Sashe 16
Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da farko zaman ba laifi sai da hammayo ya kuma yola, nashiga cikin azaba nice sarfe, inayi daka sai gari yayi laushi, nice wanke wanke, ashe jin haushinsu da biyune akwai wacce sukeso su bashi ya auroni. shine suka shiga azabta dani, nasha bakar wahala, a hanun Mahaifiyar Hammayo da yan uwanshi da matan yayunsa,
koda ya dawo, na ɗauka wahalarmu xata kare, a'a wani muka sake shin dan ya nemi aiki babu, sai dai kwadigo. Shi yatafi gonar mutane aiki, nikuma nayi sarfe da daka,sai kace ba yar gata ba,. Ina ganin wulakanci iri iri, ga gori, na rashin haihuwa,
Shekaranmu ɗaya da rabi, na haifi, sadeeq sunan mahaifins yasa min, watan sadeeq goma sha huɗu nasame cikin fatima, kuka kan nayi har nagodewa Allah, dan lokacin kome ya dagule min, ga Hammayo, yana shirin juya min baya. cikin ikon Allah na haifi fatima, kayan sadeeq nake saka mata dan ko suna ba'ayi ba,"
Kukanta ya tsananta amma haka tacigaba.
"Fatima tana, da wata goma, nasame cikin hamdiya,, naga tashin hankali da gori, har Allah ya sauke ni lafiya, kafin suna na tattara kuɗaɗen da na tara, na haɗa, sannan ta rubuta, wasika, zuwa ga sarkin yola, inda naje har gidan sarkin misau na nime agaji, akaiwa sarkin yola akawo min, agaji ina cikin gararin rayuwa,
Sarkin misau ya tambaye matsala nace masa babu ni dai akaiwa Sarkin yola,
Allah sarki. a cikin satin aka kai sakona dan ko hammayo bai sani ba,
da sakona ya isa, sarki yasa Aliyu, ya karanta masa sai da suka zubda hawaye sabida halim da nake ciki."
ɗago kai tayi tana kallonsu, wani murmushin yake tayi sannan tace.
"Kuma sabida ku, na sadaukar da farin cikin mahaifina dan rabonkune yasa na bijire masa, akan idanunku ake dukan Shkurah babu wanda ya ci ayi hakuri sai da nace zan tafi sannan shine kuke cewa ai.hmmm.!
Aliyu aka tura yakira babana, bayansun gaisane ya mika masa wasika ya karanta shiru yayi jikinshi a sanyaye sarki yace,.
"Kaji halin da take, ciki idan zata ci abinci sai tayi daka da sarfe, yarka ka maida ita baiwa, suturan da zata saka sai ta ɗinka da zare da allura, haba Abubakar kayiwa Ibrahim adalci kuwa, idan yaji kayi watse da yar kanwarshi, dan haka nake shawartaka da kaje kaga halin da take ci,"
Haka kuwa, ranar da akayi suna washe gari sai ga babana lokacin na fito ina daka, naji dirin mota, ta danga na leka sau naga babana a hankali nafita ina kuka, ina zuwa gabanshi na zube ina rokonsa da ya yafe min ɗaga ni yayi yana, kallon yanda na koma, kaman sabuwar halitta duk na tsofe, alkyaban jikinsa yacire yasame yana kallona idanunshi yana zubda hawaye.
Yace"
Habiba kece haka."
Sai ga mahaifin hammayo, yayiwa Babana iso cikin gida, nan aka shiga hidima dashi be cikome ba daga garesu sai kallonsu yake dake ana tashigowa gaidashi. har inna kallon kayan jikinsu yayi da na yaransu, sai yaji hankalinshi ya tashi kallon baban hammayo yasakeyi, sannan yace,
"Malam bilal, nayi mamakin ganin Habiba, haka sai kace mahaukaciya,, dubi suturan jikin ta da na sauran mutane, kasan inda tafito kuwa, kasan wazata aura ɗanka ya hure mata kunne, da tabi zaɓina da bazatayi kuka haka ba, kai a cikin yaranka mata, akwai wacce take surfe kafin taci abinci, amma ba kome ita tajowa kanta,"
Sai lokacin, Hammayo ya shigo, ya kalle cikin nutsuwa, sannan ya kalle Baban hammayo yace.
