← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 32

Sashe 14

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Ummi tayi tana mai jin maganar kamar dukan guduma,sai da Mother ta sake cewa "Hello Hajiya"Kafun Ummi ta dawo daga shock É—in da ta shiga,ajiyar zuuciya tayi tace"zan nemeki Hajiya i need to digest this".tana kashe waya Mother ta saka dariya tana mai faÉ—in"indai nice wallahi muzuba mu gani domin kuwa nafi karfin bataliya guda",zama Farry da mamaki Ya kusa kashewa tayi tace "mother mai yasa kike yin haka wai don't you think Bai kamata ba sannan ni dake munsan Kiswa is decent kuma da Aure aka sameta mai yasa zakice yar karuwa ce,beside ni mai yasa kike san haÉ—a ni da Haidar?.

Wani irin Kallo mother ta bita dashi kafun ta kamo hannun Farry tace "kalli Nan Faridha,kowa da kike gani kansa ya sani sannan a maganar da na faÉ—a ai ba duka ne karya ba cos Zubaida Na da reputation ,but ba wannan ba ,ki saurareni da kyau,duk duniya babu mai sanku sama dani ,ina san ki sani Kiswah ba sanki take ba,da zataga abunda zai cutar dake bazata taba faÉ—a miki ba ,iyakaci ma ta tura ki,ni Na tabbata idan kika kuskura kina gidan nan ta Auri mai kuÉ—i kamar Haidar to kisa a ranki wulakanci da sharri a gurinta sai ya baki mutukar mamaki,She's Just using you a gidannan domin zuwa wani matsayi mai girma,and gradually zata kai dan tunda Appanku ya fara wannan Abun wata rana zakiji ya tsigeki daga Kujerar ki ya bata.

da sauri Farry tace"God forbid Mother kar ki mun baki mana"ajiyar zuciya mother tayi tace "abunda nake nufi kenan kuma zai faru idan baki bani HaÉ—in kai ba zaki sha mamaki dan haka dole ki kwace Haidar a hannunta,a hankali cikin karfin Zancen uwa ga É—anta Mother ta wankewa Farry kwakwalwarta tass inda ta fara disgusting tunanin marasa kyau kan Kiswa ,

Kai tsaye bayan ta gama da Mother ta nufi É—akinsu da zummar korar Kiswa daga dakin ,tana shiga ta tarar da Kiswa kwance ta rumtse idanunta Ta lullube da bargo, kanta tayi kai tsaye ta yaye bargon wanda yasa Kiswa buÉ—e idanunta amma bata tashi ba,fahimtar idanunta biyu ya saka Farry cewa"bai dameni ba ki tashi Ko kar ki tashi amma Nasan kunnuwanki suna saurarena,to kiji nan you're selfish,san kanki yayi miki yawa ,idan ba haka ba mai zakiyi da maza biyu indai ba zalama ba tunda kinsan mutum É—aya zaki Aura and maganar Saleek kuma ai kinsan i appreciate Handsome guys idan da na ganshi bazan taba cewa bana sanshi ba sannan bazan taba kirkirar masa halayyar banza da na lissafa ba,da Kin bani hint bayan dawowarki yarda yake da yanzu komai ya dai dai ta tsakanin mu"

Tashi zaune Kiswa tayi tace "madam Hold on ,kina nufin duk abunda kika faɗa mun kan Saleek karya kike?"murguɗa baki Farry tayi tace and so?after all kuɗi kike yiwa cos ina baki baki taba so mun abu mai kyau ba a rayuwa,you're always this greedy ga san nuna ke mai gaskiya ce bayan cewa mamanki ma dake bauchi reputation gareta...wani irin tashi Kiswa tayi inda Kafun Farry ta ankara a dauke mata fuska da mari mai kyau Kafun tace"wallahi tallahi idan kina haukanki da aka doraki akai kika zo inda nake kina ƙokarin faɗan abu mara kyau kan mamana to baki ɗaya garin nan yamana kaɗan,sannan magana da kike akn kuɗi ko mene ke kinsani abunda nake dashi baya mun kaɗan sannan a kullum ina godewa Allah da abunda ya bani and kuɗinki idan har ba daƙiƙiyace ke ba kinsan ban taba roƙonki ba sannan in faɗa miki idan baki sani ba duk da ban taba kawowa zaki mun gori ba amma ban taba kashe su ba suna nan a account and i will send Your fucking shit back,sannan maganar Saleek da kika hada kika saka nayi making fool of myself shima zan baki mamaki ,sha sha sha kawai wadda bata san inda yake mata ciwo ba".

Cike da fitina Farry ke riƙe da kuncinta hawaye na mata reto a fuska,cije lebe tayi tace "ni kika mara Kiswah?"kaɗa kai Kiswah tayi tace ki rama mana sai naga adadin haukanki,ai Kafun kace ƙwabo faɗa ya kece a tsakaninsu ,hayaniyarsu Mother ta fara ji,dakin tayi kai tsaye dan ganin maike faruwa,ganin yarda suka chakume gashin Juna ya saka Mother shiga da gudu tana fadin"wanne irin hauka kenan"ganin yarda Kiswa ke neman fin karfin Farry yasa Mother shiga ta kama Kiswa a rike kam tace ma Farry "oya zo ki yamutsa mun fuskarta da mari,aikuwa kamar Farry na jira ta fara haɗawa fuskar Kiswa mari,tana ƙokarin yin na huɗu Appa ya Sameer da sagir suka shigo,cikin zafin Nama samer ya shiga ya dauke Farry da wani irin mari da saida ta tuntsura,kafin ya farga Mother ta rama mata tana mai faɗin"'dan baka da hankali kasan mai tayi mata da zaka rama mata."wani irin fushi ke daukar Appa dangane da Mother wadda idan ya biye ta yau bazata kwana gidan sa ba ,a hankali ya saita kansa yace kai Sageer je ka riƙeta kamar yarda Mother ta riƙe Kiswa,Babu musu sageer ya riƙeta ba tare da ya saurari mai Mother ke faɗi ba,kallan Kiswa da fuskarta ya tashi yayi yace"idan har na isa dake ina so yanzu ki rama adadin Marin da tayi miki "aikuwa ba abune mai sabuwa ba"mother ta faɗa hannunta a kugu".

