← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*........*
Ta bangaren Mashkur da jikinshi da sauki sosai dan har ya tashi kuma, umma ce a wajenshi ya ɗan sake kaɗan sunyi hira jefe jeje,

  Can umma ta kalle shi, cikin nutsuwa tace.
"Ka faɗawa Kausar kuwa, baka da lafiya, naga matarka ma batazo ba ko tana can azare ne,"

dariya yayi yace.
"Umma kina son mommah ta birkice kenan kawai a barta idan nasamd sauki, zan faɗa mata."

         "Toh shi kenan, Allah yabaka lafiya."

*.......*
Washi gari.......
A can gida shirin ɗaurin aure ake, amma asibiti ba haka abun yake ba dan daga shkurah har mashkur, babu wanda ya runtsa kowa da nashi fargaban.

        Abubakarne yazo ya canza umma, dan ta koma gida, yana zaune sai surutu yake, mashkur ya sunkuyar da kanshi baya uhh baya hmm,  karfe sha ɗaya dai rabi aka ɗaura auren, kiran Abubakar umma tayi ta faɗa mashi, ajiyar zuciya yasauke tare da cewa.
"Ubangiji ya basu zaman lafiya, da zuri'a ɗayyiba,Allah yasa karshen wahalarsu kenan"

      addu'a sosai yayi sannan ya katse kiran ya kalle mashkur, wanda ake wayar agabanshi, tsare abubakar yayi da idanun alamun tamvaya, dariya abubakar yayi, yace.
"An ɗaura aurensu shkurah ne"

          lumshe idanunshi yayi, kafin yace.
"Allah ya bada zaman lafiya," daga haka be sake magana ba, sai ma rufe idanunshi da yayi, dan zuciyarshi ta mashi nauyi, tankar a ɗaura masa dutsen warinji.

  *........*

Hankalin mommah a kashe har gida biu,ga jama'a da suka cika gidan, ga kuma rashin ganin mashkur, ɗaurewa take amma ta gama sarewa da zuwanshi..

      Mika mata waya, Zuhra tayi tace.
"Gashi Umman bauchi take kiranki,"

          Karɓa tayi cike da damuwa, tace.
"Habiba, ya naku jama'a da fatan an ɗaura cikin kwanciyar hankali,"

"Alhamadulillah, da fatan kuma haka, daman nakirakine na faɗa miki an ɗaura auren autarki da yarona, don Allag karki hanasu cikar muradin yaronane don Allah ki samusu albarka,"

dariya mommah tayi kafin tace.
"Allah yayi musu albarka amna idan yan kawo amarya sunzo ki haɗasu, akawo min ita bari na sanar da cikin gida."

     kashe wayar tayi, ta aika cikin gidan wato fada, nan akaje aka faɗawa sarki hussain yayi murna sosai, sannan ya tura cikin gida aka faɗa,

      Lokacin da zubaida taji maganar auren mashkur haukane batayi ba dan gigicewa tayi tana kuka da ihu.

*.......*
  A bauchi kuwa abinda, ya faru shine. Bayan na'im ya bar asibiti yaje yasame faruq ya faɗa masa yanda sukayi da Shkurah kwarin gwiwa faruq ya bashi da ya hakura da ita,

       Shine da akazo ɗaurin aure kawunshi da kanin babanshi, suka nimawa mashkur auren shkurah a madadin Na'im abin ya bawa kowa mamaki,  ansa aure da kai an ɗaura da wani mutane da yawa sun saka mashi albarka, da yashiga gurin umma kuwa gaza ɓoye kukanta tayi sai da hawayenta ya zuba, tayi masa godiya sosai.

Asibiti ya tawo, shi da faruq suka shiga gaisawa sukayi, sannan ya zauna a bakin gadon yana kallon mashkur, gani yayi ya ɓata rai yayi ciki-ciki da fuska, dariyar da na'im yake dannewa ne yafito,

        dafa kafaɗar mashkur yayi, yace.
"Kalmar ina sonki ko nace (I love you) word ne masu sauki faɗawa, amma ayukarsu ba kowa yake iyawa ba, sai zaɓaɓe, naga finafinai na karanta novel da hikayoyi akan So, amma banga wanda yayiwa so Bauta kaman kai, ka sadaukar da rayƴuwarka dan Soyayyarka, ko laila majnun, da romeo da julient kashe kansu sukayi, akan so kai kuma, soyayyar kabawa rayuwarka bazan ɓoye maka ba, ko a wasa bazanyi abinda kayi balle a zahirance, kai masoyine na haka kika, dan haka nabar maka lailarka majnun, dan dakai tadace ba dani ba, sai kasake fiskarka dan tunda nashigo kake, hararata, sai kayi hakuri da rayuwa nadai bar maka matarka, indan mutum baeyi dagaske ba, tabbas zaka iya kai mashi nauhi...."

