← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 28

Sashe 11

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shiru bata ce komai ba sae da ya dawo gabanta a hankali ya kara mata tambayar snn ta nuna masa, ya mike ya dauko ya saka cikin ruwan, ya cire mata rigar jikinta da xani snn ya shiga matse tawul din yana goge mata jiki da shi, karfe goma yace xae tafi bayan ya lallabata ta sha tea kadan, har lkcn tana rungume jikinsa, ta gyada masa kai kawae, snn yace "gobe da safe xan xo da magunguna da injectns dinki kinji kanwata," kai kawae ta gyada masa, ya daura mata kiss a bakinta, ta lumshe ido da sauri, yyi mata sae da safe, ta bi shi da kallo har ya fita, ya fita da minti biyar momy ta shigo, xani ne kawae jikinta, kunya ya kamata ta rufe ido da sauri kmr me bacci. Kullum sae Aliyu ya xo sashinsu da safe da dare, ya kan siya masu fruit ko nama, duk da ko kadan momy bata sake masa, sae dae yyi ta xamansa a falo idan ta fita sae ya shiga dakin, laulayin inteesar ya dawo sabo kullum cikin wahala da amai take yana mugun tausayinta har mmki abun yake bata, duk da tasan duk sbda cikinsa ne, wani lkcin idan ya shigo gidan sae karfe sha daya yake wucewa duk da bbu wanda yasan yana xuwa har inna, idan kuwa tayi bacci me ddi to a jikinsa ne, don yana xuwa ya rungumeta bacci yake xuwa mata, wani lkcn ma sae dae ya kwantar da ita kawae yyi ma momy sallama ya wuce, duk dare Abba ma na shigowa dubata hka Haisam, inna kam bata san ashe jarababbun yara na makale jikin inteesar ba, su kansu Hajiya basu sani ba. Yau ta cika sati biyu gun mamanta, momy na kula da ita ssae kuma tana tausayinta ganin yanda cikin ke bata wahala, karfe hudu na yamma Aliyu ya shigo gidan ranar yaci sa'a bbu kowa tsakar gida ya nufi sashinsu inteesar, xaune ya tarda ta da momy a falo ta sata gaba sae ta shanye kunun da ta dama mata don bata cin komai, ya gaida momy tayi kmr bata ji sa ba ta fice daga falon, ya dawo gefen inteesar ya shiga lallabata yana bata kunun har ta sha rabi, snn ya ajiye ya rungumota jikinsa yana buga mata baya kar tayi amai, tayi lamo tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace "fateema," ta dago tana kallonsa ya mayar da kanta kirjinsa yace "gida nake son tafiya dake fateema, nasan sae da amincewarki Abba xae yarda na daukeki, ki tausayamin plss my wife" . Inteesar ta kwace kanta daga rungumar da yyi mata tana masa mugun kallo tace "waye wife din taka? Sae yau da kaga ciki a jikina kasan ni wife dinka ce, to ni ba matarka bace wllh, bari ma kaji abinda baka sani ba ya Aliyu, wllh bana sonka bana sonka, tun ynxu nake son mu ajiye yarjejeniya da kai a kan cikin nn," yyi shiru yana kallonta xuciyarsa na tafarfasa, tunanin me yake hka har ya kai sa ga kiranta da wife dinsa, ya rike temper dinsa yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "yarjejeniyar me," tana masa wani irin kallo tace "na farko ina haifa abinda ke cikina xaka bani takardata, na biyu kuma ni baxan shayar da danka ba tun ynxu ka sani, idan ka yrda da deal din nn, to na yrda xan bar cikin nn, idan kuma akasin hka, to wllh wlh xan sake komawa a cire min cikin kuma baxa ku sake gani na ba," ya sauke ajiyar xuciya yana kallonta, ransa yyi mugun baci, amma da yake yaransa kawae yake so, sae yace "ok na yrda xan baki takardarki kuma baxa ki shayar da su ba," tace "ka rantse da mahaliccinka," yyi shiru yana kallonta snn yyi wani irin murmushi yace "na rantse," tace "kuma ni daga ynxu ka daina xuwa gurina na yafe maka," yace "ok ngdd," snn ya mike ya fice ba tare da yyi mata sallama ba ma, ta mike ta koma daki da kyar ta kwanta kan gado ta lumshe idonta dake cike da hawaye, yes hkn kadae ne mafita a gareta, Aliyu bae cancanci ta xauna da shi ba ko kadan, idan yana shisshige mata hka xata iya canxa ra'ayinta. Tun daga ranar Aliyu bae sake xuwa sashinsu ba duk da tasan yana xuwa gidan, yau kusan sati knn tayi forcin din kanta xuciyarta taji hkn da yyi yafi burgeta yafi mata ddi amma ta kasa, baccin kirki gagaranta yake duk da ynxu laulayin nata da sauki cikinta ma ya dan fara fitowa, in kaga yanda inna ke ji da ita da cikin sae ka rantse kace ba ita ke jinjina mata xubar da cikin da tayi kwanaki ba, tunda ta gane ciki na nn maimakon a ga inna ta bata rae ko makamancin hka sae aka ga ta buge da murna har da rawanta, kullum ita ke ma inteesar girki safe da yamma wae don yaran suyi karfi, su Hajiya ma ba karamin girgixa suka yi ba da kursum ta gaya masu ae ciki na nn