← Book details Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 29

Sashe 11

Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   saɓata sadeeq yayi a kafada aka fita da ita aka sakata a motarshi umma tashiga baya bilal ya zauna a gaba sukace alhaji hammayo ya zauna suje kar a watse a bar gida sai mata.

         Asibitin ni'ima suka tafi dan, ana Alhaj hammayo ya buɗe musu file,   suna zuwa aka amshesu da sauri cikin gaggawa aka shiga da ita ɗakin gaggawa.
              Idanun Umma sunyu ja bata iya ko magana sai tasbihi da Ahilal da salatin Annabin,  cikin ikon Allah ubangiji yasa mata juriya da tawakkali,

          tun kusan sha biyu zuwa ɗaya suke cikin asibitin kuma aka shiga da ita, har hudu da rabbi, suna jiran tsamani.

       biyar saura kwata likittotin suka fara fitowa sai goge gumi suke suna tattauna irin halin da take ciki kuma basu taɓa karo da tashin hankali irin wannan ba, sai wannan.

      Babban cikinsune me suna Dr bukar zaki. ya kallesu sannan yace,
"Kusame ni a ofis, yanzu,"
      bayanshi suka bi, kusan tare suka tare isa ofis ɗinshi kujera ya nuna musu, zama sukayi amm zuciyarsu bata zauna ba, zan iya cewa a tsaye take.

       Rubuce rubuce, yayi sannan ya ɗago ya kallesu fiskanshi cike da alhini yace.
"Shekarun mara lafiyanku kunce sha bakwai ko?"

      "Eh dr" inji bilal kenan.

     "Ok" jim yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Amma babu abinda ya razanata, ko aka razanata, dan a halin da muke ciki jininta yayi mugun hawa, har yakai zuciya bata iya sarrafa shi,a yanzun haka ya taɓa brain ɗinta wanda yaja mata ɗaɓin hankali, bamu taɓa cin karo da haka ba, baya da zazzaɓin da yaci karfinta sakamakon sanyin da yashiga jikinta, a gaskiya a wannan stage ɗinta yana da matukar hatsari ciwon a gareta, dan ko dariya taga wasu nayi zata iya fita hayacinta. Idan batayi haka ba zata zama taware kanta a cikin mutane kowa ganinshi take kaman dodo,a gskiya ciwon yana da matukar hatsari kuma babu lokacin da zan lissafo muku, yanayin ciwon amma zan baku magani, kafin tafarka, amma kuma dole zakuyi hakuri da ita babu hantara ko kyara."

     sun jima a ofis ɗinshi yana musu bayani halin da zata iya fuskanta

       Fitowa sukayi daga ofis ɗin jikinsu a sanyaye ɗakin da aka kwantar da ita suka shiga sai barcinta take a nutse ga bakinta da tattaunashi.

            Zama Umma tayi a kujeran cikin asibitin tana tofa mata addu'a tana gamawa tace.
"Zaku iya tafi sai ku faɗawa babanku an bata gado sannan kuzo min da kayan bukata kuce Aisha ta haɗa muku."

***
Mashkur. shima likitoci ukune akanshi sai kaiwa da komuwa suke cikin tashin hankali suka gama duk abinda da zasuyi amma be farka ba asalima ko numfashi bayayi dole aka ɗauko oxygen aka samashi amma abun yaki numfashinsa sai kasa yake, cikin gaggawa likittotin asibitin suka taro akanshi dole a turashi India a cikin satin dan aduk bayan awa uku bugun zuciyarshi ce take k'asa abinda ya gigitasu kenan, nan suka kira ɗaya daga cikin yaranshi suka tambaye shi ina family ɗin mashkur suke,

         kallon dr yayi sojan yace.
"D'an sarkin katagum ne,"

              Komawa likitan yayi ya faɗa musu ɗan waye a cikin daren aka kira gidan sarki husain, cikin tashin hankali Abba ya tura gidan Momma aka faɗa mata halin da, mashkur yake ciki,amma gobe tashirya ana za'azo ɗaukarta.

        tashin hankali wanda ba'a samashi rana,
                 kowa na barci amma momma idanunta yaki barci burinta gari ya waye,

       ***
Kano
Ta idar da sallar isha,i kenan ta duba buks ɗint cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, hankalinta ya tafi ga karatunta.