"Sabida ya aurota, dai dai niman aiki idan yaje kai kake hana , a ɗauke shi, ko sabida kar yazo ya ciyar da ita, bayan auren da kayi masa toh kasani Akwai Allah,"
sannan ya maida kanshi zuwa ga hammayo yace.
"Akwai gida a bauchi, a gwallaga, zaku iya komawa can sai ka fara aiki a can, sannan ga amanar y'ata duk abinda kayi matukar na zalimcine Allah ba zai barka ba. muje ni yanzun zan koma,"
Fita sukayi har da ni ya saka aka sauke kayan da ya kawo min ɗaukar yarana yayi yana saka musu albarka, sannan ya cire wasu takardu ya mika min, yace.
"Akwai check na banki, akwai takardun filaye nasaya miki jiya sai kuma wasu shaguna har guda shida, akwai tsabar kuɗi masu matukar yawa kafara kasuwanci sannan nasama maka, aiki, ka rike min y'ata ka rike min yata ga amanar yata, mika min Hamdiya yayi, sannan ya tafi yana me zubda kwalla, kwashe kayana nayi nasaka a cikin ɗan ɗakina nashiga tsabga gaba, sai a lokacin kunya ya kama Babanshi ya har bakin kofa yana bani hakuri,
Har da matan gidan masu kirana da me farar kafa, duk suka ji kunya,
satinmu ɗaya muka dawo bauchi da ni dashi da Mama, daga nan kome ya fara zuwa mana, cikin kwanciyar hankali, ina da cikin Aisha ya auro Ummi , wacce itama muna tare, bayan a hankali na koma karatu dan babana ya roke shi, lokaci da akayi jarabawar sharan fagen shiga jami'a har dani a ciki, kuma nasamu point, nan na ɗauki Psychology, a cikin shekara hudu na gaba, ina shirin ajiye karatu nasame labarin mutuwar babana, inda naje, yan uwana suka min koran kare,dan haka ina dawowa, na koma degree na biyu, ina da shekara guda na sake haihuwan inda na haife shkurah Mama ta yafi salma Amarya ta haifi rafi'a,
koda nagama ban sake komawa makaranta ba,
Duk lokacin da natuna rayuwar da nayi, akanku nakan sake godewa ubangiji, laifina na bijirewa iyayena yasa shkurah ta fuskanci Rayuwa,"
Duk ɗakin kuka ake, sabida tausayin umma taga rayuwa sake kallon Mommah tayi tace.
"Wallahi ranar da nafara ganin mashkur naji,ina kaunarshi da shkurah,ashe jinina ne shi,sai dai kashh koda shkurah tana raye haɗi ba zai yuba, sabida wani dalilin."
"Menene dalilin da haɗin ba zaiyu ba," inji mommah.
Nan Umma ta faɗa mata, abinda ya faru, jikin mommah har rawa take kiran Ubaidatu tayi ta tambayeta ina Maina, shiru tayi sannan tace.
"Mommah baya kasan, dan kusan wata uku kenan da barin kasan,"
" Amma, kinsan abinda yayiwa ɗan uwanki kuwa" inji mommah,
"Eh nasani, mommah nima dan kar na ɗaga miki hankaline amma ya jima sa sakeni kuma, kowa yasani keda Yayane baku sani ba, don Girman Ubangiji karki sa shi ya rabu da, Zubaida yaya yana niman wacce zata kwantar masa da hankali kuma , tayi iya don Allah kiyi hakuri"
Dan dole mommah ta kashe wayar umma ce ra shiga bata hakuri da karta shiga tsakanin mashkur da Zubaida.
****
Sun isa kd da, tsakiyar dare idan hajiya umaima yayi parking ɗin motar nan yafito da ita, yashiga da ita, sake fito da ita sukayi inda suka nufi asibiti da ita, prvtne asibitin am basu kulawa, na musaman.
