← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 26

CHAPTER 1: Not just the beginning!

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

"Jannat ki buÉ—e kunnuwanki ki saurare Ni da kyau!"
Abuya da ke zaune kusa da Ummi ya faɗa muryarsa a kausashe yana nuna ni da yatsa yayin da nake durƙushe gabansu kaina ƙasa "Matsawar ina da daraja a wurinki kuma kin yarda ni na haife ki to dole ki amince da zaɓin da na miki, auren ki ke da Khalil babu fashi matuƙar dai ina numfashi a doron duniyar nan, wajibi ne, dole ne ki rabu da so called Doc

Wani mugun kallo Ummi ta aika min tare da dungure min kai tana faɗin "Wallahi Jannat, kin ji na ce wallahi ko? Matsawar za ki take umarnin da muka gindaya miki na auren Khalil, wallahi zan iya yafe ki cikin ƴaƴana, ke in ba da ma ƙaddara me Khalil zai yi da ke? Ba Ni na haifi Khalil ba amma ya fiye min ke sau dubu miliyan, don ina da tabbacin cewa ko Ni nan in na shata masa layi ba zai take ba, ke fa? Um?"

Wani irin kuka na saki da da ran za su tausaya min, irin kukan nan da ake wa laƙabi da marayan kuka, kukan da duk wanda kunnuwansa suka jiyo sautinsa ba makawa tausayi da kuma rangwame za su mamaye zuciyarsa, amma kash, ban da Ummi da Abuya, wanda cikin kwanakin nan da suka fahimci alaƙar da ke tsakanina da BB suka riƙe min wuta kamar ba su suka haife Ni ba.
Cikin muryar tawa mai haɗe da fitar Kuka na ce "Ummi, Abuya, wallahi ku kuka haife ni na san wannan, ku ne kuka min gata har na kai yanzu, don Allah Ummi na roƙe ku kada ku ruguje min rayuwa ta hanyar aura min BB, wallahi ba shi ne wanda...."

Hannu Ummi ta kai min za ta buge bakina, Abuya ya yi saurin riƙo hannunta ya dawo da ita mzauninta, cikin ƙunar rai da takaicin abun da na ce ta aiko min da wani mugun kallo da ya sa ƴaƴan hanjina juya, sauƙe kaina ƙasa na yi babu shiri.
Ummi ta ce "Ba shi ne wanda kike so ba ko? To ƙanin uwarki kike so um?"

Abuya kam numfashi ya sauƙe yayin da yake Ƙoƙarin saisaita ɓacin ransa, cikin wata irin murya da na gagara gane manufarsa ta ce "ba sai kin sa hannu kin dake ta ba Amina, rabu da ita, idan har ta san wata ai ba ta san wata ba, aure kuma da Khalil na faɗa miki babu fashi, idan ya so ki kashe kanki in an aura miki shi, yarinya ƙarama da ke ba za ki lalata mana zumunci Ni da ɗan'uwana ba don ke a sama na same ki, shi kuwa da shi muka yi gwagwarmayar rayuwa har muka kawo matakin da muke ba tare da an taɓa jin kanmu ba, ke a wankin ce za ki zo min da banzar magana Jannat?"
Abun da ya maƙale masa a maƙoshi ya haɗiye sannan ya ce "Ko bayan raina Jannat, ban amince ki auri wani ɗa namiji ba in ba Khalil ba, kin ji abin da na ce ko?"

Cikin shesheƙar kuka na ce "Don Allah Abuya kar ka min hak..."
"Za ki rufe min baki a nan ko sai na ɗauko bulala na fara bugun ki?" cewar Ummi wacce ranta ya gama ɓaci da rashin ta ido da nake sheƙa musu.

