← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 32

Sashe 27

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zage Zage take ɗugunzumawa Sameer na Kamota har suka fito daga ofishin likitaan,kukan suka tarar da Farry nayi gefen gadon Sagir wanda ya ɗan samu bacci,kamar wata kamun hauka Mother taje ta zauna gaban sa ta kama hannun sa tace"indai nice na haifeka Sagir ,yarda Kiswa ta ƙwace maka farin cikin ka na zama uba sai na ƙwace mata nata farin cikin na zama matar wani balantana ta zama uwa,sai na mayar mata da rayuwarta cikin rayuwa mafi muni da ƙasƙanci,wallahi sai taji dama baka kanta Tayi cikin ruwan sanyi babu gardama,abunda ta hanaka sai na saka maza goma sunyi amfani da ita a lokaci guda,bazan huta ba sai wannan alwashin nawa ya cika '".

"Wow Mother wow,Wallahi kinsaka ina jin kunyar wani ya wuce nace masa ga mahafiya ta nan,ina jin kunya da ƙyamar abunda kuka aikawa Kiswa ,yarinyar nan cikin dare kika koreta babu koda suturar arziki,baki san Wane hali zata shiga ba ko wanne hannu zata faɗa,idan da ace Farida ce fa,koda baki tausaya mata dan komai ba zaki tausaya mata for the sake of humanity,amma abun kunya da takaici kece zaune kike alwashi munana akan yarinyar da ɗanki ya nemi ya ƙetawa haddi,ai koda kashe sa tayi Batayi laifi ba,ya godewa Allah a nan abun ya tsaya,Good for nothing bastard".yaya Sameer ya faɗa babu koda guntun tausayin Sagir a ransa.

Tasowa mother tayi ta tako gaban sa ,sai da tazo daf dashi ta ɗauke sa da mari mai zafin gaske ta nuna sa da yatsa tace"kaine Good for nothing bastard ba yaran da ya nemi tsayar da hawayen dake bin kuncin mahaifiyar sa da ƙanwar sa ba,sannan kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa abunda nace sannan ka ƙara da cewa nice nan na bawa Sagir goyan bayan haike mata,duk inda kuma take idan ka nemota ka faɗa mata ta shirya tarbar fushin uwar da akayiwa ba dai dai ba,sannan kar tayi gangancin dawowa gidan mu ta cigaba da buya domin duk abun nan da kaji na furta sai ya faru da ita,wutar tsanarta tana yi mun rurin da babu mai iya kashewa sai biyan buƙatar fansa ta,bari kaji koda hakan yana nufin zan rasa aure nane,abu kuma na ƙarshe da nake san ka sani Shine ,idan ka sake goyan bayan Kiswa a gabana ban yafe maka nono na da Kasha ba."

Wasu irin hawayene suka fara zarya akan kuncin samir yana mai jinjina tsantsar jahilcin dake cikin maganar Mahaifiyar sa ,bai ce komai ba ya juya ya fita a ɗakin,kai tsaye motar sa ya shige ,cikin rashin tsammani ya tsinci kansa da fashewa da wani irin kuka mai cin rai,tunanin sa halin da Kiswa take ciki da wanda Mother ke neman saka ta nan gaba,tun da ya tsinci labarin abunda ke faruwa yake gwada layinta amma baya samu,tunanin sa kuma da inda zai sameta baki ɗaya ya gushe,yasan a duk inda take tana buƙatar ɗan uwanta,numbern Appa ya sake nema a karo na babu adadi dan so yake ya zamana a bakin sa ya fara jin labarin nan,amma still a kashe bai sameshi ba,abokinsa masu binciken boye ya kira dan su fara cigiyar inda take,baya sun gama waya kai tsaye ya wuce gurin sa Ayi binciken dashi.

