← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 29

Sashe 24

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......
Ruwan sanyi kalau, ya watsa mata wani ajiyar zuciya tayi ta buɗe idanunta sai akan maina,
       hawaye masu zafi suka sauko mata daga idanunta, cikin rawan murya ta ɗago kai tace.
"Me kake bukata, kuma a rayuwata me yasa bazaka barni haka ba, me yasa bazaka barni na karasa sauran rayuwata a haka ba, Maina kabarni hakw don Allah."

       Wani kukane me cin raine ya kwace mata,

     Janyo kujeransa yayi, zuwa gabanta ya zauna dab da dab da ita, yatsar hanunsa yasaka akan lips ɗinshi, yace.
"Shhhhh, kiyi shiru ya isa haka, nima sonki nake shi yasa nazo a wargaza auren, ina son ki haifa min kyawawan yara masu kama, dake kinga ni bazan cutar dake ba, ga Yarana a nan idan wanca sha-sha-shan yazo sai yazama waliyina ke kuma wani daga cikin yarana yazama naki, idan kuma kika ce a'a" juyawa yayi
        yakalli wani kwai wuta, sannan ya maida kanshi gareta, tana kallonshi jikinta na rawa, cikin idanunta ya kalla sannan ya ɗaga hanunshi kafin ta kalle inda ya saita hanunshi sai karan harbi taji ba karamin razana tayi ba, rike kanta tayi cikin tashin hankali tana kuka,

"Idan kika kuskura kika ce bazaki aureni ba, haka zan fasa kan wanca banza i don't care, kin fahimceni ko"

        ɗago kai, tayi cikin rashin kunya tayi dariya, tace.
"Kayi kuskure Allah, daga kai har shi baku gabana, dan jirgin da ya kwasoku bansan shi ba, balle kuma wai,"

      dariya yayi sosai, kafin ya kalle ɗaya daga cikin yaranshi yace.
" ɗauko sillytap karufe mata baki, kince baki damu dashi bako, ok bari mugani idan da gaskene, kurefe mata baki sannan ku ɗaureta akan kujeran, mu zuba ido mugani."

  *.......*
Suna shigowa, gubi dam daman da jirgin ruwansu suna zuwa suka fito da shi, aka sakashi take suka tada inji,

Tafiya a cikin ruwa, cikin minti 30 suka iso wajen ingiza keyar shi har cikin wajen, daga nesa ya hangota, tana ganinshi ta fara girgiza kanta, cikin saurin tana nuna masa bayanshi dakanta, tana kuka har da bubuga, kujeran da take tana kuka.

       Kafin ya iso gurinta, duka aka sake masa akeyarshi wanda yaja, yayi mugun faɗuwa jini nafita ta bakinshi da hanci, rike kanshi yayi cikin azabar zafin da yake ji kaman kanshi zai cire,

         Sillytap ɗin maina yacire yana dariya, kuka take tare da ihu,

       "Maina wallahi wutarka, daban take kai devil ne, acikinsu kai ogan shaiɗanune Wallahi sai kayi mutuwar wulakqnci" take faɗa masa.

       Murmushi yayi, rike da karfe da yabugawa, Mashkur yana kallonta, ɗagawa yayi zai maka masa tace.
"Don girman ubangijin karka taɓashi ka barshi haka, maina kana tunanin mutuwa kuwa, Maina mashkur bai deserve kake mashi ba, Maina zokayi abinda zakayi min don Allah karka taɓashi."

       Cikin kuka take, maganar tana bubuga, kujeranta.

        Dakyar mashkur yake iya buɗe idanunshi, maina natsaye akanshi ɗaura masa kafa yayi akan kafaɗar mashkur,

          dariya maina yake yana kallon shkurah yace.
"Hhhhhh, kekika ce baki son mashkur yanzun kuma kice min, kar na dakeshi, toh faɗa min, kina sona,"

        saka kafarshi yayi ya duke fuskar mashkur.

      "Maina ban sani ba, nidai kabarshi kawai ko ina sonshi ko bana sonshi, ɗan uwanane kuma kaima ɗan uwankane maina kana da imani kuwa, da kana dashi ba zaka taɓa dukan mashkur ba na amince ina sonka kabarshi don Allah."

