← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 32

Sashe 3

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin aiki taji an buɗe kofar office dinta,ba tare da ta ɗaga kanta ba tace"Yauwa Ameera thank you kamar kin san..."bata ƙarasa ba sakamakon Kamshin HAIDAR dinta da ya ziyarceta wanda yake ɗaya daga cikin abinda ke burgeta dashi baya rabo da kamshi ,sannan wannan kamshin guda ,a hankali ta daga kanta dan tabbatarwa da zuciyarta tunanin da Take na ko shine,suna haɗa ido tayi saurin dake nata tasha kunu,murmushinsa mai kyau ya Faɗaɗa yana mai Takowa gareta hannunsa dauke da bunch na red roses ,zagayawa yayi ta inda Take zaune ya duƙa cikin sassanyar muryarsa yace"Haba Love kinsan dai fushinki baya barina na samu sukuni daidai da na minti ɗaya ,mai yasa zakiyi kwana uku kina fushi dani bayan kinsan kece rayuwata?"

Wani irin kallo ta bashi cike da haushin da Take ji na Abunda ya faru tace"Haidar ka rabu dani tun muna shaida juna cos banga amfaniin da zai saka na cigaba da kula ka ba bayan gidanku an maka mata so gwanda ka tashi ka tafi gurin tasleem da zaka Aura nan da wata biyu ka rabu dani. "Shafa sumar kansa dake sheki yayii yace "ya Allah,so tasleem ta fada miki ni da ita zamuyi Aure nan da month shine kike ta wannan fushin?zata ci ƙaniyarta kuwa ,tashi tsaye yayi ya ciro wayansa Ya danna kiran wayan Tasleem yasa a speaker wadda a kira ɗaya ta dauka tana mai fadin"hello favourite brother"katse ta yayi ta hanyar faɗin"a gidan uban wanene zamuyi Aure ni dake nan da wata biyu?"

She was dumbfounded for a Moment kafun realisation yayi hitting dinta na haduwa da tayi da Kiswa a shopping mall tayi franking É—inka akan ita fiancee É—in Haidar ce sannan Aurensu nan da two months,she was only joking tunda daga bisani tayi introducing kanta ma Kiswa a matsayin sister É—in Haidar batayi tunanin ta dauki maganar da zafi ba .

Dariya ta saka tana mai faÉ—in"Yaya i was only joking fa and after all na faÉ—a mata kai yaya nane and nothing more Bansan She's This possessive ba im sorry.

Ƙaramun tsaki yayi yace "possessive or not ni nata ne insha Allahu na har abada ki kiyaye ni"yana jin dariyarta Ya kashe wayansa cos Tasleem yar banzan yarinya ce idan Ya biyeta hurasa kawai zata cigaba dayi.

Kujera Ya jawo Ya zauna yana facing É—in Kiswa wadda borin kunya Ya saka Ya haÉ—e rai,kafun yayi wata magana tace"okay naji i was only mad which is justify dont say a word im embarrassed right now".dariya Ya saka yana mai jin santa yana É—ibarsa,yana mutukar san Kiswa ba kaÉ—an ba sannan shima Ya yarda da soyayyar da Take masa cos bata iya boye masa sannan ita macece mai kishinsa Ya sani tabbas yau idan akace bashine Ya Auri Kiswa ba zai shiga mawuyacin hali dan tabbas badan shi musulmi bane Ya kuma san hukuncin musulmi yakashe kansa da yace zai kashe kansa Ya huta da rayuwa baki daya , flower din hannunsa ya kalla yace"so ya zanyi da roses É—in nan?"

Hannunta ta saka ta kwace tana mai faÉ—in "rose is a symbol of love and im your love and life kaga kuwa rose É—inka a hannuna zai kasance."

Cike da kaunar juna ta ringa guiding É—inta yana tayata paper work kana suka fita cin abinci tare.

Shin wanene wannan HAIDAR É—in?

TBC

CHUCHUJAY ✍️

08130229878
[5/2, 4:16 PM] Chuchujay✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
KISWA

(Linked through Surrogacy)

Na

CHUCHUJAY ✍️

Book1⃣

Page3⃣.

