← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 29

Sashe 14

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Suna gefen hanya ne wani wak'iya ta runtsa da motoccin wajen dan wata tankar mai ce tazo wuccewa tsawa ta faɗoasa, take tankar ta fashe man ya tarwatsu a ko ina dukda ana ruwa, tare ya kama motoccin da suke wajen, tashin hankalin, nan motar mutane sukai ta kamawa da wuta, har da motarsu shkurah ayya ganin haka driven ya ruɗe ya shiga rubass ya juya yayu karo da da wata mota nan yayi, nan motar ya fara dungure yana kamawa mutane ciki suna ihu, can cikin daji motar ta tsaya duk glass ɗin motar ta farfashe, sannan takama da wuta, dan ma anan ruwa,

                 A can titi ana tacire mutane a cikin mota, sai da sukq ci karfin na waje sannan suka faɗa dajin dan ceton na cikin wancar motar duk sun kone.

            haka aka janyo motar sai lokacin yan sanda suka iso wajen,

      suna bincike, suna gamawa, sukafito yaje da niyyar yin fitsari yaji nishin mutum yana lekawa yaga shkurah a kance tana fitar da numfashin wahala jini nafita ta hancinta murmushi yayi yace.
"Lady kinyi samuwa,"ciro wayarshi yayi daga aljuhun rigarshi ya latsa kiran,

     "Uban me zan maka corpru bala ince na biyaka kuɗin" inji lady kenan.

     murmushi yayi yace.
"Shegiya uwar karuwai samuwa na miki. wannan karon kuɗi nake so, kizo hanyar kaltigo ga kaya nan musu kyau amma zamanta a gurinki na da hatsari, zan bar miki alama, zan tsinki ganye na zuba a wajen da haka xaki gane."

     ***
Indian Hospital.....
Karan nauran da aka saka masa ne yayi kara alamun numfashinsa ya hawura sama da casa'in da tara. lokacin Momma tana rike da karamin alkur'ani tana karanta suratul yasin, da gudu, drs suka nufi ɗakin.

         Nan aka shiga bashi kulawa sujadan godiya Mommah,

  bakinshi ne yaketa motsi yana magana, dr Lakshman ne yakai kunnenshi jikin bakinshi, sai ji yayi yana faɗin " shkura"

***

       Daukar nombar motar sukayi sannan suka kai station nan aka kira tashan yankari aka faɗa musu motarsu tayi hatsari, kuma duk mutane ciki sun mutu.

       Umma tana zaune a ɗakinta, aka kira bilal dake nombar wayarshi ya bada nan aka faɗa masa muguwar sako.

            Falon Alhaji Hammayo yaje, duk da mutane, duk ya barki ce, sai zufa ne yake karyo masa kallon sadeeq yayi yace.
"Bros pls zo mana"

      tashi yayi yabi bayanshi, nan ya faɗa masa, salati ya tare da tashin hankali ya shiga falon duk da bilal yana ce masa karka ɗaga musu hankali, ina yana shiga falon yace.
"Baba shikenan, shkurah ta rasuuuuu"

             Cikin tashin hankali Alhaji Hammayo ya mike, sai kuma ya koma ya zauna ya rike kanshi ya fashe da kuka,

             mutane da suke falone suka fita waje nan suka fessa.

  Take  gidan biki ya koma gidan zaman makoki, a nutse mama tashiga ɗakin umma ta jima sosai sannan ta fara kawo mata, ayoyi da hadisai can tayi shahadar kuda ta faɗa mata, tunda ta sauke kanta, tare da ajiyar zuciya ta ɗago tayi kalle mama sannan tace,
"karki damu Allah da yabani ya amsheta toh me ye nakuka, wallahi bana jin kome, akan mutuwar sai ma shakkun da nake........

