Sashe 32
Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Komai da Kiswa zata buƙata Ya hallarta ,kama da wadda zatayi mata gyaran jiki,kai,lalle da komai da amarya zata ɗauka wanda hakan nauyine da Ummi ta ɗora a wuyan ta domin kuwa irin mutuwar san da Ummi ke yi wa Kiswa abun ba'a cewa komai,gidan babu abunda kuwa ke tofawa sai irin sa'a da Kiswa tayi na samun mace ta gari a matsayin mahaifiyar miji dan soyayyar da Ummin ke nuna mata kana gani ba wai soyayya bace ta ƙarya musamman idan ka duba daga bangaren irin soyayyar da takewa Haidar wadda itace ta shafi Kiswa ɗin,kafun kace mene amarya ta fito ɗas kamar za ka saceta ka gudu,Fitowarta daga wanka turaren da Dada ta saka tayi taji wayarta na ƙasa,ɗauka tayi ganin sunan wanda ke jin wayar,da sallama a bakin ta tace"Boss Saleek good evening".karamin murmushi yayi kafun yace"kin san dai baki da kirki ko?,bai kamata ace bikinki a media zan gani ba,Kinsan koma mene im Your well wisher mai yasa zaki boye mun,abune na farin ciki fa".zama tayi kamar yana kallanta tace"im sorry, Like im very sorry kayi haƙuri nasan bazaka yarda ba idan nace maka nima yau nake sanin za'a ɗaura min Aure gobe iswear,kaima kasan kana na gaba cikin masu sanin Aure na bazan taba boye maka ba,abun kaji da yarda yazo"..ɗan shiru yayi kafun ya sauke ajiyan zuciya yace "its okay na yafe miki Just this one time nasa Abba ma ba mamaki ya rigani sani 'dan ina maganar Ɗazu ya katseni yana mai sabanta murnarsa ,but any ways im very happy for you naji miki daɗi sosai,sannan ina miki fatan shi ɗin abokin Alherin ki ne,and bazan boye miki ba,duk da yau ne last day amma ya kamata ki sani,'ina mutuƙar sanki Kiswa amma duk yarda naso da san kaina bai kai yarda nake sanki ba,dan haka ina miki fatan Alheri a sabuwar rayuwarki,sannan kamar yarda na faɗa ni dake mun zama family dan haka just a call idan kina da wani damuwan and i wil be right away,sannan kafun na manta,company ya baki month honey Moon leave,kiji daɗin ki"..tsintar kanta tayi da share ɗan hawayen da bata san taya ya fara fitowa ba,ta yarda tayi sa'ar samun mutum kamar Saleek a rayuwarta,goge hawayenta tayi tace"nagode Saleek im blessed to have you in my life ,sannan ina fatan Allah ubangiji ya baka mace wadda ta fini komai da komai ,inayi maka fatan Alheri,and im looking forward to meeting you as Mrs HAIDAR BULA."..bayan sunyi sallama ya kashe wayan Khalifa dake gefensa ya kallesa yace "mutumina kana da ƙarfin Hali da imani,wannan Babe ɗin fa you dey do her ne kana santa kaƙi kula kowa akanta amma gashi magana ake ta Aurenta fa Har kana da ƙarfin kiranta kayi mata fatan Alheri,omo nagode ƙanin Mother teressa.".Kallansa Saleek yayi kafun yace "abu guda ɗaya na yarda dashi wanda Shine babu wanda ya isa 'ya Auri matar wani sannan ga dukkan alamu ya bayyana cewa Kiswa ta Haidar ce so mene kake so nayi,kana san na halaka ne saboda ina santa?abeg idan zakayi mun Addua Allah ya kawo min sassauci kayi mun idan baza kamun ba ka zuba mun ido,kuma kar ka Sake kiranta babe".tabe baki Kalipha yayi yace"kaji dashi ni bari kaga tafiyata ma kafun yanzu saboda nasan akan Kiswa za ka nemi ka zageni."Bai ce masa komai ba har ya fita,komawa yayi ya ƙwanta ya rufe idanun sa abun duniya na mutuƙar damun sa ,ya kasa yarda da cewa wai Kiswa zata zama matar wani gobe da safe sannan yana addu'ar Allah ya bashi ikon Hallarta ,he Just can't bear it.
💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥💥
__Kamar yarda komai ake saka masa rana ya tabbata cikin yardar Allah haka nan ranar da aka saka domin Kiswa da Haidar tazo,Babban Masallacin na central mosque a cike yake da manya mutane domin amsa gayyata Ɗaurin Auren da yazo babu zato babu tsammani,bikine na kuɗi wanda cikin rana ɗaya suka tsinci Ɗaurin Auren amma kasancewar lahadi ne yasaka duk wanda ya samu gayya yayi ƙokari wajen ganin Ya amsa ta, taro yayi taro inda da albarkar jama'ar gurin Waliyin Haidar ya karba masa Auren Kiswa akan sadaki naira dubu ɗari biyar daga hannun Waliyinta,inda shi kuma waliyyin nata ya bada Aurenta bisa shedun mutanen da suka hallarci wannan Ɗaurin Aure mai Albarka,wani irin yanayi na farin ciki da Haidar ya tsinci kansa abun ba'a magana yayin da Saleek wanda yazo a daddafe yaji Abun ya saukar masa kamar Aradu,a haka dai ya ke ta faman washe baki gefen Abban sa wanda Shima nasa bakin ya kasa rufewa .
Ana ɗaura Aure maganar ta isarwa mutanen gida inda take masu hancin guɗa suka kama,Kiswa dake zaune bakin gado cikin wani irin sassanyan ado kuwa ji tayi kirjinta yayi wani irin mugun bugawa,Kallan ta Dada tayi tana mai shafa mata baya tace"Alhamdulillah,maza kiyi sujjada ki godewa Allah da ya kaiki wannan matakin da kowacce mace take san ta ganta Akai."babu musu Kiswa tayi abunda Dada ta umarceta tana mai nunawa ubangiji godiyar ta da ya nuna mata wannan ranar da ta daɗe tana dako,guɗar da aka ɗauka sabuwa ce daga waje ta ja hankalin su,Baba Baraka ce ta shigo tana mai cewa "gafa mahaifiyar Haidar nan da tawagarta sun kawo akwatin Kiswa"Tashi Dada tayi tana mai cewa ,akaisu ɗakin masaukin baƙi za'a zo a tarbesu,hakan kuwa akayi inda sukayi musu tarb'a cikin mutunci da karramawa,kaya kuwa kamar za'a buɗe shago,Ummi ce ta nemi ganin Maman Kiswa domin gaisawa da ita sannan tayi mata godiya na haifan ɗiya kamar Kiswa wadda ta tafi da dukkan wata soyayyar Haidar,sanarwa da Mama akayi inda ta kimtsa tace a rakota dan itama tana san ganin Mahaifiyar Haidar domin tayi mata godiya da bata amanar ɗiyarta. Sallama Ummi tayi inda sallamarta ta katse sakamakon ganin Mama yayin da amsar Mama da farin cikinta ya katse ganin Wadda tayi sallamar a matsayin sirikarta .
Tashi Mama tayi tace"wa nake gani kamar Hajiya zainab?"da mamaki Ummi tace nice Zubaida ba dai kece mahaifiyar Kiswa ba,
Ƙaramun murmushi Mama tayi kafun tace"yanzu na fahimta sannan kema nasan Kin fahimta,wannan Auren dake tsakanin Kiswa da Haidar shi da zuba ruwa a rariya Ya tsiyaye haka yake ,dan Wallahi babu shi bama zai taba iyuwa ba".da sauri Ummi ta shigo ciki tana cewa"kar kice haka mana Zubaida,farin cikin ƴa ƴan mu ne kar mu bata da hannun mu"ƙarasawa tayi ta kama hannun Mama idanunta sun fara kawo ruwa..ƙwace hannu Mama tayi tace"tun ran gini tun ran zane wallahi indai nice na Haifi Kiswa wannan Auren babu shi ba zai taba zama da Akwai ba har abada".
Dan dan dan dan dan dan
Shin meke shirin faruwa ne?
MuhaÉ—u a littafi na biyu domin jin Mai ke shirin faruwa mene zai faru,kamar kuma yarda na sanar a book 1 book 2 na kuÉ—i ne kan 300N kacal.
0264267657
Gt bank
Amina jamil Adam
Shaidar biya
08130229878.
Ku zo maza ku biya kudin ku domin a cigaban da tafiyar dakuâ¤
Nice Take a kullum
CHUCHUJAY âœï¸
(Amina jamil Adam)
â¤