← Book details Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 26

CHAPTER 6:

Kuskurena Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Kwanci tashi, in ji bahaushe wai asarar mai rai, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ba mu samu halartar graduation party ɗinmu na Dolphin ba, wanda hakan ya sa na ji ba daɗi sosai, a ɓangarenmu da Ibada sai dai mu ce Alhamdulillah don yanzu kusan babu sallar da ba ma yi, asuba da kanmu muke tashi, idan mun idar sai mu tisa haddarmu ta Makaranta, gari na wayewa muke shirya wa saboda gudun makara, don in mutum ya makarar ba ƙaramin bugu yake kwasa ba daga perfects ga kuma shara da za a ba shi ya yi, musamman ma mu da muke juniors, tun da BB kuma ya koma Cairo Bai ƙara zuwa gida ba.

Alhamdulillah, cikin iko da sahalewar Ubangiji muka kammala aji ɗaya na secondary, tarin nasarori kan mun fara artabu da su a rayuwarmu don wani lokacin har tunani nake dama muma muna da Sa'a a rayuwa haka ne? Lallai a yanzu muna enjoying karatunmu a sabuwar makarantar da yanzu muka saba da ita, Rafi'at ce ta karɓi kyautar ta ɗaya Ni kuma ta biyu a wannan shekara ga kuma best subjects gifts da muka kakkarɓa, hakan ya sa ahalinmu yin farin ciki sosai, shi kam Abuya ƙarin farin cikinsa bai wuce nasarar da muka samu a fannin addini ba, mun kammala littattafai da dama, fagen hadda kuwa ma sha Allah, don makarantarmu ba baya ba a wannan babin ma, ga shi mun tashi da tagomashin haddar hizifi biyar masu kyau da ingattaciyar hadda.

A haka muka shiga aji biyu, uku har muka yi jssce, izunmu talatin talatin lokacin. Muna aji ɗaya na Babbar sakandare ne girma ya fara riskar mu, cikin ƙanƙanin lokaci muka yi wani irin girma na ban mamaki musamman Ni, domin in ka gan mu za kayi tunanin mun kai shekaru sha bakwai bakwai a duniya while bamu wuce sha huɗu huɗu ba. A lokacin ne kuma girma ya riske mu, kasancewar dama tuntuni muna da ilimin akan al'amarin ya sa komai ya tafi yadda ya kamata sai ƴan shawarwarin da Mommy ta ƙara mana da su.

Rayuwar duniyar ke nan, a yanzu haka ajinmu uku na babbar sakandare, gaba É—aya mun sauya kamar ba mu ba, mun samu damar haddace Alqur'ani mai girma, a yanzu haka muna gab da fara jarrabawoyin fita, don mun riga mun yi registration na jamb, waec da kuma neco though a ra'ayin Abuya da Ummu kawai da zarar mun kammala secondary kawai mu yi aure ne don ya lura Ni ina da rawar kai.

A tsukin wannan lokacin ne Daddy ya saya mana wayoyin hannu Ni da Rafi'at, wannan ne ya fara buÉ—e min damar fara yin soyayya a rayuwata, to a yanzu dai soyayya nake fafa, duk wanda ya ce yana so na amsawa nake mu yi soyayyar mu tun da ina da waya, ita dai Rafi'at babu ruwanta da wannan dabi'a hasali ma dai Banda Ya Sadiq Babu wanda take kulawa, wasu lokutan nima takan yi min nasiha kan na daina biyewa samari sai na ce mata ta rabu da Ni, Murmushi kawai take in na faÉ—a mata haka ta ce "Allah ya shirya mana ke Jannat, tashen balagar tsuntsaye ke É—awainiya da ke"
Nima dariyar nake yi kawai daga nan sai mu bar zancen, duk da yadda nake kule-kulen mazan nan ko kaɗan ba na wasa da karatu na, a haka muka fara rubuta jamb ɗinmu, bayan sakamako ya fito na ci maki 134, Rafi'at Kuma maki 230, dama can Ni medicine and surgery na cika, ita kuma law, wannan sakamako shi ne ya rage min karsashina har ma Fara tunanin gyara ɗabi'ar da na lulluɓawa ruhina ita.