A tsorace na É—an ja Baya ganin kamar Ummin za ta dake ni.
"Shashasha kawai! Madadin ma ki fahimci inda muka dosa jeji kike ƙara nausawa, anya kuwa kan ki ɗaya Jannat?"
Abuya ya faÉ—a cike da kokonton sabbin halayen da nake displaying a Æ´an kwanakin nan.

Hausawa suka ce Abun da babba ya hango, ko dutsen dala yaro ya haye ba zai iya gani ba. To kamar haka ce take faruwa a wannan gida, duk wata hanya ta lallami Abuya da Ummi sun bi wajen ganin na karɓi soyayyar ɗan'uwana amma abun ya ci tura, na dage dole sai Dr. Junaid, mutumin da ba ma ɗan garin ba ne a binciken da Abuya ya sa aka yi akansa.
Yadda nake ke kuka gaban su Abuya kamar raina zai fita ya sa ran Ummi ƙara ɓaci, cikin hargagi ta ce "Ɓace min da gani kafin na zuciya na miki dukan da sai kin yi zaman jinya, wawuyar yarinya kawai"

Da mugun sauri kamar wacce ke zaune gaban dodo na fara ƙoƙarin barin gaban nasu har ina dungurawa, cikin kaɗewar hankali da na samu na tashi sai na ruga da mugun gudu har ina cin tuntuɓe kamar zana faɗi har lokacin sautin kuka na na fita.

Ɗakina na nufa kai tsaye tare da faɗawa kan lallausan gadona wanda a yanzu nake jinsa tamƙar ƙaya, kai ba ma gadon ba, gidan kansa a yanzu ya gama isata, ba Ni da wani buri a yanzu ko fata irin a ce an ɗaura min aure da Dr. Junaid mun tare a gidanmu Ni da shi, rufe fuskata na yi da tafukan hannayena biyu ina mai ƙurawa chandelier da ke sarƙafe jikin farin POP ɗin da ke ɗakin ta tsakanin ƴaƴan yatsuna. Kukan na ci gaba rairawa tun muryata na fitar da sauti har ta dashe, tun hawayena na zubowa har suka daina zuba ya zamana kukan da nake yi na fita ne daga zuciyata har wata irin ƙuna nake ji daga can cikin ƙirjina.

Tabbas ina cikin mawuyacin hali a yanzu, iyayena da ya kamata su nuna min kulawa a wannan yanayin sun juya min baya akan mutumin da ya raine n da tsantsar ƙiyayya da mugunta, mutumin da bai ƙi igiyar numfashinmu Ni da ƴar'uwa Rafi'at ta datse ba tun muna yara ƙanana, mutumin da bai taɓa dubanmu da idon rahama ba bare kuma tausayawa sai zallar son ganin hawayenmu.
"Ta yaya suke tunanin zan so shi?" Na ayyana hakan cikin raina daidai lokacin da nake sauƙe wata nauyayyar ajiyar zuciya, Zaune na miƙe tare da jingina kaina da fuskar gado, cikin dasasshiyar muryata da ke fita da ƙyar kuma cikin sauti mara amo na ce "Don kawai ya buɗe baki ya furta min kalmar soyayya sai na yarda da shi? Babu yadda za a yi maƙiyinka ya ce yana sonka rana ɗaya! So na da yake a yanzu ba zai canza komai ba, don har yanzu ba na jin zan iya mance duk wata nau'in izaya da cutarwarsa gare ni ba."
Ba wai ban yarda yana son nawa ba ne a yanzun, a'a Ni kaina ina iya ganin tsantsar soyayyata cikin ƙwayoyi idanuwansa amma dai, zuciyata ta riga da ta gama soyewa, ta bushe ƙayau, ta ƙaiƙashe, kai ta ma zama gari in dai akan ta so shi ne, ji nake a raina ba zan taɓa son BB ba, so dai so irin na soyayya kam, ba na jin zuciyata za ta ji shi akansa, kai ko a mafarki ba na tunanin hakan, bare kuma kuma a zahirance, har babban al'amari wato aure ya shiga tsakaninmu, Dr. Junaid shi ne zaɓin raina, shi ne wanda nake muradin rayuwa tare da shi a ƙarƙashin inuwar aure, don haka babu gudu babu ja da baya, Dr. Junaid shi ne wanda zan ta aura ko da kuwa gaba ɗaya duniya za su juya min baya ne.

