← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ce tafito hanunta rike da casbi ta zubawa shkurah ido sannan tace,
"me yafaru ? a hanyar makarantar ba mamaki garin wasan banza ko ?"

       Rafi'a da tagama cire takalminta zata shiga part ɗinsu taɓe baki tai, sannan tace
"Idan suka haɗu su uku yanda kuka sannan dabobbi, haka suke wasan banza saura kaɗan da mota ta bita kanta, kuwa da kowa ya huta da haukarta da jin kai."

    Wannan maganar da rafi'a tayi ba karamin zafi yayiwa Umma ba amma dake tasan me take sai tayi murmushi kawai fuskarta cike da fara, aikuwa shkurah ta gaza hakuri da maganar ta nufeta dagan-dagan ta fisgota ta hankaɗa da jikin kofar part ɗinsu, tace
"Uwar me na tsare miki da kike min fatan mutuwa me bak'in zuciya wallahi idan baki fita idanun, ba zan miki shegen duka, wawiya kawai ina ruwana da rayuwarki."

     "Toh wucce muje ko bana son rashin hakuri kul kar nasake ganin haka, dan zan saɓa miki kina jina ko,"

               Ba musu ta ɗauki skull bag ɗinta tashige abinta amma ranta na zafi tana mamakin wannan al'amarin,

        Suna shiga palorn ta zube a kafet tana mai da numfashi lumshe idanunta tayi amma exactly fuskanshi take gani a cikin k'wayar idanunta buɗe ido da tayi da sauri tana zarresu, Aisha da tafito daga ɗinkisu ta kalleta, sai tayi tsaki ta wucce dan tasan wani, shirmenta ne ya zaunar  da ita a wajen,

        Tashi tayi tashiga ɗakin ta cire kayanta ta ninke sannan ta faɗa wanka ta jima sosai, aban ɗakin sannan tafito, kaya marasa nauyi tasaka sannan, ta gabatar da sallar magarib, buks ɗinta ta ɗauko ta fara dubawa.

          ***
Shima mashkur kusan shkurah yake gani abinda tayine ya bashi dariya sosai har hak'oranshi suka bayana, cikin nutsuwa ya shirya sannan yafita masjid,

      bai dawo gida basai bayan isha, abinda zai ci ya nima, yana gamawa yafita palo da laptop ɗinshi da wayarshi, momma ya kira zama yayi ya rufe idanunshi  bayan ya zuba kafafunshi a saman center table yana kaɗasu wani nishaɗi yake ji haɗi da nutsuwa bai san me ya janyo haka amma yana cikin nutsuwa , kiran ta yanke, ba a ɗauka ba ajiye wayar yayi yacigaba da aikinshi,

                 ***
Maina kenan duniya tazama sabuwa manne yake da wata yarinyar, kallo ɗaya zaka mata ka gane daga inda tafito,  sabida yanda gashin doki ya cika mata ga wani nail da tasaka a farcenta tana da kyau ba laifi, kallon shi tayi sannan tace
"Maina katagum me yasa baka sex dani skin to skin  wallahi bani da matsala, tun ɗazun nazo amma kak'inyi kome dani, sai shan win i swear bani da wata cuta, kuma kaine mutum na farko dana fara sani why not kacire shakku akaina."

       Wani shegen murmushin gefen baki yayi mata sannan ya ajiye kofin glass ɗin dake hanunshi ya juya ya kalleta kirjinta ya kalla yaji kome nashi ya ɗauki chaji yanda ya dace,

    dake a falo suke, kuma a kujera ɗaya suke me ɗaukar mutum biyu, janyota yayi a hankali yashiga sarrafata son ranshi, hmm shaiɗani dole mata su bishi dan ya iya sarrafa mace bana wasa ba,

            Duk iskanci Maina baya taɓa yarda yajewa mace babu condom ba yana tsoron ɗaukar ciwo, (Ashe iskancin karyane😂)