Ɓangaren su Abuya babu wanda ya ce min komai da sakamakon jamb ɗina, wannan dalilin ya sa na fuskanci cewa zuru suka yi min, daga nan kuwa na ajiye samari a gefe na dawo kan hanya yadda ya kamata.

Yau ta kama Litinin, tun dama tashi daga Bacci nake ji na wani irin, bugun zuciyata ya hauhawa haka nan fitar numfashi da shaƙarsa, shima da sauri yake fita, na tabbata da zan je na gwada daga bugun zuciyar zuwa numfashi na yanzu sun sauƙa a layin daidai, addu'o'i na ci gaba da yi cikin raina ina roƙon Ubangiji da ya kawo min komai da sauƙi yayin da na yi sukuku kamar ba Ni ba, tun Rafi'at na tambayata ina share ta har ta gaji ta yi fushi tare da zuba min idanuwa.

Har dare haka nake ji na wata irin kamar an sauya Ni, ina yin sallar isha' ban tsaya cin abinci ba na wuce ɗaki na kwanta, a maimakon Bacci ya ɗauke Ni sai tunani ya yi wa zuciyata ƙawanya, tsaki na ja tare da ƙara tuƙuiƙuye kaina cikin bargo ina fatan baccin ya ɗauke Ni.

Rafi'at ce ta shigo ɗakin, kallon mamaki ta bi Ni da shi kafin ta wuce toilet, ko da ta fito ba ta kula Ni ba, itama sai ta samu wuri ta kwanta, duk yadda aka yi haushina take ji ba kaɗan ba, ban ba ta haƙuri ba ita ma ba ta kuma tambayata me ke damuna ba, har wuraren goma idona biyu Ni da na shigo tun ƙarfe takwas da niyyar Bacci. Rafi'at kam tuni ta fara barcinta har da minshari, ajiyar zuciya na sauƙe tare da niyyar sauƙowa na yi alwala na yi salla, vibrating ɗin da wayata ke yi ya sa na sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya Tare Da miƙa hannuna na ɗaga pillow na ɗauko wayar ina mamakin mai kira na a irin wannan lokaci.

Baƙuwar lamba na gani, har na ji kamar kada na ɗaga sai kuma na duba farkon numbern, a maimakon na ga irin lambobinmu na gida Nigeria sai naga akasin haka, tdantsar mamaki ne ya bayyana akan fuskata, har wayar ta katse ban samu damar ɗagawa ba, saurin shiga Google na yi don duba wace ƙasa ne ke da county code mai +1...

Ban kai ga searching ba kiran ya sake shigowa a karo na biyu, ba tare da wani tunani Ba kawai na yi picking tare da karawa a kunnena ina faÉ—in "Hello"
Shiru ba a amsa ba, na ƙara faɗin "Hello" still ba a amsa ba, jinjina kaina na yi kafin na ce "Wai waye ne? Idan mutum ya san ba magana zai yi ba dalla can meye na kiran, aikin banza kawai" na ja tsaki na kashe kiran ina jin takaici sosai cikin raina.


Washegari ma da daddare an ƙara kirana da wannan numbern jiyan, ko da na ɗaga ba a yi magana ba, hakan ya matuƙar tunzura ni na balbale mai kiran da masifa duk da cewa ba Ni da tabbacin yana jin Yaren nawa duba da cewa mamallakin numbern mazauni ko kuma ɗan ƙasar Canada ne.

Haka kawai na kasa yin Bacci daren ranar ina tunanin waye wannan yake kirana? Na farko dai danginmu ba wani yawa ne da su ba, hasali ma daga Kaka sai Mommyn Misau da Mommyn Jama'are, to bayan su da iyalansu ba mu da wasu dangi na kusa haka, ƴaƴansu suma gaba ɗaya suna cikin ƙasar, babu wanda ya ƙeta hazo, to waye wannan ya samu number ta har yake kirana after all numbern ma sabuwa ce?"

