Sashe 6
Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin bbu wanda ya iya cewa komai a falon don duk jikinsu yyi sanyi ya sa inteesar ta tsagaita kukan da take ta cigaba "snn Abba ni bada yardana ya sake aure ba, hasalima ni ban san xae yi aure ba sae ranar da ya kawo ni gunka da daddare kke tambayata ko nasani, to a nn ne ma nasan aure xae yi, kuma dama tun a hanya yyi threatn dina kan cewar ko me xaka tambayeni nace nasani, kuma Abba har yau yaki daukar batun karatuna da muhimmanci da nayi magana sae ya dinga hantarata wae baxan iya course din da nace nake so ba, kuma Abba da yake cewa na xubar masa da ciki a tambayesa ko kula dani da cikin yake, Abba sae nayi kwana uku ban gansa ba gashi bbu abinda nake iyawa kullum a wahale nake kwana nake yini a gidan ga kuma yunwa, tunda ba iya girkin nake ba," tayi shiru tana share hawayenta snn a hankali tace "lastly Abba kayi hakuri ba rashin kunya nake maka ba, amma ka tausaya min kayi masa magana ya sauwaka min, don baxan koma gidansa ba wllh na gama aurensa," Aliyu ya mike yana mata wani mugun kallo yana huci yace "munafuka, makaryaciya kawae, ki xo ki shake ni na baki takardar taki kuma wllh sae kinyi da kin sanin xubar min da ciki," ya juya xae bar falon Abba ya dakatar da shi a fusace, inteesar ta fashe da kuka tace "wllh Abba kace ya bani takardata bana auren kuma, bana sonsa," Abba yana kallon Aliyu yace "dawo ka xauna," ya kai minti kusan biyar a tsaye kmr baxae xauna ba, sae da Anty Nafeesa tace "ba magana ake maka ba ka tsaya ma mutane kallon rainin wayo," ya juya ya kalleta, snn ya koma inda yake ya xauna yana ma inteesar wani irin kallon, da ganinsa kasan ran maxa ya gama bacewa, Abba yace "cikin maganganun da Fateema tayi a nn akwae wanda xaka karyata," ya kauda kansa bae ce komai ba sae huci da yake, Abba yace "gud, dama tun ba yau ba nasan halinka, na kuma san xaka iya aikata duk abinda fateema ta lissafo a nn, kai kam ban san wani irin mutum bne Aliyu, kuma gwara da Fateema ta gaya min abubuwan da ta dde tana boyewa a cikinta tana cutar kanta," ya juya yana kallon Inteesar yace "amma fateema ke abinda kika aikata a ganin kinyi dai dai knn, me xaki ce ma mahaliccinki, ashe dama karamin tunani gare ki ban sani ba" inteesar dai kanta na kasa tana hawaye ta kasa cewa komai, Abba ya ci gaba, "a nan kin nuna kmr rashin kulawar da yake nuna maki ne yasa kika aikata abinda kika aikata, to Fateema baki san hanyar gida bne, ko in kin xo akwae wanda xae ce maki don me" a hankali tace "Abba banyi wnn tunanin ba," Abba ya girgixa kai yana kallon Aliyu yace "to malam rubuta mata takardarta, Allah ya hada kowa da rabonsa, ni nayi kuskure tun farko na baka auren fateema duk da ka nuna min baka sonta" Aliyu ya juya yana kallonta, ita ma kallonsa take, ya maida dubansa ga Abbansa yace "srry ba rashin kunya nake mka ba Abba, amma taxo ta shake ni ta kwata, ko kuma ta saki kanta da kanta," yana kai wa nn ya mike yana huci xae bar falon, Abba ya daka masa tsawa yace "don uwarka ni nayi maka magana ko fateema" Inna ta mike a fusace tace "yau naga tsiya, yarinya tace bata son aurenka ka sallameta mana ko ana yi dole ne, ae ba rasa manema tayi ba, ko gobe ta fita titi santalelen yaro me katuwar mota wanda ya fi ka komai ne xae biyo ta wllh, yo tsami gaye da kai idan ba tsautsayi ba ma me xae kai ta aurenka sai tsayi ba hankali kmr bishiya," abun dariya abun takaici, a walakance Aliyu na kallon inna yace "ae sae ki rubuta mata sakin ki bata, ko kuma ku hadu ku shake ni ku karba," yyi tsaki a fusace ya juya xae fita Abba yace "kar ka kuskura ka fita daga falon nn, kanka rawa yake Aliyu, ita mahaifiyar tawa kke gaya ma magana" inna ta fashe da kuka tace "yo sabon abu ne wnn, ae sae Allah ya mana hisabi da Aliyu" Haisam ya mike ya fice daga falon, hkn ma Momy, ran Abba a bace kuma a nutse yana kallon Aliyu yace "bani takardar Fateema ynxun nn Ali kar na nuna maka d odza side of me," cikin tsawa ya karasa maganar, Aliyu yyi shiru yana kallonsa yana huci, inna tace "ba magana ake maka ba salubabbe kawae," ya juya yana kallon inna tace "daina kallona Munafuki kawae," inteesar dae kanta na kasa, ya juya ya kalleta snn yyi huci me xafi ya ciro takardar da ke Aljihunsa da pen ya daura takardar kan hannun sofa, snn ya duka ya fara rubutu a jiki. Inteesar ta dago a sanyaye tana kallonsa hawaye na bin kuncinta, Abba ma kallonsa yake ko kiftawa baya yi, hka ma Anty Nafeesa, inna