CHAPTER 14
Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read
Gaida shi ta yi, Ni kuma na yi kamar ban ga shigowarsa ba, ya ƙare min kallo Sannan ya kira sunana"
Na ce "Na'am, a BB ban san ka shigo ba, ina yini"
Kallon kin raina Ni ya aika min cikin raina na ce "Mai halin tsiya da na kirki, in ya juye akwai kirki, ya birkice kuwa ya fi tsohuwar mota iya iskanci"
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya ya juya ya nufi bedroom É—in Mommy.
Yaya Sadiq ne ya shigo, na gaida shi daga nan na miƙe na ba su wuri shi da abar ƙaunar tasa.
Bayan kwana biyu wani abu bai ƙara haɗa mu da BB, don kuwa muna ƙoƙarin ganin mun kiyaye duk wani abu da zai haɗa mu da shi ɗin muma, yau ta kama juma'a, bayan mun dawo daga school muka yi wanka muka yi kwalliya kamar masu fita wani wuri, ƙananan kaya muka sanya, da yake sun Kama jikinmu sai muka ɗaura kimono akai muka yi rolling veils ɗinmu, tsakar gida muka fito muna snapping pictures, ba mu ankare ba har BB ya shigo gidan muna ta yin videos abun mu. Hankalinmu na can gefe muna ta iye kawai muka ji Muryarsa kusa da mu, da wani mugun speed Rafi'at ta filla a guje sai part ɗin Mommy, Ni kuma na dake na fara tafiya a hankali, takuna huɗu na ji ya kira sunana.
Ba tare da wani tsoro Ba na amsa ina mai zuwa gabansa na tsaya, ya duba Ni ya ce "Wato ke ko a jikinki ko jannat?"
Na ce "To Ni me na yi BB" maganar tawa ta fita cikin sigar shagwaɓa.
Hararata ya yi kana ya ce "Wai ke ba ki jin magana ne kam? Ba ki san me da me ya dace ba ba kuma ki san abun da bai dace ba?"
Na girgiza masa kai, ya ce "Jannat" na ɗan saci kallonsa Sannan na mayar da kaina ƙasa
"Ba wai don ba na sonku ba ne nake faÉ—a muku gaskiya ba, hasali ma soyayyar ce ta sa nake faÉ—a muku amma na san ku gani kuke kamar ina takura ku ko"
Shiru Na masa, ya ce "Har yanzu ku yara ne Jannat, ba za ku fahimci me nake nuna muku ba har sai kun yi hankali"
Bakina na É—an tura gaba jin ya kira mu da yara, wai shi kam me yake nufi da mu ne? Shekarunmu sha takwas takwas har mun shiga ta sha tara amma still he's calling us kids, ban san sai yaushe ne za mu girma a wurin BB ba.
"Jannat" ya ƙara kiran sunana a karo na ba adadi har sai da na ji inama bai san sunan ba musamman yadda yake yawan faɗinshi kamar mai jin daɗin hakan. Amsa masa na yi, ya ce "Yanzu wannan abun da kuke yi ɗin kuma ganin kuma kyautawa kanku ne?"
Na yi shiru ban ce komai ba
Ya ce "Ki dubi kayan da ke jikinku, sai ka ce ba ku san kun fara girma na Uhm?"
"BB me ai...."
