← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yabo bbu fallasa yace "ae dae don Allah nace," cikin tsawa tace "ka fice min a falo tun banje na hadaka da ubanka ba, da can ni na raba ku da xan hada ku ynxu, lallai ka cika fitsararre mara tunani" ya mike yana murmushi ya fice daga falon, tayi tsaki ta shige bedroom dinta ranta a bace. Sashin inna ya koma, inna na xaune da inteesar tana shafa mata bayanta wae xuciyarta na tashi, daga bakin kofar yana kallon inteesar yace "in har kika koma gidana to baki cika yar halak, kiyi ta xama gidanku, cikin ma in kinga baxa ki iya ba kya iya xuwa ki xubar da shi ynxu," ya ja dogon tsaki ya sake labulen ya juya yyi gaba, inna da ta kasa rufe baki ta mike da sauri ta bi shi tace "ka dawo ka bata takardarka don uwarka, idan ba kaddara ba me xae kaita auren mahaukaci," ya juya yana kallon inna yace "sae dae in ku ne ke hauka," yyi gaba abunsa. Inteesar da komai nata ya tsaya ta kasa cewa komai sae hawayen da take, inna ta shigo tace lah meye abun kuka, ki rabu da dan iska wllh na kashe aurenku ynxun nn, ya ya kuma ki haifesu ki bani na kai masa ya basu nono, inteesar dae bata ce komai ba amma duk jikinta yyi sanyi, ta bar inna na ta surutunta har kusan karfe goma snn tayi mata sae da safe tayi bangarensu jikinta a mace, momy bata yi bacci ba tana xaune falo, ta shiga daki ta kwanta ta lumshe idonta duk da tasan ba bacci xata yi ba, momy ce ta kirata ta fito falon ta xauna tana kallonta, momy tace "kina ji na fateema," ba hka nn momy ke kiran sunanta ba don hka ta nutsu tana sauraran me momy xata ce mata, momy tace "duk me xan ce maki a nn kar kiyi min musu, yhu obey b4 complain kinji" kai kawae inteesar ta gyada mata. Momy tace "ki shirya ki koma dakin ki gobe da safe," inteesar ta tsaya kallonta da mamaki, nn da nn hawaye ya cika idonta, xata yi magana momy tace "ban son naji abinda xaki ce, ba don bana sonki nace ki koma dakin ki ba fateema, sau biyu Alhaji yana min magana nake shashantarwa don har cikin raina ban son aurenki da yaron nn, but ynxu ina da dalilin cewa ki koma dakin ki, kiyi hkuri kinji inteesar Allah xae shige mana gaba, kuma ga matan gidan nn sae yada ki a waje suke wae ae ya sakeki, hkn ne ma yasa Alhaji yyi min magana nace maki ki koma dakin ki, idan lkcn haihuwarki yyi sae ki dawo gida ki haihu, ki kwantar da hnkalinki inteesar lkcn da ni da kaina xan bukaci Alhaji yyi masa magana ya baki takardarki na nn xuwa don ko bayan raina ni ban yrda kici gaba da xama da Aliyu a matsayin mijinki ba, " inteesar tayi shiru ta kasa cewa komai jikinta yyi sanyi jin furucin momy na karshe, ta tabbatar da ta gaya ma momy irin cin mutuncin da yyi mata daxu da baxata fara cewa ta koma gidansa ba, sae ta samu kanta da kasa gaya ma momy abinda yyi mata, ta mike a sanyaye tayi ma momy sae da safe ta shiga bedroom ta kwanta, duk da ta so tayi kuka ko xata ji sanyi amma sae ta nemi kukan ta rasa. Washegari da safe karfe takwas ta gama shirinta ta dauki dan hanbag dinta tunda ba wani kaya xata dauka ba, momy ta bata dubu daya kudin mota, momy tace "kije kiyi ma inna sallama," tace mata "to" snn ta fita Momy tayi mata Allah ya kiyaye, sae ta samu kanta da rashin son xuwa gun inna don kar ta hanata tafiya, kasa xuwa yi mata sallaman tayi ta fita daga gidan kawae ta taka har babban titi snn ta tsayar da tricycle ta gaya masa inda xata ta shiga, suna isa ta fito ta mika masa kudinsa ya bata canjinta snn ta yi hanyar gate ta danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga gidan, a sanyaye ta karasa balcony ta murda kofar falon taji shi a rufe, ta kai minti kusan goma a tsaye snn ta rumtse idonta ta danna bell, safeena ce ta sauko bude kofar kyanwar da a cewarta ta dauko daga gidansu don tana mugun son mage na biye da ita a bayanta, shi dae Aliyu ya rasa yanda xae yi da ita da magen ne amma har ga Allah baya son mage, ta juyawa taga magen a bayanta sae wani tsalle yake ta sa kafa ta hauresa ya koma sama da gudu, Aliyu yyi tsaki ya maida dubansa ga TV, duk da ofcourse tasan ko waye a bakin kofar sae ta shiga cewa "kai bala sae ynxu ka ga daman xuwa kai da nace maka tun karfe takwas, ynxu da bbu kwata kwata ya kke son nayi gashi baya cin komai sae potatoe da safe" a fusace take maganar kmr gske, inteesar ta dan koma baya ta bude kofar, safeena tayi turus a bakin kofar tana kallon cikin inteesar tana dan murmushi, kallo daya inteesar