← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

      kaf ilahin falon kuka, suke kansu a sunkuye mikewa umma tayi,zata bar falon mommah tace.
"Habiba Abubakar Waziri yola."

     cak ta tsaya, a hankali tasake juyowa, hawayen da bata son su zubo suka kuwa ɓalle kaman an buɗe famfo.
       Umma tace.
"Kausar  Muhmud Elkanami"

    girgiza kai umma ta sake cewa.
"ɗauke shi kutafi shkurah babu ita dan wanda ya bamu ya karɓeta, yayi hakuri, kowani rayuwa akwai jarabawa Allah yabamu ikon cinyeta"

       tana gama faɗan haka ta juya tayi tafiyarta cikin gida yana kuka, sai yau tasan shkurah ta mutu.

     Baki ɗaya network ɗin mashkur ya ɗauke......

Yaseen nima wata ta ɗauke,
Allah sarki mashkuri😔

3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

*Tabbas na yarda da maganan da ake cewa,kayi me kyau zakaga me kyau,Alhamdulillah, tsakanina daku sai godiya reader Allah yau bani da niyyar typing sabida uzurin gabana, Amma sai gashi, sabida ku dan farin cikinku, na sadaukar da lokacina dan na kyautata muku,Allah yasaka da alkhairin*

_Wannan shafin sadaukarwace ga Mahaifiya, ina nufin Uwa tawa taku, Uwayenmu dukkansu, Musamman Mahaifiyata Ubangiji ya gafarta miki, da sauran musulmin baki ɗaya_Allahumma Amin👏👏👏

     '''Swry duk wacce ta min magana taga banyi reply ba,tayi hakuri Saurayin kakata Fatima ne ya rikeni tun jiya Wato network sannan zaku ce toh fa'''😹😹😹

*Page 13*
Ga baki ɗaya yaji, kome ya tsaya masa cak,  mikewa yayi ya ɗago idanunshi wanda sun kaɗa jajuri kaman gaushi, jijjiyar kanshi, sun tashi raɗa-raɗa, sauke idanunshi yayi akan Salmah da take kuka, a rakuɓe a guje tashigo, tana zuwa gabanshi ta ɗauke shi da mari, tasake ɗauke shi da mari durkusa kasa tana kuka me cin rai,
cikin muryan kuka tace, " daman ba sonta kake ba. shi yasa ka zalunceta, anya kai mutune kuwa, kasan zunubin da kayi, kuwa, wallahi koda Bestie tana raye, nasan bazata taɓa yafe maka ba, koda zata yafe maka, sai na hanata, kaman yanda kasasu kuka, kaima sai ansaka, kafita, kabar gidan nan,"

       Inji Aisha Abbas kenan babbar kawar Shkurah. salmah ce tazo ta ɗagata tana kuka, itama ko kallonshi basu sake ba.,

       Baba galadima shi yayi gyaran murya yace.
"Meke faruwa, ne? sannan kunsamu a duhu kifitar damu haske."

         Ashe kuka rahama ce, dan mashkur ya nemi kukanshi ya rasa, kallon baba galadima yayi sannan yace.
"Me kuke son kusani, Maina ya rabani da kome, ada ina kallon kaina kaman ba maraya ba, amma daga ranar da maina, ya ruguza mana, farin ciki nake jin kaman narasa kome na, Idan nace Allah ya wulakanta maina, kaman zunubi nakara yi, Amma mun barshi da Allah, Wallahi ina jin bugun zuciyarta tana raye bata, mutu ba duk inda take zan nimota, zan kawota amma don Allah karku sake cewa ta mutu.."

      Haka yayi ta sambatu kaman mahaukaci, komawa jikin mommah yayi yana ajiyar zuciya, dan babu kuka, babu hawaye sun kafe zuciyarce kawai take.Nata kukan.

                Sarki hussain da aboksn tafiyarsa suka, lallaɓa sikayi musu, sallama dan izuwa yanxun jikin Abba yayi sanyi yasan maina kuma zai iya kome dan ba imanine da shi ba balle tsoron Allah,

     Mommah ta kalle sarki hussain tace.
"Abbansu kaje da shi, ni zan gana da mahaifiyar shkurah Classmater ɗina ce, tun muna, Fggc yola zuwa gobe sai na tawo."

            "Ba kome kausar, kije kawai,amma zan tafi da Son Asibiti dan naga kaman, har yanzun da sauransa." inji sarki hussain.