        Dariya suka saka, dukkansu, ɗago kai mashkur yayi, ya ma rasa tacewa  sunkuyar da kanshi yayi.

💋💋💋💋 Nima narasa abin cewa dan wannan irin Sadaukarwa haka.....
3/4/21, 9:48 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*

  '''LOVE AND TOUCHING HEART'''

MAI DAMBU CE

*Page 23*

A can azare kuwa, banda tashin hankali babu abinda Zubaida take, a ranar Abba ya korota,  tabiyo an kawo amarya taci, alwashin sai taga bayan amaryan da mashkur ya aura.
Da wannan tunanin take har suka iso bauchi abin dariya bata san nan gidan amaryarta ba ita ubaidatu tasani amma bata faɗa mata ba, a daren akaita gida a bakin yaranshi tasamu labarin abinda yasame, shi a ruɗe ta nufi asibiti.

*.......*
"Basan ta inda zanyi maka godiya ba, amma zan iya cewa ka ceto rayuwatane dan nasan idan narasata toh narasa farin cikina kenan dan zan rayune amma ruhina da zuciyana suna mace, itace masarafar rayuwata, Idan baxaka damu ba, nabaka kanwata zuhra, saura shekara ɗaya ta gama jami'a amma bazan maka dole ba, idan bata maka ba zaka iya faɗa min nagode." yace masa,

      "Wai waneni, ince bata min ba wallahi farkon ganina dakai ban zata kana jin hausa ba, sai da na lura har da zane kake dashi, a fuska da kuma yanda kake hausa yasa na yarda bahaushene kai, Ai a tunanina baindiye ne ko balarabe, Allah ina sonta koda bata kai kyau ba, balle nasan zata fika kyau."

      Zaro idanun Abubakar yayi, cikin mamaki irin na wasa, sannan ya ɓata fuskarshi yace.
"An fasa, dan nine yake sonta kawai ka sadaukar min da ita shi yafi, dan naga yanda kakewa sirikinka babu ɗa'a nikuwa zanyi ɗa'a da biyayya idan aka naɗaka sarkin katagum a bani sarautar, sirikin sarkin katagum,"

      Fillon dake kusa da mashkur ya ɗauka ya wurga, musu yayi fuskarshi ɗauke da kasaitacciyar murmushi,
            wacce ta karawa fuskarsa kyau duk da kasumbar da yatara, nurse ce tashigo duba, shi taga yanda yake murmushi, take love bird ya sureta😹

         gyara murya tayi, tashiga ciki nan ta shiga dubashi tana satar kallonshi, har ta gama tafito sai cizon yatsa take ina ma itace tasame Gentle guy irin wannan.

          Mikewa na'im yayi ya mika, masa hanun yace.
"Toh bako zaiyi halinsa, inaha Allah nan da wata me zuwa zanzo mu dai daita da ita, inyaso sai ku manya kushiga cikin zance na barku lafiya a kula da amarya dan akwai ciwo a jikinta, sai mun sake zuwa walimar sunan Insha Allah."

       Dariya sukayi, cike da farin ciki da annashuwa suka rabu,
           Sun dan taba,hira da abubakar sannan suka fita zuwa d'akin da maina yake,duk ya cika dakin da wari da d'auyi sai da suka rufe hancinsu wai ma, akwai masu kula dashi, kare masa kallo mashkur yayi cikin tashin hankali da tsoro, ganin yanda take finciko naman gabansa yana ci kuka mashkur yake wiwi cikin tashin hankali, nan ya shiga gyara masa kwanciya,  cikin muryan kuka mashkur yace.
“Kaga abinda kowa yake, nuna maka illar zina ga abinda yasameka, yanzun da wani idanun zan kalle Abba nace masa ga halin da kake ciki fisabilillahi kasan halin da kajefa kankuwa Maina yanzun duba idan Yar da kahaifa tasan abinda ya kashe mata, mahaifinta shine  wannan me make son race ko kataba tunanin xaka bar bayan tabbas kayi kuskure Dan kabar baya da kura.

