shirum na hi, ganin bai da niyyar magana ya sa na ce "Rafi'at ta ce kana son ganina"
Cikin Wata kasalalliyar murya ya ce "E"
Na ce "To Allah ya sa lafiya" ya amsa min da "Amiin"
"Jannat!" Na ji muryarsa ta kira sunana cikin wani irin salo da zan iya cewa ya kere duk wani wanda ya yi amfani da shi a baya. Shiru ya yi kamar mai tattara kalaman da zai yi amfani da su ya ce "Ina so ki ban aron hankali da kuma lokacinki, there's something important I want to discuss with you"
Kaina na jinjina tare da ƙara nutsuwa wuri guda duk da cewa deep down my heart I'm wondering what is he discussing with me right now da ba zai bari sai gari ya waye ba.
"Jannat" ya ƙara kiran sunana tare da gyara zamansa "Ina so ki fahimce Ni, kuma ki ɗauki duk wata kalma da zan furta a yanzu a matsayin wani sirri da ke fitowa daga ƙarƙashin zuciyata wanda na jima ina ɓoyonsa"
Duk da cewa maganar tasa ta zo min a wani irin bauÉ—e hakan bai hana gabana faÉ—uwa ba.
Wani irin dogon numfashi ya ja da Ni kaina sai da na saci kallonsa.
Ƙasa ya ƙara yi da muryarsa kamar mai raɗa ya ce "Ba komai nake son sanar da ke ba Jannat, illa iyaka ina ƙaunarki, ina sonki kuma ina so na rayu da ke zuwa numfashina na ƙarshe"
A ɗan firgice na ɗago kaina tare da kallonsa sai dai yanayin fuskarsa da na gani ya cire min shakkun tunanin da nake akan kalamansa da suka min sauƙar ba zata a cikin kunnuwana.
Ganin kamar a rikice nake ya sa shi ƙara faɗin "Yes Jannat, i love You, ina son ki, ina ƙaunar ki, sannan ina so na rayu da ke tsawon numfashina"
Wannan karon kallon wadda ya fice daga hayyacinsa nake masa, don na san ko a mafarki hakan ba za ta taɓa faruwa ba matsawar dai BB ɗin na cikin hayyacinsa, gaba ɗaya kaina na ji ya cushe na kasa yin ko da kyakkyawan tunani ne, anya kuwa BB ya san me yake faɗi? Anya kuwa ya san da wa yake magana?
Saurin girgiza kaina na yi ina ƙara tabbatarwa kaina abun da zuciyata ke raya min.
Tabbas wannan ba BB ba ne, ba dai wannan miskilin yayan namu ba ne da izza da kuma taƙama suka gauraye jinin jikinsa, idan kuma har shi ne to tabbas ba ya cikin hayyacinsa.
Wani sashe na zuciyata ne ya yi saurin tunatar da Ni cewa shi ne, yayin da É—aya sashen ke faÉ—in Ko dai ya sha wani abun ne? A'a, BB ba ya shan komai, ko sigari da ake cewa sojoji na sha zan iya shaidar Yayanmu ba ya sha.
Kamar ya san me nake zantawa cikin raina kwatsam na ji ya ƙara kiran sunana.
"Kar ki yi mamakin abun da na faɗa miki, Ni ɗin dai Ni ne, ban sha kayan maye ba bare ki yi tunanin ba na cikin hayyacina, hasali ma Ni na kira ki Saboda fallasa wannan daɗaɗɗen Sirrin da na jima ina adanawa gudun kada wata rana riƙe shi ya yi ajalina."
Ɗan dakatawa ya yi kafin ya ci gaba "Na san kina cikin ruɗani da kuma fargabar kalamaina, kina da buƙatar tabbatar da su sakamakon ban taɓa ajiye wata alama da za ta sa ki fahimci hakan ba"
"Jannat! Ina son ki ba batun wasa ba, duk wata takura da kike ganin ina muku saboda ke ne, saboda ƙaunar da nake miki ne, saboda ina son matar da zan aura ta kasance bar kwatance wurin kyawawan ɗabi'u, ta'ammali kuma da wasu maza a waje da nake ƙoƙarin yi muku Shamaki da shi Jannat, saboda ina tsananin kishinki ne, a duk wata rana da zan yi arba da ke wani namijin bayan Ni na magana dake nakan kasa rintsawa, zuciyata takan yi nauyi sosai har nakan ji kamar za ta daina aiki."