        Komawa ciki, tayi ta kalle Mama tace.
"Kaini wajen Habiba,"
          part ɗin Umma aka kaita, duk yaranta sun kewayeta, suna zubda k'walla da sallama mommah tashiga cikinsu, tana kallonsu, fuska a sake tace.
"Kimanin shekaru talatin da huɗu kunsan wacece ita," ta ɗago tana kallonsu sannan ta maida idanunta kan Umma tacigaba da cewa.
"Me yasa kika ɓoye musu Asalinki, Habiba me yasa kika baki faɗa musu, girman darajarki ba, kin zauna shiru, idan baki manta ba ranar da muka gama makaranta na faɗa miki babu kyau bijirewa Iyaye, ko baɗe ko bijima, zaki zubda hawaye, Mahaifinki yaga ke marainiya tasa ya bada aurenki ga ɗan ɗan uwanshi Aliyu sarki yola na yanzun,  Mahaifinki yayi miki tanadi. na musaman yaso kicigajiyar zama cikin gidan sarauta amma so ya buɗe miki ido kika k'i, Yau kimanin shekaru talatin da huɗu, bakiyi kuka ba sai yau, a ranar da na miki magana habiba marina kikayi, sabida na faɗa miki gaskiya..."

      Kukane yaci karfin Mommah inda tasa hanunta ta rufe fuskanta, haɗiye kukanta tayi sannan ta kallesu Abubakar tace.
"Kaman yanda kuka sani, sunanta Habiba Abubakar yola, yanzun haka babban yayanta shine wazirin yola na yanzun, kasancewa ita ɗaya ce mace, a cikin maza tara, a cikin gidansu yasa Babanta ya ɗauki son duniya, ya ɗaura mata karkuyi mamakin haka,Ni da Habiba yan uwane, Mahaifiyar Habiba, kanwar Babanane, kuma itama itace , auta agunsu Babana,"

      Jan numfashi tayi, sannan tacigaba da cewa,
Mahaifin habiba abokin babana ne, dan tare sukayi karatu a Oxford university dake birnin london, dansu huɗune, da sarkin katagum na da Da sarkin yola na da,
        Bayan sun gama suka komu kasarsu inda kowa ya dawo jaharsa. Mahaifina tun kafin ya tafi karatu aka ɗaura masa aure da Mahaifiyana kuma, ya tafi ya barta da karamin cikin Bakura, Sarkin yanzun kenan dan haka yana dawowa ya fara aiki a lagos,

      lokaci ya tafi, dake mahaifiyata ba me yawan haihuwa bace, shi yasa muka kasance mu shida, sai sauran ɗakin, Aunty Habiba wacce ake kira da  Yana, tazo wajen babana hutu a lagos, sai akayi dace, Mahaifin  habiba shima yazo, har gidanmu wajen babana, ana yaga habiba yace yana so.
       Aikuwa sanin halinsa Babana be yanke nime shawara ba ya yanke hukunci inda, a cikin satin yabi jirgin kasa sai maiduguri, nan yaje yasamu kakanmu da batundan har yayiwa Abubakar alkawarin ya bashi ya ture magabatanshi, dan lokacin Yana tagama makaranta, kakanmu jin haka, yace ba damuwa,

       Sati na kewayowa sai ga baki daga yola, nan aka basu auren Yana, ganin sutafi su sake dawowa aka ɗaura aure aka kwanakin tarewa, wata biyu.

       Cikin ikon Allah wata biyi ya cika suka kawo kome na bukata, daga nan aka basu ita,
       Yana tana da hakuri sosai, dan haka koda aka kaita cikin manyan mata bata taɓa samun matsala dasu ba,   wata da ta shiga a wata aka sami cikin Habiba, lokacin nima mahaiyata yana ɗauke da tsohon cikina,
         Cikin yana matukar bata wahala Allah sarki ashe ta sanadin Cikin zata rasu, koda cikin yashiga watan haihuwarsa sai ya kasance bata iya barci abun cikin yana zuwa ya tokareta, a haka , har ta shiga kwanankin haihuwarta,
        Ranar da ta haife habiba ko kallon abinda ta haifa batayi ba, ta koma ga mahaliccinta, Abubakar ya shiga wani hali,

         Tsiran tskanina da Habiba kwana uku, dan har Mamata tazo, jijjigar mota yasa nakuɗa yatashi mata, daman Habiba taki karɓan madara, tana haihuwana tace.
"Don Allah ku bani, ita na shayar,"

       ganin haka, suka bata dan har lokacin, Abubakar baidaina zubda hawaye ba,

             Kwanansu Mamata goma, suka dawo lagos inda tacigaba da rainonmu har muka kai yaye, aka ciremu a nono,

       Muna da shekara huɗu, aka samu a makrant, cikin kulawa muka,gaba primary, anan Abbanta yace a maidamun arewa muyi karatun sakandiri.

