← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 26

CHAPTER 4:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

A can ɓangaren BB kuwa yana barin ɗakinmu part ɗin Ummi ya nufa sannan ya nufi nashi bedroom ɗin ya shimfiɗa Sallaya ya fara raira karatun Alqur'ani cikin muryarsa mai daɗin gaske da yake kwaikwayon irin ƙira'ar Sheikh Muhammad Ayyub (Rahimahullah), sai wuraren seven thirty ya rufe Alqur'anin tare da mayar da shi muhallinsa ya kuma naɗe praying mat ɗin, jallabiyar jiknsa ya cire ya sauya zuwa wasu kaya da alamun motsa jiki zai fita, bayan ya sauƙo ƙasa har ya nufi ƙofar fita ko me ya tuna sai ya nufi kitchen, to his suprise, yaran can ba sa nan, ko da ya tambayi Salaha wacce ke taya Ummin girki tace ba su shigo ba, sosai ransa ya ɓaci, cikin ransa kamar wadda ake hurawa wuta yace "Lallai yaran nan sun gama raina Ni, zan mugun saɓa musu kuwa."

Kai tsaye part ɗin Mommy ya tafi, ɗakinmu ya nufa, ko da ya buɗe ƙofar sosai ransa ya ƙara ɓaci ganinmu sai sharar baccinmu muke a ƙudundune a cikin blanket, kansa ya jinjina sannan yayi maza ya fice ya ƙara ɗauko ruwa mai sanyi bottles biyu wannan karon, tun kafin ya shigo ya buɗe su, sai da ya daidaita kowaccenmu ya kifa su shaasss, a matuƙar firgice muka tashi zaune kowacce na ƙoƙarin yaye bargon ta nata ɓangaren. Bayan gwagwarmayar da muka sha daga ƙarshe muka cilla bargon gefe muna zazzare ido. Rafi'at ce ta samu ƙarfin guiwar faɗin "Wallahi BB Jannert ce..." Bai bari ta kai aya ba ya dakatar da ita da faɗin "I don't need any elaboration, kun raina Ni Ko?"

Idan aka ce tashin hankali, to fa ba a sa masa date, Idona da na ji Rafi'at na shirin mayar da laifin kaina take ya yi zuru-zuru yayin da cikinna ke bayar da wani irin sauti.
"Zan wuce gym, ku tabbatar yanzun nan kun wuce kitchen ku taya Salaha haÉ—a breakfast, after that."
Ya dube mu fuskarsa haÉ—e ya ce "Ku tabbatar kunyi watering duka flowers É—in gidan nan, today no breakfast for idle girls like you, ku kuma tabbatar kun same Ni a garden by nine, kada ku kuskura ku bari ba ku gama komai ba before nine, wallahi wannan karon ba zan muku da daÉ—i ba, silly girls!"
Yana gama faɗar haka ya fice tare da banko mana ƙofa ya nufi gym room abunsa.

Kallon kallo muka fara aikawa juna tsakanin Ni da Rafi'at yayin da kowacce ta kasa magana mun kuma kasa aiwatar da umarnin BB. Rafi'at da itama ke tsiryace tace "Wallahi Jannert duka laifinki ne, har na fara karatuna kika ce na ajiye mu kwanta, ga shi kin jaza mana bala'i wurin BB, mukan mun gama yawo yau"
"Ke dallas ki bar mu da halin da muke ciki tunda dai nima ba ware Ni yayi ba, kuma da kike cewa Ni na jawo miki ai ban ce dole ki yi baccin ba, Ni dai fatana Allah sa kar ya ba mu wannan mugun punishment ɗin nasa da Gara duka akansa." Na faɗa ina ƙarasawa cikin wata irin murya mai cike da tsantsar tsoro.

"Mu ci gaba da zama Jannert, in ya ƙara dawowa ya tarar da mu wallahi sai dai a a ƙara haifarmu in ana yi, Gara ma ki lallaɓa mu je mu yi abun da ya saka mu kafin lokaci ya cika." Ai kafin Rafi'at ta rufe baki na dire daga gadon ma nufi ƙofa, bayana Rafi'at ta bi.