Ni dai a wannan lokacin ba zan iya banbance halin da nake ciki ba saboda tsananin mamaki, na yi ƙoƙarin auna kalaman nasa a wani scale, zuciyata ka sa yadda cewa shi yake furta min su, to idan ma shi ne babu shakka kawai yana faɗa ne don Ni matsayin tatsuniya ɗaya da wannan jawaban masa da yake min.
Shiru ya yi don ya huta sannan ya ci gaba "Jannat, kin san tun yaushe na fara sonki?"
Kamar wata wacce ta rasa tunaninta na girgiza kai, wani irin sihirtaccen Murmushi ya saki wanda ke ɗauke da wasu sirrika da Ni ban iya fahimta kana ya ce "Tun ranar da aka haife ki! A ranar babu kowa a gidanmu daga Ni dai Ummi, Ni ne nan mutum na farko da na fara daukar ki a hannunsa bayan Ummi, Ni ne wanda ya fara sanar da ƴan'uwa samuwarki, tun daga wannan ranar da na ɗauke ki Jannat! Daga ranar Ubangiji ya dasa min matsananciyar so da kuma ƙaunarki ta yadda har nake jin zan iya sadaukar da komai nawa saboda ke."
Kansa ya shafa, sannan ya ce "A lokacin ba ki da wayau, amma iyayenmu sun shaida wannan ƙauna da na nuna Miki, sun shaida sadaukarwar da na yi ta yi saboda ki yi farin ciki ki kuma rayu cikinsa na har abada, ki sani da soyayyarki na girma har na kai wannan matsayin da nake ciki a yanzu."
Sunana ya kira a sanyaye kafin ya ce "Ki saka idanuwanki cikin nawa" kasa yin hakan na yi sai ma ƙas da kaina da na yi, ba tare da ya ɗauke nashi idon a kaina ba ya ce "ba zan taɓa takura ki ki so Ni ba, zan ba ki zaɓi ki yanke hukuncin da kika yi na'am da shi, ba zan taba fitar da wannan sirri ba har sai lokacin da kika yi na'am da Ni, don fitar da shi kan iya jawowa iyayenmu su Miki dole ko da kuwa ba kya so na, ba zan aikata wannan KUSKUREN ba, Zan ba ki lokaci, ki nutsu kuma ki yi tunani, fatana da kuma roƙona ɗaya shi ne, ki dubi dakon ƙaunarki da na yi na tsawon shekaru kada ki duba abubuwan da na Miki a baya wanda na riga na miki bayaninsu yanzu, ki yi min adalci wurin yanke hukuncin Jannat"
Shiru ya yi, nima kuma a nawa ɓangaren shirun na yi yayin da kaina ke ƙasa ina wasa da ƴan yatsuna.
Ƙoƙarin miƙewa ya fara sannan ya ce "Tashi mu je na raka ki, dare ya fara"
Ba musu na miƙe tsaye, ya yi gaba Ni kuma na take masa baya, har bakin part ɗin Mommy ya raka Ni tukun ya ja gefe ya ba Ni hanya na shiga, ganin zan wuce ba tare da na ce da shi wani abu ba ya sa shi faɗin "Ba za ki tsaya mu yi sallama ba?"
Babu yadda na iya haka na tsaya, abu ya miƙo min ya ce "Karɓi wannan"
Leda ce fara ban san meye ciki ba, hannu na saka na karɓa tare da faɗin "Na gode"
Ya ce "Sai da safe ke nan?".kaina na gyaÉ—a
"Shi ke nan, ki yi bacci mai daÉ—i, sai da safe"
Simi simi na wuce kamar wacce ta kamu da matsalar ƙwaƙwalwa, juyowa na yi a lokacin da na isa bakin ƙofar ɗakinmu to my surprise Yana tsaye a wurin, hannu ya ɗaga min, daga haka na yi saurin shigewa ciki.
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*
*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*
1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA
2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT
3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN
4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE
5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA
Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.
Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k
Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu
Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇
09023907030
09161720046
+20 150 885 6397
09065856251
07061707238
*Masoya ina Æ™ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub âœï¸ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*
*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~
https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS
*No 04*
*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_
07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim
.