"Ina ai mutuwa itace, abinda yadace dashi,"

      ɗago kwalar rigar mashkur yayi, yace.
"Kalla akan idanunka, zan sake mai-maita abinda nayi mata shekara huɗu da suka wucce, sannan na harbeku baki ɗaya,"

      tunkuɗe mashkur yayi ya faɗi,

            Gurin shkurah yaje ya kifata da mari biyu sai da ta faɗi kasa sannan ya ɗagota, yashiga kunce mata ɗaurin da yasa aka mata,

    A gefen mashkur agogon hanunshi ya duba, sannan ya fara kokarin mikewa, dakyar ya durkusa akan gwiwarsa, sannan ya mike, haka yayi dai dai da kunce ɗaurin da maina yasa aka mata, tureshi tayi da gudu taje gurin mashkur,

             Cikin tsananin fusata, maina ya mike ya suri bindigar jikinsa yasaita da niyar harbin mashkur, sai a kafaɗar shkurah har sau biyu,

         Ajiyar zuciya tayi ta zube a jikin mashkur,

         Ganin yasaɓa saiti yasake ɗaukar karfen da ya bugawa, mashkur ya tunkaresu gadan-gadan yaɗaga, ashe akwai wayar wuta wacce ba'a rufe bakinta ba, aikuwa ya haɗu da karfen k'am ya k'ame, wuta tana wasan kura da shi.

(Yau kam naga masu farin ciki irinsu Aunty dada nasari Sadiya zabura, Mommy sayyed Asma'u da sauranku ni natafi zaman jinya maina)😹😹

       Allah sarki, ture kan shkurah mashkur yayi, ya shiga niman abinda zai taimakawa maina da gudu ya isa gurin kujeran da ya ɗaure shkurah, ya maka mashi ya faɗi can gefe guda yana, fizge fisgi,

        Karan harbi mashkur yayi ya kwanta sabida bullet yana shigowa har cikin wajen,  a waje kuwa, cikin sa'a yan sanda suka kashe yaran maina, dan sunki a kamasu saima buɗe musu wuta da sukayi dole yasa akayi musayan wuta, tsakaninsu.

Wasu yansanda suna waje,Na'im tare da Abubakar suka shiga, cikin da wasu yan sanda ganin mashkur sukayi ta ɗauko shkurah a hanunshi dan bata numfashi, haɗa hanya yake da sauri na'im ya isa zai karɓeta ɗago kai mashkur yayi ya kalleshi, ya kuma kalleta, sai ya mika masa ita,

           Na'im na amsarta shi kuma, ya nemi faɗuwa Abubakar da, wani ɗan sanda suka rikeshi aka fito dasu sai satar kallon na'im yake, sau biyu dai na'im yana kamashi, haka da ya gani yasa jikinshi yayi matukar sanyi,

        sakasu akayi a jirgi, sannan aka haɗa maina da yaranshi waje guda, har lokacin bai bar fizga ba.

          Dole aka bar wasu a gurin suka tawo dasu mashkur, ana tsallaka ruwa aka sakasu a mota, sai T.h,

      Sannan aka koma, kwaso su maina,

*.......*
Abubakarne yakira umma, ya faɗa musu kafin wani lokaci asibiti, ya cika da yan uwa, da abokan arziki, Allah sarki umma bata nemi shkurah ɗakin Mashkur taje ta zauna, inda kusan manyan likitotine aksnshi.

         Tabbas mashkur ya daku, dan tattaunawar da likitotin suketayi kenan akanshi, sun kwashi awa uku, kafin suka fito suna magana,

        Umma na ganinsu ta mike idanunta dab da kwalla tace.
"Zan iya ganin yarona kuwa"

      "Eh madam amma don Allah banda hayaniya dan ana son ya wuta," suka ce mata,

dasaurinta tashiga, tasame shi yana barci zama tayi a gurinshi,

Ayya maina, an kawo shi, nan dai sukayita kokarin ganin, ya dawo amma ina, saukin sai a hankali

😂😂😂😂😂😂😂😇 Allah idanuna yake hanani dogon typing, Amma insha Allah kome ya kusan kammala

Team ɗin Maina Shkurah ina gaisheku tare da
Team Mashkura ina muku fatan alkhairi ana tare.

