Sashe 12
Kaddarar Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin wannan yanayi aka sata ta koma skull, can ma bawani sakewa take ba tana takure, a class a can kuryar class take zama wani lokacin kuka taza zauna,tayi ta duk abin sai ya dame sauran ɗaliban, kuma haka ya janyo mata koma baya a karatunta, duk yanda aka tambayeta shiru take Umma tayi tambayar duniyan nan, amma tace babu.
...
Indian Hospital, tunda aka kawo shi babu abinda zai nuna maka,ana samun cigaba dan har yanzun bugun zuciyarshi yayi, kasa amma suna bakin kokarinsu, dan ganin ya farka.
Idar da sallarta kenan ta jima tana addu,a nima mashi lafiya da gafaran ubangiji, bayan ta gama ne ta koma kan.kujeran kusa dashi tarike hanunshi tana shafa kanshi.
Shiru tayi tana kallon fuskanshi da ya haɗa suma duk yayi kasumba, sai ya kara kyau sosai murmushi tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya tace.
"Yarona, nasan kai sadaukine kuma gwarzone kuma nan gaba shugaban al'umma,uban jikokinane, angon mata biyu musaman sarauniya *Shkurah* idan har shi ɗin Masoyin shkurah na gaskiyane Ubangiji ya ɗaga min kafaɗarshi."
Kusan kullum wannan shine maganarta da Mashkur.
***
Tunda Ubaidatu tasame sak'on maina ta gaza hakuri tashiga niman layin mashkur, cikin tashin hankali har gari ya waye, bata fasa ba, karshe zubaida ta tambayeta, meke.
Murmushin bakin ciki tayi sannan tace,
"Maina ne ya sakeni."
Mika mata wayar tayi a tsorace ta karanta wajen sakin bata karasa sauran ba ta mika mata wayarta cikin tashin hankali tace.
"Me yayi zafi haka da zai sake ki,"
watsa mata wani mugun kallo tayi tace.
,"Me ya hanaki karantawa, ko rainin hankali da wayo, dalla matsa kibani guri, kaman yanda ɗan uwanki yayi min nayi imani, da Allah yayana ba zaitaɓa miki ba, amma ba damuwa, yaje shi da Allah ubangiji yana madakata, shima sai ya girbi abinda ya aikata tun a duniya kafin yaje lahira"
Hawayene masu zafi suke bin fuskanta ɗaukar wayar tayi tashiga niman layin Momma amma bata samu ba, sai dai na Zuhra tasamu wajen karfe goma nasafe tambayarta tayi ina Momma takira layinta yaki shiga.
Cikin sanyi murya ta fashe da kuka tace.
"Mommah tana india ita da Yaya bashi da lafiya, tunda yasuma be farka ba har ynx"
Daman tana tsaye ne, sulalewa tayi ta zauna daɓas ta cusa hanunta cikin gashin kuka tasake cikin tashin hankali, itama zubaida kukan take kaman me, mikewa Ubaida tayi ta goge fuskanta time table ta duba, ganin saura sati hudu sufara exam yasa tasaki murmushi, fita tayi daga ɗakin ta tafi, ɗakin kusa dasu akwai kawarta a cikin nan ta faɗa mata zata india duba yayanta da bashi da lafiya, kuma zata ɗauki kaman sati biu zuwa uku ko zata taimaka mata da test idan kuma an bada assgment ta turo mata ta email, idan tayi zata turo sai ta copy mata,"
Amincewa kawar tayi, godiya tayi mata sannan tafito daga ɗakin, ɗakinsu ta koma ta haɗa kayanta cikin nutsuwa sannan tafita ɗakin kawarta taje tayi mata sallama, sannan taje ofishin jakadancin India dake nan kano taje, tacika foam ce mata sukayi taje ta dawo zuwa gobe.
Dan dole ta dawo hostel nan ta cigaba da niman wani information, asibitin dasu Mommah suke, ta baki zuhra tasame sunan asibitin.
Washi gari.....
