← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 29

Sashe 22

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuyi hkr, da wannan kusan typing ba sauki......💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆
MAI DAMBU CE*

Afuwa.......👏
*Page 19*

Yanda aka, kawo abinci haka ya dawo yasamu, har ita ɗin, mamakine, ya turnike shi taɓe baki yayi sannan ya shiga bandaki yayo alola, sannan yafito yayi sallah,

                ya jima,akan abin sallar kafin ya tashi inda take yaje ya zauna yana kare mata kallo, lumshe idanunsa yayi, sabida kukan da take yana taɓa zuciyarsa a hankali yakira sunanta, amma ko taɗago kanta asalima sake cusa kanta tayi, ta cigaba da kukanta.

      Shiru yayi yacigaba da kallonta, dan ya rasa me zai ce mata, tunda ya lura tana bukatar kukane shi yasa takeyi,

            Janyota yayi, a hankali ya rungumeta, sosai tureshi take tana kara kukanta, bakinsa yakai kunnenta yana mata ynda akewa kananun yara idan suna, kuka "seeeeee......"
         A hankali yake bubuga bayanta, har tayi shiru cikin nutsuwa, yace mata.
"Kinyi sallah kuwa,"

     shirun da yaji tayi yasa, ya leka fuskarta idanunta yagani, a rufe taɓata, yayi yace.
"Kinyi sallah kuwa? idan bakiyi ba tashi kiyi kar lokaci yatafi."

         Mikewa tayi, daga jikinshi ta shiga banɗaki, kafin ta fito ya shimfiɗa mata, abin sallah tana fitowa salla ta gabata, tana idarwa ta kwanta a gurin ko minti biyar batayi ba barci yayi, gaba da ita.

       Zama yayi, yasata a gaba yana kallonta cikin nutsuwa, shi kaɗai yasan yanda sonta yake ɗawainiya da shi,

......
             Karfe uku, saura kwata na dare ya tasheta dan hudu da rabi zasu bar chicago, har yagama haɗa musu kayansu, mika mata brush yayi taje tawanke bakinta mika masa tayi, karɓa yayi sake mika mata wata doguwar riga yayi, da gyalenta,

         A gurguje tasaka, dan taga sai, kallon agogon hanunsa yake, yana kallonta yana son mata magana, amma yasan ba lallai bane ta amsa masa,

            jakarsu yafito musu, sannan ya juya, yace.
"Bamu da lokaci, in dan ne ki shirya a nutse, zan iya jiranki har iya karshen rayuwata, ba xan gaji ba, kuma bazan damu ba, kuma zanji daɗin haka pls ba dan ni ba, ko dan sonki da kowa gida, ki hanzarta."

               Fitowa tayi, bayan t ɗaura gyalenta ɗaukar handbag ɗinta tayi, tafito dan tabashi haushi tashiga tafiya kaman me jin tausayin k'asa, tafiya yayi wajen lifter ya buɗe ganin da gaske tafiya, zaiyi yabarta yasa ta haɗa da gudunta,

       tana zuwa, dab dashi yashi itama tabi bayanshi, tunda kofar ta rufekanta, ta koma gefe, ta takure kanta, haɗi da kame jikinta, waje guda ganin haka, yasa yayi banza da ita har suka sauko kasa,

        fita sukayi daga, otel ɗin suna waje me taxi tana jiransu, har airport ya kawosu.

          Sun jima kafin jirginsu, ya tashi, sai da suka biya ta Ethopoeia, hutun awa biyu sukayi sannan suka sake ɗauko hanya,

           ****
Karfe goma, nasafe suka sauka a garin kano, wani jirgin ya biya musu, zuwa bauchi, sun iso sha biyu, saura kwata.

        Suna isowa, ya kira yaronshi yazo ya ɗaukesu, kallon yaro yayi yace.
" Ka kaimu,gwallaga"

        tunda suka, iso take share kwalla dake taruwa, a idanunta gashi jikinta yayi mugun sanyi, a haka suka iso unguwarsu har kofar gidansu tunda motar ta tsaya, ta rike hanunsa, cikin kuka tace.
"Toh ynz me zance musu, idan nashiga ciki, ina jin tsoron Baba kar yasake korata, don Allah ka kaini wani waje, ina jin tsoro."