tayo waje da ido ta dafe kirji tace "lah rubutawa xae yi Bukar" . .. Inna ta fashe da kuka ta mike tsaye tana cewa "Bukar kayi shiru, kaga fa rubutawa yake, lah ha ila ha ilallahu mahammadur- rasulillahi sallallahu alaihi wassallama, Bukar kayi wani abu mana" Abba kam kasa cewa komai yyi sae kallon Aliyun yake, Anty Nafeesa ta jinginar da kanta jikin kujera tana kallon ikon Allah, har Aliyu ya gama rubutunsa ya mayar da pen din cikin aljihunsa yana kallon Abbansa yace "gashi nn na rubuta mata," Abba yyi murmushin takaici yace "to ka kyauta," ya dauke kansa ya shiga linke takardar neatly yana kallon inteesar dake kallonsa har lkcn tana hawaye, ya karasa gabanta yana mata mugun kallo ya jefa mata takarda snn ya juya xae fita inna ta bi sa da gudu ta cakumi kwalarsa tace "don uwarka jikartawa ka mayar baxawara, to Allah ya isa bamu yafe maka ba, sae Allah ya saka mana," Abba yace "ki rabu dashi baaba," inna tace "naki din, dama nasan har da hadin bakinka ae," ta fashe da wani matsanancin kuka ta xube wajen tana daddaga hannu sama, Aliyu yyi yar dariya rainin wayo ya juya ya fice daga falon, sae a snn umma dake xaune har lkcn bata ce komai ba ta mike ta bar falon xuciyarta fal murna don dama abinda take jiran gani knn, kuma ta gani, ynxu kuma xa taje tayi break din ma Hajiya gud News din, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana girgixa kansa, Anty Nafeesa ta mike ta nufi gaban inteesar ta dauki takardar da Aliyu ya jefa mata ta koma ta xauna tana warware wa, inteesar kam hade kanta tayi da gwiwa tana rera kuka a hankali, Anty Nafeesa ta gama karanta content din takardar ta ajiye kan kujera kusa da Abba ta mike ta fice daga falon, inna ta mike ta dago inteesar tace "tashi mu je, sae me don ya sake ki, abinda ynxun nn kina fita masu mota xa su biyoki, uban waye xae kalleki yace kin taba aure idan ba dan bakin ciki ba, ae gwanda da kika kwabar da cikin don da ganin jarababbun yara ne, mu je kawae Allah ya isar mana" sae a snn inteesar taji sanyi ta mike tsaye inna ta shiga share mata hawayenta, Abba kam idonsa na kan takardar da Nafeesa ta ajiye masa bayan ya dauka, yana gama karanta cntent din ya sauke ajiyar xuciya tare da jinginar da kansa jikin kujera yace "gashi nn fateema," inna ta ja hannunta xasu fita tace "rabu da shi da'alla muje me xaki yi da shi su da suka sa shi ya sake ki ae sae su cinye," Inteesar ta kasa bin inna ta koma a sanyaye ta karbi takardar a hannun Abba, Abba yace "kiyi hkuri Fateema ni na ja maki komai," ta kirkiro murmushi ta karbi takardar inna tayi tsaki ta ja ta suka fice daga falon tana cewa "yo idan bata yi hkurin ba ya ake son tayi dama bayan an gama cutarta," inteesar dae jikinta a mace suka isa falon inna, inna ta karbe takardar hannunta da ta kasa dubawa har lkcin, tayi michi michi da ido tana kallon rubutun ita nn karatu take kmr tasan me aka rubuta jikin takardar tayi tsaki ta cukuikuye takardar ta jefar bakin kofa tace "shege kawae rubutun ma kmr ta agwawa," ta juya tana kallon inteesar da ta xauna kan kujera ta kura ma TV ido tace "maxa je ki kiyi wanka ki xo ki kwanta, kar ki sa komai a ranki kinji" a sanyaye inteesar ta mike ta shiga dakin inna tayi kwanciyarta kan gado kawae don baxata iya yin wankan ba. . Washegari da safe inna na share falo ta ga takardar da ta jefar bakin kofa, tace "na share wn shegen takardar Inteesar," inteesar da har lkcn ke kwance a daki tayi shiru kmr baxata ce komai ba sae kuma tace "ki ajiye kawae kar ki share," inna na gama sharan ta hada mata ruwan wanka ta kai mata bayi duk tana kwance, inna tace "maxa ki tashi kije kiyi wanka kadda ruwan ya huce," ta mike xaune da kyar ta fara cire kayan jikinta xata shiga wankan inna tace "to me xan hada maki na kalaci kan ki fito," inteesar ta dan yatsine fuska tace "ni waina kawae xa a siyo min," inna tace "yo ae wnn ba wani abu bne bari na kira kursum kan su tafi makaranta su siyo maki," inteesar na shiryawa a dakin inna taji muryar momynta ta xo gaida inna, ta hanxarta ta gama abinda take ta fito da sauri don ta gaidata don ba xuwa sashinsu xata yi ta jibgeta ba, gefen inna ta xauna tace "ina kwana momy," ba tare da ta kalleta ba ta amsa da "lfya lau," inna tace "ya kina amsa mata kmr ana tilasta ki," momy ta dan yi murmushi ta mike tsaye tace "bari naje na gama kimtsa ihsaan inna," inna ta tabe baki bata ce komai ba momy ta fice, inna tace "wannan wannan da ba dan a gabana ta haife ki ba