🙆 _Kowa shafi yana da nashi damuwar ina ganin zan hakura da buk ɗin baki ɗaya dan nasan yana saku kuka ni kuma bana son haka kuyi hkr sai naji daga gareku_
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: *QADDARAR RAYUWATA*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu
Litattafan da Na rubuta👇
*Yaro ma namijine*
*Kishiyata Jahadina*
*Wani  Al'amarin*
*Ni da Yaya Muh'd*
*Wani Jinkirin*

'''Kunsan kowa na da ra'ayinsa akan suna, ba wai bana son asalin sunana bane a'a Sunan Me Dambu sunane da yake da daraja a guna, kuma sunane da bazan taɓa mantawa da shi ba, Dan haka yau ɗaya nayi amfani da sunana, da kuma sunan Buks ɗin dan ku, ba dan kaina ba, Ina muku tafan alkhairi'''
*ILOVE YOU ALL*💋

'''Cigaban bayyanin Imam zubairu madaki, Tambaya ce guɗa ɗaya jal kafin na ɗaura sauran bayyanan.   malam yace idan kakori ɗa namiji ina da karfi zai iya fafutukar ya tsaya da kafarshi.
Idan kakori Y'a mace daga gidanka a matsayinka na Uba... Ya zatayi?
        da wannan tambayar ya rufe tafsirin yace yana jiran amsar a gun iyaye maza da suke cikin masjid Umar bini Khaɗab.'''

Shin kina karanta buk ɗin asa ke Ubace ga tambaya da malam ya jefa muku amsa na gareku, tunda ga Alhaji Hammayo ya kori Shkurah daga gidansa👌

*Page 12*
Sai gashi umma itake rarrashin y'an gidan lokaci guda kome ya k'wauɓe a cikin gidan biki, Alhaji Hammayo kuka, yake tsakaninshi da Allah inda yayita k'washewa Aunty Amarya albarka, har kofar ɗakinta yaje yana tsine mata, karshe dai ya haɗa mata har da saki,

            Karin tashin hankali, umma ta tubure masa da ya dawo da ita kan y'ay'anta ko tafita tabar masa, gidanshi.
Zubawa Umma idanun yayi yana rike da kirjinsa, dakyar yaje sauke numfashi durkusawa yayi cikin tashin hankali ya faɗi,kasa yana tari jini yana fita daga bakinsa, haɗi da yawun me yauki.

           Nan akayi kanshi cikin tashin hankali, akayi ni'ima dashi.
         _Saurin fushi yana kawo danasani,yanke hukunci cikin fushi, yana kawo nadama mara amfani._

        ***
Kaltingo,kaman yanda corpru bala yayi mata k'watance haka, kuwa tasame Shkurah. Cikin mawuyacin hali, cikin gaggawa aka ɗauketa zuwa, gidanta da yake cikin kaltingo, takira likitan da yake cirewa y'an matan da suke ɗauke da ciki, a cikin yaranta da suke harkan zaman kansu.

         Duba shkurah yayi sosai, sannan yace mata,
"A gaskiya lady wannan yarinyar, zamanta a cikinku akwai hatsari, dan ki dubi zanin jikinta da ɗan kunnen kunnenta, haɗi da, kidubeta da kyau y'ar manya ce, ba yar kananun mutane, bane kisan yanda zakiyi da ita."

          Murmushi tayi sosai, sannann ta gyara zamanta tace.
"Idan na turata kaduna gurin, kawata Umaima, ina ganin kaman babu matsala, ko?"

          "Eh duk yanda kikayi,dai-daine, zamanta a nan,me dai akwai damuwa." yace tare da hada kayan aikinshi yafiya.

             Cirewa shkurah kaya tayi, sannan tasake mata wasu,kiran drivent tayi tace.
"Ga yarinya nan, zaka kaimin ita, kaduna, na yarda da aikinka, katabbatar, kun isa lafiya yanzun, zankira Umaima, a waya."

     Yana tsaye takira,umaima ringing biyu ta ɗauka, lady tace.
"Ga kaya nan zuwa, wannan darajarta yafi ɗaya da rabi, dan nima sai na biya, wanda ya kawo min ita.Sannan nima nacire iya abinda zan bawa driven zai kawo miki, ki kula dan akwai damuwa a tattare da kayan. katse kiran tayi, tana murmushi,

          A bayan mota suka. Sakata, sai Kaduna.

***
Cikin ikon Mashkur ya farka, nan likittoti suka rufa akanshi, inda suka cire duk wani naura dake jikinshi,
          A hankali abinda ya faru yashiga dawowa, brain ɗinshi siraran hawaye kebin gefen fuskanshi.
         Dr Lakshman ya kalle dr Ajay yace " maybe is love problem,"
   ɗaga kafaɗa, yayi alamun  haka, ne cigaba  da aikinsu sukayi suna gamawa suka juya wajen Mommah suka ce mata.

"Congregation mah, ɗanki ya tashi mungodewa Allah dan shi yabamu ikon haka,"

       Haɗa hanunsu sukayi guri guda, kaman yanda saka saba al'adarsu.