"Idan kuwa kika kuskura kika matsa daga inda kike da zummar hanata to a bakin Aurenki,na miki alƙawari".

TBC

Chuchujay

08130229878
[5/13, 9:28 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
💥KISWAH💥

(Surrogacy was the cause)

Na

Chuchujay ✍️

Book1⃣

Page1⃣1⃣

Da mutuƙar mamaki Mother ta juyo tana kallan Appa Wanda ya haɗe rai iya mutuƙar haɗewa,kanta ta nuna da yatsa idanunta sun kawo ruwa tace"ni zaka faɗawa abakin Aurena akan yarinyar da zubaida ta haifa ?"

Cikin nuna mata rashin wasa a maganarsa yace "ƙwarai kuwa idan kuma kina ganin bazan iya ba dan Allah ki ƙara taku daya daga inda kike kiga cikakken mamaki,magana da kika akan yarinyar da zubaida ta haifa Eh ita ɗin sannan ina so ki sani zan iya chanza ki amma bazan taba chanza Zubaida da Kiswa ba"maida hankalinsa yayi ga Kiswa yace"oya fara rama marukanki"Babu musu Kiswa ta matsa ga Farry wadda ke fuzgewa ta fara shatata mata mari har saida tayi mata huɗu masu kyau Kafun ta saka kuka jin yarda Farry ke kuka,har ga Allah rana ta yau ba ƙaramun muni gareta ba a gurinta dan ita mutum ce mai bawa family ɗinta muhimmanci ,bata san abunda zai taba mata su ,yau sai gashi irin sabanin da suka samu bashi da daɗin ji,kallan Farry dake faɗin wallahi bazata yarda ba Appa yayi yace "to dan Allah Faridha ki dauki mataki ni kuma zan baki mamakin da tunda nake matsayin Mahaifinki ban taba baki ba."

Sanin Halin sa idan yayi fushi yasa Mother da tayi tsit cewa"kija bakinki ki yi mana shiru anan Farry"wani irin kallo Appa ya bata yace "better da kina faÉ—a mata tuntuni da rana irin wannan bata zo ba"'dan shiru yayi yana nazari Kafun yace"Its better ku raba É—aki, dama ai Faridha É—in ta nace tun yarinta a haÉ—a su ,so dole yanzu tunda shashanci ya fara shiga tsakani kowa ya zauna É—akin sa"

Yana kai karshen maganarsa ya bar ɗakin,kwafa Mother tayi itama ta fita,faɗa sosai Sameer ya fara yi musu inda Sagir yace "Just kallesu akan namiji wanda kilan ma yaudarace a zuciyar sa suke wannan faɗan kamar zasu kashe kan su"tsaki yayi ya fita a ɗakin yayin da Sameer ya yi musu Nasiha wadda Kiswa kawai ke gamsuwa dashi Amma banda Farry.daren Ranar Kiswa guest room ta kwana kafun washe gari tayi aikin parking to koma ɗakinta wanda yake da komai gyarawa kawai zatayi saboda Babu mai kwana cikin sa,washe gari bata iya fita aiki ba saboda ciwan kai dake damunta amma Farry kam karfin hali tayi ta fita dan da zaman gidan gwara ta fita ɗin koda ba office zata ba kuwa,Babu wani breakfast kowa ya kama gaban sa ban da Sameer wanda ya tsaya dan ganin mai Kiswa ke buƙata a saban ɗakinta ya taimaka mata.

•••••••••• •••••••••• ••••••••••

TUKUR BULA'S MANSION

"Son wait we need to talk like right now"mahaifiyar haidar ta shigo É—akinsa tana mai zama kan couch kamar an koro ta,

Haidar dake tsaye yana gyara tie É—in sa ne ya juyo yana mai cewa"Ummi hope im safe dai"kafarta ta É—ora kan É—aya tace"trust me muddin kana tare da yarinyar nan Kiswa to bazaka taba zama lafiya ba,Ko kasan cewa ba yar ALIJUA bace sannan É—iyar karuwa ce and bada Aure aka sameta ba,no bazan taba yarda da mace irin wannan ba cikin zuri'a ta".

Cike da confusion ya zauna yace"well rashin zama ƴar sa abune da na sani niece ɗin sa ce da Maman ta dashi uwa ɗaya uba ɗaya and ya ɗauko ta ne daga garin su bauchi bayan rasuwar mahaifinta ,a zallar sanina da kuma gaskiyar magana ita ba wadda aka haifa bace wajen Aure, da mahaifinta dangin sa kuma suna cikin garin Bauchi though sunyi abandoning ɗinsu,yanzu haka mahaifiyarta tana cikin garin Bauchi tayi Aure da yaranta biyu Khalel da Ra'abiatu ,Bansan Wake feeding ɗinki waccan maganar ba amma Ko wanne maƙiyin Kiswa ne and dole zan suing ɗinsa for defamation of character ki bani suna kawai Ummi.

Shiru ummi tayi tana nazari yayin da Abubuwa suka fara dawo mata daga zuwan Mother office É—inta tayi mata tallan Farry har izuwa kiran da tayi mata jiya da daddare .kallansa Ummi tayi tace "ya zaman takewarta da Barrister juwairiyyah?"
Chapter 14 · 0% Book details