Tayi sallama da kowa, amma banda zubaida abin ya dame zubaida dan har kuka tayi, a ranar takira Nana mahaifiyarsu kenan ta faɗa mata, abinda maina yayi, jikin Nana har rawa yake nan tashiga shashin sarki ta faɗa mashi abinda maina ya aikata cike da bakin ciki da ɓacin rai yakira layinshi babu baya shiga duk wani inda sarki Husain yasan zai same maina babu,
karshe kiran ogan maina yaya ya tambaye shi ko maina yana nan.
Cike da mamaki ogan yace.
"Ai maina yabar kasan nan, ya koma amurka da aikin shekara biyar da sojojin Nato, ashe bai faɗa maka ba ayya kayi hakuri, maybe sun mashi kiran gaggawane."
"Ok nagode ba damuwa Allah yabashi sa'a." sarki hussain yace.
Kallon Nana yayi ranshi na masa zafi, yace.
"Yanzun kinga illar abinda yasa nake, takura shi ko, ba iya wannan ba Maina shine shan giya, shine niman mata, duk inda kike kallon maina ya wucce haka"
dariya yayi sannan yace.
"Ai ba damuwa, duniya ce tafi bagaruwa."
yana gama faɗin haka ya wucce cikin turakanshi ita kuwa nana kuka tafashe da shi me cikin rai, tare da bakin cikin halin da maina yake ciki, can wani tunani yazo mata na ai ba mamaki asiri aka masa dan tasan kishiyoyintane dan suna gudun kar, idan sarki ya mutu kar abawa maina sarauta idan aka san yana da mugun ɗabi'a(Wai da gaske asirine ɗaukar hakki😹,)
***
Ubaida ta isa india lafiya, daga airport aka wucce da ita, asibitin nan ta shiga niman indasu Mommah suke dakyar tasamesu da taimako wata nurse ita take lura da, ganin yanda suke kama da mashkur yasa tayi mata magana cikin harshen turanci haɗi da india tace.
"Ke kanwar mashkur ne"
jikinta na rawa tace, "Eh nice"
"ok" tace mata tashiga gaba tana binta a baya har inda mashkur yake mommah ma tana zaune rike da hanunshi, godiya tayiwa nurse ɗin sannan tashiga ɗakin da sallama, ɗagowa mommah tayi tana kallonta, fuskanta ɗauke da mamaki, kukan da Ubaida ke haɗiyewa nr ya, kwace mata ajiye jakarta tayi, a kasa ta karasa wajen Momma ta, zuɓe a jikinta tana wani irin kuka me cin rai da ruhi.. hanunta na rike da mashkur ɗaya yana shafa kan Ubaidatu hawaye masu ɗumi na ɗiga daga idanunta.
Sun ɗauki lokaci a haka, kafin ta haɗiye kukan ta ɗago da kanta tace.
"Mommah meke damunshi, suka ce."
Ajiyar zuciya mommah tayi sannan tace,
"Heart attack, lokaci guda abin ya bani mamaki da al'ajabi sosai dan kafin faruwan abin muyi waya da shi yake faɗa min, ana bikin saukar Shkurah, toh tundaga lokacin ban sake jinshi ba, sai da aka kirani wai bashi da lafiya."
kallon mommah tayi cike da damuwa ganin yanda lokaci guda ta koma yasa ta ɓoye damuwarta bata faɗa mata ba ɗaura kanta tayi akan cinyar mommah.
Can ta kalleta da mamaki a fuskarta mommah tace.
"Ina mijinki yake? naga tunɗazun kika zo kuma ban ganshi ba.
k'ak'aro murmushi tayi tace.
"Baya gari, amma shima zai zo."
Haka suka cigaba da taɓa hira sama-sama
satin ubaida biyu ta dawo, amma zuciyarta yana gurinsu dan a daddafe, suka fara karatu kafin exam ɗinsu.
***
A cikin wata biyu zuwa uku, shkurah, ɗan dawo hayacinta dan wannan lokacin yazo mata da hidima dayawa ga, gama skull ɗinsu ga bikin y'an gidansu wanda shine agabansu, hankali su ya tafi da tsara event da sauransu.
Alhamdulillah yau Shkurah suka gama,paper karshe, gashi yau za'ayi kamun Aisha dan haka bata taɓa lokaci ba tafito daga class. A gajiye da kasala da yake sakata a gaba dan har barcu barci take ji, tana fita bakin gater ta faɗa mota, wani irin rana ake me ɗan karen zafi.