tayi mata ta dauke kanta, wasu shegun kayan bacci ne jikinta sae mayafin da ta yafa kuma a hka take shirin fitowa gun driver don rashin sanin ciwon kai, shi kuma da yake bae damu da ita ba bae hanata ba, gefenta inteesar tabi xata wuce ta bangajeta ta tare hanyan tace "ina kike tunanin xaki hka," Aliyu dake kwance kan kujera yana kallonsu don shima yyi mamakin ganin inteesar yace "ki kyaleta kila kayanta ta xo kwasa," inteesar ta kasa cewa komai don takaici, hawaye ya cika idonta amma bata bari safeena ta gani ba, safeena tace "ayyo," snn ta matsa daga bakin kofar, da kyar inteesar ta shiga gidan tayi hanyar stairs xuciyarta na raya mata ta kwashi kayanta kawae kmr yanda yace ta koma, safeena ta bita da kallo tana murmushi mugunta don sarae tasan da xuwanta, da sauri Aliyu ya mike yana kallon safeena yace "kin goge ruwan sama ne," safeena ta dan yatsine fuska tace "to ni na xubar," yayo waje da ido yyi hanyar stairs da sauri har yana bugewa yana kwala ma inteesar kira ta tsaya. Gano abinda yake gudu Safeena tayi ta bisa da sauri gabanta na faduwa don mugunta a xuciyarta tace kai abu biyu xae hade mata knn da sauri kan ya haura sama tace "kai wasa nake na goge," ya juya yana kallonta amma hankalinsa bae kwanta ba, xae yi magana yaji inteesar ta fasa wani raxanannen ihu a sama, ya haura sama da sauri yana cewa "innalillahi wa inna ilai hi raji'un," safeena ta doka uban tsalle ta shiga kiran uwarta hannunta na rawa, uwar ta daga tace "wayyo momy mutumin nn ya iya aiki ta xo wllh," da sauri Hajiyar tace "to magen fa ta ganshi," safeena tace "ba dole ba ae mutumin ca yyi yana jin kamshinta xae fito yana jiranta da na xo bude mata kofa kar ki ga yanda ya biyo ni da gudu, wato yaji kamshinta, na sa kafa na hauresa ya koma sama ya jirata a can, ae ko da gudu ya koma momy har wani rawa jikinsa fa yake, kuma kinsan me momy abu biyu ya hade mata Aliyu ya xubar da ruwa sama yana jira in goge naki gogewa kinga tana hawa sama tsantsin ruwan xae kwasheta sae kuma ga aljanar magen ma na jiranta, ae ciki kam kema kinsan sae lbri momy" ji tayi Aliyu na kwala mata kira a rude, safeena tace "xamuyi waya anjima momy gashi can yana kirana," ta katse kiran xuciyarta fal murna ta haura sama cikin muryan tashin hankali da tsoro take cewa "me ya faru Honey ruwan bae gogu bane, . Aliyu na rungume da inteesar dake ta kuka tana shisshigewa jikinsa safeena ta hauro sama, cikin tsawa yace "me kika ce min," da sauri ta sauka kasa ganin yanayinsa, ya dago inteesar yana girgixa kai cikin tashin hankali yace "ta ina kika fadi fateema," kin bude idonta tayi amma jikinta sae rawa yake, duk a xatonsa xafin ciwo ne yasa take haka, duk ya rikice mata ta gaya masa ta yanda ta fadi da kyar ta dago kanta tana kallonsa muryarta na rawa tace "ni ban fadi ba, wata mage ce...." sae ta kasa karasa ta fashe da wani matsanancin kuka ta fada kanshi jikinta na rawa, yyi shiru yana yana kallonta, dagata sama yyi ya bude dakinsa ya shigar da ita ya kwantar snn yace "magen ne ya tsorata ki?" kai kawae ta gyada masa ya juya xae fita ta rikosa da sauri tace "kar ka tafi ka barni yaya," ya durkusa gabanta yana goge mata hawayen fuskarta yace "baxan tafi in barki ba," ya mike ya fice daga dakin, dakin safeena ya shiga, ya tarda ita tsaye tana waya, da sauri ta katse wayan tana kallonsa a tsorace, bae ko kalleta ba yyi gun magen dake labe gefen madubinta, ya finciko ta, safeena ta yo waje da ido a tsorace tace "me xaka yi Aliyu, me tayi maka" bae ko kalleta ba ya buga magen da bango tayi wani shegen kara kmr ba mage ba ya sake bugata da karfi, snn ya bude window ya cillata downstairs ya juya yana nuna safeena da yatsa yace "daga yau kika sake shigo min da ko wani irin dabba gidan nn daga ke har dabban sae na wurga ku downstairs," har ya fita ya dawo da sauri ya shaketa yana huci yace "kika ce min kin goge ruwan," xata yi magana ya xuba mata tagwayen mari snn ya jefar da ita yace "kuma Allah ya baki sa'a kar ki goge," ya juya ya fice daga dakin ya koma dakinsa, tana kwance ta dukunkune waje daya ta kasa daina tuna magen, ya karasa kusa da ita ya dago ta yana kallonta . Aliyu ya rungumeta a hankali yace "baxa ki sake ganin magen ba kin ji" kai kawae ta gyada masa yace "daga ina kike ynxu," ta turasa da karfi tuno abinda ya gama faruwa daxu yyi dariya yace "to kiyi hkuri abinda nayi maki jiya, i was jet
Chapter 13 · 0% Book details