            Cikin ikon Allah muka, fara bamu taba samun matsala ba har muka isa aji shida anan ne aka turo Hammayo bautar kasa, yola, ana turasu makarnt sai aka turoshi makarantarmu, tunda ya gabatar da kanshi, da kuma yanda Allah yayi masa baiwar kyau yan mata suka mace, akanshi.

        Daga cikinsu kuwa, har da habiba, kaman ba jinin sarauta ba, gashi zuwana lagos Mamata take faɗa min ai amana miji, ni ɗan sarkin katagum ita kuma, ɗan sarkin yola,  ban damu ba dan nasan gidan da nafito, haka ma Habiba, sai dai kashhh, zuwan wannan malamin ya dagula kome,habiba tayi nisa naso ta gane amma taki,  haka na zuba mata, ido dake wani lokacin bama zuwa, lagos hutu, a yola ko maiduguri muke hutunmu,

      Soyayya me karfi yashiga tsakaninsu, nayi nayi ta bari taki,
      Ranar da muka gama karatu ni maiduguri aka tafi dani, ita kuma tana yola bansan me ya faru ba, sai dab bikina nazo wajenta dake za'a riga yin nata, naji wai ta auri ɗan bautar kasa ya tafi da ita bauchi, nayi kuka kaman, idanuna zasu cire.
Ita ta ɗaura muku, abinda ya faru,."

           Juyawa mommah tayi tana kallon Umma wacce take kuka, kaman me, sannan ta haɗiya kuka amma idanunta basu bar zubda kwalla ba, tace.
"Lokacin da muke haɗa kaya, kika ce narabu da Hammayo, har naji haushi na mareki, wallahi na ji zafin marin ke kike kuka amma ni nake zubda hawayen dan nasan gaskiya kika faɗa min, amma so ya rufe min idanun. bayan tafiyarki nima akazo ɗaukana, ana nakewa hammayo kwatancen gidanmu, yace zai zo amma sai na kwana biyu.

    Tunda nadawo nake son faɗawa Baba, amma ina tsoronshi, ana cikin haka, sai gashi, Aliyu yazo dan mu fahimci juna, tashi ɗaya na faɗa masa ra'ayina ina da wanda nakeso.

    Cikin ikon Allah aliyu ya fahimce ni, sosai daga nan ya tafi gida ys sanar da mahaifinsa yanda mukayi, koda babana yaje fada, sarki ya nuna masa alfanun ya bani wanda nakeso dan kar ashiga hakkina, a lokacin Uwar gidan Baba hajiya zainabu, muna kiranta ya goggo, ita mahaifina ya kira ya faɗa mata, abinda nayi yayi masa zafi, sai aka ɗauki kanwata Zaituna, wacce take aji ukun sakandiru, aka bawa aliyu, ni kuwa aka sani na nemo hammayo, ran baba ya baci sosai washe gari ya bada sadakata""

     kukane ya kwace mata har takifa kanta akan cinyoyinta sai da tayi ya isheta sannan tacigaba da bada labarinta.
"Aikuwa a cikin abinda befi awa huɗu ba baba ya haɗa min kayana " yace kije nagode Habiba, amma duk abinda yaameki karki tako min nan, kinji ko"   haka babana ya korone.

     Dan kuɗin da hammayo yake rikewa na abinci dashi yayi mana, kuɗin mota har bauchi daga bauchi muka, wucce misau.
nazata zan same kyakyawan tarɓa sai nasame akasin haka,
      dan koda hammayo ya labarta musu abindaya faru, Innarshi da Babanshi nan suka tasashi a gaba da faɗa inda suke shiga banan suke fita ba, nayi kuka,nayi danasani mara amfani dan haka na haɗiye kukana, aka bamu ɗakin da ke gefen gidan.
Chapter 15 · 0% Book details