← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

..Karfe tara na safiyar lahadi inteesar suka sauka kano daga lagos, Antynmu na rike da Hussaini ita tana rike da Hassan kmr yanda suke ce masu, Zainab na rike da wani yar jakan kayan abincin yaran don da ita aka taho aka bar yan biyu a india gun yan aiki, Abbanmu kuma na janye da trolley din kayan twins din, taxi suka dauka har kofar gida, Abbanmu ya ba shi kudinsa, snn inteesar ta shiga gaba Anty na biye da ita abaya Abbanmu ya tsaya daga waje shi da Zainab, hka kawae taji gabanta na faduwa, sae gidan yyi mata kmr tayi shekara bata ganshi ba, bbu kowa tsakar gida kuma dama sae da tayi wnn addu'ar a xuciyarta, direct bangaren inna ta nufa Anty na biye da ita a baya, har suka isa ta bude kofar a hankali, inna na xaune ita da kursum dake mata kitso tana ta bala'i Hajiya tayi tafiya ba tare da saninta ba sae jiya ta lura bata gidan, nn kitson xuwa gidan inteesar ake mata don jiya Abba ya dawo shima daga india ta sa shi gaba ko yaki ko ya so gobe xata tafi lgs gidan Aliyu, rasa me xae ce mata yyi, ita don tsabar masifa bata lura da yana cikin tashin hankali ba, a nutse ya fara mata magana yace "inna Aliyu fa bae da lfya......" da sauri tace"Allah ya basa lfya kuma ni ai gun inteesar nace xanje ba Aliyu ba," to kawae yace mata don takaici ya fice daga falon, inna aka shiga shirya kaya ba ji ba gani har da su kitso, Abba kam da sassafe ya bar gidan ranar da tace xata tafi lgs din, bayan ya gaya ma momy abinda ake ciki da kuma inteesar da basu gani ba don yaga boye mata bashi da wani amfani, momy batanuna masa komai ba, amma ba karamin kukan tashin hankali tayi ba bayan fitarsa, inna ta daga kai da sauri xata fara masifar waye ya bude mata kofa ba sallama, suka yi ido hudu da inteesar, inna ta yo waje da ido ta mike da sauri tana kallon yaron hannunta tace "me xan gani hka ni Rahmatu, har kin haihu ban je ba kuma ban sani ba," kawae sae ta fashe da kuka tace "Amma Allah ya isa tsakanina da yan gidan nn gaba daya, ynxu anyi min adalci knn" takaici ya ishi inteesar ga Anty a tsaye, gskya inna bata yi ba, shigowa tayi ta xauna Anty ta kasa shigowa sae kallon inna take, inna ta ciro waya tana huci tace "maxa nemo min layin Bukar," kursum da gaba daya hankalinta na kan yan biyu ita ma da mamaki ta karbi wayar takira mata Abba ta mika mata, cikin daga murya tace "amma Allah sae yyi mana hisabi da ku Bukar, ynxu yarinyar nn ashe har ta haihu ban sani ba, tun yaushe nake cewa a kai ni aka ki kaini," ta karashe maganar da matsanancin kuka ta jefar da wayar, Inteesar da haushi ya cika ta tace "Anty ki shigo mana," ganin har lkcin Anty na tsaye tana kallon inna, Anty tayi murmushi ta shigo falon ta xauna, wayar inna ya shiga ringin kursum ta mika mata tace Abba ne, a fusace tace "share mara mutunci kawae, uwar me xae gaya min, maxa kije ki kira min Zainabu don uwarta ita ma" inteesar kam kunya ne ya isheta kawae, da ta sani da gun momy kawae ta tafi, inteesar ta kwantar da yaron hannunta ta bude fridge ta ciro ruwa da lemotunda sun karya a lagos, ta ajiye ma Anty snn ta dauko kofi mata ajiye mata, Anty tace "da kin bar shi kawae inteesar, cikin yyimaki sauki ynxu ko," inna ta mike da sauri tace "cikinta ke ciwo," inteesar ta galla mata harara bata ce komai ba, kursum ta shigo rike da wayar momy tace "inna wae Abba xae maki magana," inna tace "da'alla ni a rabu dani me xae ce min," ta fixge wayar ta kara a kunne tace "me xaka ce min Bukar," wace inteesar din kasani, ae ni sae Allah ya saka min gata nn da yan biyunta sun xo da wata doguwar mata fara me dogon hanci, yo ina xan sani Bukar," ta katse wayar ta ajiye, tana kallon Kursum tace "baki ce ma Zainabu ina kiranta bne," kursum tace "tana xuwa," inteesar na kallon kursum tace"kursum Abba fa," inna tace "yace yana xuwa," inteesar ta daure fuska tace "tare da bako muke a waje inna," inna tace "toki shiga da shi falon Abban naku," inteesar ta mike ta fita ta yi kofar gida tace "Abbanmu ku shigo," har falon Abba ta kai sa, Zainab na biye da ita a baya, ta bude fridge ta ciro masa lemo da ruwa ta ajiye masa da kofi, yyi mata godiya snn ta kama hannun Zainab suka fita daga falon, a sanyaye momy ke tahowa daga bangarenta duk da kursum tace mata inteesar ceta xo sae ta kasa yrda bayan ga abinda Abba ya fada mata jiya, suna hada ido da momynta ta ruga a guje ta rungumeta cikin farin ciki, ji tayi kmr ta fi shekara