            Zubaida ce ta ɗaka mata duka cikin wasa tace,
"Shegiya kin ji daɗinki, kinsan daɗin mijinki ni kuwa nawa mijin tsakanina da shi sannun kawai, ko ɗan rungumata bai taɓa yi ba, asalima a kanwarshi nake, kinki kibani sirrin naki mallakar da kikayiwa yayana."

       Ajiye buks ɗin tayi akan gadon ta gyara zamanta sannan tace,

"ni dake akwai bambancin tayu ke mijinki ba kaman nawa bane shi ya haka ni dai bani da matsala da yaya maina kome Alhamdulillah, kuma nima ina kokarin sauke hakkinshi da yake kaina kuma kema ya kamata ki janyo hankali Ya mashkur, namiji kaman yarone dole ki lallaɓa shi."

   haka sukaita hiran akan mazajensu har kusan karfe goma sha ɗaya sannan suka kwanta sai lokacin ta duba wayarta,
        kiran maina tayi amma layin yaki shiga, can da bara ta faɗu mata ta dube Data mssg ne sukayita shigowa har da email kuma sunan maina tagani dan haka, tashiga ta buɗe.

     A hankali tashiga karanta sak'on da take ganinshi kaman sak'on mutuwarta hawayene ya shiga zuba mata, a hankali kuka ya kwace mata cikin tashin hankali cusa kanta tayi tsakananin cinyoyinta tana wani irin kuka me ban tausayi.
   (Nasan me karatu ya shiga ruɗan bari na taya ku duba sakon nima amma karku min kuka fa dan na lura kowa kuka yake)
   ga sak'on kamar haka.
_Assalamun Alaikumun_
*Da fatan kina lafiya, hmm ba zan ja dogon bayani ba amma, abinda zan faɗa miki ni na aurekine abisa dole, karki ji haushina nima takurani akayi na aureki, kisani yayanki shine ya janyo na miki haka, duk da nasan nine me laifi amma kisani babu wanda ya isa ya takani nayi shiru, ya kyamaceni,ya nuna min kazantane ni, ko ruwa nasha a cup Mashkur baya ɗauka balle kuma wani abu, yasha faɗa min yana ganin kazantana yafi daraja shara datti akaina, Toh sai akayi dace aka haɗani aure da ke kanwarshi, hhh tun aranar da aka kawo min ke naso dan karamiki  saki, amma dake na lura kina da abin hutawa yasa na kyaleki idan nagama cin moriyarki kuma naji daɗin haka, kaiiii gaskiya bazan ɓoye miki ba kina da abinda ake bukata amma ni kisani mace irinki bata gabana,   Shi yasa nasake ki har uku, auw ban baki labari ba, yau naje na ɓarje yarinyar da yayinki yake so wai shin shi kaɗai ne zayita nasara a rayuwarshi ya zama cinye du kenan toh nima na, bar mashi tabo na har abada, shi da farin ciki sai dai yaga wasu nayi amma shi yarasa kenan, dan haka niyi nisa na bar muku kasarku, saura ku haɗani da iyayena su min baki dan nasan kun iya munafurci wow ayi zawarci lafiya*

          kuka take me cin rai tabbad maina ya zalincesu Allah kasaka mana abinda yayi mana.

        ***
Washi gari...
Kafin wani lokaci asibiti ya cika mutane katagum sun cika dan karfe sha ɗaya suka iso har momma a cikin awa uku aka sama musu visa indiya cikin gaggawa dan zuwa wannan lokacin bugun zuciyar Mashkur yana 31½ hankalin kowa baya kwance sai da aka sami jirgin da ya ɗaukesu, zuwa abuja suna zuwa nan ma, sai da aka ɗauki lokaci kafin jirgin india

       fatan nasara mashkur.

   .....
Shkurah itama tana cikin yanayin damuwa dan har ynz bata farka ba, gashi tayi wani fayau, sai uwar hanci da yasake fitowa.