         Zuba mata idanun yayi, cikin damuwa, dan sai yanzun yayi danasanin tafiya da ita har na tsawon wata uku, batare da sanin iyayensa da matarsa ba, toh idan ya kaita, ciki me zai cewa umma idan ta gansu tare,kar tayi tunanin daman yasan inda take, ya ɓoye mata hura iskar bakinsa yayi, sannan ya cire hanunta, daga rikon da tayi masa,

            share mata, kwallar dake fuskarta yayi sannan yace.
"Ki nutsu, mu shiga babu abinda zasu miki, kinji ko asalima kullum dake suke kwana dake suke tashi. Idan zan iya faɗa miki kiyarda shine basu san kina, raye ba amma muje kiji da kunnenki."

             Tare suka, fito daga motar a hankali ya zagayo, wajenta a hankali ya riko hanunta suka haɗa, hanunwarsu suka sarkafe da juna, kusan atare suka kalli juna.

          Shi yake, gaba ita kuma tana baya da sallama suka isa, cikin gidan duk suna tsakar gidan, zare hanunta tayi daga nashi ta koma bayanshi tare da rike rigarsa, shiga cikin gidan yayi,su Ummi da Mama, da Fauziyya, matar Abubakar sai leka bayanshi suke dan cike suke da mamaki kaman, shkurah suka, gani a tare da shi.

        Basu tabbatar ba, sai da ya gaishe dasu ummi, inda ya durkusa, nan duk suka mike a tare,
         suna salati,  fauziya kuwa, ta cikawa bujenta isa, dan ta gama razana,

        Umma ce tayi karfin halin cewa,
"Shkurah, kece ? ko watace me kama, dake ?"

        jijjiga kanta tayi, cikin kuka, matsawa tayi, gurin Ummi rike hanunta mama tayi suka shiga da ita, har falon Alhaji Hammayo, dan umma tana gurinshi.

              Har gaban Alhaji hammayo ta kaita,

      mikewa umma tayi, cikin tashin hankali, durkusawa shkurah tayi jikinta har yana rawa,
        cikin kuka, tace.
"Babana kayi, hakuri karka sake korana, idan na tafi, bansan inda zan sake faɗawa, ba ku yafe min wallahi ba laifina bane, kaddarace ta faɗo min don Allah kayi hakuri"

          A hankali umma ta zuba, gwaiwarta a kasa tayi, sujidar godiya kirari takewa, ubangiji kafin tasake kuka, me sauti inda ta tashi tarungume, shkurah Alhaji Hammayo, kuwa shima kuka yake,

         ganin haka, mashkur ya juya yayi tafiyarsa zuciyarsa cike take da farin ciki.

       Ko da ya isa, gida yasame gidan a hargitse wuccewa ciki yayi, ya rage kanyan jikinshi sannan ya faɗa banɗaki yayo wanka, sannan ya sake kaya marasa, nauyi kwanciya yayi, dan ya gaji sosai.

       Hmm, Zubaida nacan ɗaki tana, barcin asara duk ta rame tafita hayacinta,

        tun karfe goma take, barci har ynx da yunwan cikinta yasa ta juya, sannun a hankali ta farka, wanke bakinta tayi a banɗaki.

       Fita tayi, daga ɗakin kicin tashiga taje nimawa kanta abinda zataci.

              Taliya, da manja da yaji, tayi, taci sannan tafito kallon falon tayi, duk yayi kura tsaki tayi, dan tasan laifintane, saunawa ana kawo mata yan aiki,amma suna guduwa, ga aiki amma babu abinci dan dole suke guduwa, bandan ransu nakin aikinba,

ga kishin jaraba, dan yar aiki bata isa ganin mashkur ba koda yazo fita koranta ɗaki ake dan karta ganshi😜

         Shi yasa yaran basu zama ga tsangwama da hantara.

           Sai karfe biyu mashkur ya farka,

      dogowar riga, yasaka sanan yatafi masalaci.

         Aikan yaronshi, yayi yaje ya sayo masa, abincin dan yasan ba samu zayi ba.

       ****
A can gwallaga kuwa, kafin wani lokaci, gidan yacika da yan uwan da abokan arziki ana barka da dawowanta,

              Abinci ma umma ce ta bata a baki, tsakaninta da mutane sai kuka, dan bata taɓa kawowa a ranta iyayenta zasu neminta haka, ba gashi kowa bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta ake,

......