Kamar wata mahaukaciya haka na sauƙo daga kan gado ina kewaya ɗakin, gaba ɗaya na kasa gano wannan mai kiran nawa, tsaki na ja a bayyane sannan na ce "To miye abun ɗaga hankalin bayan nan san wane ne ba? Ya kamata na manta da ko ma waye ne na maida hankali na ga abubuwan da ke gabana"
Ina faÉ—in haka na gyara zaman hular da ke kaina na koma na kwanta.

Zaune nake a garden Ina shan iska yayin da na langwaɓar da kaina jikin kujerar da nake zaune, Shekaru shida ke nan cikakku yau da tafiyar BB, tun da ya tafi ban ƙara tunawa da shi ba sai yanzu da na ga date a jikin wayata, tsaki na ja kafin na ce "Mugu mai baƙar zuciya, Allah ya sa kar ya ƙara dawowa" na faɗa cike da tsantsar kiyayyarsa da nake ɗorawa kaina nake kuma ƙoƙarin ganin jikina da ruhina sun aminta da hakan.

"Ko ya yake rai?" Na tambayi kaina yayin da nake yamutsa fuskata, tun da ya tafi ba mu ƙara magana da shi ba, ba kuma mu jin ana zancensa ban da sau ɗaya da Kaka ta zo mana hutu, ita dai kam tana yawan yin zancensa wani lokacin har na ji kamar na kai mata duka saboda takaici.
Duk yadda na yi na yage tunanin BB da yake shirin maƙalewa zuciyata, kamar mai taɓin hankali haka ma wani kwaɓe fuska tare da miƙewa tsaye, screen ɗin wayata na zubawa ido kafin na tunkari hanyar fita, karo muka ci da Rafi'at.

Kallo Mai cike da tarin tambayoyi ta jefa min Ni kuma na kawar da kaina gefe da niyyar in raɓa gefenta na fita kafin ta fahimci wani abun.
"Meye hakan kike yi Jannat?" Rafi'at ta faɗa yayin da ta riƙo hannuna tana ƙoƙarin ganin idanuwanmu sun haɗu "Sai wani avoiding ɗina kike? What's wrong with you um?"
Ajiyar zuciya na sauƙe kafin na ce "kin ga Rafi'at, sake Ni na fita, babu abun da yake damu na, kawai dai yawan magana ne ba na so a halin yanzu."
Ina rufe baki Rafi'at ta ce "Ƙarya kike Jannat! Akwai abun da yake damunki mana, kar fa ki raina min hankali" ta faɗa tana tsare Ni da ido
Janye hannuna na yi na wuce ina faɗin "Sai kuma ki yi ai, Ku bar mutum in Yana cikin yanayin nan don Allah, haba mana" da ido Jannat ta bi Ni har na shige, ta sauƙe ajiyar zuciya ta biyo bayana.

A parlour na tarar da Mommy, kallo ɗaya ta min itama ta fahimci cewa ba daidai nake ba, ba ta iya ɓoyewa ba ta ce "Zo nan Jannat" na amsa da "To" Sannan na ƙarasa na zauna kusa da ita.
"Ba ki da lafiya ne?"
"Lafiyarta ƙalau Mommy Amma dai wani abun na damunta" faɗin Rafi'at wacce ta shigo yanzu, harara na Banka mata kafin na ce "To uwar kanzagi, nima ai ban ce ba Ni da lafiya ba, Mommy" na mayar da kallo na gare ta "Lafiyata ƙalau, kawai yawan magana ne ba na so yanzu"
Mommy ta É—an murmusa sannan ta ce "Iyeeeee?"
Murmushin nima na yi ina faÉ—in "Allah Mommy, yanzu ba na son yawan magana ko kaÉ—an ita kuma Rafi'at yanzu kamar wata aku haka take, ta dinga damuna ke nan"
Mommy ta ce "Haka abun yake? To ke Rafi'at kin ji me É—iyata ta ce, in kin san na za ki iya kiyaye abun da ba ta so na salin alin ki bar part din nan"
Hararata Rafi'at ta yi tana faÉ—in "bari na haÉ—a kayana na koma part É—in Ummi, idan kin koma daidai na dawo"
"Ki fi ruwa gudu" na faÉ—a ina juya idanuwana.