Sai da tayi wata huɗu me kyau sannan ta farka lokacin cikinta yakai wata bakwai sai dai likita ya tabbatar musu, ta manta kome, nata, dan haka yanzun kome nata sai an koya mata, Umaima taso a zubda cikin amma likita yaki kuma koda yay, yunkurin haka, sai ya ɓuge da barci shi yasa ya hakura.
Cikin na shiga wata tara, aka cire itakam bata sam meke saka cikin girma ba, gidan marayu Umaima takai Yarinyar me kama da Ubanta, kaman an tsaga kara (Boss maina kenan mutane U.S)
Umaima taci buri akan Shkurah wace tasaka mata Preety, da kanta tayi jinyarta har ta warke, tunda ta koma normal, nan tashiga tsara yanda zata ci kuɗin akanta kayan mata tashiga loda mata, hardasu dilke, kafin wani lokaci shkurah ta goge, ga shigan banzan da ake koya mata rashin kunya da futsira Mutumin, na farkon da ya fara ɗaukar Shikurah gaskiya, shkura ta zama irin yan gayun nan, ga kyau ga class, dan yanzun haka, tafiya suke wani yauki take da jan hankali duk ya susuce dakyar suka isa hotel ɗin tundaga bakin, kofa, ya fara matseta, suna shiga kuwa suka zube akan gadon, nan ya shiga rabata da kayanta, yana arba da kirjinta ya kaikanshi wani, mugun barcine yayi gaba dashi, tashi tayi ta faɗa ban ɗaki ta sake ruwa, haka kawai ta tsinci kanta da kuka, yaune ta fara fita, amma ta tsani abin kuja take tsakaninta da Allah, fitowa tayi ta saka kayanta tafita, tana kuka, haka ta isa gida babu wanda san ta dawo
Bayan shekara huɗu, shkurah wani irin gogewa takara girma, dukda gogewarta tsakaninta da yan iska shafe shafe idan suka matsa toh karshe barci sukeyi, Hajiya Umaima tayi kuɗi a jikin shkurah dan manyan mutane suke fita da ita, amma tsakaninsu😹😹😹
****
Sannun a hankali lokaci yaja sosai cikin shekara hudu kome ya faru, Mashkur ne zaune a ofis ɗinshi yana ta aiki, a computer, ya jima sannan ya mike ya haɗa kayanshi sai gida fuskan nan ba yabo ba fallasa.
Gidanshi ya koma, tundaga bakin kofa yake jin zazzakar muryanta tana ihu da kiran Daddy Daddy, da sauri ya shiga ya sameta tayi kuka idanunta sunyi jajur yar mashkur yarinya me kimanin shekara uku, ɗaukarta yayi yace.
"Shkurah me ya faru kike haka ke dawaye"
turo baki tayi, gaba tace.
"Nida Mahne ta hanani shan bobo, wai batason wanca aunty me sunana" tayi point ɗin babban Hoton shkurah wanda aka ɗauketa ranar saukarsu,
murmushi, yayi sannan yace.
"Manta da ita, mukan muna sonta ko," sauke ta yayi ya taka har wajen yana kallon hoton fuskasa ɗauke da murmushi kaman yanda take murmushi yace.
"Kina ina, ne nasan kina raye, yaushe zaki dawo gareni, oo, okni nazo kenan"
tsaki Zubaida tayi, tace.
"Romeo sai muje kacire kaya, kazo wajen gunkinka ne, karka damu ta jima a kasa dan tsutsa sun gama wantadarta"
Shiru yayi, yana kallonta.
****
U.S.A
Kanal muh'd Hussain Muh'd a gaban ogansu, yace.
"Muh'd zamu turaku siriya, kuma muna son aiki me kyau, bamu son wasa, katabbatar ankai harin wuta tasama da takasa zaka iya tafiya."
sarawa oganshi yayi, yafita wani murmushi, ogan yayi, sannan yace.
"Nasan yanzun, kakusan mutuwa, saura kaɗan zan gama da kai very soon"
Fita yayi zuciyarshi ba daɗi, kusan sati biyu kenan, yake fama da wani mugun mafarki, gashi yana ganin iyayensu suna gudunshi sai, watsar da mafarki yayi ya shiga mota.