← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kayan aiki a dakinsa, ya koma falo ya xauna ya dafe kansa, to wat's d meanin of dis, Safeena ce ta sauko rike da handbag dinta ta tsaya gabansa fuskarta daure tana kallonsa tace "xan fita," da kyar ya dago yana kallonta snn yace "Allah ya kiyaye," ta juya fuu tayi kofar fita, duk tana sane da abinda ya faru a gidan, don tana gama hada break ta haura sama taji muryarsu, kuma ta gane abinda suke yi, ta dde labe jikin kofa tana jin duk me suke fada takaici yasa ta koma dakinta da sauri ta fada kan gado tana kuka, can ta kira uwarta ta sanar da ita komai, uwar ma ta rude don a xatonsu ae ya saki inteesar kmr yanda Hajiyarsa ta gaya masu, uwar tace maxa ta taho gida su san abun yi, hkn yasa ta shirya ta sauko ta kuwa samesa a falo, kuma yana ce mata Allah ya kiyaye kuwa tayi gaba, don dama tayi niyyar ko yace bbu inda xata tace bae isa ba kuma ta fita, Aliyu ya mayar da kansa bayan ya bita da kallo don bae da lkcnta, bayan kmr minti talatin doctor Maryam ta sauko tana kallonsa ta gaya masa magungunan da xae siyo da Allura snn ta koma sama, ya mike da kyar ya haura sama ya shiga dakinsa ya dauki makullin motarsa da Atm ya fita, bayan kmr minti ashirin ya shigo gidan rike da ledan abubuwan da ta lissafo masa, yana shigowa falo ta sauko ta karba ledan ta koma sama, ya kwanta kan kujera ya lumshe idonsa ya rasa gano abinda ke damunsa, karfe sha biyu da kwata doctor Maryam ta sauko, rike da makullin motarta da glass alamar tafiya xata yi, ya mike tsaye da sauri yana kallonta yace "ya ake ciki doctor, bleedn din ya tsaya," ta dan tabe baki tana hararansa tace "ni dae na kusa fara kiranka quack doctor wllh, dama likita na da rudewa hka? Ni kam ban taba sani ba sae a kanka," Aliyu yyi murmushi ya kasa cewa komai tace "to ynxu dae da sauki Alhmdllh, don har ta samu bacci kuma jinin ya tsaya, kuma tana da karancin jini wllh, ka dinga sa ta tana cin vegetables da dae abubuwan da ya kamata kae sae kace ba likita ba, ni abubuwan ka na bn mmki Hydar, nd lstly please n please doctor kayi hkuri ba dan ni ba ka dan sarara mata har bbies dinta su kara kwari don Allah," . Da mugun mmki Aliyu yace "wat? Kina nufin ciki na jikinta doctor?" Doctor maryam tayi masa kallon rainin wayo tace "kai kuma kana nufin kace min baka san tana da ciki bne ko me," Aliyu ya girgixa kai duk yyi confuse da sauri yace "ok ok, doctor ngdd ssae," ya juya da sauri ya haura sama, likitan ta tabe baki,tace "Allah ya shirye Aliyu," snn ta fita daga gidan tana murmushi, ynxu da ita ce xata haifa masa yan biyun nn amma Allah bae yi ba, ta kaudar da tunanin da sauri daga ranta, coz bygones re already bygonea, ta shiga motarta mai gadi ya bude mata gate ta fita daga gidan. Aliyu na shiga dakin Inteesar ya tarda ta kwance tana bacci, Maryam ta lullubeta da bargo ga drip a hannunta, ya karasa a hankali kusa da ita ya xauna yana kallonta, ya ma rasa irin farin cikin da xae yi, a hankali ya cire bargon daga jikinta yana kallonta, yes ga signs of pregnancy a tare da ita, a hankali ya daura kansa bisa cikinta muryarsa na rawa yace "plss Fateema, ki gaya min me kike bukata daga gareni, don Allah kar ki cire min cikin nn kuma, i beg yhu fateema ki bari na ga jinina a duniya plss," duk ya rikice mata har da hawayensa kmr idonta biyu, ita ko baccinta kawae take amma da gani ba me ddi ba hka ya gama haukansa ya dawo gefenta ta baya ya kwanta ya rungumeta yana shafa cikinta, ya kai minti kusan sha biyar a hka snn ya mike da kyar ya shiga bathroom dinta yyi wanka yyi alwala ya fito, nn dakin yyi sllh, ya dde xaune yana Adduar Allah yasa kar Fateema ta kuma yunkurin cire masa ciki, ganin tana ta mutsu mutsu ita kadae ya sa ya mike da sauri ya dawo gefenta ya riketa yace "fateema, me ya faru," cikin baccin tace "cikina," ya daura hannu a mararta yace "sannu xae daina kinji," ya daga kai yana kallon ruwan dake hannunta yaga ya kusa rabi, ya gyara mata kwanciyarta ganin ta koma baccin ya dawo bayanta ya kwanta ya rungumota, yana shafa mararta, a hkn shima yyi bacci yana rungume da ita, sae kusan la-asar ya farka ya mike xaune da sauri yana kallonta, bacci take har lkcin, ya kalli ruwan hannunta ya ga ya wuce rabi, ya mike ya shiga bayi yin wanka kuma kafin yyi sllh, ko minti biyar ba ayi ba da shigar sa bayi ta farka, ta fara kalle kallen dakin da mmki ta mike xaune