_Wata tace Kamata yayi nasaka Love and touching heart story karkuyi tunanin karanbanine a'a gyara aka min shi yasa na antayo muku.💋_
3/4/21, 9:48 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*

*LOVE AND TOUCHING HEART STORY*

MAI DAMBU CE*

*Page 22*

"Na'im zan baka shawara a matsayina na abokinka, idan zaka iya kahakura da shkurah Allah ba matarka bace, ka dubi ƴanda ya bada rayuwarshi dan nata, kai koni akace nayi wannan kasadar Allah ba zanyi ba, dan akwai mata da yawa a duniya karewa ma ba ahaifi uwar watq ba shawara kayi hkr ka bar mishi ita." inji faruq kenan abokin na'im,

      Shiru na'im yayi, yana nazarin maganar Faruq, ɗago kai yayi cikin karfin hali yace.
"A'a ni bazan barmashi ita ba har sai naji daga bakin shkurah shin meye ya shiga tsakaninsu haka da taki aurenshi."

       Dariya faruq yayi, kafin yace.
"My guy karka wahalar da kanka, ka janye kawai shine gaskiya, amma tunda kace haka ina jiranka, malam majun."

      Sun daɗe suna tattaunawa, akan abinda ya faru.

        Shkurah kan dakyar aka cire mata bullet ɗin, dan ji jiki sosai sai kusan asuba ta farka tana rarra raba idanunta, a ɗakin da take Aisha ce ta matso kusa da ita tace.
"Sannun ya jikin ina ke miki, ciwo."

"Adda ina mashkur yake?"

      tana kokarin mikewa daga kwanciyar datake, shiru Aisha tayi kafin tace.
"Meƴe matsalarki dashi, tunda hankalinki ya kwanta sabida ke, ya rasa..."

         "Isa!!! haka barni da ciwon dake damuna, karki kara min wani akai..." tana gama faɗan haka tajuyar da kanta gefe ta fashe da kuka, mara sauti ita kaɗai tasan halin da take ciki,
    har gari ya waye, bata daina kuka ba, shigowan Na'im ta haɗiye kukanta kallonta yayi cikin nutsuwa yace.

"Preety kukan me kike? ko kinji wani abu yasame mashkur ne, da kike kuka."

       D'ago idanunta tayi takalle shi, sannan ta aro dariyar dole akan fuskarta tace.
"Haba ina, ruwana da wani can, kawai hannuna ne ya dameni da zafi yasa nake kuka, amma babu kukan da nayiwa wani kato."

    Kallon cikin idanunta yayi, abinda bakinta yake faɗa daban, wanda idanunta suke faɗa dabam, murmushin yake yayi kafin yace.
"Ai kuwa, naji labari mara daɗi akan ciwon da yaji,dan likitoti sunce yasame matsala akanshi brain ɗinshi ya taɓu bazai wani jima zai mutu, kuma hankalina zai kwanta dan bani da wanda zai damar min mata a tunani."

A tsorace ta ɗago kanta, bakinta na rawa kansan wanda akace kuwa, mashkur ko maina, waye ya same matsala a brain ɗinshi."

        "Ooo maina nake nufi ba mashkur ba, kinsan sunan sune kusan iri ɗayane amma ya naga kin damu daga maganar mashkur, ko kina sonshine na janye."

        Tsareta yayi da idanun, ɓata rai tayi cike da borin kunya tace.
"Ban gane ba, mana zargina ne idan da ina sonshi da tuntuni ina gidanshi, bana son haka karka manta ɗan uwanane, da kake wannan maganar."

"Kenan kina sonshi? kike kokarin ɓoye emotion ɗinki akanshi Shkurah ki fada min me ya rabaki da shi, yanzun kuma NA hango sonshi a cikin idanunki ni mutum ne meson adalci idan kika min wallahi ashirye nake namiki, common fada min"

       D'ago kanta tayi duk kokarinta da taboye hawayenta amma ta gaza hanasu saukowa, a hankali tashiga bashi labarinsu.

         Har izuwa yanzun, jinjina kai yayi kafin yace.
"Hmm, Allah yasa mu dace zan tafi, kinsan gobe za'a ɗaura auren anso ɗagawa nace ayi haka muje ki karasa jinyarki agidana, da fatan banyi garaje ba."

     Girgiza masa kai tayi alamun a'a, yana fita ta fashe da kuka, tarasa meke damunta sai zuciyarta babu daɗi.
Chapter 24 · 0% Book details