      Bayan kwana, biyu mutane sunyi sauki nan, umma take tambayarta, yanda suka haɗu da mashkur iya abinda tasani ta faɗa mata, suna zaune sai ga kiran Na'im ya shigo nan,

    yake mata mita kashe wayar da tayi, na tsawon lokaci, dariya tayi sannan ta faɗa masa ai wayar ce ta ɓata, idan ba haka ba sai suta rigima sun jima sosai faɗa masa, tayi tana bauchi nan, murna ya rufeshi yace mata.
"Ina nan zuwa, kuma idan nazo zan nime izinin niman aurenki."

        Zuciyarta fess, ta tace.
"Haba, dai ai ba yanzun ba sai na kwana biyu dan nayi. kewar gida sosai,"

      dariya, yayi sannan yace.
"Allah baki isa ba, nida nake so nan da wata gudu, muna tare Wallahi ina zuwa, zan gabatar da kaina"

       Sun jima, suna musayar yawun kafin sukayi sallama,
   Murmushi Umma tayi, tace.
"
Auta mashkurne, naji kuna musayan kalamai dashi."

Kallon umma dan ta manta da shi, a shafinsa ma girgiza kai tayi, tace.
"Wani ne, a kaduna, Na'im sunanshi, shine zaizo niman izinin a wajenku."

"Me kike nufi, Auta mashkur ɗin fa, "
"Umma ni bana, sonshi wallahi kuma ai taimako yayi, dane naso shi, amma yanzun ina son na'im yayi hakuri kawai ya nemi wata, da mata da yawa a garin bauchi bani ɗaya bace mace..."

         "Shkurah, anya kinsan me ake nufi da hallaci kuwa, kinsan abinda kike shirin aikatawa, kuwa, wannan shine Batulci, baki san me ake kira da adalci ba."

    Allah sarki duk wannan maganar dasuke yana kofar shiga falon duk abinda suke faɗa akan kunnenshi be taɓa jin ciwon ace ba'a sonshi ba, sai yau kalmar bana sonshi da take yayi, masa zafi jin sabom tsanar Maina yayi a ranshi juyawa yayi, ya bar gidan.

Ran umma ba karamin ɓaci yayi,ba dan haka shiru tayi, tana kallon shkurah, cikin sigar lallashi tace.
"Uwata, kinga mashkur ɗan yar uwatace, don Allah karki min haka ki amince ki aureshi zaki so shi sosai kinji, ki tayani rufa min asirinki ki amince da soyayyarsa."

           Kallon umma tayi, cikin nutsuwa tace.
"Umma kigane mana, nifa bana sonsh...."

       Ayi hakuri Dearie's💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*

_Husna Kamshi, ga wannan shafin kyautane nabawa yan grp ɗinki, bana bukatar godiyarsu Soyayyar dasukewa buk ɗin ma ya wadatar dani ina musu fatan alkhairi_💕💝

*Phatima zahra, na grp ɗin farida sweery ina jin daɗin comments ɗinki keda sauran yan grp gsky jiya naji daɗin comments ɗinku nagode sosai*💋

*page 20*

Bata kai ayar maganarta ba, umma ta kafceta da mari, irin fayau ɗin nan(😹)
      tana kan kujera yaseen sai da ta dunguro, sabida karfin mari.
          Batayi ihu ba, kuma babu alaman kuka daga idanunta hanunta ɗaya yana rike, da kumatunta,

        Idanun umma, sun kaɗa girgiza kafatan take cikin kunar rai, tace.
"Amma wallahi kin cika butulu, mara imani, har kina da bakin cewa baki son mashkur toh bari na faɗa miki abinda baki sani, mashkur shine kaɗai wanda zai aureki batare da, ya miki gori ko wani kallo ba, shine kaɗai zai rikeki ba tare yaji ko ɗar akanki ba, wallahi na rantse miki da Allah bazaki taɓa auran nagartaccen mutum irin mashkur ba, Allah yabaki sa'a. shine abinda zance miki."

      Tana gama faɗin haka tabar falon baki ɗaya ranta na mata, zafi da abinda shkurah tafaɗa mata,
Chapter 22 · 0% Book details