           Sai da ya kuna mata service sannan ya ɗauketa zuwa ɗakinshi anan yasaka condom ɗinshi amma ranta ya ɓaci da haka, kuma babu halin magana dan tasan halinshi sarai yanzun sai ya maketa, (Allah kashirya mana zuri'a al'umman muslumi baki ɗaya Allahumma Amin)

             ***
Washi gari  yau ba matsala dan harta manta Mashkur, kuma ba a same matsala, da ita ba tawajen shiryawa ba kusan ta rigasu, fitowa ba dan kome tai haka ba sai dan nasihar da Umma tayi mata kuma anyi dace, ta ɗauka sosai ya shiga jikinta,

           Suna gama shiryawa duk suka fito wajen mota suka tafi ke Rafi'a da niman faɗa tana zuwa ta bangajeta saura kaɗai ta faɗi,
      abin ya bawa kowa mamaki har shkurah juyawa tai ta kalli Umma murmushi tayi mata, alamun tai hakuri, shiga motar tai zuciyarta na mata zafi sosai,

     Sai da aka iso makarantar ai kuwa tana gaban shkurah abinda tai mata shi itama ta mata na hankaɗata sai da tafaɗi tana fitowa tai fuska sannan ta tsuguna gabanta, tace
"Ba gaba da gaba ko tabaya sai anshirya karki manta akwai watanin tsakaninmu, kuma har shida dan haka a kiyayye gaba dan idan haka yasake faruwa hmm, zan baki mamaki dan kinfi kowa sanin halina."

          Mikewa tayi zuciyarta yana tafasa sosai babu yanda ta iya da Shkurah amma da ta ɗauki mataki akanta.

           ***
Bayan sati guda yaso zuwa azare amma Allah be nufa ba, sabida tulin aikim da yake gabanshi dake yau da wuri ya dawo yana barandar gidan nasama yana wayane da momma sosai yake bata labarin wani karamin nasaran da yasamu kanshi a sunkuye, kaman ance ɗago kai sai akan fuskanta, ya zata a zuciyarshi ya faɗi haka yace
"I found my half"

      "Son me kace? you found your half wacece haka? son talk to me, " inji momma,

         gyara murya yayi ya shiga kame kame "a'a ni da maina nake kuma ai shi ɗin half ɗina ne, haba momma ba halin nai magana shikenan sai a min, fassara."

     Yanda yayi maganar cikin sigar shagwaɓa yasa tai murmushi irintasu ta manya tace
" Son just open your heart you  with feel happiness (Son ka buɗe zuciyarka, zakayi farin ciki),who are she (wacece ita) ?"
         "ayya momma na faɗa miki babu kowa fa da Maina nake fa" kaman yaron ɗan goye haka yake mata magana, jinshi take amma tafishi farin ciki, tace
"Ok tunda baka son nasanta, bawa maina mu gaisa."

        Katse kiran yayi yana lekasu Shkurah da suka wucce san yanxun ya rike bakinshi yana tuna irin katoɓaran da yayi, "Taɓ "  yace yana nazarin ya akayi ya iya rufta haka bayan shi be sani ba ɗaga kafaɗa yayi alamun ko a jikina
              ***
Duk da auren amsa shirin ko takwana amma, babu wanda yaji daɗin saka auren a kurarren lokaci, abinda basu sani ba shine dama can sarki ya gama shirinsa tsab kawai lokaci yake jira kuma Allah ya nufa,

