← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 26

CHAPTER 11:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Mamaki sosai muka yi jin yadda ya yi wannan dogon bayanin kuma cikin sassanyar murya babu wannan ƙuncin nan, da alamu dai ya yafe min abun da na yi masa nima. Tsakanina da Rafi'at sai son Barka, sati guda da fitowar WAEC result, Neco result ma ya fito, aka kira mu daga makaranta kamar yadda aka yi a lokacin da WAEC yi ta fito, bayan an cirewa kowa aka ba shi copy ɗaɗɗaya, daga nan aka ce za a nemo mu batun shirye-shiryen sauƙa da Speech kamar yadda makarantar ke shiryawa, sosai iyayenmu suka yi farin ciki da sakamakon da muka samu, daga nan suka fara tunanin abun yi, a son ran Abuya dai mu fitar da mazaje ne a mana aure, Ummi ma ba ta da matsala da hakan, amma kuma Daddy na son mu yi karatu gaskiya, ko da suka zauna a junansu wata rana da muka je Jama'are gidan Kaka sun samar da matsayar a ba mu dama mu kawo mazaje in Babu sai mu fara makarantar gaba da sakandare, idan mijin ya zo ko muna farawa ne to ba makawa za a aurar da mu, tun da muka ji wannan bayani kowaccenmu ta ce ai ba ta da saurayi, Daddy ya ce shi ke nan za a nema mana admission Amma bai ce a kaza ba.

Ɓangaren BB haka ya ci gaba da dakon soyayyata yayin da ya ci gaba da ɓoye ta ba tare da ya bayyana min ba, bayan zuciyarshi da kuma Big Sis sai Ya Khalid ne kaɗai suka san da wannan babban sirri, hatta su Mommy da Ummi babu wanda ya sani.

Watan Oktoba aka saka ranar Speech and prize giving day É—inmu da kuma memorization Walimah É—inmu, ba mu yi nauyin baki ba muka samar da BB ta wayar Rafiat don Ni dai ba Ni da ko da numbern shi bare kuma na kira shi, ya tambayi exact date muka sanar mishi.

A week to the graduation BB da Ya Khalid suka dira a Azare, Tarba ta musamman suka samu wurin Ummi, muka taya ta shirya musu abinciccika iri-iri har nake mamakin yawan abincin, ashe saboda zuwan Ya Khalid É—in ne. A mutunce maka gaisa da BB fuskarsa babu yabo ba fallasa yayin da Ya khalid kuma ya amsa mana a sake har yana tambayan wace ce Jannat cikinmu, wani iri na ji, na ce hala dai ba BB ya ba shi labarin rashin kunyar da na mishi ba ne yake son ganina, a sukwane na bi Rafi'at muka koma part É—in Mommy.

A tunanina kwana biyu BB zai yi ganin da baƙo suke, sai na ga sun zarce hakan, bamu ji wata magana daga wurin BB na game da shirin da muke, mu dai ba abun da muke shiryawa, haka ma iyayenmu mata, ana saura kwana biyu Speech and prize giving day BB ya samu shiryawar ba zata, a tare da shi da kuma Ya Khalid, sannan Ni da Rafi'at ya ɗauke mu ya kai mu wani katafaren wurin gyaran jiki, abun mamaki kuma ya ce a mana duk wani abu da ya kamata sannan ya ce In an gama se should let him know ya zo ya yi settling bills sai ya mayar da mu gida.

Banbaraƙwai, wai namiji da suna Hajara, mace da suna isa, wallahi sosai muka sha mamaki har sai da muka tattauna a tsakaninmu, nikam abun da ya zo raina ma na yi tunanin Ya Khalid ɗin ya yaba da wata a cikinmu ne, Ni dai addu'a ta Allah ya sa Ni ce Don kuwa ya yi min, yana da dukkan siffofin mijin da nake so, tun daga kyau, thought ko kama ƙafar BB Bai yi ba a wannan fagen, kuɗi ma sha Allah don na tabbata shi zai biya wannan ɗawainiyar ma, uwa uba fara'a Da faran-faran daga gani goga ne da zai iya fafatawa a fagen soyayya irin ta bugawa a jaridar nan. Ni dai da wannan tunani da hasashen cikin raina aka mana gyaran gashi, sai da ba a kitse shi ba, an mana both Jan lalle da baƙi bayan an wanke mana ƙafafu da hannayenmu da yanzu ke da wani irin sihirtaccen taushi da kuma laushi. Kusan ƙarfe biyu aka gama mana, Rafi'at ta kira BB ta sanar da shi, suka zo suka ɗauke mu tare, hakan ya ƙara tabbatar min da zargi na, cewa Ya Khalid na son ɗayarmu, dole ma ba da himma don ganin na samu wannan dama tun da ita Rafi'at already Ya Sadiq na sonta.

