← Book details Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 32

Sashe 15

Kiswa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

'dan shiru Haidar yayi yana san ya fahimta dan a iya zamansa da Kiswa bata taba nuna masa koda da wasa ba tana fuskantar matsala a gidansu ba ,sannan a iya saninsa tsakaninta da yan gidan Babu wani matsala tana san su suna santa ,dan haka yace"Gaskiya Ummi i dont know about Mother tunda ba hirarta ta cika yi mun ba amma ga dukkan alama tsakaninsu ba matsala duba da yanayi na yarda mu'amalar Kiswa take da yaran gidan".shiru Ummi tayi tana kallan fuskarsa da yarda baya so ace akwai Matsala a rayuwar Kiswan sa,ajiyar zuciya tayi tace"i need to see that girl cos na tabbata akwai wani abu a rayuwarta wanda take boyewa,sannan a wannan gidan na Alijua na tabbata akwai bangaren da bata jin daÉ—i saboda Barrister juwairiyyah jiya take fada mun maganganun nan da daddare bayan na kirata,but my instinct is telling me otherwise duk da Kafun naji ta bakin ka hankalina ya yarda da maganarta amma da nayi magana da kai yanzu hankali na ya kwanta akan cewa ta haÉ—a labari ne saboda tana san Æ´arta ta Auren ka ba Kiswa ba,koma dai yaya ne zamu san gaskiya Just bring the girl to my Boutique.

Tashi tayi ta fita tabar Haidar da jimami yana san sanin mai yasa tayi ma Ummi ƙarya sannan wacce irin rayuwa ma Kiswa ke yi a gidan ,yakamata yaje ya sameta,wayarsa ya ciro ya fara kiran layinta akashe dan haka kai tsaye da ya fita ya nufi office ɗinta, yana ƙokarin shiga Elevator ɗin da zai sadashi da floor ɗin office ɗinta Saleek ya na ƙokarin shiga,dakata masa Haidar yayi ya shiga kafin yabi bayan sa,kallo ɗaya Saleek yayi masa ya gane sa yayin da Haidar bai ma sanshi ba ,ba tare da Saleek ya kallesa ba yace "You're a doctor right"?

Kallansa Haidar yayi yana mai tabbatar dashi yake magana Ko a'a,murmushi Saleek yayi yace"i hope you made it out of Your relationship Alivee"kafun Haidar yace wani abu lifter ɗin ya tsaya a Floor ɗin da zasu sauka,Saleek ya Fara fita kafun Haidar yabi bayan sa yana mai Juya maganar da ya faɗa masa Na Allah yasa ya fita a relationship dinsa a raye wanda baya ce ga mai yake nufi ba,jan kunne ne Ko barazana,ƙaramun tsaki yayi ya nufi hanyar da zata sadaka da ofishin Kiswa , yana isa Amira ta taresa tana mai faɗin "barka da zuwa yallabai ,unfortunately yau Madam Kiswa bata shigo ba and Batayi reporting ba ina ta ƙoƙarin kiranta amma akashe,"dauko wayarsa yayi yana mai sake dialing ɗin wayarsa Kafun ya ɗagawa Amira Hannu ya fita a gurin dan zuwa gidan su Kiswa ,gudu kawai yake a titi dan a yanzu He's worried beyond expectation,koda yaje bakin gidan su cigaba da kiran wayarta yayi amma a kashe ,fitowa yayi a motarsa ya taka zuwa bakin gate ɗin gida ya Fara knocking cikin nutsuwa,yayi wajen knocking uku zaiyi na huɗun Aka buɗe ƙofar gate ɗin,sauke hannunsa da yayi ƙokarin knocking yayi yana kallan wanda 'ya fito,'ya sameer ne tsaye,Takowa yayi fuskarsa babu yabo Babu fallasa ya miƙa masa hannu yana mai faɗin "Assalamu alaikum"

Karba Haidar yayi yana mai amsa masa sallamarsa Kafun kuma yayi shiru bayan sun raba hannun su ,kallan sa ya sameer yayi da Kyau kafun yace "wa kake nema naga kana knocking hala kazo gurin Sageer ne"murmushi Haidar yayi yace "yaya Sameer right"?

Kallansa sameer yayi musamman da yaga yarda yake sinnewa ga kuma kiransa da yayi yaya wanda a ƙalla zasu iya yin sa'ani,ganin kallan da yake masane ya saka Haidar cewa"sunana Haidar and nazo gurin Kiswa ne dan ina ta kiran wayarta a kashe sannan naje gurin Aikinta an tabbatar mun bata zo ba shine nace bari nazo gida naga Ko lafiya".

Cike da Fara'a Sameer yace "kace mun wanda yayi wuff da zuciyar ƙanwata ya hanata sukuni"ƙasa Haidar yayi da kansa yana mai murmusawa kafun Sameer yayi masa jagora suka shiga yana mai dan jan sa da hira mai kama da tambayoyi har ya ajjesa falon da aka tanada domin baƙi Kafun ya shiga ciki domin yiwa Kiswa magana,ya jima yana ƙwanƙwasa mata ƙofa Kafun ta bashi izini ya shigo,da mamaki ya kalleta yace"har kin bani tsoro danaji baki amsani,ya jikin naki"?