Kai tsaye kitchen É—in muka nufa muka fara abun da ya kai mu, ita kam Salaha hakan sosai ya burge ta don kuwa ta san wannan aikin Big Brother É—inmu ne, yana mugun burge ta kasancewarsa tsayayye akan yaran, tabbas samun tsayayyun yayye irinsa sai an tona, ga shi da dai a shekare ba wani girma gare shi ba, amma kuma hankalinsa, tunaninsa da kuma hangen nesa irin nasa ko a masu shekaru sai an tona.

Da Ummie ta shigo kitchen É—in sosai itama tayi mamakin ganinmu a kitchen É—in ta kuma tabbatar da aikin waye, bayan mun gaishe ta tace "Yau kuma angels ku ne a kitchen?"
Juna muka kalla ba tare da mun ce komai ba, Ummie tace "Daga dawowa ba za ku huta ba?" Nan ma shiru "To shi ke nan, ku koma ku kwanta kawai tun da baccin bai ishe ku ba"
Ai a haɗe kamar karatu muka ce "Laa, Ummie za mu ƙarasa, ga shi saura ma kaɗan ko Mama Sala (Kamar yadda suke kiran Salaha).
"Ƙwarai kuwa Hajiya, yanzu za a kammala ma."
"Ma sha Allah" Ummie ta faɗa tana mai ficewa abun ta cikin ranta tana ƙara yi wa BB albarka don kuwa ta san ko da bayan ransu ne, zai kula sosai da tarbiyyar yaran.

Bayan mun kammala haɗa breakfast mun jera kai tsaye muka fice daga sashen Ummi muka biya mu gaida Mommy wacce ta gama haɗa nata breakfast ɗin, sosai Mommy ta yi mamakin ganinmu sassafe haka, mutanen da ke tashi daga baccin safe ƙarfe sha biyu in ba tashinsu aka yi ba su ne a waje? Kasa shiru tayi sai da ta magantu "Yau ku ne da tashi da wuri Yarinyata?"
Wani irin zare ido waje na yi kafin na ce "Yau so muke mu yi aiki Mommy, daga yau sai mu fara hutawa ko?"
Ƴar dariya tayi irin ta manya kana tace "To ku zauna ku karya yanzu sai ku ƙarasa aikin."
"Laaa, Mommy ai mun riga mun yi breakfast a part É—in Ummie" na faÉ—a ina shafa cikina da ke neman É—auki saboda yunwa.
"To shi ke nan, a É—au harama" ta ba mu amsa tana mai wucewa upstairs.

Ni da yunwa ke shirin Kaini ƙasa ne na dubi Rafi'at nace "Me yasa rai Allah ya dawo da BB gidan nan lokacin hutunmu, nikam na ƙosa a fara registration mu samu mu koma."
"Kin ga tafiyata Jannert, ba za ki jaza min wani laifin ba, ki zauna kina surutu bayan kin san lokaci ya ba mu ga kuma tulin flowers É—in da za mu ba wa ruwa."
Rafi'at ta faɗa tana ficewa abunta, kallon agogon da ke bango nayi, takwas da mintuna, hakan yasa na bi bayan Rafi'at da gudu. Sosai muka sha wahala kafin mu gama watering flowers ɗin kasancewar yawan da suke da su don gaba ɗaya farfajiyar gidan flowers ne tun daga bakin gate, iya hanyar da aka bari ne ta wucewa da mota zuwa parking space, hatta canopy ɗin da baƙi ke zama ko su idan za su huta a kewaye yake da flowers ɗin, zuwa bayan gininnika, sai kuma babban garden ɗin gidan da shi ma yake cikin lissafin BB.

Mun matuƙar ligirta kafin mu gama saboda rashin sabo da yunwa da muka yi, gara ma Rafi'at wasu lokutan akaina, ganin in muka ce za su wuce wurin BB za mu iya mutuwa don ba mu san kalar punishment ɗin da zai ba mu ba yau yasa muka yanke shawarar cin abinci, ko ma wani irin punishment ne, la'alla ma iya ɗauka idan tunbinmu ya ɗiba, yanke shawarar ci a part ɗin Ummie muka yi, fatansu ko da BB ya shigo ya ganmu In mun canki Sa'a ya haƙura idan Ummie ta musu magana.