"Rufe min baki dalla, tun da ba ku da hankali kuwa ina za ku san meye aibun kayan? Ke ga ki maras kunya da rashin tsoro kina ganina kika tsaya saboda ki nuna min ke yanzu kin fara girma ko Jannat? Tun ba yau ba nake ganin abubuwa iri-iri a wurinki, ke ce kula samari, ke ce saka ɗamammun kaya kina hotuna sai wani lallanƙwasa jiki kike yi" Cikin masifa yake maganar don har jijiyoyin kansa ana iya gani, huci ya fitar sannan ya sauƙar da Muryarsa ya ce "Na ga yadda kanku ke rawa kwanan nan daga ke har Rafi'atu, so kuke mu saka ƙafar wando ɗaya da ku kuma wallahi hakan ba zai zo muku da kyau ba, ku sani har yanzu yara nake ganinku, kar ku ga kuna higher institutions ku yi tunani kun girma, duk yarinyar da ta yi abun da bai kamata ba babu abun da zai hana na zane ta"
Dariya na ji ta kama Ni for his last statement, Wai zai zana mu? I was like lallai kam cikin raina ina jinjina kaina, yayin da a zahiri kuma na fara tarin ƙarya wanda na tabbata shi kanshi ya fahimci dariya nake, bai ƙara bi ta kaina ba ya wuce abunsa, na bi shi da kallo cikin raina ina mamakinsa, just like a chameleon, yau ya zo a mai kirki gobe kuma a ƙaton mugu, yanzu in ban da neman magana da kuma takuri irin na BB meye laifin kayan jikinmu? Mun ji sun matse mu to Kimonon da muka ɗaura akai fa?, siririn tsaki na ja sannan na wuce abuna nima.
Da daddare a parlour muka baje tare da Mommy ana kallon wani Film 172 days a wayar Rafi'at, Mommy kam da na iya karanta subtitles ɗin take yi ba saboda sun ya ƙanana yasa ta mana sai da safe ta wuce, Rafi'at ma da ta gaji ta bar min wayar ya zamana Ni kaɗai nake kallon.
Abu ɗaya da na sani shi ne, Film ɗin na soyayya ne mai taɓa zuciya, don tun ba mu yi nisa ba na fara hawaye ga shi kuma ƙarshensa ya ƙara karya min zuciya haka na yi ta zabga kuka har da jan hanci. A ba zata na ji Muryarsa don kuwa Ba na ce na san lokacin da ya shigo ba.
Sunana ya kira, gagara amsawa na yi sai yunƙurin tashi da na fara ina sauƙe ajiyar zuciya, tsugunnowa ya yi daidai fuskata har ina iya jiyo numfashinsa, ƙamshin da jikinsa ke fitarwa ya sa na sauƙe wani numfashi tare da lumshe idanuwa.
"Jannat!" Ajiyar zuciya na ƙara sauƙewa Sannan na gyaɗa kaina
Cike da kulawa ya ce "me yake damunki?"
Da ƙyar na iya cewa "Babu" coz har yanzu kukan bai gama sakina ba.
BB ya ce "Tambayarki nake Jannat, na shigo kusan 20 minutes back, you were busy shedding tears har da shesheƙa, tell me what's wrong with you, ko ba ki da lafiya ne?"
Na girgiza kai, ya ce "To me yake damunki?"
Na ce "Babu" ya ce "Ƙarya kike, za ki faɗa min ko kuwa?"
A hankali na ce "Kallo nake shi ne Film É—in ya ban tausayi"
Galala ya yi yana kallona can ya iya buÉ—e baki ya ce "Are You in love Jannat?"
A wani irin ba zata tambayar tasa ta zo min, hakan ya sa na dube shi sai kuma na kawar da kaina gefe?
Cikin wani yanayi da ba zan iya fassarawa ba ya ce "kina soyayya ko Jannat?"
Na girgiza kaina ina faÉ—in "A'a"
"Then why kike kuka while watching just a movie?"
Na ce "Mutuwa ya yi ya bar ta, shi ne nake kuka"
Da sauri ya ce "Waye ya mutu?"
Na ce "Amir"
Ya jinjina ka ya ce "That proved me right you're in love Jannat"
Saurin girgiza kai na yi ina faÉ—in "BB am not, it's that the film is heartouching and emotional"
Ya Gyaɗa kai sannan ya ce "Fine, tashi ki je ki yi alwala ki kwanta" na gyaɗa masa kai sannan na miƙe ina faɗin "Sai da safe" ga mamakina sai na ji ya ce "Allah ya tashe mu lafiya" ɗaƙinmu na nufa, shi kuma bai yi abun da ya kawo shin ba ya koma abunsa.