rabonta da ita, momy kasa cewa komai tayi sae hawaye, hkn ya ba inteesar mamaki jikinta yyi sanyi tace "momy me ya faru," momy ta kasa cewa komai sae kallon Zainab da take, da kyar momy tace "wacece wancan," inteesar tace "parent dinta suka dawo dani gida momy suna da kirki ssae, momynta na falon inna, muje ki ganta" momy bata ce komai ba suka yi bangaren inna . Suna shiga falon inna, inna ta fara ma momy jaraba, "ynxu abinda kuka min kun kyauta knn Zainabu," Momy bata tanka inna ba ta shiga gaida Anty, Anty ta amsa da fara'arta, inna tace "magana nake maki Zainabu," Anty tace "mama bana tunanin sun san da Haihuwar inteesar fa," inna ta galla mata harara tace "ya xaki ce min hka, ke me kika sani," Anty tayi murmushi tace "to mu a india muka tsinci inteesar tana nakuda sati biyu da suka wuce, a hannuna inteesar ta haifa yaran nn, kuma bayan ta dawo hankalinta na tambayeta gun wa taxo a india, tace ita ma bata san wa ya kawota ba, satin ta kusan biyu a gidanmu muka maido da ita nan Nigeria da mai gidana," inna tayi tsaki tace "ni ban gane shirmamman hausan nn naki ba, uwar wa inteesar ta sani a india da xa ki ganta a can, da ma lagos kika ce min, wnn karya kike yi" sallamar Abba ne yasa inna yin shiru tace "ka xo kaji min karyar bnxa Bukar wae a india aka ga inteesar tana yawo," Abba ya shigo falon yana kallon inteesar da mamaki, ya xauna ba tare da ya shirya ba ya sauke wani ajiyar xuciya ya dafe kansa yace "Alhmdllhi," inna tace "ta me," kasa ba inna amsa yyi yana kallon Anty yace "baiwar Allah a ina kuka ga wnn yarinyar don Allah," Anty tace "a new delhi ni da mai gidana mun fito daga wani plaza," Abba yace "Allah ubangiji ya taimake ku kuma kmr ynda kuka taimakeni ya saka maku da alkhairi," inna tace "yau naga tsiya, wae me ke faruwa ne," Abba ya juya yana kallon inna yace "baaba yau kusan wata uku knn Fateema bata cikin hankalinta bamu gaya maki ba, mu ne har india daga lgs nemo lafiyarta satinmu uku a india aka nemeta aka rasa yau sati biyu da kwanaki knn da muke nemanta a india......" inna ta katse sa da sauri tace "kmr ya bata cikin hankalinta, hauka take ko me," Abba yace "kwarae kuwa baaba amma wa ya bamu karfin gwiwan xuwa mu gaya maki wnn mummunan lbrin mara ddin ji , baaba na shiga damuwar da ban taba shiga ba a rayuwata, ynxu hka Aliyu na can a asibitin shima ba hankalin tun bayan da muka nemi fateema muka rasa, su Nafeesa da Haisam ae duk suna can" tunda Abba ya fara magana inteesar ta tsaya da mamaki tana kallon Abba, wae ita ce tayi hauka, maganar Abba ta karshe yasa ta hawaye, inna ta mike jikinta na rawan bala'i tace "waye ya haukatar min da jikata a gaya min don bamu gaji hauka a xuri'armu ba," Abba ya sauke ajiyar xuciya bae ce komai ba, kuka ssae inteesar take, hka ma momy, Anty kam jikinta yyi sanyi, don bata san a haukace suka tsinci inteesar ba, kuma bata ga alamar hkn ba, inna ta dinga ihu da kuka a gidan wae a kaita gidansu safeena tasan baxae wuce aikin asiri ba su suka mata asiri, Abba ya mike bae bi ta kan inna ba ya fice a xuciyarsa yana hamdalar bayyanar inteesar da gaggawa hka, wae bayan komai ya lafa inna ta sani amma dubi reactions dinta yasan bae yi kuskuren rashin gaya mata da bae yi ba, yana fita Nafeesa ya fara kira ya sanar mata snn ya shiga falonsa ya tarar da Abbanmu xaune yana kallon news, yace "ashe bako gareni basu sanar da ni ba," ya bashi hannu suka gaisa snn ya shiga yi masa gdya kafin yyi masa bayanin abinda ya faru. Momy ta mike ta fita tayi bangarenta ganin irin haukan da inna take ba ji ba gani, Anty na bata hkuri, "ki kyaleni nayi yarinya, a haukatar min da jika bata yi masu komae ba, kuma nayi shiru, ae da wani abu ya sami inteesar a duniyar nn da kowa kashinsa ya bushe a gidan nn, shi kuma Aliyu ya karata da haukansa tun da shi ya siyar ma kansa dama na sha gaya masa shi mahaukaci ne," ta karashe maganar tana huci ta shige daki, inteesar dae sae kuka take duk hnklinta na gun Aliyu da Abba yace ke hauka sbda ita, Anty ta shiga hada ma Hassan dake kuka abinci, inteesar ta mike ta bi inna daki jikinta a sanyaye, katuwar tunkuyarta take kkrin fitowa da xata je daura ruwan wanka, inteesar na hawaye tace "inna don Allah kice ma Abba su barni na je gun ya Aliyu tunda......" inna ta dakatar da ita a fusace tace "kina danyan jegon xaki tafi gun wani mahaukaci can," inteesar ta fashe da kuka tace "ni ki daina ce masa mahaukaci, ki
Chapter 22 · 0% Book details