Da wannan shawarar muka ba wa cikinmu hakkinsa duk da cewa a ɗaɗare muke kada ya shigo ma ya tarar da mu. Lokacin da cikinmu ya ɗauka ne muka fice don zuwa karɓar sakamakonmu, garden muka nufa kai tsaye, tun daga nesa muka hango shi hakan ya sa zukatanmu fara luguden tsoro, kamar an jiƙa tsumma saboda yadda jikinmu yayi lirif, a haka muka nufi wurin da yake yana sipping hot tea ɗinsa hankali kwance yayin da mu kuma ya bar mu cikin tashin hankali.

Sallama muka yi, ba tare da ya ɗago ba ya amsa mana sallamar yana ƙara sipping tea ɗin.
"BB ga mu" Rafi'at ta faɗa tana wani irin lanƙwasa harshe tare da fatan ko zai tausaya mana. Tsawon wasu daƙiƙu ya share ba tare da ya ƙara duban yadda muke ba, in bacin amsa sallamarmu da yayi da sai mu ce bai ma san da zamanmu ba ne.


Ganin yadda ya banzatar da wanzuwarmu ne yasa Ni tunanin ko dai ya manta da su ne? Hakan yasa na yanke shawarar yin Magana da fatan ko zai tuna da mu. Cikin murya mai É—auke da tsoro nace "BB..." hannu ya É—aga min, take ta gimtse bakina na kuma yi wa kalamaina sakatar fita.

Don kansa ya gaji da shan ƙamshinsa can ya ajiye cup ɗin hannunsa a gefensa tare da dubanmu. Fuskarsa ya ɗaure kamar wani soja a filin daga kana yace "Wato ku kun raina Ni Ko?"
Da sauri muka fara jijjiga kai a tare muka ce "Wallahi a'a BB"
"Good" ya faÉ—a yana mai gyara zamansa "Na ma ce muku ku same Ni a nan by nine shi ne kuke so ku nuna min cewa wuyanku ya kai ko?"
Kanmu muka fara girgizawa yayin da muka gama tsorata, tsoronmu ɗaya dai Allah yasa ba ƙara lokaci muka yi ba.
"Da ku nake kuma wani jijjiga min kai, ba ku da baki ne?" Ya faÉ—a a É—an tsawace
"A..a...a BB, muna da shi" na faÉ—a, cikin raina ina da na sanin komawa baccin da muka yi.

"Tun ba yau ba na ga yadda kanku yake rawa, musamman ke Rafi'at" ya faÉ—a yana nuna Rafi'at, Allah sarki, take hawaye suka fara zarya daga eyes É—inta, ta san suna da rawar kai don ba iya BB ke faÉ—a ba amma dai duk rawar kanta ai ba ta kai Ni ba.
Wani kallo ya aika mata take ta share hawayen da hannunta "Na duka ki ne kike min kuka?"
Ta ba shi amsa da
"A'a"
"Then kar na ƙara ganin ko da drop ɗaya ne na hawayen, ok?"
Kai tayi saurin gyaÉ—awa.

Bai ƙara kallonmu ba ya janyo wayarsa da ke gefensa ya kunna tare da juyo mana da screen ɗin yana fuskantarmu "Ku duba what's the time and tell me yourselves "
Ƙwalalo idanuwa muka yi ganin mun ƙara kusan 30minutes. Kasa samun mai magana a cikinmh aka yi, hakan kuma ba ƙaramin ƙara fusata shi yayi ba.
"Are You people deaf?" Ya tambaya a fusace
"N...no"
"Duk cikin rainin ne ko?"
"No?" Muka ba shi amsa da sauri a wannan karon
"Shi ke nan, I'll make sure that you people get to know how to mind yourselves."
"Don Allah BB ka yi haƙuri ba za mu ƙara ba"
"Don Allah wallahi ba za mu ƙara ba"