ALIYU'HAIDAR TUKUR BULA shine asalin sunan sa matashin saurayi mai shekara ashirin da tara ,haifafen cikin garin Abuja ne amma asalin su mutanen dutse ne dake cikin garin jigawa amma a tashin Haidar Abuja Ya sani gidan dan tunda yake da iyayansa biyu basu taba cewa yau Haidar shirya muje usulin Garin ka ba a yayin da shi ma bai damu ba ganin yan uwan nasu na chan garin suna zuwa inda suke.

Haidar É—a guda ne tilo wurin iyayen sa Alhaji Tukur Bula da Matarsa Hajiya zainaba Bula dan haka suka dauki soyayya ta duniya suka É—ora masa ,Babu wani abu da Haidar yake nema a rayuwar sa ya rasa tun yarinta indai kuÉ—i ne zai bada su ,irin girman sangarta da akayi masa kawai ya ishe sa lalacewa a yayin girmansa Amma sai Allah ya rainesa cikin sahun mutane masu nutsuwa da sanin ya kamata,sau da dama mahaifiyar sa kan É—orasa a abu mara kyau wanda zahiri tasan mara kyau dinne amma saboda dabia ta nasara sai ta danne inda shi kuma idan ya hanga rashin dacewar wannan abun sai yayi kokarin wajen ganin ya dorata a hanya.

Iyayen sa shahararrun masu kuÉ—i ne domin mahaifiyar sa babbar sananniyar yar kasuwace a garin wadda keda boutiques É—in da zaka gaji da irgawa a yayin da mahaifinsa yake babban custom,magana ta rashi a gidansu Haidar fa babu ita domin kuwa Allah ya azurta iyayensa wanda dalilin hakan yasaka basu damu da subi danginsu inda suke ba sai dai su su biyosu inda suke su dan lasa.,

Rashin samun wani haihuwar bayan haidar baya damun iyayensa illa shi din da suka samu suka duƙu fa wajen tara masa abunda yake nasu ne ma'ana dukiyarsu,

Sanin iyayen Haidar Nada kudi bai taba kashe masa zuciya ba wajen neman na kansa duk da kuwa yarda mahaifiyarsa ke nacin yaji dadin rayuwarsa kawai domin kudi sun tara masa ba sai ya wahalar da kansa wajen nema ba amma yayi fafur akan cewa su barshi yayi aiki domin career ɗin abunda yake mafarkinsa ne kuma abune wanda yake da sha'awa tun yarinta wato aikin Likitanci,ganin ga abunda yaran nasu yake So shi yasa suka bude bakin jaka wajen ganin sun bashi ilimi isashe wanda ya samu ƙwarewa a harkar inda daga bisani suka tamfatsa masa Asibiti wanda yaci sunasa "AL'HAIDAR PRIVATE HOSPITAL "Haidar kwararren likitane wanda ya taba fannika daban daban ,sabida san zaman komai dai dai a asibitin Nasa yasaka yake daukar likitoci wadanda suka san mai suke ,a kalma guda Asibitin Al'Haidar asibitine wanda baza kace likita daya ke duba zuciya ba sannan ya duba hakori ya duba kunne ,ya duba ƙashi da dai sauransu,asibitine da ke dauke da zuga na komai da ruwanka.

Da kansa ya samawa kansa ilimin addini duba da iyayensa sunfi bada muhimmanci akan bokonsa cos bai taba zama ajin islamiyya ba sai dai malami yazo gida yayi masa wanda shima bayan fara tasawarsa aka sallamesa acewar Hajiya zainaba 'ya samu 'na sallah ,sanin yana bukatar bunkasa saninsa akan addininsa 'ya saka ya dage wajen sanin littattafai domin duk yarda yake san iyayensa yayi alwashin idan ya haihu bazai taba Bawa yaran sa tarbiyya irin wadda 'ya samu ba,mutum ne shi mai nutsuwa kamili wanda bai damu da sabgar yan mata ba duk da harin da suke kawo masa domin shi din mai kyaune da kyawun kira irin wadda duk wani namiji ke fata,sau da dama idan aka tada ma mahaiffiyasa maganar 'ya kamata yayi Aure sai tace "duka nawa Haidar din yake,abarsa yayi rayuwarsa cos life is too short duk lokacin da ya gama gwara kan yan mata ya samu ta Aure"jin Wannan furucin yasa ƙanwarta mahaifiyar Tasleem ta kawo tasleem gidan da zummar tana daukewa haidar din kewar rashin dan uwa amma a kasan zuciyarta ta kawo tasleem ne domin ta Auri Haidar nan gaba.