Sulalewa na yi daga jinginon da na yi na kwanta tare da Juyi ina mai dafe kaina da ke mugun ciwo sakamakon kuka da kuma rashin cin abinci da na saka gaba wanda nake ganin kamar shi ne mafita gare na, ina ganin ta iya wannan hanyar ne in na ɓullo Abuya da kuma Ummi za su janye tsumagiyar da suka ajiye mata kan hanyata tare da cika min muradin da nake jin bayan shi na gama samun duk wani farin ciki, jin daɗi da kuma walwala a rayuwata, tunanin yadda zan samu Wayar da zan yi magana da Dr. Junaid nake amma babu wata dama, Ya Sadiq ne dama hope ɗina, shi ma kuma a yanzu na san cike yake da matsanancin haushinna, ko da kuwa zan shura ne ta mutu na san ba zai ba ta wayarsa na kira wani ba ma, bare kuma Dr. Junaid da a yanzu na tabbatar illahirin gidanmu babu wanda bai tsane shi ba, domin gani suke kamar ya yi min wani abu ne shi yasa nake behaving so strange about him.

Rafi'at ce ta faɗo min a rai. Hakan ya sa Ni miƙewa zaune ina furta sunan Rafi'at ɗin cikin dasasshiyar muryata "Rafi'at?" saurin girgiza kaina na yi ina faɗin "Nooooo, Ban da Rafi'at, ta yaya ma zan iya kallon tsabar idanuwanta na ce mata ta ban wayarta na kira Dr. Junaid after all ido cikin ido na ce mata ba na son ɗan'uwanta?"
Na ƙarashe ina girgiza kaina, duk da cewa dai Rafi'at ba ta juya min baya akan abun da ke faruwa ba sai dai kuma Ni kaina ina da yaƙin cewa cikin ranta tana tsananin jin haushina, ko ba komai BB ɗan'uwanta NE, ƙyamarsa da na nuna kaɗai ya isa ya yanke alaƙata da Rafi'at, amma abun sai bai zo a haka ba, ko a fuska ba ta nuna min hakan ba tun daga ranar da ta fuskanci abun da ke kai kawo tsakanina da kuma Yayanta, ko ma dai meye, ba shakka alaƙar da ke tsakanina da Rafi'at alaƙa ce mai ƙarfi da ake wa take da Mutu ka raba!.
Ban kai ga samarwa kaina mafita ba na jiyo sallamar Rafi'at a parlour suna gaisawa da Ummi. A kunnena na ji Ummi na ce wa Rafi'at ɗin "Tana ciki tana fama da baƙar zuciyar tata irin ta kafuran farko, Ke ma dai na rasa wace irin mace ce maras kishin kanta, yarinyar da ta nunawa duniya ba ta son ɗan'uwanki ita ce kike yi wa jinyar zuciya? Iska dai tana wahalar da mai kayan kara wallahi"

Murmushi kawai Rafi'at ta yi wa Ummu sannan ta ce "A yi haƙuri Ummi, bari na shiga na duba ta."

Babu kunya bare tsoron Allah ina jin Rafi'at na sanya ƙafarta cikin ɗakin na wani juya mata baya.
Cikin sassanyar muryarta ta ce "Ni kika juyawa baya Jannat?"
Banza da ita ma yi, ina jin ta sai da ta ƙara cewa "ba za ki juyo ki kalle Ni ba ko?"
"Shi ke nan na fahimta. ƙiyayyar da kike yi wa BB Nima a yanzu dai ta shafe kasancewa ta jininsa ko?"

