← Book details Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 28

Sashe 18

Inteesar Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana ihu ta shiga cewa "baxa ku bude min ba," da sauri likitoci suka shigo dakin, suka kwacesa daga hannunta, snn aka mata allura aka xaunar da ita, nn da nn ta nutsu, likitan yace "i warned yhu 2 be careful y did yhu come so close, i told yhu she's under medicatn," Aliyu bae ce komai ba ya juya ya fice daga dakin ransa a dagule, suka fito suma suka rufe kofar, faruuq ya dafa Aliyu yace "kayi hkuri ka daina xuwa inda take har sae ta fara samun lfya," Aliyu bae ce komai ba suka xauna. Da daddare Anty nafeesa tasauka lgs, faruuq ta kira ya xo har airport ya dauketa xuwa asibitin duk hankalinta a tashe yake, kawae son ganin inteesar take, amma likitoci suka hana sae ta fashe masu da kuka, hkn yasa aka bar ta ta tsaya daga bakin kofa kawae, kuka ssae ta dinga yi ganin wae da gske inteesar ce ke hauka wnn wace irin jaraba ce, kasa komawa kano tayi tayi xamanta nn lgs a asibitin, Abba ma yaxo ya dubata ya koma ransa a dagule, ranar da suka cika kwana hudu a asibitin Aliyu yace "ni fa faruuq am tired ni banga wani improvement ba sae allura suke yi ma yarinya duk bayan mintoci, kuma tana nn yanda take," faruuq yace "to lkci daya dama aka ce maka ake magani Aliyu, ni kuma naga improvement tunda har tana iya xaunawa na awa daya bata yi buge buge ba," Aliyu ya xauna ya dafe kansa yace "wllh na gaji faruuq, ban san me ya sami fateema," kullumshi ke kai mata abinci ya ajiye mata a gaba ya dan xauna nesa da ita, sae don kanta yaga ta matso kusa da abincin snn shimaxae matso ya dauki cokali ya dinga bata a hankali cikin ikon Allah kuma tana karba, idan ya bata sae shima ya ci nn kadae ne yake samun cin abinci idan yaga tana ci don baya iya ci, ko cibi uku baxa su ci ba xata kwabar da shi tayi kaca kaca da shia gun, shi knn kuma cin abincin ranan, wani lkcn sae yaji da ma shi Allah ya daura ma haukan, satinsu daya a lgs Aliyu yace ma faruuq "look ni kawae ku barni na fita da matata waje na gaji da shirmen da ake yi a nn," faruuq yace "haba Aliyu meyasa kke da gajen hakuri ne, wae hka muka kawo inteesar asibitin nn," Aliyu yace "no faruuq ni sbda cikin jikinta ne yasa nace hka, saura fa wata daya da yan kwanaki ta haifesu, a cikin wnn halin? no plss help me persuade my father mu fita daita india," a raunane ya karasa maganar faruuq yyi shiru ya rasa me xae ce masa. Ko da suka yi ma Abba maganar fita da inteesar waje Abba ca yyi a'a idan na asibiti bae yi ba a dawo da ita gida kawae ayi na Hausa, duk wnn abinda ake inna bata san me ke faruwa ba har lkcn, ita dae kullum maganarta a gidan a kai ta gidan inteesar ae ta kusa Haihuwa, sae dae Abba yace mata kar ta damu xa'a kaita, duk momy ta xama wata iri a gidanciwon inteesar ya tsaya mata a rai ta so tace ma Abba a dawo da ita gida kawae a nema mata magani kuma a dage da yi mata addua amma bata son su ga kmr bata gode abinda ake mata bne, ita kam taga alamar ba ciwon asibiti bne amma bata ce komai ba, kullum jiya e yau ciwon inteesar idan kaga ta nutsu to Allura aka dirka mata, sam ita kawae so take ta tafi dae ko ina xata oho, Aliyu duk ya rame kmr yanda bata cin abinci shima hka baya ci, ya kan xauna kusa da ita duk damben da xa'suyi yyi ta tofa mata addu'a ko dago kanta baxata yi ba har ya gama ya fita, su kansu likitocin suna tausayinta sbda halin da take ciki, duk bayan kwanabiyu Abba kan xo ya dubata, kuma idan xae xo ya kan damu momy su xo tare amma sae taki xuwa, faruuq ma yakan koma kano yyi kwana biyu ya dawo, ko Zainab bata san me yake xuwa yi a lgs ba ya dae ce mata aiki yake kaisa, har ta gaji da rokansa ya barta taje gidan inteesar don ca yyi mata sae ta haihuwa xata je, safeena na sane da abinda ke faruwa farin cikinta da na uwarta baya mitsaltuwa ta mayar da gidan Aliyu nata sae yanda tayi da shi ta shigo da wancan ta shigo da wancan, tana da tabbacin inteesar ta kusa shiga duniya kmr yanda aka yi assure din ita da uwarta, shknn Aliyu xae xama nata ita kadae na har abada sae yanda tayi dashi, ta kan kirasa lkci lkci idan yaga dama yana daga wayar sae dae su gaisa tace "wae har ynxu baxa ku dawo daga honey moon din naku ba ko bata haihu bne Aliyu," ya kan katse wayarsa ne don bae taba sanin wae safeena tasan abinda ke faruwa ba. Ranar da suka cika sati uku a asibiti Aliyu yasa abbansa