Abun mamaki BB sai gwaɗa lallen namu yake a hanya though ban ma tunanin ya gani ma, ga shi kuma ya sake mana fuska kaɗan har da yin dariya, Ni kam sai na ji abun banbaraƙwai don ba sabun ba ne, wai tinkiya da gilashi, kafin mu koma gida sai da muka biya ta wani Bakery, BB da Ya khalid suka shiga suka ce Mu jira su, bayan sun dawo muka ƙarasa gida, Ummi da Mommy suka yi ta saka masa albarka, Ni dai na ja bakina na tsuke ban ce ba shi ya biya kuɗin ba Ya Khalid ne, ashe Gara da ban faɗa ɗin ba shi ɗin ne ya biya.


Washe gari ba mu je ko ina, though da mun tambayi Ummi Driver ya kai mu gidansu wata ƙawarmu Amina Zubair Mu tambayo ta me da me yake shiryawa muma mu dawo a mana, Ummu ta ƙi amincewa, saboda haka muka haƙura tare da zubawa sarautar Allah idanuwa.

Daren ranar wani zumuÉ—i muke ji, haka muka yi ta surutu ba mu yi Bacci ba har wuraren asuba, Ganin haka ya sa muna yin salla muka yi wanka, na É—auko kaya zan saka Rafi'at ta dube Ni ta ce "Ke lafiyarki?"
Na ce "Me kika ga?"
Ta janye kayan daga gabana ta mayar da su closet
"Tsabar zumuÉ—i ne za ki saka kaya tun yanzu? To ba za ki sa ba"
Babu yadda na iya sai da muka yi breakfast tukunna, nan ma ta ce ba zan saka ba sai 8:00 ta cika, sai da ta cika ya bar Ni, muka shirya cikin sabuwar atamfar mu da Mommy ta É—inka mana.

Da mun so bin motar Baba Driver ne, sai da ga mamakinmu BB da abokinsa sun hakimce cikin wata sabuwar motarsa da ba na ce Ga ranar da ya saya ba, ƙarasawa muka yi muka gaida su, Ya Khalid ya ce Mu shiga tare da mu tafi, su Mommy za su biyo su Daddy, ba musu muka shiga, tun da motarmu ta shiga cikin makaranta idanuwa suka yi kanmu, bayan ya paka a wurin da aka tanada domin ajiye motoci muka fito, na nuna musu canopy ɗin guests, suka zazzauna, muma muka nufi sashen da aka tanada dominmu.
Muna isa ƙawayenmu suka fara murnar ganinmu suna yaba kyan da muka yi, musamman Ni da kalar Hijab ɗin namu ya haska sosai, kafin ka ce me mutane sun zozzo, manyan baƙi sun zauna a rumfarsu, organizers tuni sun daidaita komai ana jiran ƙarfe takwas da rabi ta cika a fara komai.

A ƙa'idar taro a makarantarmu, ana buɗe shi ne da opening recitation daga students ɗaya namiji ɗaya mace sannan a yi national anthem, sauƙa ita ce agenda ta farko da za a fara. Nan aka jera mu ɗaya bayan ɗaya mata na fuskantar maza, sannan aka bayar da amsa ƙuwwa guda biyu wa mata biyu wa maza, cikin ƙwarewa da kuma bayarwa harrufa haƙƙoƙinsu Malam Misbahu ya fara yi mana ja a cikin Alqur'ani muka ɗauka muka yi, can ya dakatar da mu ya mana sabon ja, shi ma muka yi shi, ja biyar ya mana, na shidan kuma ya ja mana surorin ƙarshe na Alqur'ani, daga ahad zuwa ƙasa, nan kam haɗa baki muka yi tare da shi har muka kai -Minal jinnati wannas!" Nan wasu daga cikinmu suka fashe da kukan farin ciki, ciki kuwa har da Ni, bayan an kammala sauƙa aka ba wa kowaccenmu certificate na shaidar ta haddace Alqur'ani tukuna muka koma wurin zaman mu.