Motsawa na fara yi da niyyar juyowa, a hankali na gama juyowa sakamakon yadda kaina ya min wani mugun nauyi kamar an ɗaura min ƙaton dutse akai, kallo ɗaya na yi wa Rafi'at daga nan na kawar da kaina gefe, tsare ni da ido Rafi'at ɗin ta yi.
Cikin sassanyar muryarta ta ce "Yanzu ke Jannat abun da kike yi kina ganin shi ne daidai?"
Ko kallo Rafi'at ba ta samu daga gare ni ba bare ta yi tunanin zan tanka mata.
"Hukunta kanki da yunwa da kuma kuka ba shi ne mafita ba, ya kamata a ce ƙwaƙwalwarki ta fayyace miki komai Jannat, wai shin wace irin zuciya ce a ƙirjinki? Wace irin ƙiyayya ne kike yi wa BB um? na san cewa BB ya wahalar da mu da izaya iri-iri a baya, amma in za mu dubi hakan da buɗaɗɗiyar zuciya wallahi tsantsar ƙaunarsa gare mu ce ta sa shi yin hakan, meye aibun BB um Jannat? Shin ko don Ni bai cancanci ki masa alfarma ki so shi ba? Ina da tabbacin cewa BB ya ɗara Dr. Junaid ɗin da kike tinƙaho da shi ta kowanne fanni..."

Saurin katse ta na yi yi cikin dasasshiyar muryar tawa da ke fita a hankali na ce "Ya isa haka Jannat, idan har abun da ya kawo ki ke nan, gara tun magariba ba ta miki ba ki koma gida, ya kamata Ku fahimci cewa soyayya da kuma yafiya akwai banbanci, Ni ban ce ban yafewa BB ba, amma dai son shi ne kawai ba zan iya ba, saboda ina da wanda nake so, akwai wanda zuciyata take muradin yada shi, amma ku kun gagara fahimtar hakan, yaya kuke so na yi ne? Na haƙura da zaɓin zuciyata na bi naku zaɓin ke nan?" Ta ƙarashe tana ɗan ɗaga muryarta da ba wani sosai take fita ba saboda kukan da ta ci.

Kasancewar Rafi'at mai raunin gaske ya sa ta fashewa da kuka tare da ƙarasowa kan gadon, ba tare da na aune ba na ji ta rungume da Ni tana kuka mai cin rai, sanyi sosai jikina ya yi da hakan, iya sanina, tsawon. mu'amalata da Rafi'at tun yarinta Ni ke cutar da ita, kusan duk wani hukunci da BB zai mana a baya ma Ni ce ke jaza mana laifin don kuwa ita Rafi'at babu ruwanta, irin mutanen nan ne masu bin doka da ƙa'ida.

A hankali na tsinci kaina da fara shafa bayan Rafi'at, can dai na ji ta tsagaita da kukan tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai. A hankali ya raba jikinta da nawa tare da kallonsa, sanya idanuwanta cikin nawa ta yi sannan ta ce "Ina da yaƙinin cewa wanda kike so ba ya miki kwatankwacin soyayyar da BB ke Miki, ki nutsu Jannat, kada ki biyewa don zuciyarki wurin yankewa BB hukunci, duk da na San irin tsanarsa da kika yi da wuya ki iya tuna alkhairansa gare ki, ba wai ina goranta miki ba ne, at least i'm just telling you the fact, wannan shi ne alaƙar gaskiya, Ina so ki nutsu ku yi tunani, shin alkhairansa kaɗai ba su kai ki masa alfarma ki so shi ba?"

