← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajen, sae kallonsu ake gwanin ban tausayi, faruuq ya dafa bango ya kai minti kusan biyar a hka da kyar ya haura sama ya shiga ward din da inteesar take, duk alluran da suka dinga yi ma Aliyu bae nutsu ba don hauka karara ya dinga gwada masu, duk aka fita aka kulle dakin aka barshi shi daya ya dinga buge buge yana jijjiga kofar abun dae ba ddin ji, likitocin suka hana faruuq shiga ya jingina jikin bango hawaye ya cika idonsa da kyar ya ciro wayarsa ya shiga neman layin Haisam, muryarsa na rawa yace "Haisam abu ya baci Haisam inteesarta fita daga asibitin, Aliyu baya cikin hankalinsa shima brain dinsa ta samu matsala, ka sanar da Abba baxan iya gaya masa ba" bae jira me Haisam xae ce ba ya katse wayar sae hawaye. Inteesar kamnata tafiya abunta sae dae idan taji kmr an mintsileta a mararta ta xauna ta huta snn ta ci gabada tafiya ko ina tabi sae an kalleta, hadari ya hadu garin ssae tana ta tafiya abunta kowa nata kkrin ganin ya isa gidansa, har daga karshe ruwa mai karfi ya sauka ta xauna kan wani dakali ruwan ya dinga dukanta amma bata damu ba, har ruwan ya tsagaita bayan kmr awa biyu, ta mike da kyar ta ci gaba da tafiya tana rawan sanyi, kasa ci gaba datafiyar tayi dae dae wai babban plaza ta dalilin wani mugun ciwo da taji mararta da kugunta nayi a tare da kyar ta ja kafa ta samu wani gefen mota ta durkushe gaban plazan tana rike da kugunta sae rawan sanyi take tana yarfe hannu alamar axaba, indiawa sae kallonta suke suna wuce ta, don su dama basu gaji taimko ba ko a tsakaninsu, kuka ta shiga yi ganin ta kasa daure ciwon Abbanta ta shiga kira tana juye juye jikin motar da take taji an bude motar ta koma baya da sauri, da ganinsu matada miji ne, matar na kallonta da yaran india tace "keme kike yi a nn," kai ta daga tana kallonsu bakaken fata ne kmr ita amma da gani xasu Haifeta, ta mike da kyar tana rike da kugunta xata bar wajen matar tace "amma ke yar Nigeria ce kuma bahaushiya ko,"ko kallon matar bata yi ba taku daya biyu ta xube wajen tana wayyo cikinta, matar ta juya tana kallon mijinta dake tsaye kmr wani tsoko yana kallonsu tace "Abbanmu kalli fa yar uwar mu ce ga kuma alamar bata da lfya mu taimaka mata," bata jira me xae ce ba ta karasa kusa da inteesar da sauri ta dago ta tana kallonta tace "sannu kinji yan mata daga ina kike hka," inteesar bata ce komai ba sae girgixa kai da take don axaba, matar ta dagota da sauri ta saka ta bayan mota ita ma ta shiga tace"mu je Abbanmu," ya shiga motar ya tada suka bar wajen, ihu ta dinga masu a mota duk ta rikice jin axaba na neman kasheta matar na rike da ita tana tofa mata addua, mijin ma duk ya rude yace "asibiti xamu ko," tace "A'a muje gida kawae xan karbi haihuwar," babban gida ne ssae, matar tace "ka taimaka min mu fito da ita Abbanmu," ya xagayo yana kallon inteesar da ta gama fita hayyacinta ciwo ya ci karfinta, tace "help me mana Abbanmu," ya koma baya da sauri har lkcn yana kallon inteesaryace "baxan iya ba, bari na kira maku yan aiki," yyi cikin gidan da sauri sae gashi ya fito da yan aiki suka taimaka mata ta shiga ciki da inteesar . .. Da taimakon matar Inteesar ta Haifo santala santalan yaranta maxa biyu, ba karamin wahala ta ci ba, matar ta tausaya mata ssae, babban likitace don hka tayi mata duk abinda ya kamata snn ta kaita bedroom dinta ta kwantar da ita kan ta hado mata tea har tayi baccin wahala, mai gidanta kuwa kasa xaune yyi har sae da inteesar ta haihu, snn hankalinsa ya kwanta, matar ta gyara yaran ta kaisu gefen uwarsu ta kwantar dasu gashi gaba dayansu basu da lfya, inteesar bata farka ba sae can tsakar dare matar na xaune gefenta rike da dayan yaron dake ta kuka ta kwantar dashi tana mata sannu, kai kawae inteesar ke gyada mata, ta kira yan aiki su kawo mata tea, suka kawo suka ajiye, matar tace maxa ki sha ki basu nono yunwa suke ji kuma duk basa jin ddi, inteesar bata ce komai ba matar ta taimaka mata tamike xaune snn ta mika mata tean ta shiga kurba a hankali, maigidanta ya shigo ya xauna yana kallon inteesar yace "sannu baiwar Allah ya jiki," ta dago kai tayi shiru tana kallonsa, wata yarinya ce da baxata wuce shekara goma sha biyu ba ta bude kofar ta shigo ta karaso kusa da inteesar da harshen hausa tace "Sannu Anty," inteesar tayi murmushi tace "na gode" yarinyar ta xauna tana kallon bbies din, ba karamin kama suke da inteesar ba iyayen sae kallonsu suke, daga karshe Abbanmu ya mike ya bar dakin, inteesar ta ajiye tean hannunta matar tace "har ya isheki," ta