kuma har ya fara fitowa, umma tace "tab, wllh ki san abun yi tun wuri Hajiya," Hajiya da abun duniya ya isheta tace "to umma ya xanyi ni wllh duk jikina ma ya mutu, taya xa'ayi Aliyu ya hada xuriya da marasu asali kuma mugaye, umma ta tabe baki tace "ki shigo anjima da daddare ina da shawara da xan baki," Hajiya taji ddi ssae tace "to umma naji ddi amma, xan shigo anjiman" Yau lahadi inteesar na xaune tsakar gida da inna da yamma wajajen karfe biyar suna ta hira tana cin gyada kursum na kwance kan tabarma a gefensu tana danna wayarta, ynxu kam bbu laulayi sae shegen kwadayi kmr xata ci bbu, sae nauyi da jikinta yyi mata don cikinta ya fito ssae watan shi na biyar knn, duk da tana tattare da damuwar da bata san dalilinsa ba sae kyau take karawa abunta kmr ba ita ba ga wani haske da ta kara a kan nata, cikin ya amsheta ssae yyi mata das das a jiki gwanin sha'awa, ta mike knn xata dauko ma inna tsintsiya ta tattare bawon gyadan da suka ci don kursum tace baxata tashi ba tunda bata ci gyada ba, suka ji an bude gate, gaba daya suka maida hankalinsu ga gate din, Aliyu ne ya shigo gidan safeena na biye da shi a baya, kallo daya tayi masa ta dauke kanta tayi gun inna rike da tsintsiyar a hannunta, ya kasa dauke idonsa daga kanta sae binta da kallo yake, ya sauke idonsa kan cikinta ya sauke ajiyar xuciya, muryar inna ne ya dawo dashi cikin tsawa tace "su waye wa innan xasu fado mana gida kmr tsofaffin arna ba sallama," safeena da ta kasa daina kallon Inteesar ita ma xuciyarta na harbawa ta maida kallonta gun inna tana mata wani shegen kallon rainin wayo, Aliyu ya harari inna yace "ke dae kin banu wllh, ae randa xaki mutu a gidan nn sae na xuba ruwa a kasa nasha," a fusace inna tace "karyanka yaro kuma sae ka riga ni mutuwa," inteesar ta juya da sauri tana kallon inna tace "kai inna," inna ta mike tana gyara daurin xani tana huci tace "ku fita ku ban waje, kar na walakanta ku ynxun nn," Aliyu yyi dariya yace "to mai gidan," safeena ta tabe baki tayi bangaren Hajiya inna ta sha gabanta tana huci tace "ina kike tunanin xaki mahaukaciya," inteesar ta mike da kyar tayi sashinsu Aliyu ya bi ta da kallo har ta bace masa, snn ya maida dubansa ga inna dake fada safeena na fada, bbu tonan sililin da inna bata yi mata ba, yace "ke safeena," ta juya ranta a bace tana kallon Aliyu tace "ka ja ma tsohuwar nn kunne ta fita harkata don ni nafi karfinta wllh," ya daka mata tsawa yace "tunda tace ki fita ba sae ki fita ba, sa'ar kakarki ce aka ce maki wnn" safeena ta shiga hawaye tana kallonsa, yyi tsaki ya karasa gun inna yace "kiyi hakuri inna, bata cika hankali bane yarinyar," inna tana wage baki tace "ae naga alama maxa ta fitar min daga gidan dana, sannu da xuwa Aliyu ina ta cigiyarka" yyi murmushi yace "ae gani innata," tana dariya ta ja sa suka yi sashinta, shi ko sae murmushi yake don yana da dalilin yin abinda yyi Safeena ta juya tana kukan takaici ta bar gidan, da sauri Hajiya da umma dake leke ta taga suna kallon duk abinda ke faruwa suka fito, Hajiya tabi bayanta tana kiranta cikin lallashi tace "kiyi Hkuri safeena ki kyaleni da shi, wancan kuma me ya kai ki musanyar yawu da ita baki san mayya bace," Safeena tace "ae kam naga alama Hajiya, amma ni dae wllh nafi karfinta" ta karashe maganan tana kuka, Hajiya ta ja suka yi sashinta umma na biye dasu a baya suna lallashinta, kursum ta tabe baki ta mike tace "lallai wnn jaka ce mara xuciya," fura inna ta shiga dama ma Aliyu yana kwance kan dogon kujera suna hira, yace "ae idan yarinyar nn ta haihu ke xaki je mata xaman jego," da sauri inna na wage baki tace "haba," yace "eh mana," tace "wayyo amma naji ddi wllh, Allah yyi maka albarka," ya dan tabe baki yace "Ameen, to ma taya xaki je xaman jegon tana nn," inna tace "yo ba sae ta koma ba," ya danyi murmushi yace "to kiyi mata magana, don tafi jin maganarki kan na kowa a gidan nn" inna tace "to bari na aika a kira min ita na gaya mata ynxun nn ma, yo ae wnn ba wani abu bne," dae dae nn khadija ta shigo, ta gaida yayanta snn tace "inna an aiko ni wajen ki," inna tace "waye," khadija tace "wae mamata tace naxo na amshi dari biyar din da kika ara hannunta kwanaki," inna ta bude baki tace "lah ku ji min mata, ki je kice mata taxo ta danne ni ta kwata, naga dae gun dana take samun kudin kajin min fitsararriyarkawae," khadija ta juya xata fita Aliyu ya kirata ya ciro dubu daya ya mika mata yace "gashi ki kai mata," inna tace "ae da ka
Chapter 11 · 0% Book details