Duk da cewa maganar tata ta so yin tasiri a cikin zuciyata don ba kaɗan ba ta buge ni, a hakan dai na ƙara haɗe fuskata kamar ban ma fahimci ina ta dosa ba, ganin ban kula ta ba ko ma na nuna alamun ina sauraronta ya sa ta sauƙe numfashi tare da faɗin "Shi ke nan. Zan ba ki wuri Jannat, zan je na yi jinyar zuciyar ɗan'uwana, Amma ina ba ki shawara, ki nutsu ki yi tunani, ba na fatan ki aitaka Kuskuren ƙin amincewa da auren ɗan'uwana, idan kuma muka yi hakan, ki sani ya zama min wajibi nima na rabu da naki ɗan'uwan!"

Dim! Gabana ya bayar da wani irin sauti, gaza ɓoye halin da zuciyata ke ciki na yi sai da na waro idanuwana da suka yi ja suka kuma kumbura saboda kuka, sai yanzu ma na tuna ashe Ya Sadiq da Rafi'at suma soyayya suke yi, sanin irin tsananin yadda Ya Sadiq ɗin ke ƙaunar Rafi'at ya sa ta dafe ƙirjina, na san waye BB, mutum ne mai juriya da kuma ƙarfin hali.
Tabbas Rasa Ni da BB zai yi na san zai shiga wani hali sai dai ina da tabbacin na wani lokaci ne ƙalilan. Amma Ya Sadiq fa? Tabbas idan har Rafi'at za ta iya aikata abin da ta faɗa. Wato ta ta rabu da shi zuciyarsa za ta iya bugawa nan take.
Idanuwana na ɗan waro ina jinjina girman al'amarin a zuciyata ban gama wannan nazarin ba na ɗago don na lallaɓa Rafi'at sanin cewa ita mace ce mai haƙuri da sauƙin kai, sai dai me? Ta riga ta fice a ɗakin. Ajiyar zuciya na sauƙe ina tunanin yadda duniya ta juya min baya lokaci guda.

A yanzu dai ba Ni da wani buri da ya wuce na auri Dr. Junaid saboda yadda nake ji a raina idan har ba ta same shi ba numfashina zai iya rabuwa da gangar jikina wanda hakan zai iya zama silar rasa rayuwata, takunkumin da su Abuya da Ummi suka sa min ya yi min tsanani, sun ƙwace wayata, system ɗin ma da take ɗebe min kewa sun karɓe ta sun ba wa Jadeed, ga shi yanzu har mai gadi an masa gargaɗin kada ya kuskura ya bar Ni na fita waje, haka nan kuma sun gargaɗe shi da ya sanar da su idan wani ya zo wurina, to yanzu saboda ni Ummi ma ta koyawa kanta zaman parlour Wanda da ba ta fiye yi ba.

Cikin wannan yanayi wani ɓarawon bacci ya sace ni, kasantuwar jikina na tsananin buƙatar baccin ya sa na yi shi hankali kwance, ba ni na tashi ba sai wuraren magrib sakamakon karatun da sauraye ke raira min cikin kunnuwana, wani irin juyi na yi ina sakin wani kasalallen nishi sakamakon rashin ƙarfin jiki da nake ji ga kuma yadda kaina ya ƙara min wani irin nauyi ga yadda jijiyoyin idanuwana suka wani matse wuri guda.

A daddafe na iya tashi na nufi toilet, alwala kawai na yi na fito ina bin bango, da ƙyar na iya kawowa gaban gadona na faɗi rigijib kamar tarin kayan wanki sakamakon jirin da ya ɗebe ni. Idanuwana nake ƙoƙarin buɗewa amma abun ya ci tura, da ƙyar na iya buɗe su a wahalce sai dai me? ba abun da nake iya gani sai duhu.

Tsoro ne da kuma fargaba suka ziyarci Ni lokaci guda, ƙoƙarin ƙara ware idanuwan nawa na kuma yi, but same, ganina ya ɗauke ba abun da nake gani ban da duhun da ya mamaye ko ina. Wani irin wahalallen ihu na saki ina kiran sunan Ummu, daga nan ban ƙara sanin inda nake ba.

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*


*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 2 · 0% Book details