Daren ranar kasa rintsawa BB ya yi don kuwa abun da idanuwansa suka gane masa ya tsaya masa cak a rai, da dai ya ga alamar tabbas ba zai iya baccin ba kawai sai ya tashi ya ɗaura da salla yana addu'ar Allah ya kawo masa komai da sauƙi, washe gari BB ya koma Abuja bayan ya saka mu gaba ya mana faɗa sosai, har mun tashi da mu tafi ya ƙira sunana, hakan yasa na dawo.
Ya dube Ni ya ce "Jannat"
Na amsa ina gyaÉ—a kaina
Ya ce "Kin ji abun da na faÉ—a muku ko?"
Cikin raina na ce Ni ba kurmiya ba ai na ji, amma a zahiri sai na ce "E"
Ya ce "ko da wasa kada ku kuskura ku aikata ɗaya daga cikin abubuwan da na lissafa muku, ban da kula samari, Engagement in to social media, iya Whatsapp na amince muku shima saboda hidimar karatu ne, ban da biye ƙawayen banza da kuma yawo, ki kula Jannat, abun da ya sa na ƙara jaddada miki na san kin fi kowa taurin kai a gidan nan, ko kowa ya kiyaye dokata ke ce mai kunnen ƙashin taka ta, wallahi Jannat wannan karon zan ba ki mamaki na ji labarin kin yi wani abu da bai kamata ba, kin ji ko?"
Na ce "e" ya ce shi ke nan, je ki abun ki.
Nikam kamar an tsoma Ni a aljanna haka na rinƙa ji da tafiyar BB duk da cewa Ummi sai da ta min faɗa akan yadda ta ga ina murnar tafiyar tasa, amma dai ko ma meye dai ai ya tafi, mun samu freedom.
Ko da na shiga part din Ummi bayan tafiyarshi a parlour na ganta, gaida ta na yi ta amsa, na ce Ummi ina Ayman?
Ta ce "Shekaranjiya da Khalil zai je Misau ya tafi da shi wurin Mommyn su Mu'awwaz (Ƙanwar su Abuya).
Kwaɓe fuska na yi na ce "Ummi me ya sa mu ba kwa barinmu mu je wurin Family? Ki duba fa bai fi sai uku na taɓa zuwa Giade ba, duka ƴan'uwanki ban da Uncle Munir da Uncle Sagir ban san su ba, su ɗinma in ban da Maza ne suna zuwa ai da ba zan san su ba."
Hararata ya yi ta ce "Kin taɓa cewa kina son zuwa wurinsu ne? Tabbas da Inna na da rai ne ma za ki san yan'uwana sosai, nima kin ga sai ƙarshen shekara nake zuwa ai"
Kamar zan yi kuka na ce "To Ummi yaushe za ki je da Ni?"
Ta amsa min da "Sai dai ku shirya ke da Rafi'at ku je idan kun samu hutun makaranta, dama na so ku zaga dangi sosai sanda kuka gama Ummul Qura to hakan kuma ba ta kasance ba, amma dai tabbas ya kamata kuke leƙawa wurin ƴan'uwa kar su ce mu muke hana ku"
Na jinjina kai na ce "Haka ne kam"
Ummi ta ce "kin gani ai, zan yi wa Yaya Turai magana akan hakan".
Shiru muka yi can kuma na ce "Wallahi duk BB ne ya janyo ba ma ziyarar ma, da ba a mayar da mu..."
Gwaɓe min baki Ummi ta yi ta ce "Oh saboda ya tafi ne kike faɗin haka ko? Don ubanki a duniyar nan ba ki da kamarsa in faɗa miki, yarinya kamar mai tosasshiyar ƙwaƙwalwa?"
Na tura baki gaba na ce "Haba Ummi, wai shi BB É—in nan..."
Ummi ta daka min tsawa ta ce "Rufe min baki, sakarya kawai"
Bakina na kuma turawa na ce "Gara ma da ya tafi Abujan, in ya je ma ya yi zamansa a can mun yafe musu shi" bugun da Ummi ta kawo min ya sa ba shiri na fita daga parlourn a guje.