Da daddare yau ma an kira Ni da wannan numbern ta ƙasar Canada amma dai yau Ban ɗaga kiran ba, ko da aka kira a karo na biyu ma ban ɗauka ba, sai ma kashe wayar tawa gaba ɗaya da na yi na ajiye a ƙasan pillow na kwanta.

Sati guda ke nan ana damu na da kira da wannan numbern, abun takaici yanzu da safe na sai an kira Ni, ga shi kuma ba a magana in na yi picking, wannan dalilin ya sa nake ta tunanin blocking number sai dai da na shiga kan numbern sai wani abu ya shiga kaina na manta abun da zan yi.

Tsakanin Ya Sadiq da Rafi'at soyayya ce ta ƙullu, shima yanzu yana ajinsa na ƙarshe a matakin karatun jami'a, yanzu haka yana Gamawa zai fara housemanship ɗinsa, daga nan kuma zai zama cikakken likita, sai kuma ya yi residency na shekaru bakwai don zama consultant.

Tun ranar da Ya Sadiq ya furtawa Rafi'at kalmar soyayya ta sanar da Ni, sosai Na ji daɗi ko ba komai ɗan gida ne, kuma ina da tabbacin zai riƙe min ƴae uwata amana, ba wai don ya kasance jinina ba kawai, sai don sanin kyawawan halaye da Dabi'un da yake da su, uwa uba sanyin hali da tausayi ba kamar BB ba.

"Ko ina yake rai?" Na furta a bayyane ina riƙe haɓata
Fuskata na yamutsa na ce "Matarsa ta shiga uku, Allah ma dai ya sa ya samu wacce za ta so shi"
"Kamar ya samu in Sha Allah" FaÉ—in Rafi'at wacce shigowata yanzu ta zauna gefe na, idanuwana na zaro cike da mamakin yadda maganar ta fito fili.
Dafa Ni Rafi'at ta yi kafin ta ce "Wani ya sani ma ko ke ce matar tasa?" Da wani irin ƙarfi na runkuɗa ta gefe har sai da ta kusa faɗuwa, dariya ta saka tana sanya idanuwanta cikin nawa ta ce "Irin wannan hasala haka miss Jannat? Don kin auri BB ɗin wani abu ne?"
"Tuf" na yi kamar mai zubar da miyau kafin na fara yamutsa fuska "Allah ya sauwaƙe min wannan wahala Jannat, to wahala mana zan ce don wallahi duk wacce ta aure shi wahala ta kwasa"
Bugu Rafi'at ta kai min sannan ta ce "lallai ba ki da mutunci Jannat, to meye aibun Yayan namu?"
Caraf na ce "Aibubbuka dai Rafi'at, ke ce kawai ba kya gani saboda É—an uwanki ne"
Ta ce "Gaskiya dai ba lallai na ga aibunsa ba Ni kam, kema kuma bai kamata ki gani ba, BB mutum ne mai kyan dabi'u ke kan ki kin sani"
Nace "tab, kyan fuska dai in kin ce yana da zan yadda, don na tabbata matar da za ta aure shi ma Kyan fuskar ta gani"
"Ashe dai???"
Na ce "Ko ma meye, Ni dai ki daina min fatan auren BB, hasali ma ba ya da siffofin irin mijin da nake so, All I need is a caring husband ba wai irin BB mai cunkusasshiyar zuciya wanda na tabbata ita kanta zuciyar tashi yana takura mata"