      Kusan kwananta goma tafarka cikin ihu da fizge fizge, faɗowa tayi daga gado, tana kurma Ihu da kururuwa.
      Allah sarki umma tana cikin sallah take jin ihunta amma bata katse sallar ba har nurse da likitoti suka, shigo ganin tayi sujada abin ya basu mamaki dan haka suka rufa mata, lokacin har tashige kasar gado tana tattare rigarta, da sikati ɗinta tana rike rigarta idanunta a rufe tana kuka duk wanda ya kuskura yaje kusa da ita ɗauko abu take tana jifarsu da shi. Duk akarasa wanda zai tunkareta lokacine Umma ta idar da sallah addu'a tayi a nutse sannan ta juya garesu, taga sunyi cirko-cirko ratsasu tayi ta wucce har inda take, kallon ta umma tayi kukane yaso kwace mata amma ta haɗiye, takawa tayi cikin nutsuwa idanunta cikin na shkurah tace.
"Zainabu Abu, zo ga ummanki nan, kinji ajiye abin hanunki kinji, ko yawa Shkurah Ummanta  hawayene yake zuba daga idanu shkurah, yayinda Umma ta ɓoye, nata hawayen,  ajiye kwalbar asteme tayi, karasawa umma tayi wajenta ta rungumeta kuka tasake, likitotine suka karaso aka mata allura,

     Qaddaran Rayuwar Shkurah,har ynz aka fara wallahi shafin nasani kuka, kuma ba'ayi kome ba
3/4/21, 9:45 AM - Ummi Tandama: *QADDARAN RAYUWATA*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

Al-Baasit Al-Khaafid Al-Raafiu Al-muizillu👏👏👏👏

'''Ayya wallahi kuna ragen kwarin gwiwa da kukanku Don Allah ku biyo litafin a hankali Insha Allah zaku ji daɗinshi nan gaba Ina muku fatan alkhairi'''💋

    *Wow gaskiya da Whatsapp da Watpad bansan suwaye sukafi son wannan buk ɗin ba sai ruwan comment da Voting nake gani Allah yayi muku albarka*💃 💃 💃 💃 💃

*page 10*
     Allura suka matan sannan suka samata,ruwa nan suka maida hankali suna magana cus-cus.
        D'aya da cikin drs ɗn wacce musuluma ce, ta kalle dr zakari murya kasa-kasa tace.
"Wannan yanayin ciwonta kamar raping ɗinta akayi shi ya janyo wannan laluran,"

      kallonta dr zakari yayi sannan yace,
"Ba lallai bane haka tafaru, idan damuwa tayi yawa tana haifar da haka amma zamu turasu T.H, akwai k"wararrun drs da zasu taimaka mata insha Allah bazata fi wata ɗaya ba zuwa biyu ta warke."

             A cikin daren aka maidasu T.h, inda aka shiga kai kawo akan Shkurah.

     Allah sarki Umma duk duriyarta da Jarumtarta sai da ta zauna tayi kuka me tsuma zuciya, lokacin da ta idar da sallar asuba, zama tayi tana kallon yanda shkurah take barci  a tsanake,

      cikin sati biyu zuwa uku, Alhamdulillah jiki ya fara sauki dan har ta farka amma bata hmm bata uhum sai dai tayita kallon mutane, haka ya sake jefa hankalin iyayenta da yan uwanta yakara tashi sun tunkari dr Dalhat da maganar halin da take ciki,
      rubuta musu magani yayi da wasu drip ɗago kai yayi ya kalle, Alhaji hammayo yace.
"A hankali sauki zaizo kuma, alamun akwai damuwa ne a ranta, Insha Allah zata koma kamar da amma kuma ya kamata ku tsaya mata da addu'a, sosai da wannan ku sayo zamu mata amfani dasune."

               Cikin yan kwanaki  sosai sauki yasamu dan takanyi magana shima da Umma kaɗai, dakyar take iya kallon kowa suma sai umma tasa baki take, iya amsa musu, cikin wata gudu da kwanaki aka sallameta,

    Suka dawo gida, haka yan uwan da abokar arziki duk suke shigowa musu ya-ya jiki umma ce ke amsawa amma ita kam tana ɗaki a kwance, cikin kuncin rayuwa, sam bata kaunar hayaniya ko surutu, idan a ɗakin umma suka sameta toh barcin dole zatayi har sai sun fita.
Chapter 11 · 0% Book details