← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 32

Sashe 11

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallanta mijinta Tukur Bula yayi yace"sweet heart ya dai?mene aibu dan ya yabi abincin Tasleem When Its not a lie She's a Good cook"Kaɗa kai Haidar yayi yace "oho Baba tell her ,idan Ban yabi girkin ƙanwata ba Wane zai yaba?"kallan Tasleem wadda ke ɗan yaƙe yayi yace"girl you can cook for Africa Abincinki da daɗi amma kina da masu jealousing Ummi kuma tana ciki amma ni da Baba we have Your back".one spoon Baba Ya sake yace "For real Boy"

Ƙaramun tsaki Ummi tayi ta cigaba da cin abincinta ,bayan sun gama Ummi ta fara tashi tana mai cewa"Haidar ka sameni a falona zamuyi magana, bata jira mai zai ce ba tabar gurin yayin da suka cigaba da cin abincin su ba tare da kowa ya damu da sudden Halayyar Ummi ba idan aka cire Tasleem ".

Bayan gama cin abincin sa Ya nufi sashen Ummi dan jin kiran da take masa,zaune Ya tarar da ita tana Kaɗa kafa ɗaya,zama yayi gefenta yana mai kama hannunta yace"Ummi na wanene Ya taba mun ke aji kan mu a garin nan na Abuja"ƙaramun murmushi tayi ta kallesa tace"ai ka iya wannan dama and Wane kake gani zai tab'ani garin Abuja Ya kwana lafiya dama,"yar dariya Haidar yayi yace "Allah Ya jada ran Ummon Haidar "serious face ta saka tace "mene tsakaninka da Tasleem"?

Da mamaki yace"Tsakanin mu kuma Ummi ,ƙanwatace da nake Alfahari da ,kema Kin sani ina jin Tasleem kamar ke kika haifeta ba Aunty Maryama ba"

Da kyau Ummi ta kallesa tace "ka tabbata baka kallanta romantically cos bazan so hakan ba Ko kaÉ—an".

Dariya Ya saka lokacin da ta kai karshen maganarta yace "Ummi Tasleem fa?tayaya zan kalleta romantically?dariya Ya sake fashewa da yace"Allah yasa daga ni sai ke Ummi babu wanda yaji wannan maganar taki".

Yar Dariyar itama tayi tana mai jin daɗin yarda Haidar ya dauki Tasleem ,wayarta ta dauka ta shiga images ɗinta kana ta miƙa masa tace "oya kalli ka faɗamun ya ta jikin hoton nan take".hannunsa ya saka ya karbi wayan yana mai fadin "hope ba matchmaking zaki mun ba Dan im taking,"idanun sa ya ɗora kan hoton da mamaki yace"Farry"?Dago idanunsa yayi ya kalleta yace "Ina kika san Farry Ummi and mai kike da hotonta"?

Kallansa Ummi tayi da Mamakin jin ya ambaci sunan Farry wadda ga dukkan Alamu ya santa,cikin ƙaguwa tace"kasan ta ne?abun ma yazo da sauki kenan cos wannan yarinyar ina san nayi bincike mai kyau akanta kaje ku sasanta Dan a yarda na gana da mahaifiyarta na gamsu ."

Gyara Zama Haidar yayi yace"wait Ummi let me understand,Wane ya gana da Wane sannan Wane zai sasanta Dan Wane im lost".murmushi Ummi tayi tace"mahaifiyarta ta sameni yau a office ta kawo mun tayin Aurenta gareka so na zauna nayi tunani naga offer ɗinta is not bad cos yanzu duk macen da zatazo tana sanka dole She's after money and Your look amma wannan yarinyar atleast koda iyayenta basu kaimu kuɗi ba bazatayi ƙwaɗayi ba since itama shes loaded so na faɗawa mahaifiyar ta zan nemeta idan na gana da kai and of course Babu dole amma inasan ka bawa abun nutsuwa da tunani mai kyau sannan ka samu kaga ita Farry ɗin".