Dim, na ji dundu a bayana, a hasale na ce "Wallahi ba ki isa ba Rafi'at, don na faɗi gaskiya sai ki wani sa Ni gaba da duka, wa ma ya san yanzu ya BB ya koma, yana da ƙarancin shekaru ma yake mugunta bare kuma girma ya kama shi?"
Rafi'at ta kwashe da dariya tana faÉ—in "ÆŠazu Na ji Ummi na waya da shi, kamar wai zai dawo wata mai kamawa"
Wata irin zabura na yi na miƙe tsaye tare da zurawa Rafi'at da ta yi magana zararrun idanuwana.
Cikin yanayi mai kama da rashin hankali na ce "What? BB É—in ne zai dawo?"
Rafi'at ta jinjina min kai.

Kamar wata zararriya na ce "Shi ke nan mun shiga uku kuma, don Allah ki roƙa mana Ummi ta roƙe shi ya zauna a can mu mun yafe musu shi wallahi"
"Wasa ma kike yarinyar nan"
"Wallahi mun yafe musu shi, da dai ya zo ya sauƙe muguntar shi ta shekarun nan masu yawa, ga shi yanzu soja ne ma ba wai ɗan ƙwallo ba, mun shiga uku Rafi'at" na ƙarashe a ɗan kiɗime don iyakar gaskiya wannan maganar ta buge ni sosai.
Ita dai Rafi'at dariya kawai take yayin da take nuna Ni da yatsa
Cikin fusata na ce "Dalla Malama Ni ki daina wani dariya, wannan ba abun dariya ba ne abun mu jajantawa kanmu ne"
Ko a jikinta ta ce "To meye abun tashin hankalin, duk tafiya in ya dawo na san Mommy a gaba za ta saka shi ya yi aure, da zarar ya yi aure kuma shi ke nan"
"Allah sarki wacce ƙaddarar auren BB za ta faɗo kanta, ina jiye mata"
Rafi'at ta ce "sai aka ce miki yadda ya mana haka zai wa matarsa? You must be out of your senses jannat, AI Ina faÉ—a miki irin mazan nan idan suka yi aure wasu sololi suke zama"
"Sololi kuma?" Na tambaya ina jiran amsarta

*Albishir ga ma'abota bibiyar litattafan mu, mun zo muku da ƙayatattun labarai waɗanda za su kayatar daku sannan su nishadantar daku. Kamar dai yadda aka saba ku kasance tare da mu a wannan tafiyar.*


*TEAM WOW 5 WRITERS HUB*


1- Ummulkhairi Sani Panisau (Khairatup)
GABA TAZO BAYA

2-Harira Salihu Isah
Uwar Batoorl
YARIMA BAHJAT

3-Zainab yahaya Amzah
NOUR AYN

4-Fatima A. Hassan (Daimond Batool)
KUSKURENA NE

5-Khadija Abdulrahim (Deejerth Abdoul)
WAHEEDA


Duka gaba ‘daya zasu zo maku akan.

Guda É—aya 1k
Biyu 1500
Uku 2k
HuÉ—u 2500
Biyar 3k


Account Number 9126022777
Bank: Opay
Suna: Ummulkhair Sani Panisauu

Bayan kun tura kuɗi, ku tura shaidar biya ta nan 👇

09023907030

09161720046

+20 150 885 6397

09065856251

07061707238

*Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar Team wow 5 writers hub ✍️ babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.*

*TEAM WOW FIVE WRITER'S HUB*
~Paid novels~

https://chat.whatsapp.com/IbrJm5T2VIgFCb2rDXAwXS

*No 04*

*KUSKURENA NE*
_(From the choice I made)_
*©® Fatima Adamu Hassan*
_(Diamond Bhatool 🦋)_


07061707238
Bismillahir Rahmanir Rahim

.
Chapter 7 · 0% Book details