Haka sauran yan uwant suka shiga mota, Kawarta Aisha Abbad ce ta leko ta motar tace.
"Dan girman Allah faɗa min sunan man da kike shafawa, babu kyau wulakanci fa"
tsaki tayi sannan tace.
"Ke ni kirabu dani, wallahi bana shafa kome vase line nake shafa, muje don Allah."
Dariya salmah tayi sannan tace.
"Dear wallahi kowa ya ganki dole yace kina shafa mai, kuma kin kara girma kinji kome hip hop ɗinki sunyi tam " duka takaiwa salmah ita kuma sai dariya har ɗa rafi'a tsokananta suke."
Haka suka isa gida wanda ya cika makil da jama'a haka ta ratsasu tashige ɗakinsu kwanciya tayi ta zubda kome dake hanunta, ta hawu sauke ajiyar zuciya na gaji barcine yayi gaba da ita.
Bata tashi ba sai, karfe biu da rabi ta farka wanka tayi tayi sallah azahar, siket fari da wani riga me ɗan guntu hanun tasaka, farin ɗan kune tasaka tufke gashinta tayi zuwa gefen kanta ta fito ɗakin Umma shiga tayi ta gaida yan uwan babanta sannan ta kalle Umma cikin shagwaɓa tace.
"Zanci ɗan wake umma, da kayan haɗi.."
dan shi take bukata dan har wani haɗiye yawun daɗi take idan tatuna, yanda ɗan waken zai ji yaji....
Hararanta umma tayi sannan tace.
"Ki wucce kicin akwai kayan ɗan wake kisa Sahura ta miki bana son, fitina ina da mutane a nan."
"Toh umma" tafita, dariya yan uwan baban shkurah sukayi sannan ɗaya daga cikinsu tace.
"Habiba kin sakalta shkurah dayawa fa, shi yasa take rigama son ranta."
Dukkansu dariya suka cigaba da yi.
Karfe biyar aka tafi kamu, kome na wajen yayi kyau sosai.
Washi gari....
Akayi waleema, da wasu.hidima dake ranae juma'a ne.
Ranar asabar hidima ya karu, daga cikin bakin gidan har da kanwar maman Aunty amarya, duk suna tare a waje ana aiki, tana xaune shkurah tazo ta wucce, ta bita da idanun tasake dawowa haka tasake binta da shi mikewa tayi ta kira aunty amarya ɗaki,
kallonta aunty amarya tayi sannan tace.
"Lafiya kika kirani,Inna."
Cike da tsoro tace.
"Yar mijinki tana da aurene,"
"wacce kenan a cikinsu" inji Aunty Amarya.
"Shrkul take ko shkulce ke ni ban iya sunanta ba wannan me kama da larabawan gidan naga alamun ɗanyen ciki a jikinta kuma wallahi baxan miki karya ba," inji Inna kenan.
dariya tayi sannan tace.
"Tunda kika rantse nasan bazaki min karya ba, kuma nima na jima ina mata kallon haka, lokacin rugujewar fadarki yazo Habiba dan sai nasaki kuka a yau farin ciki haɗi da bakin ciki, abin zai bada ma'ana."
Fita Aunty amarya tayi daga ɗakin tana jiran fitowar shkurah bata fito ba sai, da ta shirya cikin Atamfar super holland ɗinki riga da zani, wanda aka mata 6 pieces tayi kyau sosai, kamar itace amaryar,
Dake a masalacin gida ake ɗaura auren Aisha, Abubakar kuma a masalacin gwallaga sai aka raba wasu suna gwallaga wasu nan, sanarwa akayi an ɗaura auren Aisha guɗa ake tayi, lokacin Aunty amarya, ta ɗaga murya da karfi dan lokacin Alhaji Hammayo ya shigo gidan kenan tace.
"Shkurah rabonki da al'adarki wata nawa kenan, kina min kama da masu juna biyu,gashi rabon Mashkur da zuwa kusan wata uku kenan, yaci moriya ya gudu, ko"