Bangare Haidar kuwa babu inda bai duba ba akan neman Kiswa ,Baga asibitoci,Sashen aje gawa da duk wani guri da tunaninsa zai bashi amma bai ganta ba,abinci kuwa bama shi da lokacin tunawa da yanajin yunwa tun safe har dare baici ba,tracking layinta shima yaje a ayi a kashe wayanta amma suka tabbatar masa da zasu cigaba da gwadawa har Allah yasa ta kunna wayarta ,karshe dai da kyar ya iya komawa gida dan kanshi sakamakon zazzabi mai zafi da ya rufe shi.

Shin ina labarin Kiswa kuwa?

CHUCHUJAY ✍️

08130229878
[5/31, 11:42 PM] Chuchujay✍️: 💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

Na

CHUCHU JAY ✍️

Book1⃣

Page1⃣9⃣

________Da wani irin matsanancin ciwan kai Kiswa ta tashi washe gari sakamakon irin kuka data raba dare tana yi,babu abunda ke damun ta idan ta tuna yarda tsakaninta da Yaya Sagir yake,they were this close da take jin babu wani abu da zai kawo mata matsala muddin tana dasu,babu abunda yake da ciwo sama da buÉ—e ido ka wayi gari ace yau family É—inka sunyi back stabbing É—inka saboda kawai wani selfish abu nasu na san zuciya wanda bai chanchanci yaudara da lalata zumunci ba,Baccin da tayi baifi na Awa biyu ba wanda Shima tana farawa zata tashi a firgice wanda cikin deren anxiety ya ziyarce ta,yanayi na tsoro da kuma tunanin abunda yafaru zai sake maimaita kansa.

Bayan tayi sallar asuba bata iya komawa ba,tana jin Saleek na mata knocking kan ta tashi lokacin sallah ta sanar dashi idanta biyu ta tashi,bayan nan bata iya komawa ba ta zauna tana neman Allah ya kawo mata ɗauki ya saka mata hannu a rayuwarta,gari na fara haske ta shiga wanka tana tunanin sake mayar da bathrobe ɗin dake jikinta dan da ita ta Ƙwana ,locker ɗin da aka tanada domin aje towels a bathroom ta buɗe ta gansu jere tsaf dasu ,guda ɗaya ta jawo ta ɗaura kafun ta fito ta zauna kan gado ta ɗauki wayar ta tana tunanin kunnawa ,tasan mutum uku sun nemeta basu sameta ba,Haidar ɗinta da yaya sameer sai Appa idan ya san labarin ko 'ya dawo,amma ta shirya saka idanunta cikin nasu?,bata san mai zata fara faɗa musu ba domin kuwa mayar da zancen kawai sakata yake ta jita cikin wata irin matsananciyar kunyar da ba'a saka mata rana,san kiran Mamanta ne ya faɗo mata amma bata shirya tada mata hankali ba domin tasan Mama najin maganar nan zata taho Abuja ne wanda tasan abun babu kyau,hakura tayi da kunna wayar ta koma ta kwanta tana mai jiran tashin Saleek ta ari wayarsa ta kira Baba Baraka ta kwaso mata wasu kayan ta a boye da jakar ta boye dan koda zata koma gida ba yanzu ba sai abun nan 'ya sake ta.

Tunanin abun ya cigaba da dawo mata da yarda Baba baraka bata kwana gidan ba,ta yarda sun gama shirya abun su ne Allah ya nuna musu bai yarda abu ya samu bawan sa ba muddin ba Shine yaso ba.

Ƙwanƙwasa mata ƙofa da ake ne ya fito da ita daga dogon tunanin da take,daga inda take tace "wanene"?

Saleek dake tsaye bakin ƙofar ne yace "Nine,Saleek na kawo miki kaya ne and breakfast is ready".tashi tayi ta jawo Hijab ta saka kafun taje ta buɗe kofar ,da murmushi ɗauke a fuskarsa ya nuna mata ledar yana mai faɗin "Good morning"

Murmushin itama ta mayar masa kafun ta karbi ledan hannun nasa tace "Good morning and thank you".ɗan sosa gefen safen fuskarsa yayi yace "well ban san 'ya zanyi dake da godiyar nan ba,imagine da sanyin safiyar nan,well get dressed ki fito mu karya,and i hope komai na ciki is to Your liking na saka An siyo ne anjima idan na fita zan shopping miki kaya da abunda zaki buƙata".

