← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 29

Sashe 5

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Zaune yake a ɗakin momma, yayi zurki cikin tunani ƴa marasa meke damunshi, kuma ba wani abu bane illa tunaninta shi bai san meke damunshi akanta ba amma idan da za'a ce ya zauna kusa da juna zaiyi fari ciki sosai, taɓa shi momma tayi hanunta rike da abinci zama tayi kusa da shi tana karantar fuskanshi, ɗiban abincin tai da spoon ta kai mashi baki, ba musu ya amsa amma baya jin daɗin abinci sake bashi tayi, ya amsa, sannan ta fara magana tace

" Son, kana try ɓoye wani a ranka, wanda nina rasa gane maka Son idan baka faɗa min ba wa zaka faɗawa, nifa mahaifiyarka ce kuma abokiyar shawaranka me ye matsalarka Son."

      Gyara zama yayi sannan yace
"Momma ban san meke damuna ba, ni dai kawai ina cikin damuwa, idan naganta sai naji ina tsoron mata magana, wallahi momma ban taɓa jin kome akan zubaida ba amma ita idan naganta ina samun nutsuwa sosai, nakan tsinci kaina cikin farin ciki fiye da tunanina momma ban taɓa jin kewar wani abu arayuwata kaman ita, ina matukar kewarta bazan iya ce miki ga yanda nake ji ba momma yau da nayi nisa da ita jinake kaman nayi shekara dubu, momma kawo hanunki kiji yanda heart ɗina yake buguwa, toh momma me haka yake nufi"

           Hawayene ya cika idanun ga koshi ga kwanan yunwa murmushi tayi wanda yasa hawayen ya zubo mata ta rasa kukan me take farin cikine ko bakin cikine,

          hanunta na kirjinshi, tana jin ynd zuciyarshi yake bugawa, idanunshi a rufe tausayin shine na ɗa da uwa ya kamata,

          Hmm Ayya

#Comments
#Share
&
#Voting
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *QADDARAN RAYUWATA*
_SHUKRAH_

Mai_Dambu

       Al-Salam Al-Muhmin Al-Muhaymin Al-Azeez 👏👏👏

       *Fatan Alkhair gareku Aunty Kyauta,Jelatyna,Aunty Dada Naseer,Aunty Fatima,Momina Zainaba Misau, ina jin daɗin kasancewa daku da fatan kuma haka*💕💞💋

_Bestie kina hanani magana dake nake alfahari bani mantawa dake kuma nayi hakuri_😍

*Page 5*

Cire hanunta tayi daga kirjinshi, sai lokacin ya buɗe idanu ya zuba akan, fuskanta yana kallon hawayen da yake zuba daga idanunta, gyara zaman yayi yace,
"Momma," shiru yayi be sake magana ba, kuma be fasa kallonta ba, damuwa ce ta bayyana karara a fuskanta share kwallarta tayi sannan tace,
"Son you too later,(Son kama kara) ni ina goyon bayanka amma, kasan halin da kake ciki kuwa ?, kasan meye yake damunka kuwa, ?"  tsare shi tayi da manyan idanunta, masu cike da kwarjini irin na jinin sarauta,
       gwauron numfashi ta sauke sannan tace,
" Son dagsk duk abin, ka faɗan kana jinsu akanta *?*"

  zuba mata ido yayi cikin nutsuwa, sannan ya langwaɓar da kanshi kaman ɗan karamin, yaro da yake son amashi wani abu,

             tsintar kanta tayi da farin ciki, mara misaltuwa tace,
"You are deep in love,(ka faɗa soyayyane) son yanzun har ka faɗa so, bakasani ba amma wata sarauniya ce haka da tayi nasaran sace, min zuciyar yaro, ok ko itace wacce ka taɓa ce min, you found your half, hmm ba half ɗinka bace kasamu, zuciyarkace tayi lucking sacewa,"

  matsanancin kunya ce takama shi har sai da yarufe idanunshi, yana sake murmushi a hankali, zuciyarshi tayi masa daɗi.

