← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 32

Sashe 8

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tana barin gurin Saleek dake boye yana sauraran wayar da take ya fito daga gurin boyansa yace "so she even have a man,well muje zuwa a yau sai na san wacece ke And menene dalili ki da hujjarki na aran identity' É—in wani,Cos dole yasan Kiswah version is her identity not Faridha".

Tana sauka ta fara ɗaga ido tana neman inda zata hango Haidar,har lokacin wayarta na kunneta bata cire ba,taune lebenta na ƙasa tayi tace "Baby just show your self mana ,"murmushi yayi yace kizo inda kikayi parking motan ki,Babu musu ta taka inda ta aje motan ta tana cewa "i hope you're not playing any frank"tana isa figure din sa yayi mata sallama jingine jikin mota irin tata sak komai da komai,maida hankalinta tayi kan tata motan Wadda ke aje inda ta aje ta Kafun ta sake maida kallanta kan HAIDAR wanda ke faman kada key a hannunsa yana mai bata expensive smile ɗinsa mai kasheta,

Cire wayarta tayi a kunnenta tana mai kallansa cikin ido tace"okay now tell Me motan wanene wannan kuma"?

Murmusawa yayi har haƙoransa na fitowa kafun yace "tawa of course,na siya mota ne irin taki dan na nuna miki zan iya zuwa ko wanne level akan ki muddin nan kike san muje,i dont mind na ringa hawa okada indai kema Shi zaki hau ,so daga yau bazan sake hawa wani luxurious car ba sai wadda kika hau ,so daga yau ga motan Haidar nan masoyin Kiswa".

Cike da kulawa ta matsa kusa dashi tace"habibi this is not necessary and i told you wasa kawai nake maka ,you dont have to stood to this so abunda ya hanaka nemana koda jiya kenan ka fita da Farry".

Kashe mata ido guda É—aya yayi yace"Well ina san baki surprise ne so Farry ta rakani siyan mota irin naki And We went for lunch after that,she was teasing Me wai na fara tunani irin naki ,kinsan Shi soyayya babu abunda bata sakawa,a nawa bangaren kuma soyayyata takice komai kuma zan iya domin zama dai dai dake so tell Me Farry tace mun you went on a date ,who was it with,it doesn't matter idan ex boyfriend ne,stalker Ko crusher cos duk zanji dasu dan yanzu you're mine i just cant wait to mark you kowa ya gani ya fahimta"

Dariya ta saka ganin yarda ya kare maganar tasa Kafun ta jiingina ita ma da mota tace"business date ne naje so calm down kar ka fasa ma mutum baki cos Ba sai kayi marking dina ba duniya zata san ni takace And only yours,juyo da fuskarta tayi tana kallansa tace'i really do love you habibi ,bana ganin Ko wanne namiji a matsayin kallan da nake maka,i can give up my everything for you idan da bukatar hakan,my identity,my work ,my life and everything indai iyuwar hakan ta kama,but kamar yarda kasan sirrin zuciyata da irin raunin da take akan ka ina roƙonka kar ka karya ta,Ban san soyayyar wani da namiji ba bayan kai bama mahaifina ba cos ban ma rayu dashi ba ballantana Nasan dadin soyyyarsa".

Dan shiru Haidar yayi yana kallanta,da ace tasan yarda zuciyarsa ke fitinar santa da bazata taba kawowa zai karya tata zuciyar ba wata rana,kallan sa itama take inda ta hango moist na ƙwalla a gefen idanun sa, nuna sa tayi da ɗan yatsa tace"habibi mene a idanunka kamar hawaye?"

Saurin gogewa yayi yana mai cewa"Na sanki ne kafun ya saka dariya yace"how wish nayi recording confession É—in nan na bazaki iya rayuwa Babu ni ba for future use.

Dariya suka saka a tare Cos sai a karshe dukkan su suka bama juna dariya,juyawa yayi ya buÉ—e motan yana mai fadin"kar na manta da kyautar ki,"

Dan shagwabe fuska tayi tace "kai kam baka gajiya da batani da kyauta kullum idan zaka zo gurina"

Ciro dan box yayi daga motan yana mai cewa"well ba hakarum bane idan nayi spending ma matata kuɗi after all ina dasu kuma dan na kashe miki nake nema,"miƙa mata box ɗin yayi da ƙaramar package bag ɗin da yake ciki yace ba yawa.