A can ɓangaren BB daren ranar da ya koma bakin aiki na gagara Bacci ya yi wuraren ƙarfe biyu Ya Khalid ya farka ya gan shi zaune ya jingina na pillow yayin da fuskarsa ke lafe akan fuskar gado.
"Are You alright K?"
BB ya ce "Babu komai, just thinking on how to confront that girl, na ga alamun bari ya wuce zai iya kawo rabon wani"
Ya Khalid ya zauna gefensa tare da dafa kafaÉ—arsa Sannan ya ce "my friend ya kamata kam ka san abun yi"
BB ya É—an yamutsa fuska jin yadda kanshi ke sarawa, zamansa ya gyara kafin ya ce "Kana ji Khalid, ban fiye son yi gaggawa akan al'amuran rayuwata ba ne saboda mafi aksari gaggawa na iya karewa da da na sani wanda ba na fatan hakan, ka ga kuma ba wai Mommy da Daddy sun damu da rashin aurena ba ne yanzu bare na ce zan gaggauta fitar da maganar, kuma Ni ba na so na jawo mata wani tsaiko cikin karatunta"
Ya Khalid ya murmusa sannan ya ce "Lallai abokina maganganunka gaskiya ne dukka, amma kuma abun da za ka duba shi ne, shirunka akan al'amarin nan babu alkhairi ciki, ka san da Hausawa sun ce, a bari ya huce, shi ke kawo rabon wani, kuma sun ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, tun ba yau ba nake nuna maka fa'idar sanar da ita yarinyar tun kafin wani ya riga ga fada mata kalmar soyayyar amma kai ka ce A'a, na yi tunanin ka yi abun ɗaya kamata wannan zuwan naka gida ashe ba ka yi ba, to wallahi bari ka ji, in ka tsaya sanya wani katon ne zai riga ka kuma ka ga babu yadda ka iya ba za ka mata dole ba"
BB ya jinjina kai tare da faÉ—in "Haka ne kam, amma.."
Ya Khalid ya daga BB sannan ya ce "Look my friend, the only solution you get shi ne ka sanar da yarinyar nan Jannat, ka ajiye duk wani ji da kai da ƙi faɗinka gefe, kana son ta, ka san hakan, then why za ka ci gaba da wahalar da kanka ne Uhm?"
BB ya ce "Wannan zuwan nawa na fuskanci wani abu game da ita, ba na fatan a ce hasashena ya zama gaskiya."
Ya Khalid ya ce "Ai kuwa dai in har kana sonta you've to save yourself and confront her, Ina tsorace maka aikata kuskuren da za ka zo kana nadama daga baya, kawai ka faɗa mata tun kafin ta kamu da son wani, ka ga a wannan gaɓar dole ka haƙura da ita.."
"wannan shi ne mafi munin labari kuwa da zan taɓa riska a rayuwata, Ni tsoron da nake ji ma yanzu shi ne, na sama da ita ta yi rejecting ɗin soyayyata, for sure zan iya rasa rayuwata"
Daga shi Ya Khalid ya kuma yi, cikin sigar lallami ya ce "Ba ma fatan hakan, burinmu shi ne mu cika mota mu tafi Azare bikin Captain Ibrahim Abubakar Shirama da kuma Jannat É—insa"
Wani ƙayataccen Murmushi BB ya saki har sai da haƙwarensa suka fito.
Daga nan ya ji wani irin nauyi na zuciyarsa ya ragu masa, tabbas aboki irin Ya Khalid gare shi babbar ni'ima ce daga mahalicci, Faransa shi ma Allah ya ba shi damar yi masa abun da zai yi alfahari da shi wata rana.