           Buɗe idanun yayi, sangarce yace,
"Momma toh, taya zan faɗa mata bayan itama yarinyar bata wucce 17yrs ba, yanzun fa take shirin gama skull, ina tsoron kar nashiga hakkin  karatunta kuma, ina son nafaɗa mata kafin lokaci ya kure min,"
             shiru sukayi, dukkansu cike da damuwa can momma tace,
"Ina ganin kanuna mata, alamun kana sonta ai basai na faɗa maka  yanda zakayi ba, kafini sanin yanda zata faɗa sonka, dan haka kyaleni naje naji da bak'ina suna bukata sannan, ya kamata kashirya kashiga faɗa, dan kasan kaima ɗaya a cikin Emirate  councillors, dan Abbanku ya kawo min k'aranka baka son shiga fada, bansan me ye reason d'inka ba, but nabashi hakuri kuma, nace idan kazo zaka shigo har cikin gida wajensu Hajiya kilishi, zan fita amma ak'wai kaya a cikin wanca ak'watin, ka bud'u kayane daga Maiduguri yaya Zanna da Abbalawan, suka aiko maka suma ranar juma'a zasu iso, Dan haka kad'auki ak'watin ka kai d'akinka,"

        Tana gaba fad'an haka tafita daga d'akin, matukar tatsaya a ɗakin toh wallahi ba zaije fada ba, wai dogawara suna takura masa, da kirari shi yasa ya tsani zuwa fada,

              Babu yanda ya iya haka dole ya ɗauka yafita, da kayan.

             ***
Tafiya suke kuma, sauri take dan yau tana son taisa gidan, suna dai-dai quarts ɗin ta dago kozata hangoshi, tunda taga baya nan bata damu ba, daman addu'a take Allah yasa baya nan, dan idan yana nan tana jin yanda yake binta da idanu har susame napep,

          A gajiye suka isa, gida kwanciya tayi a falo dan kusan six da y'an mintoti suka shigo, tana wajen har aka kira sallah, sannan tashige ɗaki tayi wanka takwanta dan na up, buks ɗinta ta baza akan gado, tana dubawa sallamar Aisha yasa ta ɗago kai, tana kallonta bayan ta amsa, mata. 

     Zama Aisha tayi kusa da ita tace,
"Shkurah, nikuwa kinsake haɗuwa da wannan gayen da yayi mana siyayya, arbia market."

      Gabantane ya faɗi a razane ta ɗago tana kallon, Aisha yatsina fuska tayi tacigaba da aikinta tace,
"Kin bani ajiyar shine da zaki, tambayeni nasake haɗuwa, da shi zan haɗaku da umma tarabani dake, dan ni ba y'ar iska bace da zanta kula kowa,"

        tana gama faɗan tayi shiru tacigaba da duba buks ɗinta,
     mamakine ya rufe aisha tana kallonta, bakinta buɗe da mamaki daga tambaya, sai masifa haushine ya gama rufeta kaman ta tsinka mata mari, shareta tayi itama.

***
A azare kuwa maina ne tare da yarinyarshi Ruth, wacce maina yasa tazo dan biyan bukatar kanshi, giya yasha sosai dan duk lokacin da zai kwanta da mace ɗabi'arshi ce k'wank'waɗar giya, sai da yaga sannan ya kai hanun zai riketa ta fizge daga gareshi tace,
"Na gaji, bazan iya maka ba Maina katagum saura kwanaki ayi aurenka,amma ni baka tuna gobena sai naka kawai baka ɗauke ni abakin kome ba, sai dan biyan bukatarka na gaji, idan kuma zaka aureni fyn."

          Wata uwar ashariya ya maomalo mata, ranshi a ɓace ya fisgota yashiga kiciniyar rabata da kayanta, kai mashi duka take dan ya kyaleta amma ina, karshe ihu tasaka, wanda yayi da shigowar Mashkur kenan gidan dan anan matansu zasu zauna, da sauri ya shiga ɓamgaren Maina,yana kusa kai falorn idanunshi yayi masa tozali da abinda maina zai aikata,

           da sauri ya karasa ya ture shi, lokacin har yayi nasaran rabata da kayanta juya mata baya mashkur yayi sannan yace,
"maza kibar gidan nan, kafin na miki rashin mutunci."