gaba yana hawaye kan cewar yyi hakuri ya bari ya fita da inteesar, Abba yyi shiru shima hankalinsa a tashe yace "to ae Ali wae da mukoma da ita gida a fara yi mata na hausa," da sauri yace "A'a Abba duk bata lkci ne wnn kayi hkuri don Allah mu fita india suna da kwararrun likitoci" Abba yyi shiru ya rasa me xae ce, can dae yace "to shknn Ali, Allah yasa hkn shine mafi Alkhairi kuma yasa a dace a can," da kyar yace "Ameen Abba," ranar aka fara shirye shiryen fita da ita xuwa new delhi, Abba na nn lgs har suka tashi bayan kwana uku tare da Anty Nafeesa, faruuq da Haisam, snn shima ya koma kano. Shi tsoron sanar da inna yake amma dabae ci ace duk wnn abinda ke faruwa inna bata saniba, to innan ce sae a hankali, da ya sanar da momy sun fita india bata ce komai ba sae hawaye, Hajiya ta gaji da rashin ganin Aliyu sati da satittikae ta kama hanyar gidansa da kanta, ba kowa gidan sae mai gadi ya sanar da ita ae matar gidan ba lfya suna asibiti, tace "wacce ciki," yace "me juna biyu ae sun fi wata daya basa gidan nn kmr dae mai hauka ka ta koma, Hajiya ta dafe kirji tace "kai haba inteesar kke nufi," ganin baxata samu information ssae gun sa ba yasa ta kama hanyar gidansu safeena don yace mata daxu ta tafi gida wae, jikintahar rawa yake taje taji gulma, shknn abunsu ya koma masu yau, murna fa cikinta ta shiga gidansu safeena, suna xaune ita da uwarta a falo kmr kawaye sae shewa suke, hajiya ta shigo falon . .Hajiya ta karaso cikinsu ta xauna tana washe baki tace "kuna sha'aninku wllh ina ma nima xainab dina xata yrda mu dinga yin hka tare mu kashe mu rufe, kuna bani sha'awa wllh" safeena tayi dariya hka ma uwarta snn uwar tace "ae ke kika bari aka kwace maki ita tun farko kika kasa yin komai," Hajiya tace "to ya na iya Hajiya salame," safeena tace "daga ina kike hka Hajiya?" Hajiya tace "daga gidanku can nake wllh, naga kwana biyu Aliyu bae xo gida ba nace to ko sun kara basa ya cine don a dauke hankalinsa kaina tunda suka yi ma ubansa ma bare shi, sae kuma naga ba kowa a gidan wae me ke faruwa nesafeena ina suka je?" safeena tayi dariyar keta tace "kina ina Hajiya, ai suna can lgs ta haukace yau kusan wata daya knn canake ma kin sani," Hajiya ta daura hannu a ka ta bude baki alamar mamaki tace "wayyoo Allah mae saka ma bawansa da gaggawa, kice min abun su ya koma kansu, da cikin ta haukace ni Aisha" Safeena tayi dariya tace "kwarrae kuwa," Hajiya ta daga hannu sama cikin murna tace "Alhmdllhi, Alhamdllhi, shiyasa naga uwarta ta koma abun tausayi a gida ashe ashe kaikaiyi ne ya koma kan mashekiya," suka kwashe da dariya Hajiya tace "amma fa ina ga kmr inna bata sani ba ba'a sanar da ita ba, don naga jarabanta sae wanda ta manta, ae kuwa tsaf xanje in daga mata hankali da kaina xan fada mata yau yau din nn" da sauri uwar safeena tace "ke Hajiya Aisha don me xakiyi hka, ae magani xata nema mata ta warke," Hajiya ta hade rae tace "ita likita ce da xata nema matamagani ba kunce suna asibiti a lgs ba," Hajiya safeena tace "to bari kiji Aisha mu ne nn muka haukatar da ita don danki ya koma gunki, don an tabbatar mana da cewa asiri uwarta tayi ma Aliyu ya manne ma yar ta baya jin maganar kowa sae na yar karamar yarinyar nn, ko baki lura bne? Kuma wnn ciki ancemana ba na Allah da annabi bne, ba cikinsa bne so wae suke su ci gadon Aliyu " Hajiya da jikinta yyi sanyi lkci daya ta bude baki tana kallonsa tace "ku kuka Haukatar da ita knn," daga safeenar Har Uwarta suka hada baki "kwarrae kuwa, hkn kadae shine mafita," Hajiya ta danyi murmushi tace "ikon Allah,ina ma nima xan xama kamar ku wllh kuna burgeni, to amma ya xa'ayi dana ya dawo guna, tunda dae ynxu suna can tare kar ma ta shafa masa haukan, shi yasa Aliyu ya daina daga kirana ashe" Hajiyar safeena tayi murmushi tace "kar ki damu Hajiya Aliyu xae dawo gare ki amma fa ba hka nn ba don asirinsu na nn jikinsa," hankalin Hajiya a tashe tace "to ya xa'ayi ya karye," Hajiyar safeena tace "ynxu xuwa xakiyi ki lallaba maigidanki, kawae marairaicewa xaki yi kice ynxu Alhaji ashe abinda ya samu yarinyar nn knn kke boye mani, da fa na kowa ne, kuma dan adam baya wuce kaddararsa, xaki gajikinsa yyi sanyi hka xaki ta jan ra'ayinsa kmr ta kirki nn da nn xaki ga ya baki hkuri, to daga nn sae kice don Allah kina son yabarki kije ki dubota nasan xae bar ki, to kina xuwa can akwae wani magani da xan baki cikin abin sha xaki
Chapter 18 · 0% Book details