← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 32

Sashe 29

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shiru Mother tayi tana nazarin abun kafun tace"oya maza tashi kije gida ,ya kamata kiyi welcoming Appa ɗinki properly ."murmushi Farry tayi fahimtar abunda Mother ke nufi dan haka ta tashi ta ɗauki jakarta ta fita tana tunanin yarda zata gamsar da Appa da yaya sameer kan cewa ba'a bayan su Mother take ba..koda ta isa gida ganin motar Yaya sameer ta tabbatar mata sun dawo gida,tana shiga taci karo da Baba Baraka na arranging dining,kamar wadda tayiwa sarki ƙarya ta shiga tace "ina wuni"da mamaki Baba Baraka ta kalleta dan sabon abune wannan tsakaninta da Farry,amsawa tayi tana mai cewa sannu da zuwa,ɗan yaƙe Farry tayi kafun tace"yaya sameer fa?"

"Yana sashen sa"ta bata amsa ta cigaba da abunda take yi ,kai tsaye Farry ta nufi gurin samir dan shi ya kamata ta kama tukunna, tana shiga Kamar munafuka tayi masa sallama,yana zaune ya rufe idanunsa abun duniya duk ya ishe ta,jin muryarta ya saka shi buÉ—e ido ya kalleta kafun yace"Na yi imani da Allah duk wani Abu da Mother zatayi da saka hannun ki,uban mene kuma ya kawo ki inda nake?wallahi Kin bani kunya da Mamaki Farry,akan duniya da abun duniya kike Name ki zama abun tsoro.

Zubewa tayi kan gwiwowinta ta saka kuka tace"Wallahi yaya sameer ni ban da masaniya akan abun nan,na yarda muna da matsala tsakanina da Kiswa amma tunda aka saka bikinta na janye,ka tambayi Mother É—in kaji,koda wasa basu sakani cIkin wannan abun ba dan da ace sun sakani baza'a zo nan ba,im also disappointed yaya sameer sannan na kiÉ—ime da ban san cewa Mother ta kori Kiswa ba sai bayan na dawo nake nemanta ban ganta ba"

Kallanta da kyau sameer yayi kafun yace"ki tabbatar wannan abun ba wani game É—inne kuka haÉ—o ba,domin wallahi idan na kamaki da rashin Gaskiya Faridha kiyi kuka da kanki,'dan da kaina zan miki hukunci mumuna ba sai Appa ya saka baki ba.suna cikin haka Appa ya shigo yana mai cewa"Sameer zamu iya tafiya ."ganin Farry ya saka shi cewa "Allah ya saka tunani na n cewa dake ba gaskiya bane"

Kuka ta sake rushewa dashi tana mai yi masa rantse rantse,haka nan dai shima yayi mata gargaÉ—i kafun suka wuce shi da samir domin sake saka cigiyar Kiswa.

*********

____________wasa wasa jikin Haidar yaso yaƙi hannu amma kasancewar sa likita ya saka bai bari sun gane ba domin kuwa shi yanzu zama bai ganshi ba,fitowar sa daga wanka kenan guy ɗin da yasaka yayi masa tracking wayar Kiswa ya kirasa ya shaida masa labari mai daɗi inda yake sanar masa da cewa sunyi tracking layin ta amma cikin minti talatin ta kashe wayarta amma kuma duk wani bayani na location ɗin ta da suke san sani sun samu.

Jikinsa har rawa yake yana shiryawa domin sun tura masa address É—in da zai ga Kiswa,bai fadawa kowa ba ya fita domin zuwa gare ta ,mamakin da yake kai Shine wanda ta sani a gurin domin gurine mai nisa kuma downtown ,dama 'ya sani jikinsa kuma ya bashi a duk inda take zai ganta duk kuwa nisan gurin da taje,a haka ya isa Unguwan cike da zumuÉ—i yana mai duba address É—in da suka tura masa, he blv sun san abunda suke a aikinsu sannan shima ya ware bakin aljihu wajen neman ta ,baga gidaje radio da tv's ba baga trackers ba,he is just meant to find her.

Yana cikin motar sa yana san gano gidan motar Saleek ta wuce sa and for real Saleek ya gani sannan ya tabbata hakan ba coincident bane,ganin yana horn bakin gate ya saka shi saurin fitowa a motarsa ya isa gurin motar tasa da gudu gudu sauri sauri,yana zuwa ya ƙwanƙwa sa masa glass,wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Saleek lokacin da idanun sa suka saka kan Haidar,tambayar da ya fara yiwa kansa ita ce"shin Haidar binsa yake?amma saboda mene?fitowa yayi domin yi masa wannan tambayar amma ga mamakinsa kafun yace wani abu Haidar ya kai masa naushi mai kyau a fuska yana faɗin"ina ka boye ta".yana ƙokarin sake kai masa wani ya riƙe hannunsa ƙam yace"kar ka kuskura,'dan mene daga ganina zaka fara kaimun duka,sannan lafiya Why are you stalking me?

Cike da fushi Haidar yace"A for Audacity ,Just the temerity And the fucking guts,ni kake tambaya ko ina stalking É—in ka ne,nasan kasan da b'atan Kiswa sannan nayi tracking É—inta tana nan dan haka kada ka bani wani act din banza i know kayi kidnapping É—inta ne and im calling the police yanzun nan ".

Ɗaga kafaɗa Saleek yayi yace"suit Your Self amma kasani ni banyi kidnapping kowa ba had it been ka bini da sauki da na tausaya maka amma tunda ƙarfi zaka nuna mun ga fili ga mai doki saura sukuwa,motan sa ya buɗe zai shiga Haidar yayi saurin kama hannunsa desperately yace "kana nufin Kiswa na cikin gidan nan?"please kayi hakuri Just let me See her dan Girman ubangiji.

Kallan sa Saleek yayi lokaci guda yana mai jin kishin sa inda bangare guda kuma yake mutuƙar tausayin sa ,ya tabbatar Haidar na mutuwar san Kiswa sannan ba ya so ya zama third wheel akan abunda bazai samu ba,kallan sa yayi a karo na biyu kafun yace"bismillah ".

BuÉ—e motar Saleek yayi ya shiga inda ya sake horn aka buÉ—e masa tare suka shiga Saleek na mota Haidar wanda kejin kamar anyi masa babbar kyauta yana biye dashi a a baya yana Allah Allah yaga Kiswa ko zai ji daÉ—i a rayuwarsa.

Chuchujay ✍️
Chapter 29 · 0% Book details