A nawa ɓangaren bayan tafiyar BB abubuwa da yawa sun fara sauya wa a tare da Ni biyo bayan wani taɗi da muka yi Ni da wata colleague ɗina Halima Madaki, wacce kowa a ajinmu ya san yadda idanuwanta ke buɗe, duk wani social media handle in ka leƙa za ka ga Sady-Madaki tun daga facebook, Whatsapp, Instagram, tiktok da sauransu. Yarinyar wayayya ce ta ƙarshe, Ni da ba na kula ta yau ma ƙaddara ne ta kai Ni seat ɗinta na tarar ana taɗi kasancewar lecturern mu na Behavioural sciences bai zo ba, nan fa ana taɗin Novels da irin mazajen Novels na ce musu ai ina da yaya shi ma haka yake, suka fara zuga Ni kan kar Na sake na bari ya kuɓuce min, Ni kuwa cikin halin ko in kula na ce "Ai ko kaɗan BB Ni bai burge Ni, mun san saboda me?"
Suka ce A'a
Na ce "Saboda tun ina yarinyar yake cin ƙaniyata, suka babu irin wanda ban sha ba, punishment kuwa ba a magana, kun san sojojin nan ba su da tausayi"
"Ai soja ne ma?" wata a cikinmu ta tambaya
Na ce "ƙwarai kuwa, mugu ne kuwa na ƙin ƙarawa though he's very kind at times, tun da ƙofar samu ta buɗe masa shi yake sponsoring karatunmu, har Yayanmu Dr. Sadiq, za mu gani shi a Labour ward ko kuma Post Natal ward"
Khairat ta ce "Wai dama Dr. Sadiq yayanki ne? Sai yanzu ma na ga kamar"
Na ce "Yayana ne, daga shi sai Ni, sai ƙanina Ayman"
"AI guy ɗin nan akwai ƙwaƙwalwa in ji sister na, kin san su sun fara speciality posting, hotunansa da yawa a wayata ban san a ina ta samu ba, tana crushing mass over"
Na ce "Ai kuwa shi kam an bayar shi"
Muka sheƙe da dariya gaba ɗayanmu, Ni na fara tsagaitawa na ce "Da gaske, bestie na kuma cousin sis ɗina yake so, ƙanwar wannan Boss ɗin gidan namu"
Sady-Madaki ta ce "To amma ke meyasa ba ki son shi"
Na yamutsa fuska na ce "A matsayin ɗan'uwana shi ɗin na daban ne, amma ina jin ko da a ce shi ya ce yana so na ba zan iya soyayya da shi ba, kun san saboda me?" Suka ce A'a na ce "na rasa me ya sa duk lokacin da zuciyata za ta hasaso Ni a wannan ɓigiren sai na ji na fara tuna izayar da ya mana, gaba ɗaya sai tsanarsa ta cika raina"
Khairat ta ce "Wai! Da aiki gabanki class Rep, wallahi za ki so shi, don kuwa tsaf a gidanku za a ce za a haÉ—a ku aure"
Na waro idanuwana tare da rufe Mata baki da palms É—ina sannan na ce "Bakinki ya sari guntun kashi. Ina na isa na auri BB, Ai BB sai miskila irin shi su je can su kwaÉ—a mugun halinsu su cinye"
Su Sady-Madaki suka yi dariya, Khairat ta ce "Sai ka ce jaruman meye ma sunan novel É—in? Oho, na manta a tiktok dai na ga ana recommending a je a karanta"
Cike da mamaki na ce "Ku kam kuna tiktok abunku"
Ta buÉ—e baki tana kallona, na ce "ya dai? Kallon kuma na miye?"
Ta ce "To ai dole na kalle ki class Rep, sai kina nufin ke ba ki yi? Mukam muna ɗanawa, Instagram, Twitter Dukka muna taɓawa, followers ba adadi nake da su, ke kuwa da kina yi yadda kike kyakkyawar nan, hmmm"
Na ce "Ai ko app É—in ba Ni da shi, BB ya hana mu, iya Whatsapp ya yarje mu yi amfani da shi"
Shewa su khairat suka yi kafin Sady-Madaki ta ce "Lallai hasashe na ya zama gaskiya, wallahi Jannat wannan BB É—in naku son ki yake"
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*
*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*
1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA
2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT
3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN
4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE
5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA
Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.
Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k
Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu
Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇
09023907030
09161720046
+20 150 885 6397
09065856251
07061707238
*Masoya ina Æ™ara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub âœï¸ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*
*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~
https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS
*No 04*
*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_
07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim
.