     Maina kacucemu, ka zalumunce mu, kayi man's gibe, amma xanyi maka alfarma guda d'aya na rikeni yarka tsakanina da Allah zan mata tarbiya me kyau yanda koda taji labarin abinda ka aikata, addu'a kawai xata maka, bazata tsaneka ba, da wannan nake CE maka, Allah ya nufa shkurah ta zama matata, Kai kuma da mask irin halinka, ubangiji ya shiryeku."

      Yana gama fad'ar haka yajuya, ya bar masa d'akin dan matukar yana ganinsa wallahi zuciya zata iya janshi da yawa Dan yau jin kishin shkurah take sosai abinda be iyaba ma, yau gashi bar tsanar maina yake ji sosai ba nawasa ba.

           *........*
Large bakwai da rabi Zubaida ta iso, Asibitin tana wani cika Rana batsewa, kallo d'aya yayi mata tuni tanemi kome ta rasa, Dan wani kwarjini yayi mata, ganinta yasa ya sallame abubakar ya taxi gida Dan shine a gurinsa,

           Abubakar nafita ta mike, tsaye tashigo surfa masa bala'i kanshi yana kan wayarshi, har ta gama sauka yayi daga gadon ya rike hanunta suka fita, sai ward din da maina yake nan ya kaita, toshe hancinta tayi tana shirin amai.

Murmushi yayi cikin nutsuwa, sannan yace.
"Kardai baki game wanda take kwance ba ?, naga kina to she hanci wari ko, ya zakiyi Indan NA fada miki mains ne, akwance nan shi yasa ake son mutum yayi,me kyau  ko rayuwar zata masa kyau kinga dai karshen alawa kasa, karshen tika tiki tak kenan toh yarinya kibi duniya a sannun, wanda yake cikima tana jiranshi balle wanda yazo."

      Yana gama faɗar haka yayi, waje abinsa, ransa na mashi zafi ainun ji yake dama basu haɗa kome da maina ba, dan ya cutar dasu matuka gaya.

   Bayan tafiyar mashkur itama fitowa tayi takira wayan Nana tw faɗa mata, halin da maina yake ciki.

        Komawa ɗakin mashkur tayi, kujeran dake ɗakin taja ta zauna,kuka tasaka masa dan dole ya, tashi ya ɗagota daga kujeran ta dawo kusa dashi. Nan yashiga rarrashinta, tare da magana masu daɗi,

       ganin haka yasa ta narke a ɓ
jikinshi, tana zubda k'walla tace.
"Yaya me yasa, kayi aure baka faɗa min ba, Sannan wacce yarinya ka aura,..."

    "Duk wannan tambayar, ni zan amasa mikisu, kwantar da hankalinki Idan ta tare zaki ganta da idanunki"

         tunda ya faɗa mata haka bai sake magana ba,

*.......*
Tunda na'im yabar, asibinti take nimanshi a waya amma shiru kake ji, abin yayi matukar ɗaga mata hankali bashi babu alamanshi, tuntana boyewa har tayiwa Mama magana, nan ta rufe idanunta tacimata kaniya, sannan ta faɗa mata, yanzun ba da bane, dan da auren wani akanta.

       Haka tawuni sukusuku, har dare, ga faɗuwar gaba, da mugun tsoron dake addabarta.

*.......*
Washe gari...
Aka sallame, mashkur dan nashi da sauki, suna komawa gida yana wanka, ya ɗauki Zubaida zuwa gidanshi da yagina, a can new g.r.a, gidan ya haɗu ba karya kuma abin mamaki, part ukune sai Bq,

      Kome na gidan ashirye yake, daman shkurah yake jira shi yasa yayi gidan amma ba'a tare ba kallon Zubaida yayi, sannan yace.
"Kizaɓe ɗaya, daga zaɓi ɗaya daga cikinsu,"

        Kare musu, kallo tayi sannan tashiga ruwan idanun,dakyar tazaɓe wanda daman shine nata,
Chapter 25 · 0% Book details