Taro ne aka yi mai ƙayatarwa, mun kuma ji daɗin yadda ya tafi a nutse babu hanyaniya, manyar mutane sun yi Speech kala-kala masu muhimmanci da taɓa zuciya, haka hukumomin tsaro, ɗaliban primary section sun yi drama, presentations and debates also by students, sai kuma farewell speech da head boy ya yi sannan aka kira sunana a matsayin headgirl nima na yi. Bayan mun kammala da wannan sashen aka ba mu prefectship certificate, daga nan aka fara raba kyaututtuka.

An shafe awa guda a wannan sashen daga bisani aka kammala aka dawo sashen outgoing students, kyaututtuka huɗu na karɓa, Rafi'at shida, na karɓi kyautar best in Qur'an, best in mathematics, best in Chemistry da kuma best in Agriculture yayin da Rafi'at ta karɓi kyautar best in History, most obedient student, most punctual student, da kuma best in Government da geography.
Kusan duka kyaututtukan mu muka kwashe su, hakan ya matuƙar sanya iyayenmu alfahari, a haka aka kammala taro lafiya, aka fara daukar hotuna, BB ya kira wayar Rafi'at ya ce ta kira Ni, ga mamakina hotuna wai za mu ɗauka, hotuna a tare da BB da sauran mutanen gidanmu, hotuna sosai aka cire mana masu kyau daga nan BB ya faki idonmu ya yi wani wajen, ashe zuwa ya yi ya karɓi details ɗin malamin da ya sauƙar da mu da kuma asusun makaranta, yana dawowa muka tafi gida.

Yana ajiye mu ya ƙara fita, da yamma muka shirya domin zuwa walimar da makaranta ta shirya mana, bayan an kammala jawabai aka fara raba souvenirs, mu kam babu abun da muka yi, muka ja gefe abun mu, muna tsaye wayar Rafiat ta fara ringing, tana dubawa ta ce "Ke BB ne" na ce "Don Allah?" Ta gyaɗa kai tare da ɗaga wayar ta kara a kunnenta, ban san me yace mata ba sai gani na yi ta washe baki tare da daka tsalle ta ce "To ga mu nan zuwa" tana sauƙe wayar ta ce "Ke ki zo mu je, Allah ya sa wani abun su Ummi suka bayar ya kawo mana, gaba ɗaya sai yanzu na ji dama mun karɓi kuɗi wurin Daddy mun yi hidimar mu"
Na ce "Mu je dai yanzu kam"
Muka fita, a gefe can muka hango motarsa, ta can baya yake jingine da motar ya yi kyau abunsa, muna isa Ya Khalid ya fito sannan ya ce "A'a, Æ´an gatan BB kin iso ke nan?".na kalle shi na jinjina kai cikin raina na ce, ba ka san Æ´ar tsamar da ke tsakaninmu ba.
Boot ya buÉ—e mana, ya nuna mana Boot É—in da hannunsa, waro idanuwana na yi saboda mamaki ban san lokacin da na ce "Dukka wannan É—in miye?"
BB ya amsa da "Idon matambayi, malamai in za ku ɗauka ku ɗauka in ba ku so kuma na shiga na kira ƙawayenku na ba su kyauta"
Ai bai rufe baki ba muka sa hannu don mu janyo buhuhhuna guda biyun da ke ciki but ba mu da ƙarfin hakan, ya Khalid ya ƙaraso ya ce "Kada ku damu, mu je za mu shigo muku da su"
BB ya harare shi ya ce "Mu É—in bayinsu ne?"
Ina ji Ya Khalid ya ce "To ai watarana hakan ne, haba babban yaya "

Wata irin murna na ji ta kama Ni, na ta'allaƙa hakan ne Ni kuma da kalaman Ya Khalid na watarana hakan ne, ke nan da gaske yana son ɗaya daga cikinmu, a yanzu fatana shi ne Allah ya sa na zamto wannan mai Sa'a, ya kuma sa ya furta min wanann abu a yau ɗin nan.
Wannan shi ake kira da neman nema, shi BB yana nan yan dakon soyayyata Ni kuma ina nan ina dakon ta abokinsa.