       Murmushi tayi sannan itama ta haɗa hanunta tace.
"tabbas Ubangijine ya bashi lafiƴa, ta sanadinku ina muku, godiya akan namijin kokarin da kukayi akanshi Allah yabaku sa'a akan aikinku mungode"

          Murmushi sukayi sannan suka fita suna girmama karfin tauhid mommah.
     Ba dole ba,yar borno ce idan bata, san tauhidi ba ai a tambayeta.

     Kwananshi biyu, ya warware, magani nurse take bashi tunda yasha ya kafe mommah da ido, cikin sanyin murya yace,
"mommah don sonki da ubangiji, ki maidani, gida ina son sanin halin, da Shkurah take ciki."

           Shi tayi tana nazarin maganarshi, tasowa tayi tazo har inda yake,

        shafa kanshi tayi, tace.
"Insha Allah, jibi zamu koma gida,kaji kuma, muna komawa za'a nima maka auronta, kaji ko My son"

       Kwantar da kanshi yayi a jikinta, zafin kirjinshi yake masa, amma baya son yasake ɗaga mata hankali, dan yana faɗa zata iya ɗaga tafiyar. idan ya tuna Maina, ji yake kaman ya ɗauki Ak47 ya juye masa, duk bullet ɗin ciki, ak'ok'on kanshi, haɗi  wani yawu me matukar ɗaci yayi.Yana kisima yanda idan yaga Maina zai masa, dukan kisa,

          A cikin kwanaki biyu, su mommah, suka tarkato sai gida bayan Drs ɗin sunce duk bayan wata uku, yazo ana dubashi.

      ***
  A ɓangarensu Alhaji hammayo toh, akwai alamun nasara, sai dai, lokaci guda yasame mutuwar, ɓarin jiki, wato paralyze amma kome da sauki, wheel chair aka bashi.

  Rayuwa kenan.

      A ranar da shkurah keda kwana biyar da rasuwa, (inji mutane) a rana aka sallamo alhaji hammayo, suna zuwa ko minti goma basuyi ba, Mashkur da tawagar Sarki da suka je tarɓanshi, suka tawo gidansu shkurah.

         A hankali ya fito daga motar sauran mutane suma haka, Mommah da Nana, suma suka fito, shi yayi musu jagora zuwa cikin gidan, tare da sallama.

      Suka shiga bilal da yake, ɗakinsu shi ya fara fitowa, sabida jin muryan mashkur yasa ya fito ya gani ko karya kunnenshi yake masa.

  Yana ganinshi ya isa gurin tare da musu barka da zuwa, falon Baba aka kaisu. nan yake ya faɗawa Umma ɗakin Alhaji Hammayo, ya shiga ya ɗauko shi a kekenshi sannan yafito da shi.

       Su umma ne suka shigo da abubuwan drinks, nan aka shiga gaisawa, mashkur kan da bakinshi yayi masa nauyi sunkuyar da kanshi yayi ya gaisu,

        Baba galadima shi yafara, gabatarda sarki hussain da dalilin zuwansu yace, mun zo gidan nan ne  niman auron y'arku wa ɗanmu ne, da fatan bamu shiga wani niman ba."

        Shiru falon ya ɗauka, duk suka sunkuyar da kansu, sai umma ce kawai tayi karfin halin magana,amma taki yarda ta kalle inda mashkur yake dan karya mata, zuciya yake,
           tace.
"Ayya,sai dai kunyi hakuri dan, shkurah kan,"
    zaburowa, mashi yayi, yazo gabanta, yace.
"Don Allah, karkuce zaku hanani Abinda raina yake so, kuyi hakuri, na haɗaku da Allah kubani shkurah itace cikon rayuwata, sannan yankin rayuwatace, don Allah Umma, indai rashin zuwana na wani lokacine umma ku yafe min, amma kubani shkurah."

        Juyawa yayi ya koma. Wajen Mommah yace.
"Mommah kisa baki mana, don Allah karna rasata, nima rasa tawa rayuwar zanyi,"

     komawa wajen sarki hussain yayi ya rike kafarshi, yace.
"Abba bantaɓa saɓa umarninka ba, ni mai biyayyane, sannan zan iya kome dan farin cikinka, Abba don sonka da Ubangiji, kace subani, shkurah wallahi sai na maida ita macen da babu wata irinta, Abba kasa baki don Allah."
Chapter 14 · 0% Book details