          Meqewa maina yayi, cikin zafin nama mashkur yasaka kafa ta taɗe shi, ya faɗi k'asa rsnshi a ɓace ya sake yunkurin mikewa, mashkur yasake, mai maita masa, zuciyarshin zafi yace,
"Mashkur, zan maka abinda zai baka mamaki, matukar baka kyaleni ba"

        sam mashkur be wani damu, ba idan da sabo yasaba ganin haukar duk lokacin da yakora mashi kayan marmarinsa,

      jan center table ɗin da yake falon yayi ya zauna, a nutse yana kallon Maina,
        kauda kai yayi jin motsin yarinyar tafito zata bar gidan, maida hankalinshi yayi kan maina da yake bim ruth da ido ranshi yana kuna,

       gyaran murya mashkur yayi, sannan yace,
"Sai yaushe zaka daina bin matan layi, ina matukar jin zafin yanda kafito babban gida,amna sam bakasan ciwon kanka ba rayuwarka babu abinda kasani sak niman mata, maina Wallahi kaji tsoron Allah, katuba kafin lokaci ya kure maka, kukan kurciya....."

        "Ina ruwanka, eyye toh tsoron zanji Allah maina kafita harkata kayi hidimarka nima nayi nawa, bana son sa'ido ai kaima idan kasame mace ba kyaleta zakayi, ba gwara ni nawa yafito fili, irinku wayasan me kake aikatawa, Allah idan baka daina takurani ba zanje na faɗawa Momma, kana shiga rayuwata."

         Dariya ce takwace masa sosai sannan yace,
"Maina katagum, sarkin gobe ni kuma nayi maka alkawarin idan kaje, ka iya samun momma da wannan maganar, ita kuma ta tambayeni me yasa, nake shiga rayuwarka sai na faɗa mata gaskiya abinda kake na niman mata, muga kozata kara kallonka da mutunci, sannan da ake cewa wayasani ko nima inayi,hmmm ai wallahi idan nace zanyi matan da kansi zasu kawo min kansu, ni ina da mutunci kuma ina martaba mata, bazan iya cutar dasu, kuma bana son tarihin ya mai-maita kanshi akan yarana, Maina ina son kasani gyara kayanka baitaɓa zama sauke muraba ba, kacigaba maina."

     koda yabar gidan maina gidansu ya wucce ranshi yana jin ciwon abinda Maina yake aikatawa, koda yayi parking sai da yakifa kanshi a kan sitiyeri, can dai yafi daga motar yashiga cikin falon, shi da zai bita, kofar baya sai gashi ya biyo ta main falorn, ƴana shiga yasame Ubaida da sauran dangin momma, tunda yaƴi musu sallama yashiga ciki be ɗaga kai ya kalle kowa ba, ta kicin ya fita kofar baya dan yana shiga falon momma zai tarda mutane,

            Kwana yayi da damuwa aranshi har kusan asuba yasamu barci.

              Ranar asabar aka ɗaura auren Muh'd Hassan Muh'd(Mashkur) tare da Amaryar sa Zubaidatu Muh'd Hussain Muh'd.
          Sai  Muh'd Hussain Muh'd( Maina) tare da Amaryasa Ubaidatu Hassan Muh'd,

       biki yayi dan mashkur ba laife yayi wanka, sosai kowa ma haka, a wajen ɗaurin auren duk da fuskanshi a saketa amma kasan zuciyarshi cike take da marmarin Shkurah da muradinta. Baza gane haka dan fuskarshi bata nuna haka ba,

      Bayan ɗaurin auren ne aka tafi, Reception an goge wuya balaifi kan,

     A gida kuwa mata walima suka haɗa, bayan antashi aka kaisu wajen sarki hassan yayi musu nasiha akan zaman aure sosai ya tsoratar dasu,

          Bayan ya gama musune aka kai Zubaida cikin gida, ita kuma Ubaida gidansu daga can aka kaisu gidajensu bayan kowacce tasha faɗa, sosai.

           Bayan ankaisune suka sake shiryawa sai dinner, kome yayi kyau na wajen Ubaida, sanyeta da wani gown purple, Zubaida kuma,Peach colour sunyi kyau, sosai, Mashkur wani suite   yasaka me dark blue, Maina kuwa ashe colour,

        Anyi kome lafiya, a cikin kawayen  Zubaida  sai da maina ya jone da wata yarinya me suna Ma'amurah, ta haɗu iya haɗuwa,
    bayan antashi ne kowani ango ya ɗauki matarshi, ka idar kenan.

Wshi gari..
Akayi buɗan kai, inda Mashkur yafitar da Zubaida kunya haka ma maina ba laifi sunyi abinda ya dace,
Chapter 5 · 0% Book details