Dan buÉ—e kayan tayi cikin ledan ta É—an kalla kafun tace"Well wannan ma na gode anjima zan saka a kawo mun kaya na office ka taho min dashi ,but bari na shirya na fito".kaÉ—a mata kai yayi kafun ya Bar gurin yana faÉ—in yana jiran ta.

Kulle ɗakin tayi ta juye kayan kan gado,doguwar rigace ta material ready made sai inners,wani irin kunyace ta kamata ,thank God bashine yaje ya siya ba,pant ɗin baiyyi mata kaɗan ba baiyyi yawa ba amma Bra ɗin ya ɗanyi mata kaɗan,haka na ta saka ta ɗauki JC veil ɗin dake ciki ta ɗaura,Room Slipper ɗinta wanda dama dashi ta fito ta saka ta fita .tana fitowa ta hango shi zaune kan dinning table gefe guda kuma mace wadda bazata wuce 35 years ba tana jera abinci kan table ɗin,karasa tayi nervously tayi sallama ,ɗagowa yayi ya sauke idanun sa akanta ,wani irin santa yaji yana yi masa yawo a cikin zuciyarsa musamman yarda ya ga tayi masa kyau ɗin nan,kome ta saka kyau yake mata, she's Just pure and natural,saurin saita kansa yayi tunawa da yayi akwai neman wani akanta sannan yayiwa kansa alƙawari zai tsarkake Alaƙar dake tsakanin su,zama tayi tana mai faɗin"barka ".murmushi yayi yace"barka and Guess What? you look Good"yauwa zarah je ki kira mun kowa ,"To yallabai"

Bayan wucewar Zarah ta kallesa tace"hope bazan zamar maka damuwa ba dan ina so nayi koda sati biyu ne out of any matsala and ina san kamun alfarmar kar ka faÉ—awa wani inda nake,i need a break for this madness,and ina san kiran Mai aikin gidan mu zata kawo min wasu kayan ka taho mun dashi,and ina san ka ara mun wayan ka,sai na kira ta".

KaÉ—a kai yayi yace"baki tunanin ita bazata fitar da maganan ba,i mean do you trust her"

100%" ta bashi amsa tana mai yi masa murmushi da ƙara ganin girmansa musamman da bai tambayeta abunda ya faru ba,matar da ya aikace ta dawo tare da mata uku,ɗaya zatayi tsarar zarah ɗaya kuma dattijuwa ce sosai dan Aƙalla zata daki hamshin,cike da mutuntawa bayan isowarsu yace musu"Good morning and na saka kuzo ne dan na gabatar muku da baƙuwata Kiswa,she's a family and tazo ne zata ɗan zauna annan dan haka yarda zaku bani service haka zaku bata bana san naji complain,kallan babbar yayi yace "Mama asabe dan Allah a kula da ita idan bana nan".murmushi matar da ya kira dan Mama asabe tayi tace"Insha Allahu yallabai,sannu da zuwa Hajiya,sunana Asabe,nice kuma nake kula da gidan nan bisa umarnin Yallabai Babba da ƙarami,ga Zarah ita ke kula da kitchen ga kuma Jamila Ita ke kula da shareshare ".gaishe da Kiswa sukayi cike da girmamawa wadda ta tsinci hakan weird dan bata san taga babba yana nuna mata girma tana ƙasa dashi,bayan sun bar gurin Zarah tayi serving nasa kafun itama ta wuce. A hankali ta fara cin abincin tana mai kallan Saleek wanda shima abincin yake ci kafun tace"baka tsoran ko na kashe wani ne aka koreni daga gida ka bani masauki,what if ni wanted killer ce,atleast ka tambaye ni."
Chapter 27 · 0% Book details