Wata irin gajeriyar dariya yayi yace "Ummi you cant choose yarinya for me Just Dan mahaifiyarta tazo ta sameki akan tana san É—anki ya Auri Æ´arta,bamafa ki sansu bafa Ummi,and Wane yace wai duk macen dake sona dan kuÉ—ine,?

Gyara zaman sa yayi yana mai cewa"Ummi Wannan yarinyar da kike gani sister É—in yarinyar da nake soyayya da ita ne for year and counting now "Da mamaki Ummi tace "ta yaya and how comes ita maman nasu bata sani ba take san ka Auri É—ayar?"

Tabe baki yayi yace "ga dukkan alama dai but Ummi Haidar dai Kiswa yake so sannan inata san na faÉ—a miki amma na shirya baki surprise ne amma abun yazo a haka,"wayarsa ya ciro ya shiga hoton Kiswa yace "kalleta nan Ummi wadda tayi gaba da zuciyar É—anki".

Karban wayar Ummi tayi tana mai ɗora idanunta kan beautiful Black Queen ɗin Haidar ,Dan washe baki tayi tana mai fadin"kuma gata mai kyau da ita,to ai ba abun tada hankali bane,im sure maman bata sani ba but na tabbata zatayi farin ciki idan taji already ma kana tare da ƴarta,i will talk to her sannan yaushe zaka kawo mun ita na ganta cos na ƙosa naga wannan Yarinya da Haidar ɗin Ummi yake ikirarin ta tafi dashi"

Sosa kansa yayi yana mai murmusawa kafin yace "Soon ummi i will talk to her duk lokacin da take da free time zan kawota ku gaisa and im sure Ummi zaki sota cos Kiswa is a very lovely girl,cute and stunning".Kalllansa Ummi take ganin yarda yake faman koɗa Kiswa ba sai an faɗa mata ba yana santa and hes happy about that and farin cikinsa shine gaba cikin abinda ke sakata farin ciki,haka nan take jin kamar taje ta dauko Kiswa ta kawo ta gidan ta,shafa gashin kansa tayi tace"badan dare yayi ba ai yanzu zan kira Barrister Juwarriyah amma da yau da goben duk Na Allah ne tunda dare yayi bazan dameta ba,nasan itama zatayi farin ciki sosai idan taji maganar nan".washe baki Haidar yayi ya cigaba dawa mami waƙar yaban Kiswa.

TBC

CHUCHUJAY✍️

(Amina jamil Adam)

08130229878
[5/8, 12:13 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page 9⃣

AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL.

Cikin Yanayi na nutsuwa Haidar ke takawa domin isa office ɗin sa inda yake mai karban gaisuwar ma'aikatan sa yana miƙa musu cikin girmamawa , yana isa bakin office din sa Ya saka key domin buɗewa amma ga mamakin sa yaji kofar a bude ,turawa yayi yana mai tunanin Ko jiya bai kulle ba Ya wuce,turus yayi lokacin da Ya shiga office ɗin ,roses ya ganin an cicire su an rubuta Good Morning love da kuma tambari na heart,kan desk kuma dauke da food pack wanda ba a bude ba ,dan kalle kalle Ya fara dan ganin Ko zaiga giftawar wani ,a hankali Ya taka dan sake dubawa,kofar shigowa da yaji an buɗe ne Ya sakashi waigawa,Kiswa ce tsaye bakin kofar hannun ta dauke da leda yayin da fuskar ta ke dauke da babban murmushi,dafe fuska Haidar yayi yana mai sauke ajiyaar zuciyar ganinta Kafun Ya ƙarasa gareta hakoran sa washe kamar anma yaro kyautar candy.

Ledan hannunta Ya karba yana mai fadin"Good morning my romantic heartrob to what did i owe this?"