Murmushi tayi tace"jiki da sauki yaya Sameer but my heart is still bleeding na rasa abunda yake Mun daÉ—i baki É—aya na".

Murmushi yayi yace"well ina tunanin maganin matsalarki yazo ,kinyi baƙo a kasa,bazan kuma tsaya ja miki rai ba mai kiranki ba kowa bane face Haidar ɗinki,"wani irin daɗi taji ya ziyarce inda lokaci guda ta nemi damuwarta ta rasa, hijab ɗinta da tayi sallah dashi ta ɗauko ta saka taɗan gyara fuskarta kaɗan Kafun ta fita dan zuwa gurinsa ranta fari tas,da sallama a bakinta ta shiga falon tana mai faɗaɗa fara'arta ,tasowa yayi cike da damuwa da kulawa yace"Baby mai ya faru,mai ya same ki?are you sick?mai yasa kika kashe wayarki sannan mai yasa bakije aiki ba?you got me worried".

Ajiyar zuciya ta sauke tana mai sauke idanunta akansa ganin yarda ya wani ruÉ—e ,murmushi tayi tace "calm down masoyina wannan tambayoyin naka wanne kake so na Amsa,?Nasan duka ne dan haka bari na amsa maka su duka,Bana jin daÉ—i ne shi yasa ban bar wayata a kunne ba cos i was very sick to talk and bana yanayin da zan iya waya kuma shine dalilin da banje office ba,kaga na amsa tambayoyin ka baki daya.

Cike da damuwar da tafi ta farko yace"baki da lafiya shine baki karani ba ,mene amfanin zamana Likita rayuwata bata da lafiya "?

Takawa tayi dan zuwa ta zauna kafun tace"calm down nawan baka ga na fito gareka ba kasan idan na saka ka cikin idona Ko wacce irin damuwata da ciwo na daukewa suke ,ka kwantar da hankalin ka ciwan Kai ne kuma na warke Alhamdulillah .

Zuwa yayi ya zauna inda take yace"ina fatan ba faÉ—a kike ba kawai dan naji daÉ—i,kinsan lafiyarki tafi mun komai a rayuwa"murmushi tayi tace "hayatee calm down im okay wallahi,and maimakon kabari sai ka tashi a aiki kazo amma kabar aikin ka Just to see me".

KaÉ—a kan sa yayi yace "yarinya kenan baki san bana tunanin komai ba muddin wani abu akace ya sameki"Serious face yasa yace "yauwa Girl we need to talk idan zaki iya idan kuma You cant talk much just tell me na bari other time.

Kallan sa take cikin ido tana mai san gano maganar da yake san mata amma ta kasa gano komai,murmushinta ta FaÉ—aÉ—a tace "na warke fa na faÉ—a maka Ina sauraran ka.

"lasar leben sa na ƙasa yayi Kafun yace "ban san ta ina zan fara ba and i wish baza kiyi fushi dani ba,im Just curious ina san nasan ya yanayin zaman ki yake da Mother cos im not understanding it ,bana san na boye miki saboda tsakanina dake bana fatan boye boye ya shiga tsakanina dake ,ummina ta kira Mother akan maganar mu so Mother take faɗa mata cewa ke ɗin ba da Aure aka sameki ba sannan mama zaman kanta take which im sure ba haka bane ,na kasa haɗa maganar guri ɗaya sannan im confuse akan mai yasa Mother zatayi hakan ,hope banyi mata ko Kin mata wani laifi ba cos im sure akwai wani abun a ƙasa."

Cikin wani irin siga da yanayi Kiswa ta tsinci maganar wadda tayi mutuƙar bata mamaki ,yar dariya Tayi tace "for real ?Mother tace ni bada Aure aka haifeni ba sannan idan na fahimta tana nufin mama ma karuwa ce,wata Dariyar ta kuma sakawa Kafun kuka ya kwace mata,bata san lokacin da ta kama hanunsa ba ta saka kuka sosai tana mai faɗin"Baby i swear To God wallahi Mama ba karuwa bace koda kuwa a baya bata taba karuwanci ba sannan ni ba yar zina bace idan Ummi bata yarda ba kuma ta saka ayi mata bincike,mahaifiyata da Aure ta Haifeni sannan bayan rasuwar Mahaifina bata zauna haka nan ba sai da ta sake wani Auren inda ta haifi Khalel da Rabiatu wallahi ba ƙarya nake maka ba ,idan ma baka yarda ba bari na kira maka yaya sameer kaji a abakinsa ,zumbur ta tashi dan zuwa kiran Yaya sameer,da hanzari ya saka hannunsa ya jawota ta zauna,tana zama ta fashe da wani irin Kuka mai ban tausayi tana mai faɗin"ban san mai na tabawa Mother a rayuwa ba da take san kushe Asalina ta lalata mun soyayya,idan ban Aure ka ba zan iya mutuwa saboda dukkan wata soyayyata na dauka na baka,bazan boye maka ba ,a soyayyarka baki ɗaya na zira jikina saboda na gama yarda da cewa naje destination ɗin karshe ,Babu wani gurbi dana ajewa wani ɗa namiji a wannan rayuwar,dan Allah Haidar kar ka rabu dani duk runtsi duk wahala".
Chapter 15 · 0% Book details