Ƙarba tayi tana cewa"awnn you're such a durlyn,tana buɗe wa idanunta suka ci mata karo da diamond necklace dake ta faman sheƙi"saurin kulle box ɗin tayi tana mai kallansa tace "no no Baby i cant take this"

Motansa ya buÉ—e ya shiga ya mata key kafun ya kalleta ya kashe mata ido daya yace"you're welcome and i love you to the Moon and back,kiss yayi blowing mata da hannu kafun yace "na samu charge dina ta hanyar ganinki ,kinga yanzu Zan iya aiki cikin walwala Babu kasala,

Ɗaga mata hannu yayi ya kunna motan yana mai bata murmushin nan nasa mai kyau,itama murmusawar tayi tana mai ɗaga masa hannu kafun ta ciro wayarta ta tura masa saƙon"lets have dinner ,Its on me".kallanta yayi yayi saluting dinta bayan ya kashe mata ido daya kafun yaja motarsa ya bar harabar gurin.

Tsaye tayi tana sake duba sarkar da ya bata tana murmusawa cike da shaukina inda a zuciyarta take addu'ar Allah ya sa hutunta yazo mata da wuri shekararnan taje Bauchi ta fara bawa Mamanta labarin Haidar ,ya kamata tasan da labarin wanda ke kaunar Æ´arta fiye da yarda yake san kansa its high time,tafin da taji anayi a bayanta shine abunda ya katse mata hazari ta juya...

TBC

CHUCHUJAY ✍️

08130229878.
[5/6, 8:16 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page7⃣

Da mamaki Kiswah ke kallan Saleek wanda ya bayyana gaban ta yana tafa hannunsa yayin da fuskarsa ke dauke da wani irin murmushin da take ji kamar ta cire masa Shi da tafin hannunta domin ba sai ya faÉ—a mata ba labe yayi mata,

Cike haÉ—e rai tace"na haÉ—u da maza kala kala amma Ban taba haÉ—uwa da ill mannared irin ka ba,bana tunanin ka samu tarbiyya sanin menene labe akan maganar wasu take nufi,idan kuma ka samu to a wannan gibar bakayi amfani da ita ba.

Wani irin haɗe rai Saleek yayi domin maganar ta tayi masa zafin da bai tunanin zatayi masa ba,cikin mutuƙar bacin rai yace"Ko Me zaki ce kar ki fara jimamin yama tarbiyya ta take Cos bana tunani Kin fitini ta wani guri Cos Your personality is a mess,kinsan bake nake tausayi ba shi wanchan guy din da ya wuce shine yake mugun bani tausayi saboda he's in a deep shit da yayi getting involved da Gold digging bitch kamar ki,Just imagine baki Ko jin nauyi da tsoran Allah,mata irinki mayaudara maha'inta babu waɗanda Ban gani ba,running from one man's pants to another.....

Marin da ta dauke sa dashi cikin hawaye shine abunda ya katse masa hanzari ,hannun sa ya É—aga cikin fushi ya daki gefen motarta yana mai faman huci kan ya kama hannunta da karfi yace"This should be the last time da zaki kuma daukan wannan hannun naki mai kama da bulaliyar kara ki taba fuskanta,sannan ki gode ma Allah bana dukan mata da yau sai na fasa miki baki,and for Your information i heard it jiya kece kika je date dina wanda dama na sani i would never be wrong ,ki shirya saboda i will sue you for slender idan ba haka ba ba sunana Saleek ba "

Sakin hannun ta da ya damƙe da karfi yayi ya juya a fusace yana mai fadin"useless girl".

Kuka ta rushe dashi tace"you're the must useless stupid jerk I've ever meet sannan idan ka sake shiga hurumina Zan ci maka mutunci fiye da tunanin ka,wawa kawai"

Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da tafiya zuciyarsa kuma na masa wata irin zafi da ƙuna na tabbatarwa da yayi cewa Kiswa itace taje gurin sa jiya abunda kuma ke sake soya masa zuciya shine rashin sanin dalilin yin hakan,tunanin sa ya fara bashi kilan dan kuɗi tayi,maimakon ya koma ciki sai ya shiga motan sa ya bar harbar gurin zuciyarsa nayi masa wani irin tuya da ba zai iya fasaltawa ba.

******
Chapter 8 · 0% Book details