Musaman iyaye mata dan sunso asaka kaman wata guda kafin nan anshirya amare sosai amma haka bai samu ba saɓida akurarran lokaci aka saka bikin dan ma amaren suna makaranta a kano, idan akayi biki aka gama zasu koma skul daga Ubaidatu har Zubaidatu suna karatune a B.u.k Ubaida a fannin Englishi itakuma Zubaida a
fannin Acc
        Maina yasame zuwa ganin Ubaidatu wacce aka ɗauki hoton da za'a asaka a kalanda da memo,da sauransu. Dakyar Mashkur yasame zuwa inda aka basu hutun kwanaki dan shagalin aurensu, wani abin mamaki dukda baifi sati guda da haɗuwa da Shkurah ba, wani lokacin yana ofis take wucewa ko idan ya dawo, haka kawai yake jinshi wani empty sai yake jin kaman ya shekara be ganta ba, ga uwa uba kewarta sau biyu suka haɗu tun bayan haɗuwarsu na farko, ranar alhamis da yamma sun taso shikuma yafi gidan mike kafa, gashi kusan duk abokan tafiyarta sun tafi, sunkki tsayawa suyi sallah sabida suna da hadda itakuma bazata ba sabida tana cikin yanayin lalura, shine tafito ita ɗaya abinka da unguwar manya kowa na gida ita ɗaya take sharan tafi gashi ko mashin babu balle, napep tana cikin tafiyane wasu matasa irin masu zuwa gidan y'an siyasa rok'o suka shiga binta suna mata magana bata kulasu ba, tacigaba da tafiya sai binta suke gashi wajen yayi shiru tana tsaka da addu'a sai ga mashkur yana tafiya hanunshi ɗaya na cikin aljuhun wandonshi  ɗaya rike da waya, ganin yanda suke mata rashin hankaline ya bashi haushi tsayawa yayi, yana jiran isowarsu, ai kuwa suna zuwa ya buga musu harara take suka kama gabansu dan yana da wani sirrin a tare da shi musaman magic eyes ɗinshi, wanda yake rikita mutane,

           Wucce shi tayi ya rufa mata baya har suka fita babban titi shi da kanshi ya tsara mata napep sannan ya zaro 1k yabawa me napep ɗin, a sanyaye yace
"kakaita gida karkayi gudu sosai fa, dan" kallon idanunta yayi sannan yacigaba da cewa"
naga kaman bata da lafiyane, kuma karka ɗauki wasu, dan kuɗinta na biya ita ɗaya"

        Ita dai burinta subar wajen ko hankalinta zai kwanta,  matsawa yayi daga jikin napep ɗin, suka tafi,

          toh basu sake haɗuwa ba sai a Arbian makert sunje siyayya da Aisha shima yaje sayan kayan abinci ya shiga gurin abin mamaki yaje zai ɗauki wani turaren uhdu wa kanwarshi zuhrah itama takai hanunta dukkansun basu lura ba sai suka ɗauki k'walin shi yarike gefe itama a masifance ta juya zata masa rashin mutunci karaf idanun,sun ya haɗe ja da baya tayi cikin tsoro, mika mata yayi tak'i karɓa Aisha ce ta iso wajen fuskanta ɗauke da mamakin ganin ƴanda ya tsareta da idanun sannan ya mika mata, amma dake kanta a sunkuye yake bata amsa ba, so take ta raɓa gefensh, gyara murya tai sannan tace
"Ayya kayi hakuri ai itama shine best turarenta, shi yasa aka same akasi kuka ɗauka tare, ba damuwa zata ɗauki wani, muje Shkurah"

         gyara tsayiwanshi yayi sannan yace
"Karku damu nima wa kanwata na ɗaukawa, amma tunda Shkurah tana so takarɓa zan nima mata wani,"

        Aisha taso kin karɓa amma jin yace
"ta ɗauke shi amatsayin yaya, shi yasa ta amsa tare da godiya, yaji daɗi duk da ba itace tai godiyar ba amma yaji abin har cikin ranshi."

         Abin dariya tare sukaita wayon tsince tsince kaya wasu abin wasu Zuhra yake ta ɗibawa, haka har suka gama, sunje biyan kuɗi yace a haɗa da nashi zarro idanun sukayi cike da mamaki hanunshi ya ɗaura akan bakinshi, alamun suyi mashi shiru,

      har wajen motarsu yasa aka kaimusu kayan sai godiya Aisha take amma shi duk hankalinshi yana kanta taki yarda su haɗa ido, dan wani nauyinshi take ji ga wani faɗuwar gaba da take ji,

         Yana wajen har motarsu tabar haraban wajen,

        Tun daga ranar basu sake haɗuwa ba,
Chapter 4 · 0% Book details