Kowa yana saka da warwararsa a yayin da Haidar yayi gamo da tauraruwar da ta sace masa dukkan nutsuwarsa da tunaninsa a lokaci guda wata rana da tazo asibitinsa,yana kokarin fita daga Asibitin tana shiga a motarta wanda ta shige da zuciyarsa at first sight,bai wata wata ba 'ya koma Asibitin 'ya jirata har ta fito 'ya bita, babu kasa a gwiwa 'ya fallasa mata asirin zuciyarsa,ya dan sha wahala kafun 'ya samu hadin kanta cos a ranar bata kulasa ba sai da yayi ta bincike 'ya gano inda take aiki ya sarrafi addabarta wanda a hankali ta bude masa tata kofa zuciyar da ta gama karantarsa,yarda bai taba budurwa in a Serious way ba Haka nan Kiswa dan haka suke ma juna mayyar soyayya cos akan juna suka san daÉ—in ta.

******

Duk weekend rana ne da Kiswa da Haidar suka ware domin kasance da juna ta hanyar zaga duk wani gurin shaƙatawa domin ranar ne suke free baki ɗayansu,yau ma kamar kullum 'ya sameta gurin Spa 'dan su wuce classic restaurant ɗin da aka buɗe sabo aka bashi gayyata,chan 'ya tsaya bakin motanta yana jiran fitowarta inda bata wani bata masa lokaci ba ta fito garesa,tun daga nesa take kallansa tana yaban kyan da yayi mata a zuciya cos a ko wanne sutura takan tsinci Haidar dinta cikin kyawawan maza da komai ke fitting,sanye yake cikin royal blue button up riga mai sleeves gajere da dark Pants,sosai yayi mata kyau,cikin takunta mai daukar hankali ta ƙaraso garesa ,snapping 'yatsunta tayi a fuskarsa ganin yarda ya zama lost a kallonta,murmushi yayi lokacin da ta jingina da motan kamar yarda yayi tace"'na sake kama hala?"

Juyowa yayi yana kallanta yace"dan Allah kiyi wuff dani Girlfriend ,husband me cos kina kasheni da yawa ,i just cant wait naga kin zama mallakina,What are we waiting for?

Licking life dinta 'na ƙasa tayi tana mai tambayar kanta a zuciya "What is she waiting for?"'ya kamata ace yarda ta yarda da Haidar zuciyarta kuma ta gamsu dashi magana ɗaya 'ya kamata ace a yanzu anayi tsakaninsu which is maganar Aure,shekarar su guda kenan tare da juna amma bayan Farry Babu wanda yasan labarinsa a gidansu,itama Farry din kamata tayi suna waya ta dinga bin kwakwafi sai da ta gano wanene shi,lokacin da tasan kuwa Mai Al'Haidar hospital ne kamar tayi hauka tana mai ingiza Kiswa akan kar ta sakesa cos shi ɗin catch ne babba.

Tana san maganar Haidar ga Appa amma tana tsoran Outcome 'na Mother wanda tasan Babu daÉ—i domin duk cigabanta idan mother zata sanshi to zatayi yarda zatayi ta koresa 'dan haka ta sama ranta maganar Haidar sai ta shirya,kamar yarda take faÉ—a masa a kullum yauma shine dai wato"Babe ka bani time kaÉ—an na dan Sake gina career ta kaÉ—an ,i assure you indai ina rayuwa kaima kanayi to da yarda Allaah da ikonsa nida kai mallakin juna ne".
Chapter 3 · 0% Book details