FaÉ—aÉ—a murmushinta tayi ta shigo ciki tana mai cewa"to love masoyi,i woke up naji yau ina san ka fara sakani a idanun ka idan kazo office É—in nan and of course i made you breakfast dan na sanka da rashin san karyawa idan zaka fita office which you will have to work on dan idan mukayi Aure bazan dauka ba,yanzu abunda za'ayi ka zauna nayi serving maka breakfast Then na wuce aiki cos kar ka manta i work for someone and i cant afford being sacked".

Cike da wani irin santa dake faman fuzgarsa ya zauna inda ta masa nuni yana mai binta da ido fuskarsa dauke da wani irin murmushi na farin ciki da ya kasa cirewa ,.

Buɗe food pack din tayi ta ciro Kulan dake dauke da plantain mossa,sannan ta dauko plate ta saka masa guda uku manya a kai Then cutleries Kafun ta aje a kan cinyansa then ta ciro Cup ta buɗe karamun flask ɗin dake dauke da kunun gyaɗa a ciki ta zuba sannan ta dawo Gefensa ta zauna tace "bismillah hero and mind you sai ka cinye mossa ɗinn nan da kunun gyaɗan nan,"rufe idanunsa yayi ya buɗe yana mai shaƙar kamshin abincin dake gaban sa Kafun yace "my favourite,ya akayi kika sani ban taba faɗa miki ba idan Zan tuna"

HaÉ—a hannayenta tayi guri É—aya tace "well idan ban san favourite abunda mijin da zan Aura nayi rayuwa ta har abada dashi ba mai ya kamata na sani?,well just eat already"

"What about you?"ya tambaya yana mai zuba mata ido.

Wani fari da ido tayi Kafun tace "well ni a ƙoshe nake burina kawai kai ka ƙoshi,"murmshi yayi yayi bismillah ya fara cin abincin Cikin nashaɗi, bayan ya gama Ya kalleta da soyayya yace"Allah yayi miki albarka Kiswa,Allah ya mallaka mun ke a matsayin matata uwar ƴaƴana wallahi ina sanki da yawa sannan a kullum sake sanki nake sosai ba wai so na wasa ba,dan Allah ki dage da yin Addu'a kema Allah yasa mu mallaki juna kafun mu koma ga mahaliccin mu".

Tashi tayi ta fara haɗa kwanikan kafun tace"na faɗawa Mama maganar ka jiya da mukayi waya and ta ƙosa na kawo ka Bauchi ta ganka,i can tell tun Kafun ta ganka kayi mata already"

Cike da zumuÉ—i yace"OmG Baby i love you ,dan Allah ki samu free time muje cos ni kaina yakamata na ga macen da ta haifa mun macen da bana da nutsuwa idan akanta ne"dan shiru yayi kafun yace"Yea kafun na manta ina ganin ya kamata ace by this time Mother ta san dani a rayuwarki sabida rashin sanin yasa ta samu Ummi jiya a office tana san haÉ—ani da Farry na Aura and im sure dan bata san muna tare bane ,but i told Ummi jiya about us and tayi farin ciki sosai dan idan da dan ranta ne yanzu ma na kaimata ke ta ganki,ba kiga yarda take murna ba".

Jin maganar mother ta je gurin mahaifiyar Haidar tayi kamar almara,bata taba sunanin san zuciyar Mother ya kai har inda bata zato ba,kallan Haidar tayi da kyau cikin sigar boye abunda ke ranta ta saka wata dariya tace "so mother did that,gaskiya ya kamata yau na shigar da kai gida a samana rana dan yanzu mother taje cikin rashin sani gobe wanine zai je ."

Dariya ya saka sosai yace "ke yarrinyar nan mai kika maida ni,sai kace wani kaya a cikin Boutique din Ummi,well kima saka aranki babu wannan maganar tunda dai duk tallan yan matan da za'a kawowa mother sai na amince zata amince ,and you know my heart beats for only you,zuciyata idan tana bugawa babu abunda take ambato face Kiswy babbyyy".
Chapter 11 · 0% Book details