Har ciki suka shiga mana da kayan, ƙawayenmu da ke rabo suka ƙaraso suna gaida su duk da ba su san matsayinsu wurinmu ba, kowacce sai wani maƙale murya take, hakan ya ban haushi tare da fatan Allah sa dai ba wacce ta burge Ya Khalid cikinsu, suna ajiyewa suka juya, nan muka hau rabo muma, kaya ne sosai BB ya sa aka mana, souvenirs masu aji, kowacce jaka akwai sallaya, hisnul Muslim, counter, callender, mug, meme da kuma biro mai ɗauke da sunanmu sai kuma wata takeway rubber da aka saka half chicken, doughnuts biyu cake ɗaya da puff² biyu, sai lemon jarka guda.
Lallai dole mu jinjinawa Babban Yaya, yau kam ya nuna mana cewa shi É—in babban yayanmu ne, don ya fitar da mu kunya, hotuna muka dauka bayan kammala rabo mazanmu da matanmu coz wannan me dama ta farko da makaranta ta ba mu na yin hakan a tare da Opposite classmates É—in namu.

Sai da aka fara kiraye-kirayen sallar magrib muka fito, alhamdulillah mun samu mai keke ba ɓata lokaci muka shige abunmu sai gida, a hanya BB ya kira Rafi'at yana tambayarta muna ina? Ta ce masa mun kusa isowa ya ce shi ke nan ya kashe kiran. Muna komawa gida wanka muka yi muka sauya kaya sannan muka yi salla, daga nan muka nufi part ɗin Ummi kasancewar Kaka ma na can, ana ta taɗi sai albarka kaka ke saka mana.

A can ɓangaren BB tun da suka koma daga kai mana souvenirs Ya Khalid ke takurawa BB kan ya fitar da sirrin zuciyarsa a wannan rana yayin da BB ya ce shi sam bai san zancen nan ba, ai zan raina shi, yanzu ma ya aka kaya, shi dai zai ƙara haƙuri na ƙara hankali tukun na.
Cike da takaicinsa ya khalid É—in ya dube shi ya ce "Wallahi ka mugun ba Ni mamaki Khalil, wai kai ba ka tunanin mai zai je ya dawo ne?"
BB ya ƙi kula shi, cikin ɓacin rai ya ce "Wallahi ina jiye maka kada wani ya maka shigar sauri, wallahi in ta kamu da son wani babu abun da ka isa ka yi, don na tabbata Daddy ba zai taɓa bari a takura ta ta so ka ba wai don kana ɗan'uwanta"
BB ya juyo ya Kalli Ya Khalid ya ce "Ni na san ba kuskure a cikin shirina K, na tabbatar maka cewa, Jannat tawa ce duk wuya duk rintsi, she'll forever be mine, mine alone! Kuskurenta ne kuma ta ƙi karɓa ta a matsayin miji, amma dai na san ita ɗin matata ce, kuma in Sha Allah hakan za ta tabbata"
"Ina fatan hakan, shi ya sa nake nuna maka illar jinkiri wurin fitar da sirrin zuciyarsa, hakan kuskure ne babba "
BB ya lumshe idanuwansa sannan ya ce "Allah ya zaɓa mana mafi alheri" daga nan bai kuma ƙara cewa komai ba.

A namu ɓangaren da wuri muka yi bacci saboda gajiya, washe gari da misalin ƙarfe goma muka taru a part ɗin Mommy, da Ni da Rafi'at, BB da Ya khalid, Mommy day Ummi, Daddy da Abuya da kuma Hajiya Kaka. Tattaunawa aka yi amma an fi karkata wurin nuna mana muhimmanci aure a wannan gaɓar, la'alla don Abuya ne ke bayanin, don da Daddy ne yanzu batun boko zai kawo, ai kuwa bayan ya karɓi jawabin batun da ya yi magana kansa ƙarshe shi ne karatunmu, ya yanke shawarar nema min admission a school of nursing, ita kuma Rafi'at ta je ta yi change of institution ta yi Bsc Economics, ba ta ji daɗin hakan ba amma babu yadda ta iya, haka ta amince, washe gari BB da kansa ya kai ta café aka mata change of institution zuwa Aminu Sale College of Education Azare, ya biya ya siya min Form ɗin Basic Midwifery a Adamu Adamu College of Nursing Sciences, Azare, sai dai ya samu bayanin cewa sai December suke fara sayar da fork ɗin Midwifery.
*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 12 · 0% Book details