da sauri kmr warce ta tuno abu tana kallon ruwan hannunta, ynxu kam marar ya daina mata ciwon sae kasala, ta kalli agogo ta ga hudu saura, ta kalli kofar bayi ta gane wanka yake, da sauri ta mike tsaye ranta a dagule, tayi baya xata fadi tayi saurin dafa bango, jiri ssae take gani, ta cire alluran hannunta ta dauki kayanta da kyar ta mayar jikinta, snn ta dauki Hijab dinta ta saka, tayi hanyar kofa ta bude a hankali ta fice daga gidan, tafiya take kmr wata mashayiya har ta isa bakin titi, ikon Allah ne kadae ya kai ta titin, ta tsayar da mai tricycle ta gaya masa inda xata ta shiga da sauri ba tare da ta jira me xae ce ba tana mayar da numfashi, a wahale ta isa gida bbu kudin ba mai mashin, da kyar tace "yi hkuri bawan Allah bari na shiga gida xa'a fito maka da kudinka ynxu," da lst strength dinta ta isa falon inna ta xube kan kujera ta lumshe idonta tana mayar da numfashi, inna ta fito da sauri daga daki tana cewa "wani gantalallen ne xae fado min gida ba sallama kmr katon arne," inteesar dae bata tanka ta ba, inna ta rufe bakinta da sauri tace "lah ai ban san ke bace ba, daga ina hka? ina kayan? me ya tsayar da ke tun safe hka? A'a me ya sameki," duk a rude ta jero mata tambayoyin, inteesar tayi tsaki tace "ni da'allah ki rabu dani inna, ga me keke napepcan a waje ki kai masa dari biyar dan Allah," inna tace "ina naga dari biyar, ba daxu gabanki na ranto dubu gun Zainabu ba, ina kudin motar da na baki," inteesar ta juya mata baya tace "ki nema ki kai masa dan Allah, yana waje yana jira," inna ta fita da sauri tana cewa "to bari naje gun matsiyatan can ko xasu bani," tana isa tsakar gida cikin daga murya tace "Aisha ko shafa cikin ku wani ya ranta min dari biyar kan Bukar ya dawo," umma ta leko ta taga da mamaki tana kallon inna, "magana fa nake yi ko basa ciki ne," a tare suka fito umma tace "wllh inna ni dubu ce a hannuna," Hajiya ta fito da dari biyar din ta mika ma inna tace "gashi ina da canji inna," inna tace "yauwa dama me keke napep xa ku mika ma a waje, inteesar ce ta tafi anguwa ta xubar da kudin ta a titi, ynxu bata da wanda xata ba ma mai mashin din nima kuma banda canji, fita ki mika masa yana waje," umma ta juya tana yar dariyar keta, don dama tana dashi ta hana sae ita Hajiya me neman suna, Hajiya kam ji tayi kmr ta hadiye xuciya don takaici, a fusace inna tace "ya hka ina magana kin tsaya kmr wata sokuwa, ki fita ki mika masa mana," sum sum Hjiya ta karasa gate ta mika ma mai keke napep dari biyar din ranta a bace, ta komo cikin gidan, inna ta juya tayi gaba ba tare da tace mata komai ba, ummata shige daki ta dinga kyalkyala dariya, inna na komawa falonta tace "shegu sun ba shi,A'aah jinin meye wnn a xanin ki inteesar" arude tayi tambayar ta karaso kusa da inteesar da sauri tana gwale ido. Inteesar ta juya da sauri tana kallon xaninta taga duk ya baci da jini, inna ta saka salati kmr xata yi kuka xata yi magana inteesar ta riga ta da sauri tace "al'ada ce ta xo min a hanya," inna tace "haba," inteesar ta gyada mata kai kawae, inna tace "to Alhmdllh, ciki kam sae dae lbri tunda ga al'ada har ta xo, ynxu Haisam ya dawo ya raka ki kuje ayi maki wankin ciki, don naga bbu shegen da ya damu da hka a gidan tunda ba lfyarsu bace," inteesar ta kuma juya mata baya don ita kadae tasan yanda take ji a jikinta," inna tace "to wae ina kayayyakin naki," ba tare da ta kalli inna ba tace "ba kowa a gidan," inna tace "shegu, to ki tashi kije ki gyara jikinki mana kin wani kwanta kaman rubabbiya ko gantalallen can ya koya maki kaxanta ne, ni dae ban san ki da kaxanta ba sae dae in gunsa kika koyo", inteesar ta juya da sauri tana kallonta tace "kema dae kinsan sharri kawae xaki masa amma ya Aliyu karshe ne wajen tsafta," inna ta wage baki tana kallonta, inteesar ta mike da sauri ta shiga daki don ita ma sae taji xancen yyi mata wani iri a baki to ina ruwanta ma da har xata wani kare masa, wanka ta shiga bayi tayi taga jinin ya tsaya, ta hada ruwan xafi tayi wankan snn ta fito ta shirya cikin gown, har ta kwanta abinda ya faru daxu ya fado mata, ta lumshe idonta, can ta mike xaune da sauri tana kallon bakin kofa tace "inna ina kika ajiye takardar daxu da safe?" inna dake ta goge goge a falo tace "oho kaman yana cikin durowa, me xakiyi da shi," inteesar bata tanka ta ba ta mike ta bude drawern ta dauko takardar ta koma ta
Chapter 8 · 0% Book details