gyada mata kai tace "na koshi," matar tace "bari a kawo maki abinci ki ci kinji," inteesar bata ce komai ba matar ta mike ta fita, inteesar na kallon yarinyar tace "ya sunanki," yarinyar tace "sunana Zainab," inteesar tayi murmushi tace "nyc name, wa ya kawo ni gidan nn,"yarinyar tace "mum nd dad ne suka kawo ki daxu," inteesar tace "wani gari ne nn," yarinyar tace"india," inteesar tayi shiru bata ce komai ba gabantana faduwa ranta a dagule, india kuma, me ya kawota india . . Ba karamintashin hankali kowa ya shiga ba rashin ganin Inteesar har na kwana biyu, barin ma Abba don shi ba ma ta Aliyu yake ba, ta yar mutane yake, Hajiya dae ta dage kowa ta gani tace su safeena ne suka yima inteesar asiri ta haukace ita ma dae ta xama kmr mahaukaciyar, idan ta gaji da gantalin don bbu wanda ke kulata kowa abinda ke damunsa yafi karfinsa sae ta dawo ta xauna bakin kofar inda Aliyun yake tayi ta rusa ihu tana kuka har aka fara tunanin ko ita ma haukan xata yi ne, Aliyu kam ya xama abun tausayi ba shi da aikin yi sae na kiran fateema duk ya xama wani iri haukan nasa ma sae yafi nata shi dae a bashi fateemar shi, kullum sae an xubar masa da hawaye don tausayi, gashi kullum su Faruuq sae sun xaga india neman inteesar bayan sanarwar da suka bada gidan talabijin da sauransu, Bbu abinda yafi daga ma Abba hnkli irin ynda xae tunkari momy yace basu gainteesar ba ba a ma maganar inna da ta dage xata xaman jego, hka kowa ya xama kmr mara lfya a asibitin bbu me xama yaci kwakkwaran abinci, inteesar kam na xaune hankali kwance gidan bayin Allahn da suka tsinceta ita da yaranta, sae dae fa yaran duk basu da lfya kusan kullum allura ake masu barin hassan din, duk da rashin lafiyar tasu hkn bae hanasu ci ba kmr me, shegen ci ne dasu ssae basa koshi ko kadan ko da yaushe bakinsu motsi yake, suna mugun takura inteesar gashi ruwan nonon ma bae wani cika ba, hkn yasa matar tasa Abbanmu ya siyo masu madaran jarirae take dama masu ta basu, shknn inteesar ta samu kwanciyar hankali, ko kadan ba ita take rainonsu babarin ma ba iyawa tayi ba, matar ce take masu komai nata kadae ta basu nono, nonon ma ita ta koya mata yanda xata dinga basu, kuma suna sha tana ihu wae xafi take ji, ba karamin dariya take ba matar ba, matar tace "amma ke yar fari ce ko," ranarda suka cika kwana biyar ne Abbanmu da matarsa da suke cema Anty suka sa inteesar gaba suna tambayarta me ya kawota india, inteesar tayi shiru ta rasa me xata ce tunda ita ma ganinta kawae tayi a india, a hankali ta fara magana "wllh Anty nima bansani ba kawae na gan ni ne a nn bn san wa ya kawo ni ba," duk suka yi shiru suna kallonta da mamaki, Anty tace "a Nigeria wani state kike to" inteesar tace "kano," Anty tace "to mai gidanki fa?" tace "shima a can yake," duk suka yi shiru suna kallonta, Anty tace "kin tabbata gskya kike fada mana inteesar," inteesar kmr xata yi kuka tace"Allah gskya nake gaya maku Anty," matar tace "to shknn bari ki kara kwari sae mu kai ki gida," inteesar dae bata ce komai ba, Abbanmu ya dauki Hussaini yana kallonsa yace "wnn kmr Husainin muko Antynmu," Anty tace "wllh kuwa baka ganin ita ma inteesar kmr su kusan daya da Zainab, Allah mai iko," duk suka yi dariya Abbanmu yace "baki da nmbr kowa can gida ne kada hankalinsu ya tashi dayawa, koma dae kuna da yan uwa a nn india ne?" inteesar tace "nima ban sani ba," Antynmu tace "ka bari Abbanmu nn da sati daya ae xamu je Nigerian,"Abbanmu yace "to shknn Allah ya kai mu," snn ya mike ya fita, Anty ta shiga hada masu madara don sun fara mutsu mutsun yunwa, kmr ba jarirae ba yaran, Antynmu tace "yaran nn dae da yunwa kike barinsu suna cikin ki, yara da ci hka tubarkallah," inteesar tayi murmushi bata ce komai ba ta tsura ma yaran ido, farare ne ssae kmr ita amma bbu abinda suka bari na Aliyu, idonsu, bakinsu hancinsukomai nasu na Aliyu ne, yaran kmr yaran larabawa ga lips dinsu pink gwanin sha'awa, tayi murmushi ta kauda kanta, ko wani farin ciki xae yi idan yaga ya'yansa masu kama dashi, Antyn mu ta dauki dayata shiga bashi feeder ita ma ta dauki dayan ta daukinasa ta fara basa don ta fara koyan yanda ake yi gun Anty, Anty na da kirki ssae tunda ta haihu a bedroom dinta take, kayan da suka dinga siya ma jariran sae ka rantse kace sun taba saninta, komai nasu enuf a gidan suma autansu yan biyu ne masu shekara takwas, kusan duk yamma sae Zainab ta shigo da frnds dinta daban daban wae su xo su ga Antyn ta mai kama da ita. Inteesar taji kmr tayi ta xama a gidan don tana jin ddin xama da
Chapter 20 · 0% Book details