Kallonmu yayi yace "Ya isa! Kar ku sa min ciwon kai."
Kamar haÉ—in baki dukkanmu muka É—aura index finger É—inmu kan lips.
Gyaran murya yayi can yace "Anya ma kuna Salla a school É—in?"
Kallon kallo muka aikawa juna, Ni na yi saurin faÉ—in "Wallahi tun da muka dawo Mommy ta yi mana faÉ—a, kuma mun É—auka asubar ce aka samu akasi."
"You called it Akasi right?"
Jikina ne ya fara karkarwa yayin da na fara juya abun da ta faÉ—a a ranina ina tunanin me ye ba daidai ba a ciki.
"Shi ke nan, za mu zauna a nan ne da ku, in kun shirya yin bayani sai ku yi na ba ku punishment É—inku."

Kamar mu ɗaura hannu a ka mu zunduma ihu haka muka ji, tabbas mun san sun zo hutu tare da BB, ga shi tun ba a je ko ina ba ya sako su gaba, rama kam mun riga mun saddaƙar mun yi ta ma don in dai yana nan hatta magana a hankali muke yin ta, abu kaɗan sai yace laifi ne.

Ni ce a wannan lokacin nace "Wallahi BB mun shirya, dama can a school ba ko yaushe muke sallar ba, muna yin azahar, magriba kullum sauran ne dai ba ma yi, wallahi jiya Mommy ta mana nasiha mai ratsa zuciya har mun sauya wallahi, asubar ma rashin sabo da tashinta ne amma mun maka alƙawarin za mu gyara don Allah ka mana haƙuri in ba mu gyara ba ka mana duk abun da kaga dama ko ba haka ba Rafi'at?"
Da sauri Rafi'at ta fara gyaÉ—a kai tana faÉ—in "E wallahi BB, mun tuba mun bi Allah don Allah ka mana rai wallahi yanzu ma mun ji jiki."

Murmushin gefen baki yayi kana yace "Ba dai ba ku saba da salla ba? Karatun Qur'ani fa, izunku nawa-nawa?"
Idanuwa muka zaro a kunyace Rafi'at tace "Babu ƙarya wallahi BB iya wanda Ummie da Mommy ke mana ne muka yi, amma shi ma za mu koya?"
Ya jinjina kai yace "Good! Ba za ku kuma komawa boarding ba, a nan gida za ku zauna, gobe goben nan ku shirya duk Islamiyya zan kai ku, wato ku ko damuwa ba kwa yi ko? Ba ku iya komai ba a addini, Allah ya sa sallar ma kun iya"
"Wallahi mun iya!" Muka haÉ—a baki muka ba shi amsa da sauri.
Jinjina kansa yayi yace "Sure?"
Muka gyaÉ—a kai yace "Ok, yanzu kuzo ku yi a gabana, duk wani supplication da ake karantawa kuma ku yi a fili."

"Innalillahi!" Abun da na iya furtawa ke nan a raina don har ga Allah ba komai na iya ba. Ganin babu wanda ya motsa cikinmu yasa ya haÉ—e fuska yace "I'm talking to human beings?"
Kanmu muka gyaɗa tare da miƙewa jiki ba ƙwari muka fara kwatanta sallar munna fatan Allah yasa kar ya ce ba haka ba ne yayi mana asarar komawa Dolphin kamar yadda ya fara faɗa don ba ƙaramin buri muka ci ba. Kamar ba mu yake kallo ba saboda yadda ya lumshe ido amma a gaskiya mu ɗin yake kallo, ganin ya lumshe Idanuwansa yasa muka sauƙe ajiyar zuciya a tare, sai da ya bari muka gama tukunna ya dube su yace "Haka aka koya muku?"
Raurau muka yi da idanu tare da kallon juna cikin ranmu muna masu saddaƙar da cewa shi ke nan.

"Ku dawo ku zaun.." kafin ya kai aya mun zauna damas gabansa.

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*
*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

_No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 5 · 0% Book details